Showing 147001 words to 150000 words out of 216282 words

Chapter 50 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

a kanta kamar a mafarki sai ta zabura ta mik'e tsaye Umma ta ajjiye tea d'in ta zaunar da ita tace, "Meye na wannan zaburar kamar kinga dodo? Koma ki zauna? Ta fad'a tana zama kusa da ita. Kuka take k'ok'arin yi Umma tace, "Kar kiyi min kuka, ki mayar da wannan hawayen bana son ganin su."

Ba shiri ta mayar dasu tana kallon Umma ta mik'o mata tea d'in tace, "karb'i ki shanye yanzun nan kisha maganin ki." Ba musu ta karb'a ta kafa kai duk dan ta burge Umma tana yi tana kallon ta. Bata sauke ba sai da ta gama shanyewa tass ta ajjiye kofin Umma ta bata magani da kanta tasha amma bata ce mata komai ba. Kallon Umma Rauda take yi ta sunkuyar da kanta k'asa murya na rawa tace, "Umma wallahil azim duk abinda ya faru babu laifina dan Allah ki yafe min."

Umma ta sauke numfashi tace, "ki daina kuka ki kwantar da hankalin ki komai ya wuce yayi mana bayani kuma dukkan mu mun gamsu." Rauda ta kalli Umma tace, "Umma kema kin amince dashi kenan?."
Umma tace, "Na amince har zuciyata Rauda, yanayin yadda yayi mana bayani ya tabbatar mana da kalaman sa gaskiya ne d'an uwan sa shine ya sake ki tun farko kin san shine wanda kuke fad'an nan bazai zo yaga kin rab'i dan uwan saba shiyasa ya yanke wannan hukuncin. Amma shi mai martaba Asad bashi ya aikata wannan sakin ba."

Rauda tace, "Umma rubutun sane, kalaman sane, maganar sace, yanayin sane, hatta shaidar da ya nuna min yace da ita ake banbance su na ganta a hannun sa a ranar kuma ya sanar dani ba kowa yasan da wannan alamar ba ta yaya zai zama Aliyu ne bashi ba?." Umma ta sauke numfashi tayi shiru Rauda na k'ok'arin saka mata kokwanto a zuciyar ta amma har ga Allah ta amince da Asad dan yayi musu bayanin da dukkan su sai da suka firgita da lamarin masarauta.

Umma tace, "Duk na amince da hakan Rauda amma bazai yi rantsuwa a kan karya ba."
"Umma zai iya yi kodan ya samu abinda yake so. Yana k'ok'arin kare kansa ne daga fyad'en da yayi min amma babu aure tsakanina dashi Umma. Tabbas a Cairo ya mayar dani amma ya kuma sakina Ummaaaaa!" Ta fad'a tana can kalmar Umman cikin sanyi tana karyar da wuyan ta hawayen suka sakko mata.

Umma tayi shiru na wani lokaci kafin tace, "Lamarin akwai d'aure kai Rauda." Rauda tace, "Na fad'a masa ya fita daga rayuwa ta wallahi bana son ganin sa ko kad'an na tsane shi na tsani ahlin su gabad'aya, yaje can ya k'arata kuma wallahi sai na zubar da cikin....." kallon da Umma tayi mata ya saka bata k'arasa ba ta sauke ido k'asa ta fashe da kuka tana fad'in, "Umma na tsani kaina bana son rayuwata, ta silar Asad kika ce min baki yafe min ba Umma, ina zan saka kaina naji dad'i bayan wannan furucin da kika yi a kaina?. Kallon fasiqa kike min Umma kuma wallahi ban tab'a zina sai a lokacin shima kuma fyad'e zan kira shi Umma. Ta silar sa Baba ya d'aga bulala ya dake ni har aka fasa min jiki, Umma ciki ne fa a jikina, ciki na haihuwa ba tare da aure ba. Bazan yafe masa ba Allah ya isa tsakanina dashi" ta fad'a tana fashewa da kuka mai tsuma zuciya.

