Showing 186001 words to 189000 words out of 216282 words

Chapter 63 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

zauna kafin tace, "Allah zan zo." Rahma tace, "to ya zanyi ina nan ina jira, bara na shiga wajan Inna" ta fad'a tana fita Rauda ta bita da kallo ganin tayi haske har kib'a tayi ta juyo da kallon ta ga Umma da itama ita take kallo.

Umma tace, "Ina kika je kika dad'e haka daga rakiya?." Rauda ta fito da ledar gefen ta tace, "Wallahi masu kayan marmari na gani a gefen titi na tsaya na siya" ta fad'a tana d'auki apple guda d'aya ta fara ci. Umma tace, "bakya jin magana Rauda, ina ke ina tsayawa akan titi kina siyayya? Kin manta matsayin da Allah ya baki? Ko kin manta abubuwan da aka fad'a a gaban ki ke kanki kin san baki wuce a nemi kashe ki a wannan yanayin ba."

Rauda ta sauke numfashi tace, "sha'awa suka bani wallahi shiyasa na tsaya." Umma tace, "Wannan ba inda zaki dinga tsayawa siyayya bane malama, ki nutsu ki fuskanci abinda yake tankaro ki domin kuwa jibi ake zancen komawar ki gidan sarautar." Rauda ta tsaya da cin apple din da take yi ta wara ido waje tace, "Wacce jibin Umma?."

Umma tace, "Juma'a." Rauda ta dafe k'irji tace, "Kuma Umma sai kuka amince?." Umma ta bita da kallo tace, "to sai muce A'a? Daman ba ranar muke jira tazo ba ki koma gidan ki kema a daina miki kallon bazawara?." Rauda idon ta ya ciko da hawaye tace, "Amma Umma jibi yayi kusa, kamar wata y'ar tsana za'a ce wani jibi zan koma."

Umma ta bita da kallo kafin tace, "ke zmaan gidan bai ishe ki ba Rauda?." Tayi shiru ta sunkuyar da kanta k'asa Umma tace, "in ke bai ishe ki ba ni ya ishe ni Rauda, bawai don bana sonki ba sai dan kin wuce zaman gida zaman gidan miji shine ya dace dake. A unguwa da y'an uwa ana ta yawo dake a baki bakya jin tsoron bakin mutane?."

"Wanda suka san shi mijin kine sun sani domin ni babu wanda zan fad'awa komawar ki daga ke sai y'an uwan ki ayi komai a gama Allah yasa kin shiga a sa'a ya d'ora ki akan dukkan maqiyan ki dana mijin ki ya baku zaman lafiya mai d'orewa."

Rauda ta sauke numfashi bata ce komai ba ta tashi ta shiga d'aki ta bar kayan marmarin a wajan dan ji tayi sun fita daga ranta.
D'aki ta shiga ta cire hijjabin jikinta ta cillar tace, "Aikin banza, bai san nima haushin sa nake ji ba zai dinga wula?anta ni shi a lallai ga shugaban al'umma. Aikin banza ni gabad'aya haushi yake bani ya cika nuna isa."
Zama tayi a gefen gadon tana tunani kafin taja tsaki ta tashi ta shiga band'aki ranta duk a jagule.

*&&*

? ? ? ?? B'angaren Asad lokacin da ya koma a fusace yake bayan ya kammala shirin sa na kwanciya yana zaune yana aikin jan tsaki zuciyar sa cike take da b'acin ran abinda ta aikata. 'Ta tsaya a kan titi tana siyayya kamar wata namiji, anyi mata magana kuma ta yiwa mutane banza da yake bata da kunya, da ace ta yiwa wannan banza magana da sai na b'ata mata rai sai tayi dana sanin kula shi din da tayi' abinda yakr fad'a kenan a zuciyar sa cikin fad'a.

"Aikin banza" ya furta a bayyane yana jan tsaki gabad'aya ransa a b'ace yake a haka ya kwanta zuciyar sa babu dad'i yana ta fad'an sa shi kad'ai.

Bayan kwana biyu.

