Showing 18001 words to 21000 words out of 216282 words

Chapter 7 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

ta zauna sanyin a.c na rantsa ta amma rashin sabo da tsoro ya hana ta kwanciya. Wayar ta da take gefe ta gani ta d'auka tana duba number da ya kira d'azu ta danna number sai taga tayi kama da number da aka tab'a kiran ta ga kiran nan ma yana nan da adadin lokacin da aka d'auka ana wayar hakan ya tabbatar mata itace, ajjiye wayar tayi tace, "Kenan daman shine ya kira ni?."

K'arar bud'e k'ofa ya saka ta kalli wanda ya shigo ta ganshi ya canja kaya zuwa k'ananu riga da wando marasa nauyi hannun sa rik'e da ledar abinci ya ajjiye mata a gefen ta ba tare da yayi magana ba ya juya zai fita tace, "Baka ji ba." Cak ya tsaya kafin ya juyo ya kalle ta ya d'aga gira alamun yana jinta tace, "Zan iya kiran Ummana yanzu?." Kai ya girgiza alamun a'a da hannu yayi mata alamun ta bari sai da safe daga haka ya fita baice komai ba.

Tsaki taja tace, "Aikin banza shi a lallai ga d'an sarki, koma me kayi min dai Allah sai ya saka min" ta fad'a tana jawo ledar ta bud'e tayi karo da lafiyayyar shinkafa da kaza sai khamshi take zubawa ga ruwa da lemo a ciki ba shiri ta baje a kan gadon taci ta k'oshi tasha ruwa. Ta d'an jima a zaune kafin ta kwashe kayan ta zame ta kwanta cikin lokaci kad'an bacci ya d'auke ta.

A b'angaren Asad yana zaune a falon yana cin nasa abincin hankali kwance babu tunanin an zuba masa wani abun a ciki ya gama ya d'auko kwalin sabuwar wayar da ya siya da sim card d'in k'asar ya kunna ya d'ora email d'in sa nan take komai nasa ya dawo kan wayar ya saka card d'in kana ya saka a chaji ya tashi domin bacci yake ji ya gaji, kallon d'akin da take yayi yaga haske har lokacin sai ya nufi d'akin k'irjin sa yana bugaw, yana bud'ewa ya ganta a kwance tana bacci ta cure waje d'aya da alama sanyi take ji.

Murmushi yayi kad'an wani abu yana motsawa a ransa wanda bai san meye shi baya k'arasa inda take ya rufa mata bargon ya kashe hasken d'akin sannan ya fita daga d'akin ya shiga nasa d'akin ya kwanta zuciyar sa cike da tunani kala-kala bacci ya d'auke shi.

Kiran asuba da ya karad'e d'akin da yake kwance ya farkar da Asad ya tashi yana yamutsa fuska dan rabon da yayi bacci mai tsaho irin sa babu farkawa har ya manta duk da ba wani mai tsahon bane amma a wajan sa mai tsaho ne, alwala yayi ya fito ya kalli d'akin da take yaga still babu haske ya k'arasa a nutse ya tura k'ofar d'akin sanyi ya dake shi yayi baya kad'an dan shi ba mutum ne mai son sanyi sosai ba, sake kutsa kai d'akin yayi har lokacin bacci take hankali kwance cikin bargo mai laushin gaske ta b'oye dukka jikin ta fuskar ta kawai ake gani.

A hankali yake takawa a nutse har ya isa kusa da ita fuskar ta yake kallo cikin shaukin sonta da kuma k'aunar ta da yake ji tana shiga cikin jikin sa a hankali kamar a lokacin ya fara sonta haka yake ji, kamar zai kai hannun sa kan fuskar ta sai kuma ya fasa ya janye tsaya ya nutsu sosai kamar na shi ba sannan ya fara bubbuga gadon a hankali. Bud'e ido yaga tayi suka had'a ido sai da yaga bacci ya sake ta baice komai ba ya fice ita kuma ta bishi da kallo kafin ta kalli agogon bangon d'akin sai kuma taji kira alamun za'a tayar da sallah.

