Showing 9001 words to 12000 words out of 216282 words

Chapter 4 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

kizo ki karya" ta fad'a tana fita daga d'akin ta bar Rauda cikin zurfin tunani.

*&&*

A babbar fadar Katagum bayan sallar juma'a aka d'aura auren Asad da Rauda a kan sadaki naira dubu d'ari lakadan ba ajalan ba, babu mutane sosai daga mai martaba da Liman sai Wambai da abokan sa sai kuma Baba da k'annen Baba harda y'an uwan Umman Rauda sai kuma Hydar. Asad bai san me yake faruwa ba tunda yayi sallah ya fita daga gidan dan gabad'aya baya jin dad'in zaman gidan ko kad'an bai tsaya ba balle yasan abinda yake faruwa.

A wannan lokacin suka samu labarin rasuwar Sarkin Kano mahaifin Mama, Asad yana zaune a guest house ya kashe wayar sa gudun kar a dame shi bai ma san me yake faruwa ba. Tv da take a kunne ana haska labarai itace ta sanar dashi rasuwar kakan nasa ba shiri ya taso ya dawo gida ya tarar dasu Hydar suna niyar tafiya dole shima ya shiga cikin su akayi tafiyar dashi.

Da yake tafiyar mota ce basu isa ba sai bayan la'asar lokacin ana ta k'okarin tafiya kai shi makwancin sa an so a jira zuwa safiya sabida wanda basu iso ba amma ya'yan sa sunce suna so ya shiga a juma'ar kodan albarkar ta dole aka hanzarta komai aka tafi kai shi. Jana'izar ta had'a manyan mutane da mayan sarakuna da y'an siyasa kowa ka gani yana wane wannan, wannan yana na fika wannan ma yana nima na fika.


Basu samu ganin Mama ba sai bayan sallar i'sha suka shiga cikin gidan aka nemo musu ita idanu sunja sabida kuka. Mai martaba sarkin Katagum ya mata gaisuwa y'ay'an ta ma suka yi mata gaisuwar rashin mahaifin ta da addu'a kafin Mai martaba yace, "ina babu damuwa a turo sauran muyi musu gaisuwa." Kai kawai Mama ta d'aga kafin ta tashi ta fita jim kad'an sai gata da y'an uwan ta mata suka gaisa sukayi musu gaisuwa kafin su tafi masaukin su.

A Bristol hotel suka suka mai martaba yana zaune a personal room d'insa shi kad'ai su Asad da sauran makarraban sa kowa yana wajan da zai kwanta. Abinci aka kawo kamar ba'a so sabida yawa sa aka bawa kowa yaci ya k'oshi banda mai martaba dan su ba abincin kowa suke ci ba musmaman ma in yasan an san da zuwan sa kamar abincin dan shi akayi.

A b'angaren Baba lokacin da ya bar wajan d'aurin auren bai koma gida har yaji labarin rasuwar yasan bai da k'afar zuwa da babu abinda zai hana shi zuwa yiwa sirikar sa gaisuwa ba to yana gudun abinda zai je yazo. Lokacin da ya koma gida suna zaune gabad'ayan su har y'ay'an da suke gidan mijin su sunzo ya shigo da sallama yana cewa, "yawon ku yayi yawa fa yaushe kuka zo harda zaku kuma dawowa yau?." Dariya sukayi dukkan su kafin su gaishe shi ya amsa kana yace, "nama ji dad'i dana ganku gabad'ayan ku." Umma ya mik'awa ledar hannun sa ta karb'a yace, "kud'in hannun ki kud'i ne na kayan lefe, da kud'in na gani ina so na y'ar ki Rauda."

Gaban Umma ya fad'i ta kalli kud'in da tarin yawa ta kalle shi ta kalli Rauda da tayi sak tana kallon sa tace, "Malam ban gane ba." Baba yace, "Zaki gane yanzu ai" ya fad'a yana sake d'auko kud'i a aljihun sa ya mik'awa Rauda ganin tana kallon sa ya saka yace, "karb'i mana." Ba musu ta karb'a hannun ta na rawa yace, "Sadakin ki kenan jama'a sun shaida d'aurin auren ki da Asad ga goro da alewa" ya Fad'a yana fito dasu daga aljihun sa.

