Showing 57001 words to 60000 words out of 216282 words

Chapter 20 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

mata kai yace,

? ?? "Do you love me Muwaddaty?." Rauda bata san lokacin da ta d'aga masa kai alamun eh ba sai kuma ta girgiza kai alamun a'a tunawa da qalubalen da yake cikin auren sa. Hannayen ta ya rik'e duka biyun yana cigaba da kallon idon ta amma ya kasa yi mata magana sai kallo.
"Akwai tarin qalubale a cikin zamana dakai, bana son sai na saki jiki dakai zuciyata tayi nisa a k'aunar ka rana d'aya ka rabu dani. Abinda nake jin tsoro kenan prince shiyasa bana son sakin jikina dakai sabida nasan ban dace dakai ba" ta fad'a a hankali tana kallon fuskar sa.

Yadda take magana muryar ta na shaking idanun ta na k'okarin sakko da hawaye ya saka shi matsar da bakin sa kusa da nata yayi kissing kad'an ya janye bakin sa yace, "babu abinda zai raba mu believe me. I will be always in your side forever." Kai ta girgiza tana kallon sa hawaye suka sakko mata tace, "Promise me u never leave me." Hannun ta ya rik'e yaja baya ya duk'a a kan guiwar sa duka biyun yace, "I promise you I will never ever leave you" Sai ya d'an cije baki yace, "Kome zai faru ina tare dake, ina sonki so mai yawa" ya furta a sanyaye muryar sa na yankewa alamu sun nuna maganar da yake yi tayi yawa.

Bin sa tayi ta durk'usa itama tace, "are you sure that you never leave me?." Kai ya d'aga mata alamun eh ya matsa hannun ta yace, "I'm very much sure Muwaddaty." Kallon sa take yi da kai yayi mata alamun tana sonsa, sai tayi murmushi ta sunkuyar da kai tace, "I love you." Jawo hannun ta yayi suka yi baya ta kwanta a jikin sa shima ya kwanta a kan carpet flat yana kallon ta tana kallon sa hannun sa yana zagaye da k'ugun ta.

Juyawa yayi ta koma k'asa shi kuma ya dawo sama yana gefen ta yana kallon ta cikin blue light a hankali yace, "repeat it again" ya fad'a cikin muryar da ita kad'ai ce kawai zata ji.
"I love you so mu......" bakin ta yayi shiru lokacin da ya fara kissing d'inta cikin sauk'in soyayya mai nuna tsantsar kewa da k'auna a bayyane.

Wak'ar da take tashi ta sake jefa su cikin shauk'i sukayi nisa a cikin sabon yanayin da suka tsinci kansu, suna kwance cikin flowers masu kyau da khamshi k'auna da soyayya na sake narkar da zuciyar su cikin k'auna. Ya gigita Rauda tayi nisa a cikin duniyar da yake so taje shima yayi nisa a cikin ta.?kamar an saka masa remote ya dakata da abinda yake yi ya dafe kansa da hannun sa ya koma gefe yana jan numfashi har lokacin hannun sa yana kansa yana sauke ajiyar zuciya.

Rauda ganin yanayin da ya shiga sai ta janye jikinta ta tashi da sauri ta shiga d'aki tana sauke numfashi duk a tunanin ta ciwon da take dashi ne ya dakatar shi yin abinda yake niya. Ya jima a haka kafin ya tashi jikin sa a sanyaye ya shiga d'aki zuciyar sa cike da tsoro da tunanin dalilin yanayin sa da kuma abinda ya jawo tsayawar komai ba tare da ya shirya ba.



_Gafa Mama a hanyar Egypt, ga Asad yayi Alqawari, ga kuma aikin Mama ya kama shi.=?(?_
[17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*043.*

? ? ? ? ? Zuciyarta bugawa take tana dafe da ita har lokacin idanun ta a kulle yake babu abinda take gani sai abubuwan da suka faru a lokaci kad'an da ya shud'e. Gani take kamar a mafarki ya faru ba gaske ba ta bud'e idon ta tana fuskantar kanta a mudubi tana kallon fuskar ta sai ta kulle idanun ta tunawa da abinda ta furta masa ta sake dafe zuciyar ta tana ji yadda take bugawa da sauri.