Zaune ta mik'e tana goge idanun ta ta jawo kujerar ta zauna a kai zuwa band'aki tayi alwala ta fito ta tayar da sallah. Bayan ta idar d'auko wayar ta ta shiga application na karatun alkur'ani ta fara karantawa a zuciya amma bakin ta na motsawa. Bata jima sosai tana yi ba ta fara azkhar kamar koda yaushe har ta kai k'arshe ta ajjiye ta fara lazumi a zuciyar ta.

Motsin sa taji a bayan ta ya k'araso inda take ya kalli a.c d'akin har lokacin tana aiki ga kuma sanyin d'akin yace, "bakya jin sanyi?." Kallon sa tayi kamar baza tayi magana ba sai ta tuna nasihar Umma tace, "Ina kwana."
"Ya jiki?" Abinda yace kawai kenan ya ajjiye ledar hannun sa tace, "Da sauk'i."
Baice komai ba itama haka ya fita ta bishi da kallon mamaki tana jin zuciyar ta na karyewa hawaye suka fara zu??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????bo mata bata hana kanta ba ta dinga kuka har ta koma ta kwanta tana kuka bata kuma duba ledar ba.

Shima ya jima sosai yana karatun da ya saba yayi azkhar har k'arfe bakwai na safe yana zaune ya tashi ya shiga d'aki ya kwanta. K'arfe tara ya farka yayi wanka ya saka doguwar riga irin ta larabawa ya fito zuwa falon a lokacin ake danna door bell ya bud'e k'ofar ya karb'i abinci daga restaurant d'in hotel d'in ya mayar da k'ofar ya kulle. A kan table ya ajjiye abincin ya k'arasa inda ya jona ruwan zafi ya d'auko butar ya k'araso ya zauna ya had'a tea yana sha a nutse ya bud'e wanda aka kawo yaga kayan maiko ne kwai, dankali, planten, sai sandwich.

Sandwich d'in ya d'auka guda d'aya yana ci bayan ya gama ya rufe sauran ya mik'e k'afa akan table d'in ya d'auki remote yana canja channel d'in TV. Ajjiyewa yayi ya d'auki wayar sa ya kira number Hydar dan yasan yana can yana neman sa, bai d'auka ba bai kuma kira ba sai ya kira layin mai martaba.

D'auka akayi hakan ya saka shi ya nutsu ya sauke k'afar sa k'asa a nutse yace, "Assslamu alaikum." Daga can b'angaren Mai martaba yace, "Wa'alaika salam, Zaki ya kwanan Misra?." Murmushi yayi kana yace, "Alhamdulillah, Barka da safiya Takawa."
"Barkan ka Asad, ya kuka tashi?."
"Alhamdulillah."
"Ka kira gidan su ka had'a su da ita dai ko?." Asad yayi shiru alamun baiyi ba Mai martaba jin yayi shiru sai yace, "Hakan bai kamata ba ai Asad duk inda suke yanzu hankalin su yana kanta suna so suji ya take, ka kira ka had'a su suyi magana."

"In sha Allah" ya furta a hankali kafin Asad yace, "Abba Mamaaaa ta dawo?." Mai martaba yayi murmushi yace, "Bata dawo ba Asad, koda ta dawo kar ka damu komai zai zo da sauk'i kaji." Kai ya d'aga kamar yana gaban sa kafin yace, "Kayi gaggawar kaita asibitin ayi mata aikin nan, ka duba ina tunanin yau ne date d'in aikin da akayi booking za'a mata, ka duba dai Hydar yayi booking a Saudi German." Nan ma kai ya d'aga kamar yana ganin sa kafin yace, "In sha Allah za'a yi abinda akace." Daga nan sallama suka yi ya yanke wayar daidai nan kiran Hydar ya shigo ya d'auka.