Umma tayi shiru na wani lokaci kafin tace, "Allah kad'ai yasan abinda ya b'oye amma har zuciyata na amince dashi, badan yana sarki ko yana mai kud'i ba ke kin san halina ni ba irin mahaifin ki bace, dan haka na amince da cikin jikin ki na sunna ne bana shege ba. Zaki raine shi kamar yadda ko wacce uwa take rainon cikin y'ay'anta ki haife shi kamar kowa, kar na sake jin maganar zubar dashi a bakin ki balle ma ki aikata kona shege ne baza'a zubar dashi ba balle cikin sunna ne. Indai kina son farin cikina kar ki aikata makamancin hakan."

Rauda bata daina kuka ba maganar Umma jinta take wani iri, wai ya zasu had'e mata kai kowa ya yadda cikin sunna ne bayan ita tasan ya sake ta? Meyasa suke mantawa da ita tasan shi tasan yanayin maganar sa ba Aliyu bane shine.

Umma tace, "Bana son wannan koke-koken komai ya wuce, na yafe miki har zuciyata ki kuma yi hak'uri zargin ki da mukayi dukkan mu. Shi kuma Anas mahaifin ki zai sanar dashi komai dan ko babu aure tsakanin ki da Asad dole a dakatar da batun auren ki a yanzu."

Kai take girgizawa ta d'ago tana fad'in, "Haba Umma ya zan yiwa Anas haka? Bayan dogon jiran da yayi a kaina tun ba yanzu ba yana gab da samuna kuma ace ya rasa ni?. Umma ke kike cemin daman kinfi sonsa da Asad sabida yana sona sosai ki tuna lokacin da na samu matsala a k'afata bai guje ni ba ya nuna zai aure ni a yadda nake. Umma bazan so na rasa Anas matsayin miji ba sabida k'aunar da yake min dan Allah kar kuyi min haka" ta fad'a tana sake fashewa da kuka.

Umma tace, "Dukkan mu babu wanda ya isa ya canja k'addara sai dai mu zubawa sarautar Allah ido daga nan har zuwa lokacin da zaiyi ikon sa akan dukkan mu. Bai rubuta Anas zai zama mijin ki ba tun farko shiyasa ake ta samun matsala akan auren ku, inda mijin kine babu abinda zai hana baki aure shi ba. Mu d'auka babu auren Asad a kanki amma akwai cikin sa a jikin ki kinfi kowa sanin ba'a aure da ciki kinga kenan auren ki da Anas ba abu ne mai yuwa ba."

Zatayi magana Umma tace, "Ki daina wannan koke-koken ki kwanta babu abinda kuka zai k'ara miki sai ciwo" tana fad'a ta tashi ta bata waje ta fita daga d'akin. Hannu Rauda ta dunqule ta fara dukan cikin ta a zafefe cikin k'unar rai tana yi tana kuka sai kuma ta daina ta sake fashewa da sabon kuka.

Ta jima a haka kafin kukan nata ya tsaya sai kuma ta zubawa waje d'aya idanu kalaman sa suna dawo mata cikin kanta sai taja tsaki ta toshe kunnen ta da duka hannayen ta biyu ta kwanta lamo a kan gadon.
Bata san iya adadin lokacin da ta d'auka a haka ba maganin da tasha ya fara bin jikinta bacci ya d'auke ta.

Umma data fita daga baya ta dawo ta tarar tayi bacci sai hankalin ta ya kwanta ta tafi wajan Baba dan su sake tattauna maganar nan, a zaune ta same shi shima da alama tunanin da yake yi kenan tayi sallama ta zauna tace, "Malam nifa gaskiya yanzu ina tantama, Rauda tace akwai abubuwa da dama wanda suka tattauna ita da Asad d'in kuma lokacin da yazo sakin ta ya maimaita mata su, in bashi bane ba taya Aliyun yasan dasu?."

Baba ya sauke numfashi yace, "Wannan kuma duka zai bayyana tunda wannan d'in ya bayyana a yanzu. Abinda nake so ki fahimta a matsayin Asad bance bazai yi k'arya ba amma bazai yi k'arya irin wannan ba duba da yana da ilimin addini sosai yasan illar da take cikin zaman haramci."