Tun daga bakin gate d'in masarautar ta zaka san ana gagari min biki domin tambari ne yake tashi da busa algaita da abubuwa masu dad'i. Duk da babu jama'a da yawa a gidan amma kana ganin kasan akwai abinda ake gabatarwa a cikin sa.

Da yamma aka tura da babbar mota da jiniya aka d'auko Rauda daga gidan su zuwa gidan sarauta bayan tasha adon lalle da duk abinda ake yiwa amarya an mata itama y'an uwanta suka rako ta zuwa gidan.

Babu b'angaren da ba'a kaita ba har na Mama duk da bata nan amma y'an uwanta sun zo tarbar Rauda cikin mutunci da girmamawa suka karb'e ta kafin a zaga da ita ko ina daga baya aka kaita b'angaren da ya kasance nata.

A wannan lokacin jakadiyar ta mai suna Samira da bayin ta da komai suka gabata a gaban ta ita dai bata yi musu ba sai Yaya Ummi ce ta sallame su suka tafi itama kafin su barta dukkan su su watse suka barta ita kad'ai tana kuka kamar yarinya k'arama.

Sai da akayi sallar i'sha tana zaune a gefen gadon da ya kasance nata bayan ta idar da sallar i'sha akayi sallama a k'ofar d'akin tare da fad'in, "Barka da hutawa ranki ya dad'e." Rauda ta kalle ta dan ita bata saba da irin wannan maganar ba hakan ya saka tace, "Barka."

"Fulani Hajiya ce ta aiko ni da kanta domin na raka Fulani b'angaren mai martaba." Rauda ta sauke numfashi kamar tace bazata je ba sai ta d'aga kai tace, "ki jira ni ina zuwa." Jiki na rawa ta mik'e ta fita Rauda tafi minti biyu bata tash???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?i ba kafin ta tashi tayi wanka ta saka kaya da dogon hijjabi ta bata umarnin ta shigo.

Jiki na rawa ta shigo ta k'araso da sauri ta tsaya a bayan ta Rauda ta kalle ta tace, "Kece zakiyi gaba ai ni da ban san wajan ba." Hadimar tace, "Wane mutum, ranki ya dad'e ni wacece da zaki bi bayana? Sai dai ni na biyo naki bayan." A guje ta zabura ta kwasowa Rauda takalmi ta skaa mata da kanta sannan tace, "Ranki ya dad'e zamu iya tafiya?."

Gaba kawai Rauda tayi ta biyo bayan ta suka fito harabar b'angaren Rauda ta nan suka shiga wata k'ofa sai gasu sun bayyana a harabar b'angaren Asad d'in sai da ta rakata har bakin falon sannan ta zube a k'asa tace, "A fito lafiya ranki ya dad'e." Da amin Rauda ta amsa duk tana jinta wani iri domin bata saba wad'annan abubuwan ba mace ta haife ta ta dinga zube mata a k'asa.

Kai tsaye falon ta shiga babu kowa ta tsaya tana k'are masa kallo in akace had'uwa to falon ya had'u carpet d'in kamar jikin mage, numfashi ta sauke tace, "Ko ina zan bi kuma oho." Tayi k'aramin tsaki ranta sai taji ya sake b'aci haka kawai komai ya dagule mata ta rasa ma abinda zatayi.

Ciki ta sake shiga ta sake ganin wani falon amma bai kai wancan girma ba amma shima babba ne akwai kyau duka hotunan Asad d'in a manne a jikin sa dana mahaifin sa, stair d'in ta gani kai tsaye ta nufe su ta fara takawa zuwa saman ba tare da tsoron komai ba. Wani falon ta sake shiga mara kayan da yawa amma ya tsaru shima a nan hoton? mahaifin sa da dukkan su har Mama yake a manne baza ka gane shi a jikin hoton ba domin kaya iri d'aya ne a jikin su.

Kai ta d'auke daga kan hoton ta kalli hanyar d'akunan kamar bazata shiga ba sai kuma kai tsaye ta nufi d'akin farko ta buWe, girman d'akin ya bata tsoro domin gadon kamar ba'a saka ba gashi tafkeke a tsakiyar d'akin amma kamar babu sabida girman d'akin, har zata kulle sai ta hango hoton ta a kan bedside drawer wanda aka d'auka lokacin da suna Cairo.