'Ke Rauda anya bakiyi gangancin barin gangar jikinki da zuciyar ki fad'awa tarkon soyayyar wannan bawan Allah ba?, kin sani shi ba daidai yake dake ba meyasa zaki bari rud'in kalaman sa suyi tasiri a kanki?. Kija jikin ki ki tuna matsayin ki sannan ki tuna wacece babar sa har kashe ki ta turo ayi dan kawai bata sonki, ki san abin yi kafin wankin hula ya kai ki dare.' Salon bugun zuciyarta tane ya canja ya koma na tsoro da fargaba domin abinda zuciyarta ta fad'a mata gaskiya ne ta tabbatar ba k'arya bane.

Ita ba sa'ar Asad bace tabbas amma gashi tayi sake zuciyarta ta fara yin nisa a cikin k'aunar sa. Kanta ta dafe a bayyane tace, "Yayi min alqawarin bazai barni ba nasan kuma zai cika" ta fad'a tana dafe kanta da hannun ta.
Numfashi take saukewa a hankali kafin ta tashi jikin ta a sanyaye ta shiga band'aki.

? ? ? A b'angaren Asad tunda ya shiga d'akin yake zaune yana tunanin abinda yake faruwa dashi wanda hakan bai tab'a faruwa ba bai kuma tab'a tunanin zai faru d'in ba, kansa yake ji yana juyawa ya tashi zaune yayi shiru yana tunanin abinda ya faru har hakan ta kasance.? Tunanin yaga bazai yi masa ba ya shiga band'aki sharp-sharp yayi wanka ya fito ya canja kaya ya fita daga d'akin gabad'aya.

Asibiti ya wuce kai tsaye ya kai kansa ya sanar dasu matsalar da ta faru aka shiga yi masa gwaje-gwaje a nan take amma babu wata matsala da aka gani a tare dashi, magani suka bashi wanda zaiyi amfani dashi jikin sa duk a sanyaye ya baro asibitin. Koda ya koma d'aki kawai ya wuce ya kalli agogo yaga dare ya raba yayi alwala ya tayar da sallah kamar kullum.

Ya jima yana ibada har akayi asuba sannan ya nemi waje ya kwanta duk da ba baccin yake ji ba zuciyar sa a cushe take ya rasa tunanin ma da zaiyi gabad'aya damuwa tayi masa yawa zuciyar sa tana bugawa da sauri-sauri.

*&&&*
*Nigeria.*

? ? ? ?? "Hydar ya jikin nasa? Me likitocin suka ce?." Hydar daga can b'angaren yace, "Ranka ya dad'e tunda muka iso aka karb'e shi yanzu haka har yanzu basu fito ba nima jiran su nake." Mai martaba sarki yace, "babu wani bayani da sukayi maka ko kad'an ne?."

Hydar yace, "Babu." Mai martaba yace, "Hydar ina zargin wani abu akan lamarin ciwon nan nasa."
Hydar yace, "kamar me kenan Takawa?."
"Ina zargin da saka hannun wasu a ciwon nan, in ka duba shekaran jiya da daddare lafiyar sa lau har da babar ka sunyi magana dan tana fita ya naje wajan sa yake sanar dani fitar ta. Akwai wani abun da ya faru."

Hydar yace, "haka ne. Baza'a rasa ba dan akwai wanda da dama hukuncin da ya yanke bai musu dad'i ba, to amma Allah yaja da ranka waye ko wace? Me suka aikata lokaci d'aya yayi tasiri haka?."

Mai martaba yayi shiru yana tunanin Hydar ya katse masa tunani yace, "Ko akwai wanda mai martaba yake zargi?."
"Tabbas akwai wad'anda zuciyata take zargi, bana so zargin nawa yayi nisa a kansu ne amma zan fad'ad'a bincike."

