Showing 15001 words to 18000 words out of 216282 words

Chapter 6 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

jirgin su ya tashi, kan gadon sa ya kalla yaga Passports dinsa dana Rauda babu na iyayen ta bai damu ba ya d'auka ya saka a aljihu a lokacin Hydar ya shigo yana kallon sa yace, "Wow! Ango kayi kyau." Bai iya cewa komai ba Hydar ya d'auki jakar yace, "muje na saka maka a mota, tare ma zamu je in yaso sai na dawo da motar taka gida."

Asad yace, "Ina Aliyu da Suhaima?."
"Suhaima suna Kano da Mama Aliyu kuma kasan yana wajan y'an matan sa yanzu ai ko?."
"Yanzu zan tafi ban yiwa mutanen gidan sallama ba?."
"Haka Abba yace."
Shiru yayi baice komai ba Hydar ya fita ya barshi dan yasna in ya biye masa sai su b'ata lokaci har ayi missing flight.

Kulle d'akin yayi ya zare key d'in ya saka a aljihu yana juyowa Hafiz ya shigo falon yana fad'in, "Asad tafiya ba sallama?." Asad ya kalle shi yace, "urgently ne ban shirya ba." Hafiza yace, "Allah ya dawo da kai lafiya."
"Amin" ya furta yana yin gaba shima yabi bayan sa.

Mota ya shiga Hydar ya shiga mazaunin driver yaja suka fita daga cikin masarautar kewa tana mamaye zuciyar Asad ya juya ya kalli gidan yana ji a jikin sa kamar ya fita kenan har abada. Numfashi ya sauke lokacin da ya daina hango gidan ya lumshe ido yana jin jikin sa wani iri. Hydar ya kalle shi yace, "ya naga kana kallon gidan kamar baza ka dawo ba?." Baice komai ba suka d'auki hanyar gidan su Rauda yana jin sa wani iri kamar bashi ba har suka k'arasa k'ofar gidan suka faka.

Hydar ya kalle shi yace, "muje ciki ko?." Asad kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya fito Hydar ya bud'e bayan motar ya d'auko kujerar kome ya tuna kuma sai ya mayar da ita baya ya kulle boot d'in suka nufi cikin gidan.
Suna zaune dukkan su da alama duka y'an gidan suna nan suka tsaya basu shiga ba sai ga Baba ya fito suka gaisa yayi musu iso zuwa ciki, da sallama suka shiga cikin gidan suka amsa gabad'ayan su Asad shi dai bai kalle su ba ya gaishe su dukkan su suka amsa daga nan yayi shiru baice komai ba.

Hydar yace, "Mama zasu wuce Airport lokacin tashin jirgin su ya kusa kar lokaci ya k'ure." Umma ta sauke numfashi ta kalli Rauda da take zaune cikin doguwar riga ta Abaya mai mayafi cikin kayan da aka siyo mata da Baba ya bada kud'in fuskar ta a cushe baza ka banbance yanayin da take ciki ba lokaci d'aya.

Umma ta kalli Asad da kansa yake k'asa tace, "Amana ce gata zan damk'a maka a hannun ka, na sani kafi k'arfin Rauda ta ko wanne b'angare amma kuma kana naka Allah yana nasa dukkan mu bamu tab'a kawo haka ba ko a mafarki sai gashi ta kasance ana kiran mu matsayin ma'aurata a yanzu. Dan Allah ka duba Allah ka rik'e Rauda hannu biyu kaine ka ganta kace kana sonta a haka kar wata rana ka tuna da asalin ta kayi mata wani abun. gata nan amana ce a hannun ka ka rik'e min ita dakyau dan Allah, kar ka bari wani abun ya same ta."