Umma tace, "Ni zuciyata tafi karkata akan shine ya sake ta d'in kawai lokacin baya cikin tunanin sane, ka tuna lokacin da kaje wajan sama mana akan rushe gidan nan ya kuka yi dashi? Ai bai nuna maka ya sanka bama gabad'aya."

Baba ya girgiza kai yace, "Haka ne. Koda shi d'in ne yayi sakin tunda har baya cikin hankalin sa bata saku ba har yanzu matar sace." Umma tace, "ta ya ta zama matar sa bayan shi da kansa yazo gidan nan?, indai har baya cikin hankalin sa ya akayi ya kawo kansa gidan nan? Indai baya cikin hankalin sa ya akayi ya tuna da akwai matar sa a gidan nan? Indai baya cikin hankalin sa ya akayi yasan ya sake ta saki d'aya a baya yazo ya k'arashe ragowar?."

Baba yace, "Ke baki san aikin sihiri babu abinda baya sakawa ba? Abinda nake so ki gane a nan Asad bazai mana rantsuwa a kan k'arya ba, ki tuna waye shi mana a garin nan." Umma tace, "Zai iya malam, zai iya kodan ya d'auke hankalin mu daga cikin jikin ta mu koma yi masa kallon cikin sunnah mu daina masa kallon cikin shege."

Baba ya kalle ta yace, "Kina da matsala Binta, Rauda fa matar sace babu ta inda hakan zata kasance ba tare da aure a tsakanin su ba, yafa karantu yasan daidai da wanda ba daidai ba." Umma ta tab'e baki tace, "sai naga shaidan yana nasara akan kowa mai ilimi dama wanda bamai ilimi ba ya kamata ka tuna."

Baba yace, "to nidai na amince da abinda yace, har yanzu Rauda matar sace ko yau yace zai tafi da matar sa zan bashi ita taje gidan sarauta a dama da ita. Anas kuma na kira shi da safe zai zo ya same ni muyi magana." Umma ta girgiza kai tace, "ya dai kamata a duba lamarin, komai ya faru da Rauda damu ya faru kuma hakkin ta yana wuyan mu dukkan mu sai Allah yayi mana hisabi da ita matuk'ar muka tura ta wajan sa ba tare da munyi bincike ba kamar mun tura ta taje tayi zina ne" ta fad'a tana mik'e ta fita ta bar Baba a zaune dan shi kam baiga abinda zai hana Rauda zama fulani matar sarki ba.

Washe gari.
*11:00 am.*

Baba ne da Anas ne a zaune bayan sun gaisa Baba yayi shiru baice komai ba domin har ga Allah yana jin nauyin Anas d'in da babu yadda zai iya ne. Anas kam tunda yaji kiran jiya haka nan gaban sa yake fad'uwa dalilin da ya saka shi bai k'asa a guiwa ba ya tawo da safe dan yaji me yake faruwa ko hankalin sa zai kwanta.

Baba ya numfasa yace, "Anas nasan zakayi mamakin kiran da nayi maka zuciyar ka zata dinga fad'a maka abubuwa da yawa akan kiran, ina so ka bani hankalin ka ka kuma saurari abinda zan fad'a maka dakyau."

Anas ya gyara zaman sa yace, "to Baba." Baba yace, "Wato Anas akwai k'addarar da zaka ga ta gifta in Allah bai rubuta abu naka bane sai ya kubce ta silar wannan k'addarar da ta kusto kai. In hakan ya faru mukan d'auka daman ba rabon mu bane abinda muka rasa d'in tunda shi rabo hausawa sukace ko kana cikin mahaifiyar kane indai naka ne sai ya same ka."

Baba ya sake d'aure Anas da jijiyoyin jikin sa jikin sa ya sake yin sanyi ya kalli Baba yace, "Baba ban fahimta ba."
"Zaka fahimta yanzu Anas. Wato kamar yadda k'addarar auren ka ta raba ka da Rauda a wannan karon kuma k'addarar auren ta zata sake raba ku Anas." A firgice ya kalli Baba idanun sa a waje yana kallon Baba cikin tashin hankali, ganin hakan sai Baba yace, "Kwantar da hankalin ka Anas kaji bayanin da zan maka. Wato a kwanakin baya duka mun d'auka auren Rauda ya mutu har kai na sanarwa ka kuma nemi sake neman auren ta a karo na biyu har muka zo yau da auren ku bai wuce kwanaki goma ya rage ba. A cikin kwanakin nan abubuwa da yawa sun faru Anas ciki harda bayyanar mijin ta inda ya tabbatar mana da har gobe akwai auren sa akan Rauda bai sake ta ba."