Hydar yace, "Allah ya bada iko ya bayyana mana koma su waye suke da hannu a wannan ciwon nasa na farar d'aya."
"Amin Hydar. Ka cigaba da kula dashi zan zo in sha Allah." Daga nan sukayi sallama da Hydar ya kashe wayar.

? ? ? ?? K'arfe shida na safe motar su Mama ta sauka a Tafawa b'alewa international Airport driver da ya kawo su ya juya ita da Suhaima suka shiga cikin Airport suna jiran jirgi domin k'arfe bakwai jirgin su zai d'aga zuwa Cairo. Suna nan zaune aka sanar da zuwan jirgi suka fita suka hau motar da zata kai su bakin jirgi, hankalin Mama bai kwanta ba sai da taji jirgi ya tashi ya lula sama ya d'auki hanyar k'asar Egypt sannan ta sauke ajiyar zuciya mai k'arfi.

Awa biyar da y'an kaine suka kai Mama da Suhaima Cairo suka sauka daga jirgin a lokacin k'arfe d'aya na rana ta take sosai suka shiga mota direct suka nufi Four Seasons hotel ko hotel d'in su basu wuce ba kai tsaye inda Asad yake ta nufa.

? ? ?? A cikin hotel d'in Rauda na zaune a d'aki kamar ko yaushe tana waya da y'an gidan su tana ware kayan da suka siyo a daren jiya tana zubawa a jaka, katse wayar tayi bayan sun gama wayar ta kalli jakar tace, "kai tama yi kad'an ashe." Wata jar doguwar riga ce ta d'auki hankalin ta ta d'auka tana d'agawa sama tace, "rigar nan fa tayi kyau sosai, bara na gwada na gani" ta fad'a tana zame ta jikin ta ta saka jar ta d'aura d'ankwalin irin d'aurin nan mai v ta ta gaba gashin gaban kanta ya fito ta waje.

"Kai amma tayi min kyau sosai" ta fad'a tana sake kallon kanta tana murmushi. Sai kuma ta tsaya cak tana kallon kanta har lokacin tace, "ko ina yake?." Bata da amsa ta jiyo motsi a falon ta bar kayan ta fito daga d'akin tana kallon fallon yana nan yadda yake jiya decoration d'in wajan kamar an sake sabunta shi.

Wajan taga ya kuma burgeta tana nan tsaye taji sautin Camera alamun ana d'aukar ta hoto, juyawa tayi ta kalle shi yana zaune akan kujera da cup d'in lemo a hannun sa yana sha fuskar sa babu walwala amma kuma yana d'aukar ta hoto. Murmushi tayi ta sunkuyar da kai k'asa ya ajjiye kofin ya taso ya k'araso zuwa gare ta ya rik'e hannun ta duka biyun yana jin bugun zuciyar sa a bayyane yace, "you look so beautiful." Murmushi ta kuma yi fuskar sa tana nan yadda take bata canja ba ya d'ago da kanta yana kallon idanun ta kafin ta sake sauke kanta k'asa.

Yana so ya fad'a mata abinda ya same shi amma bai san ta inda zai fara ba domin shi ya gama amince mata bashi da abinda zai b'oye mata a duniya kuma ya kamata ace ta sani amma ya rasa ta inda zai fara cewa ga abinda ya same shi, yayi shiru na wani yana kallonta yana kuma rike da hannunta zoben da ya bata ya sake haska hannun sosai.


Kallon sa tayi tace, "kayi min al?awarin baza ka barni ba ko?." Ta d'ago ta kalle shi nan take taji gaban ta ya fad'i ya d'aga kai alamun eh tace, "dan Allah ka sake maimaitawa ina so na sake tabbatarwa." Numfashi ya sauke yayi shiru na wani lokaci kamar bazai magana ba har lokacin bai cika hannun ta ba sai daga baya yace, "ni Asad bin Nasir bin Sa'ad na yiwa matata Rauda al?awarin bazan tab'a rabuwa da ita ba, duk wahala duk dad'i duk tsanani ina tare da ita" ya fad'a yana lumshe idanun sa a kan fuskar ta.