Yadda Umma tayi magana da sanyi kamar zata zubar da hawaye sai zuciyar sa ta karye nan take yaji anya baiyi kuskuren nuna yana sonta ba duba da irin yanayin gidan da yake?, da ace baice bai furta ba da yanzu ba'a aura masa ita ba, tabbas yasan baza'a k'yale ta ba a yanzu haka baza'a rasa wanda suke neman su ga sun mata wani abun ba kawai dan a raba su. Sai yake ji a zuciyar sa ina ma ya danne bai nuna ba kodan ta zauna lafiya ita da iyayen ta, yanzu in wani abun ya same ta shi ya zaiyi kenan?. A sanyaye ya kalli Umman yace, "Ina sha Allah Mama ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai faru." Maganar sa ta fita kamar koda yaushe a tausashe kuma a k'asa in ba nutsuwa kayi ba baza kaji me yake cewa ba.

Sosai Umma taji dad'in abinda yace tace, "na gode sosai, Allah ya bada ikon rik'e ta ya kawar da duk wani abun k'i a zaman ku na tafiyar da dawowar ku." Da amin Hydar ya amsa shi kam a ciki ya amsa Hydar ya kalli agogon hannun sa yace, "lokaci na tafiya yana dakyau muje."


Tare aka mik'e shida Hydar suka yo gaba kafin su fito ma har sun shiga mota. Yaya Ummi ce take taimakawa Rauda tana tafiya fuskar ta duk ta jik'e da hawaye ta kuma kasa tantance kukan me takeyi, na farin ciki zata samu lafiya ko kuma kukan tausayin kanta take yi. Lokacin da suka isa bakin motar aka bud'e mata bayan motar ta shiga Hydar yace, "Ammmm basai ta shiga dasu ba akwai abinda zatayi amfani dashi in mun fita" ya fad'a yana kallon Yaya Ummi ganin zata saka sandinan a cikin motar.

Yaya Ummi ta kalle ta tace, "Dan Allah ki daina Kuka Rauda kamar baki karb'i k'addara ba?. Da kanki kika cemin kin daina kuka meyasa kuma kikeyi yanzu?, dan Allah ki daina tafiya ce ta d'an lokaci zakuyi zaki dawo gida dan ba tarewa kikayi ba gabad'aya. Kiyi hak'uri ban san me kike ji ba amma nasan da ciwo abinda kike ji shiyasa nace kiyi hak'uri." Kai kawai Rauda ta d'aga bata iya cewa komai ba.

Asad da yake tsaye ya kalli su Baba da murmushi a fuskar sa yace, "Sai mun dawo." Baba ya washe baki yace, "Allah ya kai ku lafiya ya dawo daku lafiya ya bada lafiyar daka je nema." Da amin ya amsa ya bud'e gaban motar ya shiga suka ja motar suka bar k'ofar gidan a daidai wannan lokacin sautin kukan ta ya cika mota.

Shiru motar babu mai magana sai kuka da take yi sosai babu wanda yace mata kanzil dan daman kuka dole tayi shi lokaci d'aya ba tare da ta shirya ba a raba ta da iyayen ta ai dole ta zubar da hawaye. Wayar Asad ce take k'ara duk hankalin sa baya jikin sa kukan da take yi har ta katse bai ji ba aka kuma kira Hydar ya kalle shi yace, "Relax Mr man, ana kiran ka." D'auko wayar yayi ya duba gaban sa ya fad'i ganin sunan Mama yana yawo a kan screen d'in wayar tasa.

Daurewa yayi ya d'auka ya saka a kunne take cewa, "Asad kana ina yanzu?." Shiru yayi kana yace, "Ina hanyar Bauchi zanje airport."
"Airport kayi me a can?." Shiru yayi bai amsa ba ta kuma cewa, "ko Kano zaka zo?." Nan ma bai bata amsa ba sai taja tsaki tace, "Bana son rashin hankali ina yi maka magana kayi min banza, wani lokacin shirun nan naka na iskanci ne in kaso maganar kana yi na lura da hakan."

Ya bud'e baki zaiyi magana tace, "kome kaje yi a airport d'in ka tsaya yanzu jirgin su Jidda zai sauka ka kaisu gida ita da Mum dinta kar kace min kuma wani abun ya tsayar dakai" tana fad'ar hakan ta yanke kiran dan a tunanin ta ba k'asar zai bari ba dan tasan baya barin k'asar sai ta sani. Sauke wayar yayi daga kunnen sa ya kalli Hydar da yake tuk'in sa ya d'auke kai baice komai ba har suka isa airport d'in.