Dammmmm k'irjin su ya buga ta kalli Baba da sauri ta kalli kud'in ta kalli Umma da take kallon sa itama ta kalli y'an uwan ta kafin tace, "Aure kuma Baba!?." Baba yace, "Eh aure Rauda. D'azun nan aka d'aura auren ku a fada ba'a masallaci akayi ba shiyasa baizo kunnen ki ba." Rauda tayi sak ta kasa furta komai sai Umma ce tace, "Malam wai da gaske ko wasa?."
"Na tab'a yi muku irin wannan wasan ne?." Inna tace, "Yau dai ka fara Malam." Ya kalle ta yace, "ba wasa nake ba da gaske nake, da waliyan ta duka akayi d'aurin auren har da yayyen ki ma suma sun shaida" ya fad'a yana kallon Umma.

Ganin sun kasa magana ya saka ya kalle su yace, "kud'in hannun ki kuyi mata siyayyar kaya dan tafiyar su Misra baza ta wuce wannan satin ba, ayi siyayya yadda ya kamata duk abinda zata buk'ata a siya ragowar kud'in kuma suna hannuna za'a yi wani abun dasu. Ke Rauda bani na hannun ki" ya fad'a yana mik'a mata hannu jikin ta duk ya saki ta mik'a masa ya saka a aljihu yana murmushi yace, "to ai kin gani, ana so a bawa yarinya sadakin auren ta a hannun ta shiyasa na baki, yanzu kuma za'ayi wata hidimar dasu."

Yaya Ummi tace, "Baba dan Allah da gaske yanzu Rauda ta zama matar Asad halak malak?."
"Mtswww! Wai makaryaci kuka mayar dani ne ko me?."
"A'a Baba abin ne muka ji shi kamar a mafarki."
"To kuji shi kamar gaske domin Rauda matar Asad ce a yanzu, wacce take ganin k'arya nake ta kira kawun ta ta tambaya" yana fad'ar hakan ya tashi ya fita yana tsaki.

Dukkan su sun kasa motsin kirki kowa yayi shiru an rasa mai magana kafin wayar Umma ta fara k'ara, Ummulkhairi ce ta mik'o mata tana fad'in, "Baba Malam ne." Umma ta karba ta d'auka ta saka ta amsakuwa daga can b'angaren yace, "yanzu abinda kika yi mana kin kyauta? Ace yau za'a d'aura auren Rauda bamu sani ba sai a lokacin za'a sanar damu?, yanzu da mahaifin nata bai neme mu ba ke ko a jikin ki ko?. Ai kin kyauta." Jin wannan kalami na Yayan Umma sai Rauda ta tashi ta shiga d'aki tana kuka domin ta tabbatar da abinda ake fad'a gaskiya ne ba k'arya ba ita a yanzu matar aure ce.

Kuka sosai take yi bata san yadda sukayi da Kawun ba sai ganin shigowar su tayi dukkan su suna tsaye a kanta hakan ya sake karya mata zuciya ta sake fashewa da kuka.

"To meye na kukan kuma bayan aikin gama ya gama? Kiyi fatan Allah yasa alkhairi ne kawai ba kuka ba" Umma ta fad'a tana kallon ta. Yaya Ummi tace, "Dole fa tayi kuka Umma, shi wanda aka bata wata magana mai k'arfi wacce zata nuna da gaske yana son ta bata tab'a shiga tsakanin su ba kawai kuma sai a bashi ita dan kawai yana da kud'i da mulki?." Yayar mu tace, "to yanzu wa kike fad'awa haka? Kaf dai nan kin san babu wanda ya bada auren Rauda sai Baba shi ya kamata ki samu da wannan zancen." Tace, "Tsakani da Allah fa ba'a kyauta mata ba wallahi, an tauye ta auren dole za'a kira wannan ba auren soyayya ba."