Fita tayi daga d'akin ta dawo falon ta zauna tayi shiru domin ta tabbatar baya nan sai ranta ya sake b'aci haushin sa ya ninku a zuciyar ta tayi shiru ta rasa abinda zatayi.

? ? ? ? ? A b'angare Asad sun fita shida mahaifin sa da Suhail da kuma Uncle kai tsaye wajan Mama suka wuce suka same ta tana nan dai yadda take sai Suhaima da taji sauk'i sosai jikin ta ya warware. Tun shigowar su Suhaima ta mik'e tsaye security d'in da take kula dasu ta fita mai martaba ya kalli Suhaima yace, "Autar Mama ya jikin naki?."

Sai kawai ta fashe da kuka tana fad'in, "Abba jikin Mama baya sauk'i ko kad'an."
"Waye yace miki baya sauk'i? Kira mana likitan muji." Ba musu ta fita sai gata da likita sun dawo ya gaishe su gaisuwar girmamawa kafin ya mai martaba yace, "Wanne cigaba aka samu akan ciwon nata?."

Dr yace, "an samu cigaba a da bp ta baya sauka amma yanzu ya sauka ya dawo normal jiran farkawar ta kawai yake yi." Asad yace, "bugun zuciyar fa?." Dr yace, "Shima ya ragu amma bai dawo daidai ba har yanzu, amma in sha Allah daga yau zuwa gobe zata iya farkawa."

Asad ya k'arasa kusa da ita yana yi mata addu'a har lokacin da oxygen a hancin ta, a wannan lokacin k'annen ta suka shigo mata su biyu ganin su mai martaba suka gaishe shi yace, "Ya mai jikin?." Ta kalli Mama kafin tace, "Alhamdulillah gata nan a kwance."

Ta kalli Suhaima tace, "Suhaima ki tafi tare da Antyn ki kije gidan ta ki huta zan zauna da Maman a nan in yaso gobe sai ki dawo kema baki da lafiya." Fuska ta kwab'e zata musa Asad yace, "Ki tafi." Dole tayi shiru bata ce komai ba a nan su Asad suka bar su suka fita kai tsaye mai martaba yace su wuce asibitin da Waziri yake.

Shima yana kwance har lokacin bai farfad'o ba suka yiwa iyalan sa ya mai jiki da addu'ar samun lafiya, har zasu juya su fita matar sa tace, "Allah yaja zamanin mai martaba daman ina so zan kawo k'ara." Abba yace, "To k'ara wacce iri?." Tace, "Akan sane ina so a bi min hakkina dana y'ay'ana sakamakon kashe su d'in da yayi, bazan bar maganar nan ba shiyasa nace zan sanar dakai ko na kai k'ara human right."

Kai Mai martaba ya girgiza kafin yace, "Ya kashe miki y'ay'a kamar ya kenan?." Tace, "Ta son zuciyar sa da neman duniyar sa mana, ya karb'o abu dan ya ksshe wani ya k'are a kan y'ay'ana ni kuma wallahi bazan yarda ba."
"Shikenan ki jira ya samu lafiya sai ayi maganar gabad'aya, banda batun kai k'ara zamuyi maganin matsalar da kan mu."
"Na gode Allah ya k'ara girma ya k'ara lafiya" suka amsa da amin kafin su sake fitowa suka shiga mota amma babu wanda yake cewa kanzil.

? ? ? ?? A can gidan lokaci d'aya wutar gidan ta d'auke duhu ya mamaye ko ina aka rasa daga inda matsalar take, Rauda na zaune taga haske ya d'auke duhu sosai ya mamaye inda take sai tsoro ya shige ta hannu na rawa ta kunna hasken wayar ta amma kamar bata kunna ba iya inda take kawai take ganin hasken.

Motsi ta dinga ji a bayanta gabanta yayi mugun fad'uwa ta kasa juyowa balle jira take kawai taji an shake ta ta baya. "Hiii Gambia Rauda!" Aka fad'a daga bayan ta ana dawowa ta gaban ta. Wayar hannun ta ta sub'uce ta fad'i k'asa jikinta ya soma rawa har lokacin bata kalli waye ba.