Mintina talatin ya rage jirgin su ya tashi suka fito daga motar Hydar ya fito da jakunnan su ya fito da kujerar ya turawa Asad alamun ya fito da ita, bud'e gefen da take yayi har lokacin kanta na kan cinyoyin ta tana kuka mai sauti, ya kasa mata magana ya kuma kasa tab'a ta balle ta d'ago yayi mata alama ta sakko ya tsaya cak kawai yana kallon ta ya rasa me zaiyi. Hydar ganin yana b'ata lokaci yace, "Asad lokaci yana tafiya fa." Kamar bazai yi ba sai kuma ya mik'a hannu a hankali ya bubbuga kafad'ar ta tana jin sa tayi masa banza dan tayi alqawarin indai bai magana ba wallahi baza ta fito ba.

"Raudaaaaaa!" Ya furta in sweet voice wacce ta ratsa shi kansa balle kuma ita da aka kira sunan nata ba shiri ta d'ago kanta tana kallon sa da idanun ta da suka jik'e sabida hawaye shima kuma ita yake kallo, yamutsa fuska yayi ganin yadda hawaye ya b'ata mata fuska idanun ta sunyi ja da hannu yayi mata alama da ta goge idanun ta ya nuna mata kujarar alamun ta sakko. Bata motsa ba sai kanta da ta mayar k'asa ya matsa sosai kusa da ita ya rik'e hannayen ta duka ya fito da ita ya zaunar da ita da kansa a kan kujerar ya kulle k'ofar motar ya danna madannin tafiya a jikin kujerar ta fara tafiya a hankali shi kuma yana bayan ta Hydar kuma yana jawo musu jakar su.

Kusa dashi Hydar ya koma yana dariya yana fad'in, "Wannan ita ake kira da silent love." Bai kula shi ba har suka shiga ciki aka duba jakar su kamar yadda ake yi suka shiga ciki Hydar ya d'aga musu hannu yana murmushi zuciyar sa cike taf da farin ciki ya juyo.

Wara idanu yayi lokacin da idanun sa ya fad'a kan na Mum da Jidda dukkan su a firgice da alama sunga wucewar Asad da Rauda sai ya basar ya maze ya d'auko izzar da ya ajjiye ya d'orawa zuciyar sa ya kalle su yace, "Mum kece?."

Ta kalle shi tace, "Hydar wa nake gani kamar Asad?." Hydar yaja fasali kana yace, "shine." Jidda tace, "Ina waje? Kuma kamar shida wata nake gani wacce ita?." Hydar ya k'are mata kallo kana ya tab'e bakin sa yace, "ki tambaye shi" yana fad'ar hakan ya fita daga wajan ya barsu da tunanin wacece da kuma inda Asad zaije bayan Mama ta sanar dasu shine zai zo ya d'auke su.
Ina yaje? Shida wace suka gani sun tafi....?. Babu mai basu amsa dole Mum tayi k'wafa suka fito suka tafi.

Asad kuwa suna wucewa basu tsaya ba daman jirgin su yana k'asa motar da zata kai su ga inda jirgin yake suka suka ba jimawa sai gasu a inda jirgin yake, fitowa yayi ya fito da ita daman jakar su an auna ta sai sun je waccan garin zasu d'auke ta suna tafiya a hankali har suka isa steps na jirgin, kallon ta yayi yaga kamar a tsorace take sai ya rik'e hannun ta guda ya matsa ta d'ago ta kalle shi ba tare da yayi magana ba ya girgiza mata kai kawai ya saki hannu ganin mara lafiya ce kujerar ta baza ta hau ta steps ba sai aka nufi d'aya k'ofar da ita ta hau kai har cikin jirgi.