Yaya Shamsiyya tace, "Yanzu duka wannan ya wuce ai rarrashin ta ya kamata kiyi ba wannan maganar ba." Yaya Ummi zata kuma magana suka ji muryar Baba yana fad'in, "Duk wacce ta d'auki k'afa tace zata je fada da niyar sanar da mai margaba abinda ya faru Allah ya isa ban yafe mata ba, duk wacce ta zuga Rauda akan k'in karb'ar auren nan itama Allah ya isa ban yafe ba" yana fad'ar hakan ya juya ya fita Rauda ta sake rushewa da kuka.

Raguwa akayi a d'akin aka barta da yayyen ta mata suka dinga rarrashin ta dak'yar aka samu tayi shiru tana goge idanun ta Yaya Ummi tace, "ko kefa, kina addu'a fa kina neman zab'in Allah ki saka a ranki wannan shine zab'in Allah gashi ya zab'a miki lokacin da baki kawo hakan ba daman haka ikon sa yake. Ki kwantar da hankalin ki ki kuma nutsu kita maimaita Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un zaki ji zuciyar ki tayi sanyi."

Rauda tace, "Yaya ya zanyi? Baba ya zab'i kaini inda za'a kashe ni sabida kud'i kawai da mulki baya ta lafiya ta da rayuwata ta abinda zai samu kawai yake yi. Dame za'a kira auren nan? Auren cushe ko auren dole?."
"Duka babu d'aya tunda shi ya fara ganin ki yace yana so babu zancen auren cushe a nan, kwantar da hankalin ki zakiyi ki kuma saka a ranki zab'in Allah kenan." Haka suka dinga rarrashin ta sai da ta dawo nutsuwar ta sannan suka k'yale ta amma kowa zuciyar sa babu dad'i.

Da daddare gidan ya rage sai su kawai matan auren sun tafi a falon da yake na Umma Baba ya kira Umma da Rauda da har lokacin bata dawo daidai ba yace, "ke in zaki nutsu ki karb'i k'addarar gaban ki ki nutsu, aure an riga an d'aura shi na kuma fad'a miki koda wasa naji wata magana ban yafe ba." Hawaye ya sakko mata ta goge yace, "Kar kiga shiru babu mijin naki kakan su ya rasu suna can Kano gidan gaisuwa, da ya dawo nasan zai zo ku tattauna." Kai kawai ta d'aga tana goge idanun ta bata ce komai ba dan zuciyar ta a raunane take.

Baba yace, "Ku fara siyayyar da wuri dan tafiya yi miki aikin nan da wasu kwanaki ne masu zuwa gwara ku tanadi komai kafin lokacin azo ana an manta wani abun." Nan ma bata amsa ba ya kalle ta yaga tana goge idanun ta sai ya sassauta murya yace, "Ita k'addara in Allah yayi nufin faruwar ta akan abinda baka zata ba Allah yake k'addaro maka ita, duk kuma abinda kake addu'a a kai kana neman yayi maka zab'in Alkhairi kaga ya zab'a maka koda baka so ka rungume shi domin shine alkhairin daka rok'a. Ki saka a ranki auren sa shine alkhairin kuma shine mijin da Allah ya rubuta zaki aura tun kina ciki, sannan kuma kiyi biyayya ga zab'in sa wannan koke-koken babu abinda zaiyi miki sai ciwo da zai saka miki aure dai an riga an d'aura shi." Kai ta d'agawa nan ma bata ce komai ba.

Baba yace, "Tashi kije ki kwanta." Ba musu ta d'auki abinda yake taiamaka mata wajan tafiya ta tafi d'aki Baba ya kalli Umma yace, "Banji kince komai ba."
Umma ta kalle shi ta tab'e baki tace, "me zance to? Me kake so nace?, hukunci ne ka yanke ka bawa y'arka wanda bata so, ka bawa y'arka wanda yafi k'arfin ta, ka kaita inda ake neman rayuwar ta, ka kaita inda za'a wulak'anta ta me zance maka kuma?." Ta fad'a a fusace tana kallon Baba da alama ranta a b'ace yake sosai.