Dariya yayi sosai ya kunna tashi fitirar ya haske kansa yace, "K'anin mijin kine Hydar, kar kiji tsoro." Maimakon tsoron ya ragu sai ya sake k'aruwa jikinta ya cigaba da rawa tana kallon sa amma bata iya cewa komai. Yace, "Zauna ki nutsu magana nazo muyi dake ta fahimta, zauna" ya fad'a yana zama shima dole itama ta zauna tana kallon sa.

"Magana ce nazo muyi dake ta fahimta wacce zaki tsira mijin ki ma ya tsira. Ba zama nazo yi ba balle surutu magana nake so muyi guda biyu ko nace zab'i ne zan baki guda biyu ko guda uku wanda kika amince dashi zamuyi amfani. Na farko ga magani yanzu ki karb'a Kisha a gabana cikin jikin ki ya fita, na biyu ko ki amince dani a wannan daren mu kasance da juna nida ke, na uku ko na kashe mijin ki. D'auki d'aya a ciki da sauri ba b'ata lokaci nazo yi ba."

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!" Shine abinda Rauda take fad'a kenan jikinta yana rawa zuciyar ta na bugawa sosai ta zuba masa ido ta rasa abinda zata yi. Jin tayi shiru ya skaa shi daka mata tsawa yace, "Baki ji me nace bane?!." Ta sake firgita tace, "Naji" murya tana rawa sosai. Yace, "iskanci ne ya saka kika yi min banza kenan? Babu wanda zai kwace ki a yanzu domin dukkan su basa nan zan iya yin duk abinda nake so dake a yanzu kuma kisha maganin ta k'arfi kuma na kashe mijin naki babu abinda kika isa kiyi. Na baki zab'i ne dan kawai ina ganin mutuncin ki amma in kina ganin baza ki zab'a ba..." ya fad'a yana tasowa yayo kanta ta zabura ta mik'e tayi baya tace, "Zan zab'a! Wallahi zan zab'a ka tsaya."

Kuka take yi tana maganar ya tsaya yace, "Ina jinki." Tace, "bani maganin zan sha, amma kayi min al?awarin in nasha zaka kyale mu." Hannu ya wara kafin yana kallon ta ta hasken fitilar wayar ya mik'a mata tablet d'in da ruwa a k'aramar jarka hannunta yana rawa ta b'alla amma ta kasa sha sai kuka da take yi.

Hannu taga ya mik'o zai jata jikin sa bata san lokacin da ta cilla maganin bakin ta ba ta kafa kai tana shan ruwan a haukace a daidai lokacin motar su Asad ta shigo cikin gidan.
[17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*087.*

? ? ? ?? Kamar walqiya sai ta neme shi ta rasa nan take haske ya mamaye d'akin duk ta jiqe da gumi sai numfashi take saukewa k'irjin ta yana sama da k'asa ruwa duk ya zubar mata a jikinta. A kan carpet ta zauna ta cure waje d'aya tana sauke numfashi tsoro yaka sake mamaye mata zuciya.

Motar su Asad tana tsayawa haske ya mamaye gidan Uncle yace, "Da me ya samu wutar gidan haka?." Babu wanda ya amsa Mai martaba ya kalli Asad yace, "to sai da safe bance ka biyo ni duba Aliyu ba." Amsawa yayi cikin gamsuwa Suhail ya raka shi har b'angaren sa. Kallon Suhail yayi sai yaga yana ta murmushi ya kalle shi yace, "Murmushin na meye?."

Suhail ya sosa kai yace, "A'a ranka ya dad'e wani abun na tuna." Asad yayi k'aramar dariya ya kawar da kansa yana jinjina kai kafin yace, "Fad'a min as your friend." Suhail ya kalle shi sai ya sauke kai k'asa yace, "Ranka ya dad'e wannan labarin baya ne ni yanzu ko iya kallo fuskar mai martaba ma bana iyawa." Asad ya murmusa ya shiga ciki Suhail ya juya ya fita.