Rauda duk ta rud'e ta gigice a tsorace take matuk'a ji take kamar ta saki fitsarin wando sabida tsoro, yana zaune kusa da ita yana kallon yanayin fuskar ta sai yayi murmushi haka kawai yake jin nishad'i ya rik'e hannun ta guda d'aya kamar d'azu itama sai tak'i kallon sa taushin hannun sa na ratsa ta amma ta jure bata kalle shi ba har aka sanar da tashin jirgi.

Ihuuu da jirgi ya fara alamun tashi yaga ta runtse ido ta kwace hannun ta toshe kunnen ta da sauri ya d'auki abinda aka tanada dan toshe kunne ya saka mata sai taji bata jin k'arar sosai ta kalle shi taga ba ita yake kallo ba a lokacin jirgi ya fara gudu a k'asa kafin ya d'aga ya lula sararin samaniya.
Tashin da yayi tayi gefe ta fad'a kafad'ar sa ya rik'e ta a haka bai sake ta ba har sai da ya tabbatar sunyi nisa a sama sannan ya cika ta ta koma ta zauna tana raba idanu tana kuma hawaye har lokaci.

A bangaren su Mum ko ta kan Hydar basu bi ba drop d'in mota suka d'auka zuwa katagum jikin Mum har rawa yake burin ta ta isa gida ta kira Mama taji ina Asad ya tafi sannan shida wa suka tafi. Tun a compound na gidan take mata waya bata d'auka ba har ta hau saman gidan ta sai a sannan Mama ta d'auka tana fad'in, "Sadiya kin san ina cikin jama'a." Mum tace, "abu ne na gaggawa Fulani shiyasa na dame ki da waya, ina Asad ya tafi na ganshi a airport a b'angaren international alamun k'asar zai bari? Sannan wacece wacce na gansu tare da ita?."

Mama tace, "What! Asad da wata kuma sun bar k'asar nan? Anya kuwa shine?."
"Shine mana bayan Hydar na gani shine ya kawo shi Airport d'in ma kuma na ganshi shima ya ganni."
"Sadiya relax babu inda Asad zaije ba tare da ya fad'a min ba, sannan kuma wacece zaiyi tafiya da ita?, sai dai in Aliyu kuka gani amma ba Asad ba."

Mum tayi shiru tana girgiza kanta cikin amincewa da maganar Mama tabbas Aliyu ta gani da wata budurwar tasa ba Asad ba Hydar ya raina mata hankali ne kawai, ajiyar zuciya tayi tace, "Haka ne fa kuma Fulani; duk na tsorata ne wallahi kar naje ko Asad d'in ne har wad'an can talakawan sun fara canja masa tunani yana yin abu baki sani ba."

Mama tayi dariya tace, "K'arya su tasha k'arya, ai nafi k'arfin su wallahi tunda na yanke alaqar nan dake tsakanin su ta riga ta yanku, tunda nace a bari nasan an bari, tunda nace bana so nasan shima yanzu baya so. Ta ko wanne b'angare na mamaye ko ina ko kara na ajiiye Asad bai isa ya tsallaka ba sai na bada umarnin hakan, zancen waccan y'ar talakawan ai ki d'auka ya zama tsohon labari."

Mum tace, "An gama ranki ya dad'e, mayi magana anjima ki huta lafiya" ta fad'a tana yanke wayar ta bita da kallo a bayyane tace, "Saura lokaci kad'an ya dawo a bayan hannun ki ba tafin hannun ki ba, in na fara sarrafa Asad baki isa ya saurare ki ba daga ni sai Jidda kawai zai dinga gani. Hmmmmm Rabi'atu kenan sai kin yabawa aya zak'in ta zumud'in zama uwar sarki zai bar zuciyar ki domin a zahiri zaki zama uwar sarki a bad'ini kuma nice uwar sarkin domin komai sai abinda nace za'ayi, zan nuna miki a wannan fannin na dame ki na shanye wallahi sai Jidda ta zamar miki ciwon ido a cikin gidan nan. ki kiyayi had'uwar mu" ta fad'a da murmushi tana kallon wayar ta kamar da Maman take magana.....