Rauda ta sunkuyar da kai tana murmushi ta d'ago idanun ta suka ciko da hawaye tace, "Na amince. Amma meyasa nake jin zuciyata tana rawa akan hakan? Sai naji kamar akwai abinda zai faru wanda zai raba ni dakai" ta fad'a k'irjin sa tana kuka tace, "Ina jin tsoro sosai, bana so a raba mu na saba dakai na fara sonka bana so son ya zamar min cuta nan gaba."

Hannu ya saka ya zagayo dashi a jikinta ya rik'e ta sosai yana jin kukanta a k'irjin sa yana bubbuga bayanta a hankali amma baiyi magana ba, sun shima a haka kafin yace, "Ki daina kuka, Asad bazai barki ba kin zama shi ya zama ke babu abinda zai raba ki dashi dan yana sonki. Ki daina kuka bana son jin kina kuka" ya fad'a muryar sa na rawa kansa na ciwo sosai.

D'agowa tayi ta kalle shi ta goge idanunta ya rik'e fuskar ta yana kallon idanunta yace, "Smile." Murmushin tayi duk da akwai hawaye a idanunta shima yayi murmushin yana girgiza mata. "Ya jikin ka?." Ya juya idanu ya kalle ta sai kuma ya kalli gefe ya sake kallon ta sai ya fasa maganar da zai fada ya rik'e hannunta suka je suka zauna.

"Wacce country kike son kije?" Ya fad'a yana kallonta. Ta sake yin dariya tace, "Suna da yawa." Da hannu mata alamun yana ji tace, "Saudia, America, England kai nifa ko ina ma ina so naje, especially Dubai ma kodan na shiga national world Quran competition." Kai ya girgiza jin dad'in abinda take so ta shiga d'in amma baice komai ba.

Kallon kanta yayi yace, "Zaki je saloon anjima kar kanki yayi ciwo" ya fad'a yana kallon gashin kanta da yake a tsefe. Murmushi tayi tana kallon zoben hannunta tace, "tohm." Hannun sa ta kalla babu agogo taga wannan zanen yana nan ta shafa zanen tace, "Ga shaida ta." Murmushi yayi ya kalli zanen ya kalle ta yace, "As my wife bazaki iya gane ni ba sai da sign?." Ta turo baki gaba tace, "Kuna da rikitarwa ne, kace fa Mama ma bata gane ku wani lokacin." Murmushi kawai yayi baice komai ba ya mayar da hankalin sa kan t.v.

Zata kuma magana kenan aka danna door bell hakan ya dakatar da ita daga maganar kafin ya mike ya k'arasa kusa da k'ofar ya cire lock yaja handle d'in k'ofar ya bud'e. Wara idanu waje yayi ganin wanda suke tsaye ido cikin ido yake kallon su zuciyar sa na bugawa fat, fat, fat ya kasa furta komai sai kallo ya kasa furta komai.

"Matsa min na wuce" Mama ta fad'a tana rab'a shi ta shiga ciki Suhaima ta biyo bayan ta. Had'a ido sukayi da Rauda gaban Rauda yayi mugun fad'uwa ta tsorata sosai har tsoron ya bayyana a fuskar ta taja baya tana cigaba da kallon Mama. Mama k'arewa falon kallo take tana girgiza kai gabanta na fad'uwa matuk'a ganin irin adon da yasha irin na gidan larabawa da India ne musamman lokacin da suke cikin nishad'in son kasancewa da iyalan su.

"Mamana!" Asad ya furta with full love emotion yana k'araso da sauri yayi hugging d'in ta very tight. Hugging nasa back tayi tana jin sanyi da kwanciyar hankali na ratsa ta zuciyar ta na dawowa bugu daidai domin tunda Asad ya bar k'asar bata kuma jin zuciyar ta na bugawa daidai ba sai yanzu.