Baba ya kuma cewa, "Bayanan da yayi mana mun gamsu sosai dasu ita kanta Raudan ta tabbatar mana da ya mayar da auren ta bayan ya sake ta,? jin hakan ya saka na neme ka dan nasan kasan a yanzu auren ka da Rauda babu shi Anas!" Baba ya fad'a a tausashe yana kallon Anas da tashin hankali ya bayyana k'arara a kan fuskar sa gumi yana keto masa daga ko wanne kafofi na jikin sa cikin tashin hankali da bugar zuciya.
[17/12, 10:42 pm] Nafisat Alwasa: *Arewabooks@ nanahaleema11*
*074*

? ? ? ? ?? Hankalin Mum ya tashi sai zagaye take a falon tana dukan hannayen ta tana yi tana kallon Jidda da take zaune tana kuka sosai sai ta d'auke kanta ta cigaba da tafiya tana kallon sama zuciyar ta cike da tunanin mafita. Zama tayi ta kalli Jidda tace, "Jidda sanar dani abinda kika yiwa Aliyu, in baki fad'a min ba bazan taimake ki ba."

Jidda tana kuka ta zube k'asa kusa da Mum tana fad'in, "Mum dan Allah a fara solving problem d'in then sai ki tambaye ni ni kuma zan fad'a miki, in aka tsaya tambaya a yanzu rayuwata tana cikin hatsari Aliyu zai iya aikata min komai, dan Allah Mum ki taimake ni kafin ya kashe ni" ta fad'a tana sake fashewa da kuka ta kifa kanta a cinyar Mum.

Eman da ta shigo taji abinda suke cewa ta zauna a kusa da Mum tace, "abinda Mum take tambaya shi ya kamata ki fara bata amsa, me kika yi masa har kike tsoron hukuncin sa haka?." Mum hankalin ta da yake a tashe tace, "Abinda ya kamata mu sani kenan in yaso sai musan ta inda zamu b'ullowa lamarin, ki duba yanayin da take ciki fa kalli yadda ta rame ta lalace ga ciki a jikinta duk ta koma bak'a kamar ba ita ba. Me kika yi masa haka?."

Jidda ta d'ago kanta daga cinyar Mum tace, "Mum kawar da Aliyu shine abinda ya kamata a fara yi ba wannan tambayar ba, in abinda nayi masa ya bayyana ba ni kad'ai ba hatta dangin ki da dangin Daddy sai abin ya tab'a su. Dan Allah ayi gaggawar kashe shi tun kafin shi ya kashe mu." Mum ta kalli Eman itama ta kalle ta kafin Mum ta kalli Jidda tace, "Ikon Allah! Bakin ki bazai iya fad'a laifin ba kenan kome?."

"Fad'ar bata da amfani! Jinta sai iya tarwarsa kunnuwan ku Mum, ku tabbatar an kashe Aliyu in ba haka ba dukkan ku sai zuciyar ku ta kusa bugawa nan gaba" ta fad'a da ihu tana cigaba da kuka kafin ta baje a kan carpet tana kuka sosai tama manta akwai ciki a jikin ta.

Eman tace, "ki sanar da mijin ki mana na tabbatar zaiyi maganin sa tunda sama yake da kowa a garin nan." Jidda da take kuka a kan carpet ta d'ago ta kalli Eman sai ta sake kwantawa tana cigaba da zubar da hawaye. Hankalin Mum ya kai k'arshe wajan tayi idanunta a waje take tunanin wanne irin laifi mai girma Jidda ta yiwa Aliyu haka da ta tsorata da hukuncin da zai mata...?