"Our groom, how was your first night? I hope you enjoy it" Hydar ya fad'a cikin tsokana. Tab'e baki Asad yayi ya murmusa kad'an Hydar yana bashi nishad'i ba kad'an b kana yace, "First night? With who?."
"Your wife mana."
"U are not serious Hydar."? Dariya Hydar yayi kad'an yace, "Oga Deaf as mijin aure, wallahi ganin abun nake kamar wasa fa."

Bai bashi amsa ba yasan kuma daman bazai ce ba hakan ya saka ya kuma cewa, "U know what deaf? Kar ka bari kayi asarar wannan time d'in da kuka samu tare kayi k'okarin nuna mata kana sonta da gaske in ka lura zaka ga kamar gani take tilasta mata akayi ta aure ka, so Is better ka nuna mata kana sonta sosai sonta ya saka ka auro ta ba wani abun ba, ka gane ai abinda nake nufi ina nufin dai ayi komai."

Baice komai ba Hydar yace, "Yeah kayi k'ok'ari before Mama ta gano komai ta dawo da kai gida." Gaban sa ya fad'i matuk'a ya sauke numfashi yace, "lemme call her, excuse me" ya fad'a yana niyar kashe wayar yaji Hydar yace, "Amma dai bada number nan zaka kira ta ba ko?." Asad yayi shiru bai magana ba Hydar ya kuma cewa, "Naga number Egypt kasan kuma bata san baka nan ba so gwara ka kira ta da layin ka in ba haka ba zata gane baka nan, daman jiya mun had'u dasu Mum sun ga wucewar ka."

"Ohhh god! Hydar I lost my phone" ya fad'a yana dafe kansa. Hydar yace, "nayu mamaki dana ga number outside country dan nasan baka canja number kai da taka kake using a ko wacce k'asa, to yanzu ya za'ayi kenan gashi babu damar yin swap online dole sai kazo Nigeria, ga Mama indai ka kira ta da wannan number zatayi saurin d'agowa baka nan kuma kasan baka fad'a mata ba."

Asad ya kasa cewa komai duk tsoro ya cika masa zuciya sam baya son abinda Mama zatayi fushi dashi gashi bazai iya jurewa har ya koma bai mata waya ba, beside bai san lokacin da zai koma Nigeria ba tunda ko aikin ma ba'a yi mata ba, laifi goma da shirin kenan ga laifin ya tawo babu izinin ta, ga laifin auren da yayi bata so, ga laifi rashin kiran ta waya sabida rashin layin sa bazai iya ba sam. Hydar ya katse masa tunani yace, "Ya za'ayi kenan Deaf?." Asad ya sauke numfashi kana yace, "bazan iya d'aukar wannan lokacin without nayi magana da Mama ba Hydar, I can't" ya fad'a a raunane kamar zaiyi kuka.

Hydar yace, "Yaushe za'a yi mata aikin da akayi booking? Ina jin yau ne in akayi mata aikin kaga zata jima a kwance sai ka siyi ticket kazo kayi swapping ka koma a gani na hakan zai fi." Asad baice komai ba ya yanke kiran dan bai san me zaice masa ba.

Shiru yayi yana kallon wani wajan daban dan Allah ya sani bazai iya jure har gobe ko jibi ba sannan yayi magana da Mama bazai iya jurewa ba sam. Motsin k'ofa yaji hakan ya saka ya juyo ya kalli inda yaji motsin ya ganta zaune a kan kujerar ta sanye da doguwar riga ta saka hula tayi kyau sosai kwana d'aya tal fuskar ta ta washe har annuri yake fitarwa, Kasa d'auke ido yayi daga kallon ta tana tawowa a kan keken wayar ta a cinyar da alama bata kula dashi bama.

Idon ta takai inda yake suka had'a ido sai gabanta ya fad'i ta d'auke ido gashi tazo kusa dashi ya bita da kallo ji yake kamar ya jawo ta jikin sa gabad'aya ko zai samu sassaucin abinda yake a ji a zuciyar sa, kallon sa take shima yana kallon ta kafin ya fara janye idanun sa daga kanta ya mayar kan TV. Itama bata ce komai tayi shiru bata motsa ba taji maganar sa yace, "your breakfast." Bata motsa ba taji kuma me yace shi kuma yasan taji shiyasa ya share ta.