*Nikam nace kun makara* @&?=??
[17/12, 10:39 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*032.*

*Four Seasons hotel Cairo.*

D'aya daga cikin manyan hotels d'in da ake ji dasu kenan dake cikin birnin Cairo wato babban birinin dake cikin k'asar Egypt kenan suka sauka, duk da kasancewar dare yayi amma haske tarrr ko ina kamar rana fitulu sun haske ko ina baza kace dare bane sai ka kalli sararin samaniya. Babban falo ne guda d'aya mai d'auke da d'aki guda biyu manya babu abinda babu a cikin su girman su kuwa ba'a cewa komai.

Tunda suka shiga falon take wara ido take kallon falon dan bata tab'a ganin irin sa ba a rayuwar ta gabad'aya shiyasa take kalla kodan ta kashe kwarkwatar idanun ta, yayi kyau komai na cikin blue hatta carpet da komai na cikin sa blue ne. Asad zama yayi a gefen kujerar dake d'aya daga cikin kujerun wajan ya shafa aljihun sa yana neman wayar sa amma yaji babu ita, ya mik'e tsaye yana duba jikin amma babu wayar sa a jikin sa.

Dafe kansa yayi ya kalli Rauda da take k'arewa falon kallo har lokacin yaga wayar ta akan cinyar ta ba tare da yace komai ba ya d'auki wayar sai a lokacin ta kalle shi amma ba ita yake kallo ba ya danna number sa ya kira, a kashe yake jin sim card d'in nasa yaja k'aramin tsaki ya ajjiye wayar tata ya kama k'ugu ya rik'e yana kallon wani wajan daban dan yasan ya yar da wayar a wani wajan. Juyowa yayi ya kalle ta suka had'a ido ta d'auke kanta baice komai ba yaja jakar ta zuwa d'aki guda d'aya ya ajjiye yana fitowa ya nuna mata d'akin da hannu baice komai ba ya fita da sauri.

Da kallo ta bishi ta sauke ajiyar tace, "Allah gani gare ka, ka kawo min d'auki da gaggawa" ta fad'a tana danna inda ya danna d'azu kujerar ta fara tafiya da yake ba tudu har tazo k'ofar d'akin, tsayawa tayi tana kallon kanta a k'aton mudubin da yake dogo tayi murmushi a bayyane tace, "Rauda a Cairo." shiga d'akin tayi lafiya wani abun bai tokare ta ba.

"kan bala'i" ta furta ganin d'akin har yafi falon ma kyau ta bishi da kallo babu abinda ya d'auki hankalin ta sai wata taga ta glass doguwa wacce kake hango titi motoci suna ta wucewa ko kana zaune basai ka tashi ba. Kallon d'akin take tana tafiya a hankali har ta isa wata k'ofa da take tunanin band'aki ce ta bud'e girman sa dakyaun band'akin ta shagala da kallo kafin ta samu damar cire kayan jikin ta tayi wanka.

Tana iya tsayawa da k'afa d'aya hakan ya saka a tsaye tayi wankan da k'afa guda d'aya sai dq ta gama taga towels da yawa a ma'ajiyar su sai khamshi suke yi ta d'auki d'aya ta d'aura tana fad'in, "Wai nima irin y'ar gayun nan, ikon Allah kenan Rauda ce yau a wata k'asar daba Nigeria ba."

Zama tayi akan kujerar tata ta fito ta koma bakin gado ta sauka akan kujerar ta zauna gefen gado ta bud'e jakar ta tana dubawa, dogayen riguna masu mayafi da riga da wando shi Yaya Ummi ta zuba mata a ciki sai na bacci doguwa guda biyu sai k'ananu sauran, ta d'auki doguwar ta saka ta saka turare mai khamshi ta hau kam kujerar tana kallon d'akin da tunanin ko ina ne alqibla, wata takarda ta gani da take nuna gabas ta juya kujerar ta tayar da sallar magariba da i'sha.

K'asaru tayi bayan ta idar taji bacci na k'okarin kama ta ga kuma yunwar da take ji a cikin ta, agogo ta kalla na d'akin taga k'arfe d'aya na dare tayi hamma ta koma kan gadon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login