Kai tsaye saman ya hau dan shi yama manta an kawo Rauda gidan hankalin sa yana wajan Mama yana hawa ya hango mutum a cure a waje d'aya sai gaban sa ya fad'i ya tako ya k'araso wajan yaga robar ruwa a wajan a yar ga tablet na magani a kwali ya kalli inda take amma baiyi magana ba.

Jin motsi ya saka Rauda d'agowa ganin sa ya saka ta zabura ta mik'e ta k'araso inda yake ta rugume shi sosai tana kuka cikin tsoro har lokacin jikinta rawa yake yi. Hankalin sa ya tashi ganin yadda take hakan ya tabbatar masa akwai abinda ya faru ya d'ago ta daga jikin sa ya rik'e ta yana kallon fuskar ta da ta jiqe da hawaye yace, "Lafiya kike?."

Numfashin ta sama da k'asa yake yi bakinta yana rawa tace, "Hydar! Hydar ne yazo nan, tsoro nake ji" ta sake fad'a tana sake komawa jikinsa jin abinda ta fad'a sai ya rik'e ta sosai hankalin sa kai k'arshe wajan tashi burin sa yaji abinda ya faru.

Zaunar da ita yayi a kan kujera yana kallon fuskar ta yayi mata alama da kansa meya faru, muryar ta har lokacin rawa take tace, "Yazo nan bayan an kashe hasken gidan" ta tsaya tana jan numfashi a hankali ya furta, "Nutsu ina tare dake" ya fad'a yana goge mata hawayen fuskar ta ta rik'e hannun sa k'am tana kallon hanya tace, "Yazo nan! Yazo wallahi na ganshi."

Ganin a rud'e take har lokacin akwai tsoro a tare da ita sai ya d'auki wayar sa da hannu d'aya ya rubutawa Suhail message ya sanar dashi Hydar yana gidan a tabbatar an nemo shi kafin safiya, ajjiye wayar yayi ya sake rik'e hannunta yana kallon ta sai hawaye take yi.

"Ya bani wancan maganin yace in ban sha ba sai ya kashe ka!" Ta fad'a tana sake fashewa da kuka. Dumm k'irjin Asad ya buya ya d'auki kwalin maganin? yaga sunan sa nan take ya d'auki wayar sa ya shiga Google yana duba maganin na meye abinda ya gani ya saka shi firgita yace, "Kin sha?."

Kai ta d'aga masa alamun eh tana kuka, ya sauke numfashi mai tsaho ya furta, "Why!." Muryar ta na rawa tace, "Yace dole na zab'i d'aya ko na sha ko ya kashe ka ko yayi min fyad'e, dak'yar na gudu yana so ya tab'a niiii" ta fad'a tana sake fashewa da kuka ya rungume ta sosai a jikin sa zuciya sa na wani irin bugu mai k'arfin gaske.

"I'm sorry naje wajan Mama ne" ya fad'a yana shafa bayan ta gagarumin tashin hankali yana sake mamaye masa zuciya musamman da ta ambaci fyad'e ji yake kamar ana soka masa mashi a zuciyar sa sabida bala'in kishi da zafin da yake ji a ciki.

Tashi yayi zai fita tayi saurin rik'e shi ya dawo ya zauna tace, "Kar ka barni ni kad'ai zai dawo, tsoro nake ji dan Allah kar ka fita." Komawa yayi ya zauna ya sake rik'e ta a jikin sa hankalin sa yakai mak'ura wajan tashi haka zalika ransa yakai k'ololuwar b'aci so yake yaje ya samu masu tsaron wajan su fad'a masa aikin me sukayi har da za'a shigo b'angaren sa har saman sa matsayin sa na shugaba babu wanda ya sani.

Hannun sa ya d'ora a kan cikin ta ya runtse ido har lokacin kuka take yi tana jikin sa yace, "Meyasa kika sha? Meyasa baki amince an kashe ni d'in ba?. Tashi mu tafi asibiti." Kai take girgizawa amma batayi magana ba sai daga baya tace, "Bazan iya ba, bazan iya bashi kaina ba, bazan iya gani an kashe ka ba, gwara cikin ya zube" ta sake fad'a tana kuka sosai.

Bayan ta yake bubbugawa alamun rarrashi duk da har lokacin haushin ta yake ji amma bazai barta cikin wannan hali

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login