Wayar sa ya d'auka ya kira number Baba aka d'auka suka gaisa ya mik'a mata wayar alamun ta karb'a, karb'a tayi ta saka a kunne jin muryar mahaifinta sai ta saki fara'a suka gaisa ta saka aka kaiwa Umma suka gaisa farin ciki ya cika zuciyar ta sun jima suna magana da Umma har ta fara kuka kafin ta kashe wayar bata bashi ba ta rik'e a hannun ta tana kuka sosai.

Yana ji bai motsa ba yana kallon ta yana jin kukan nata wani iri a jikin sa ya lumshe ido ya bud'e a nutse ya kalle ta yaga ta d'ago tana goge idanun ta tana jan numfashi alamun kukan ya tsaya, wayar ta mik'a masa ya karb'a tace, "Na gode." Baice komai ba ya kalle ta suka had'a ido sai ya nuna mata abinci alamun taci ba musu ta zuba tea d'in tana sha a hankali.

Mik'ewa tsaye yayi ya kalle ta kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya fita, ganin ya fita ya saka bud'e bowl d'in dankali ta fara ci da sauri tana ci dan yunwa take ji kawaici kawai take yi bata so taci a gaban sa shiyasa yana barin wajan ta fara ci da sauri-sauri, had'a ido sukayi dashi ya dawo sai tayi sak ta kasa cinye abinda ta zuba a bakin ta sai kallon sa da take yi sai taga yayi murmushi mai sauti kad'an ya d'auki wayar sa ya fita ya barta.

Kunya taji kamar ta nutse dankalin da bata iya ci ba taji ya fita a kanta ta shanye tea d'in duk yunwar sai taji ta k'oshi ta ajjiye cup d'in tana raba idanu. Ba jimawa ya dawo ya kalle ta yace, "Wear your veil." Gani yayi tana k'okarin komawa d'akin ya dakatar da ita ya shiga da kansa yaga mayafin rigar a kan gadon ya d'auko ya bata ta yafa suka fita daga d'akin.

Inda aka tanada dan ajjiye mota a hotel d'in suka k'arasa wajan farar mota babba mai tudu da kyau ya danna remote d'in motar sai ya kalle ta ya bud'e gaban motar ya rik'e ta ta shiga motar ya nad'e keken ya saka a bayan motar ya shiga yaja suka fita daga hotel d'in, kallon sa take a zuciyar ta tana mamakin inda ya samo wannan motar a k'asar da ba tashi ba.

*Nigeria.*

"Finally Asad ya tafi ya bamu waje lokacin da zamu gabatar da abinda muke so yayi yanzu" Fulani Hajiya ta fad'a tana kallon Waziri da yake tsaye a kusa da ita. Murmushi yayi kana yace, "Anyi mai wahalar kam, abinda ya rage a gaba yanzu shine....." kafin yayi magana yaji ance, "Duk yadda za'ayi kar a barshi ya dawo Nigeria nan kusa, kar kuma Mama tasan cewa baya nan in ba haka ba komai ya dawo baya" Aliyu ya fad'a yana shigowa yana binsu da kallo one by one.

Dukkan su bin sa sukayi da kallo cikin tsantsar mamaki da tsoron ya akayi yasan inda suke har yazo ya kuma riski abinda suke cewa, ganin suna kallon sa da alamun mamaki sai ya murmusa yace, "Kar ku damu da ya akayi nasan kuna nan, ku san sani abu guda d'aya duk motsin ku a kan idona kuke yin sa a kuma cikin kunne na yake so kar ku yi mamakin ganina ba tare da kun sanar dani ba."
Hajiya zatayi magana Waziri ya katse ta da fad'in, "Yanzu ya kake ganin za'ayi kenan?."