? ? ? ? Jin yadda take kuka sosai ya saka Mum tace, "Taso nan Jidda" ta fad'a tana bata hannu ta rik'e ta mik'ar da ita ta zaunar da ita kusa da ita ta dafa kafad'ar ta tace, "Aliyu ne bakya so ki gani a raye ko?." Kai ta d'aga da sauri hawaye na sauka daga idanun ta wani yana bin wani tace, "Eh Mum, rayuwar sa barazana ce ga tawa rayuwar, zai tarwatsa min dukkan plan d'ina Mum."

Mum ta girgiza kai tace, "Shikenan za'ayi maganin sa kar ki damu. Ko meye za'a yi akan a ga bayan sa indai hakan zai saka hankalin ki ya kwanta." Rungume Mum tayi tana kuka bata ce komai ba Mum tana shafa bayan ta zuciyar ta cike da zullumin ranar da laifin da ta yiwa Aliyun zai bayyana, yadda taga ta tsorata sosai abin ya bata tsoro tana da tabbacin akwai wani abun a k'asa, amma meye? Wanne irin laifi ne mai girma haka?.

*&&&.*

? ? ? ?? "Kai wallahi Fulani mai babban d'aki ce take tawowa, yanzu ya zamuyi gashi waziri yace kar mu bar kowa ya shiga b'angaren nan? Bamu isa mu hanata ba" mai tsaron k'ofar ya fad'a yana kallon d'an uwan sa wanda yaka tsaye a kusa dashi. Kafin suyi wani yunk'uri Mama ta iso wajan ita da jakadiyar ta a bayan ta dole suka zube a k'asa suna gaishe ta ta d'aga musu hannu ta nufi ciki jakadiyar ta ta tsaya a baya.

Mama tana shiga d'akin da mai martaban yake kwance taga kan gadon wayam babu kowa a kai gabanta ya yanke ya fad'i ta dafe k'irji tana kallon d'akin aka bud'e k'ofa aka shigo, Uncle ne ya shigo ganin ta a tsaye duk sai ya rude yace, "Ranki ya dad'e yaushe kika shigo?."

"Yanzu na shigo? Ina mai martaba?" Ta fad'a tana sake kallon gadon tana kallon sa. Kafin yayi magana mai martaba ya fito daga band'aki fuskar sa duk ruwa da alama alwala yayi suka had'a ido da Mama ta tsaya cak tana kallon sa shi kuma ya d'auke kansa ya zauna a gefen gadon ya d'auki wayar sa da take gefe????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? yana dubawa.

Kallon Uncle tayi ta kalli mai martaba ta sake kallon uncle ta sake dawo da kallon ta ga mai martaba da yayi kamar bai ganta ba yana zaune ya gefen gadon yana amsa waya. Ta juya ta sake kallon Uncle sai taga ya bud'e k'ofa ya fita ya kulle k'ofar ta sake kallon mai martaba da mamaki mai d'auke da tsoro hadi da al'ajabi.

Takowa take yi zuwa kusa dashi shi kuma ya d'auke kansa tamkar ma bai san da wata hallita a wajan ba har ya gama wayar ya ajjiye wayar ta k'araso kusa dashi ta zauna kusa dashi tace, "Mijina kai nake gani ko kuma idona ne yake min gizo?." Idanun sa ya d'ago suka had'a ido ya d'aure fuska matuk'a sai ya sake d'auke kansa daga kanta. Idanun ta suka ciko da kwallah ta kwantar da kanta a kafad'ar sa tana hawaye tace, "Mijina kayi min magana dan Allah, kai nake gani ko mafarki nake yi."

Hannayen sa ya saka ya d'agota daga jikin sa suka had'a ido yayi kamar bazai magana ba kafin yace, "ba mafarki kike ba nine dai da kaina." Sai ta rud'e ta rike hannun sa tana fad'in, "Tun yaushe mijina ya farka ban sani ba? Ka san adadin damuwar dana shiga akan rashin lafiyar nan taka amma shine har zaka tashi kana tafiya ba'a sanar dani ba?."

Hannun sa ya kwace daga rik'on da tayi masa ya hard'e hannun a k'irji yana kallon ta yace,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login