Ya lura da hakan a yanayin maganar ta yasan ranta a b'ace yake sai ya murmusa yace, "dad'in ta da kike maganar taki y'ata kike cewa tunda kuwa kin yarda y'ata ce ina da ikon yanke duk hukuncin dana so a kanta."
"Eh shiyasa kud'i suka rufe maka ido ai ka siyar da ita, dan wannan siyarwa ne ba aurarwa ba. Ka manta abinda ya faru akan maganar auren idanun ka ya rufe kawai kud'in kake gani; har gida aka zo kashe ta sabida auren amma ka manta sabida an cika maka aljihun ka da kud'i. Ka siyo mata wulak'anci da kud'in ka duk abinda ya faru da ita nan gaba wallahi kaine sila, kuma sai Allah ya saka mata domin y'ay'a ma suna da hakki akan iyayen su" tana gama fad'ar hakan ta tashi ta bashi waje bai damu ba dan daman yasan za'ayi hakan shidai tunda burin sa ya cika kowa ma yayi ta fad'an ya gaji ya daina.

A can Kano Asad bai san me yake faruwa ba har gari ya waye suka koma gidan rasuwar suka bar Mai martaba a hotel, a can suka zauna da rana tayi suka dawo masaukin su. Kira Asad ya samu daga mai martaba ya isa inda yake ya same shida Hydar a zaune Hydar yana matsa masa k'afar sa.

Waje ya samu nesa dashi ya zauna kafin ya kalle shi yayi murmushi yace, "ba yau zaku koma ba ko?." Asad yace, "Eh Abba." Ya kyad'a kai yace, "Zamu koma yanzu shiyasa kafin mu tafi na kira na sanar dakai abinda ya faru a jiya wanda baka sani ba." Asad ya kalli mahaifin nasa baice komai ba mai martaba yace, "Aliyu ko nace Asad na lura da tarin soyayyar da kake yiwa yarinyar da ka furta kana so, tsoron halin mahaifiyar ka da biyayyar da kake mata ya saka kake tauye kanka a karo na babu adadi. A wannan karon nace bazan bari ka rasa abinda kake so ba kamar baya kuma na sanar da kai zan tsaya maka a ko ina wajan ganin ka samu abinda kake so koda ita bata so, jiya nida kaina na jagoranci d'aurin auren ka da yarinyar a fada ba tare da sanin ka ba, a yanzu haka matar kace kaima kuma mijin tane!."
[17/12, 10:39 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*030.*

? ?? Da sauri ya d'ago yana kallon fuskar mahaifin sa sai kuma ya saukar da idanun sa k'asa ya sake kallon sa yaga da murmushi a akan fuskar mahaifin nasa ya sake mayar da kansa kasa cikin sakannin da basu wuce uku ba fuskar sa washe sai kuma ta koma yadda take babu alamun walwala a tare da ita, wani abu yake ji yana shiga jikin sa zuciyar sa ta dinga bugawa da sauri ya kasa furta ko wacce kalma balle ya tabbatar da abinda aka fad'a masa gaskiya ne duk? da yasan mahaifin sa bazai tab'a yi masa k'arya ko wasa da irin wannan kalami ba.


Ganin yayi shiru ya kasa furta komai sai Mai martaba ya sake cewa, "Asad baka ji me nace bane?." Asad ya d'ago raunannun idanun sa ya kalle shi yace, "Takawa ba mafarki nake ba?."
"Ba mafarki kake abinda kaji nace gaskiya ne. Kai mijin Rauda ne ita kuma matar kace."