Aliyu ya kalle su yace, "Ku san yadda zakuyi ku cire masa Mama daga zuciyar sa." Hajiya ta kalle shi tace, "Ban gane ba."
"Bana son sake maimaita magana kema kin san da hakan. Indai har zai yi magana da Mama tabbas hankalin sa zai dawo Nigeria, indai zaiyi magana da Mama nan kusa Asad zai dawo zai kuma iya rabuwa da matar tasa, dole a cire masa Mama a ransa ya daina neman ta a waya ta haka shine zamu samu cikar burin mu."

Cikin gamsuwa yake girgiza kai Waziri yace, "Very good idea our king, but ta yaya hakan zata kasance duba da irin son da yake yi mata?." Aliyu ya kalle shi yace, "Kuyi yadda kuka saba a raba shi da koda magana da Mama in ba haka ba aikin mu ya dawo sabo fil." Hajiya tace, "Wannan ba matsala bane, inda matsalar take aiki baya saurin kama Asad da sauri sai kaga ana ta abu d'aya babu nasara, bamu tab'a yin aiki munyi nasara a kansa ba ko sau d'aya."

Aliyu ya kalle ta yayi murmushi mai sauti yace, "Wannan karon zaiyi tasiri ku gwada, ina tabbatar miki da zaiyi nasara" yana fad'a ya fita da baya yana kallon su suna kallon sa. Waziri ya kalle ta itama ta kalle shi tace, "kana ganin abinda yace za'ayi?."
"Shi za'ayi mana ai maganar sa itace akan daidai."
"Anya ba kan keken b'era yake d'ora mu?."
"Wannan ba keken b'era bane gaskiya ce kuma abinda yace shi za'ayi."
"Ta yaya zamu yi aiki ya kama Asad bayan ba tun yau muka fara ba?."

Kallon ta yayi ya kalli k'ofa yace, "A wannan karon zamuyi nasara na fad'a miki, zamu cire k'aunar babar sa daga zuciyar sa zamu mayar masa da hankalin sa kan matar sa, daga wannan lokacin komai zaizo mana yadda muke so. Tabbas indai zaiyi magana da Rabi zai dawo Nigeria magana da itama tasiri ne a wajan sa ya zama dole mu dakatar da faruwar hakan" ya k'arasa fad'a da murmushi yana kallon ta itama sai tayi murmushin tana girgiza kai cikin gamsuwa da abinda yace.

*Tofa*>?-?=??
[17/12, 10:39 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*033.*

*SAUDI GERMAN HOSPITAL CAIRO.*

Tun a farkon asibitin zaka tabbatar da girman sa da kyau da tsarin da yake dashi, iya tsayawa ka kalle shi ma abin burgewa ne balle kuma ka shiga cikin sa kana gani kasan ba'a k'asar ka kake ba tabbas kaje bak'unta wata k'asar Misra.
Rauda tunda ya ajjiye motar take bin asibitin da kallo ya kalle ta yaga hankalin ta nakan asibitin sai ya d'auke kansa daga kanta ya kashe motar ya bud'e ya fita ya zaga inda take ya bud'e baya ya ciro keken da take kai ya kawo shi kusa da k'ofar da take zaune ya bud'e sai a lokacin ta kalle shi.

Hannu ya mik'a mata alamun ta kawo nata tabi farin hannun nasa da kallo mai d'auke da azurfa guda d'aya kalar golden sai wani d'an abin hannu mai kama da jarbi bak'i a zagaye a tsintsiyar hannun sa na dama, hannun nasa ma kawai abin kallo ne, murza yatsun sa yayi suka bata sauti sai ta kalle shi ya motsa duka yatsun hannun nasa alamun ta tawo. A hankali ta d'ora hannun ta kan nasa tana kallo nan taga banbanci tsakanin fatar ta da tasa domin kuwa kamar an d'auko bak'in gawayi ne an d'ora shi a kan farar fulawa.

'In banda ikon Allah ina ni ina shi? Ji hannuna fa kamar na bokaye akan nasa hannun.' Ta fad'a a zuciyar ta a lokacin da ya fito da ita ta zauna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login