Sakin ta yayi ta kalli face d'in sa tace, "Kar ka damu nazo gare ka tunda kai an hana ka zuwa inda nake" ta fad'a tana kallon Rauda da take wajan a tsaye kamar an dasa ta kanta a sunkuye. Dawo da kallon ta tayi gare shi tace, "Nasan raba mu akayi dakai shiyasa baka nema na bayin kanka bane aikin wannan bak'ar ashanar ne" ta fad'a tana nuna Rauda.

Suhaima da take ta kallon falon tace, "Wow wajan nan ya had'u ya kuma tsaru sosai, Oga Deaf waye yayi planing wajan nan haka?." Kallon Suhaima yayi sai kuma ya kalli Mama gaban sa na fad'uwa matuk'a yaga Mama ta isa kusa da Rauda babu b'ata lokaci ta tsinke ta da mari.

Da hanzari Asad ya k'arasa wajan yana kallon Maman ya kalli Rauda da hannun ta yake kuncin ta hawaye yana sakko mata idanunta a kulle tace, "Y'ar talakawa, mayya mai zubin mayu dangin mayu. Duk irin kashedin da nayi miki akan Asad baki ji ba sai da kika san yadda kikayi kika asirce min shi aka cuce shi aka aura masa ke kuka tawo nan. Gashi nan naga har canjawa kinyi anzo k'asar waje ana cin abinda ake so ke ga mai wayo ko?. Nafi k'arfin dangin ki ma gabad'aya balle ke y'ar k'aramar alhaki." Motsi Rauda batayi ba balle ta amsa hawaye ne yake zuba a idanun ta jikin ta yayi sanyi sosai tana ji a jikinta akwai abinda zai faru a wannan lokacin.

"Kin raba ni dashi baya nema na baya min waya duk a tunanin ki kinyi nasara a kaina har abadah kamar yadda kika ce, to baki isa ba yarinya wanda ya riga ka kwana sai ya riga ka tashi baki isa kiyi nasara a kaina ba daidai da rana d'aya. In ma rik'e masa kurwa kikayi yau zaki sake shi domin banga abin so a jikin ba har da zai maqale miki, kin samu riba ai tunda gashi har kina taka k'afar ki tafiya tayi miki kyau. Anyi aure ban sani ba yanzu kuma na sani za kuma a warware shi."

Asad ta kalla gaban sa ya fad'i ya saukar da ido k'asa zuciyar sa na rawa burin sa kar ta furta abinda zuciyar sa take aiyanawa domin bai san ya zaiyi ba, "Asad!." Jin yadda ta kira shi ya saka ya kalle ta da girmamawa yace, "Mama."
"Wacece ni a wajan ka?." Kansa na k'asa yace, "mahaifiyata."
"Na isa da kai ko a'a?."
"Mamana itace isa da kanta."

Mama tayi murmushi ta kalle shi tace, "umarni nake baka yanzu ba anjima ba ka saki yarinyar nan!." Runtse idanun sa yayi daidai lokacin da zuciyar sa ta buga da k'arfin gaske ya cize bakin sa ya bud'e ido ya kalle ta yaga shi take kallo sai ya sauke ido k'asa ya kasa cewa komai.

Sautin kuka Rauda ya karad'e ko ina a falon kuka take yi sosai zuciyar ta nayi mata zafi ta kasa furta ko wacce kalma sai kuka sabida tashin hankalin da take ciki ba d'an kad'an bane. Mama ta kuma kallon sa tace, "Magana nake maka Asad indai ka d'auke ni matsayin mahaifiyar ka wacce ta haife ka ta raine ka ka sake ta, in kuma kana so ka nuna min ka zab'e ta a kaina bismillah Asad."

Idanun sa sun koma jajaye haka fuskar sa ya d'ago ya kalle ta ya sake mayar da kansa k'asa yace, "Dan Allah Mamaaaaa!." Abinda ya iya furtawa kenan Mama tace, "Wallahil azim sai ka sake ta matuk'ar na isa dakai.
Muryar sa har rawa take yi? har labb'an sa kana ganin yadda suke motsawa yace, "Allah da ya halicce mu shine ya halatta saki amma kuma baya son sa Mama, Mama tana da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login