Numfashi ya sauke ya kalli Hydar sai kuma ya had'd'iye saliva kana yace, "Amma Takawa....." dakatar dashi yayi ta hanyar fad'in, "Kana sonta ba?." Asad yayi shiru na wani lokaci kana ya d'aga kansa alamun eh sai kuma yace, "Mamaaaaa!" Ya furta a hankali a sanyaye cikin rauni. Mai martaba ya murmusa yace, "Kana sonta ita kuma Maman ka bata sonta shiyasa zaka hak'ura sabida ita haka ne ko?." Asad ya d'aga kansa alamun eh mai martaba ya kuma cewa, "wannan shine karo na babu adadi da kake son abu bata so kake hak'ura sabida ita, a wannan lokacin baza ka hak'ura ba zaka mallaki abinda kake so koda ita bata so d'in shiyasa na yanke hukunci ba tare da ka sani ba ko ita ta sani."

Asad yayi shiru bai iya cewa komai ba mai martaba yace, "Ka kwantar da hankalin ka a wannan karon bazata raba ka da abinda kake so ba Asad ina bayan ka, in kun dawo gida zaku tattara kuje can inda za'a samar mata da lafiyar k'afar kuje kai da ita kuyi zaman ku har sai sanda na nemi ku dawo sai ka dawo." Kai ya d'aga bai iya cewa komai ba domin gabad'aya zuciyar sa a damalmale take baya jin farin ciki haka zalika baya jin bak'in ciki.

Mai martaba yace, "ya naga baka murna ko baka sonta ne?, Hydar naga ya had'e fuska" ya fad'a yana kallon Hydar cikin zolayar Asad d'in. Murmushi Hydar yayi yace, "Takawa ai a zuciya yake farin cikin ni na sani." Murmushi yayi yana kallon Asad da har lokacin kansa yake a k'asa bai d'ago ba. Mik'ewa mai martaba yayi suka mik'e suma yana kallon Asad yace, "Tunda baza ka nuna min kana farin ciki da abinda nayi maka ba ai shikenan ni zan tafi." Sai a lokacin yayi murmushi shi kansa ya kasa gane halin da yake ciki a wannan lokacin shiyasa ya kasa dariya ya kuma kasa kuka.

Tare suka fito suka raka mai martaba ya shiga mota sannan suka dawo masaukin su.? D'akin da Asad ya sauka ya shiga ya tarar da Aliyu yana niyar fitowa ya bishi da kallo shima kuma shi yake kallo alamun rashin gaskiya a tare dashi, ganin kallon da Asad d'in yake masa sai ya waske yace, "Oga deaf nazo duba ring d'ina ko a nan na bari ashe baya nan" ya fad'a yana ficewa ya bishi da kallo haka kawai yaji zuciyar sa bata amince dashi ba gabad'aya.

Zama yayi a kan kujera ya jingina da kujerar yana kallon sama kamar mai son hango wani abun a saman, jin sa yake wani iri in ya tuna abinda mai martaba yace masa sai yaji wani iri tsigar jikin sa har tashi take, abinda ya tsaya masa a zuciya bai wuce Rauda na son sa ko bata son sa ba dan shi dai yasan baiga alamun tana son sa a tare dashi ba, cize bakin sa yayi a bayyane yace, "that's mean ta amince?" Shiru yayi yana tuna abubuwan da suka faru sai kuma yace, "No bana tunanin ta amince, but ta yaya akayi auren?" Ya fad'a yana dafe kansa da yaji yana sara masa.

'In bata sona fa aka aura mata ni? Ya zanyi da ita ya zanyi da Mama?, na riga na yiwa Mama alqawari zan barta yanzu kuma gashi na canja anya zata yafe min?.' Abinda yake fad'a a zuciyar sa kenan yana jin komai yana fita daga kansa ga k'irjin sa yayi masa nauyi sosai kafin ya shafa kansa yana jin sa kamar ba shi ba. Motsi yaji a bayan sa hakan ya saka ya kalli wajan yaga Hydar ne ya shigo yana amsa waya kafin ya kashe wayar ya zauna kusa dashi yana kallon sa yace, "Oga deaf as groom" ya fad'a da murmushi yana kallon sa.

Asad da ya zuba masa idanu bai ce komai ba Hydar yayi dariya yace, "ka daina kallona idannun ka na rikita ni." Asad yace, "kai ka shirya komai?."
"Yeah na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login