Showing 174001 words to 177000 words out of 216282 words

Chapter 59 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

tuna abubuwan da Hydar ya nufa a kaina sai naji da ina da iko dana goge su" yayi shiru alamun yana so ya d'an huta ne kafin ya cigaba da cewa, "Ina ganin kamar wasa duk abinda suka faru Hydar ne ya shirya sai naji zuciyata tana rawa Abba, bazan iya yiwa Hydar ko wanne hukunci ba a ganina a barshi shima Allah zaiji dashi kamar yadda yaji da Aliyu" ya k'arasa fad'a a sanyaye idanun sa yana cikowa da kwallah.

Tausayin sa ya kama Mai martaba ya d'ora hannun sa a kansa yace, "Zuciyar ka mai kyau ce Asad, shiyasa nake farin ciki da katagum ta mallaki shugaba kamar ka. Kayi hak'uri k'addarar ke kenan y'an uwan ka da kuma babar ka sune k'addarar ka kayi addu'a Allah ya kawo k'arshen wannan k'addarar domin ka samu sauk'i a zuciyar ka. Nasan kana son Hydar shi kuma yayi amfani da son da kake masa ya cutar dakai, har gwara Aliyu daman kowa yasan ba shiri kuke ba amma Hydar naka ne, kayi ha?uri ka fuskanci abinda yake gaban ka domin Hydar bai kyale ka ba."

Hawayen idon sa ya mayar ya danne zuciyar sa yak'i bari yayi kukan yace, "Haka ne Abba. In sha Allah zanyi abinda akace bazan bari tasirin wannan ya hanani gabatar da abinda yake gabana ba. Duk da ina jin tsoro mulki ya sake barin zuciyata, Allah ya k'ara maka lafiya ina ganin kamar mulkin nan zai kawo k'arshen rayuwata ne, bama kaina nake ji ba ina jin Muwadda zasu iya cutar da ita sabida ni" ya fad'a a sanyaye kansa yana k'asa.

Jin sunan da ya kira yasan Rauda yake nufi sai yayi murmushi yace, "Dukkan ku babu abinda zai same ku in sha Allah. Zata dawo gidan nan kwanaki kad'an masu zuwa babu abinda zai faru da kai ko ina da izinin Allah komai ya k'are. Babban tashin hankalina in maganar nan ta baza gidan nan ban san ya abin zai kasance ba. D'ana Aliyu yayi zina da matar aure ya zauna da ita tamkar matar sa, d'ana Aliyu ya had'a kai da maqiya domin ganin bayan mahaifin sa da d'an uwan sa, d'ana Aliyu yayi abubuwa da yawa wanda basu da dad'in ji balle dad'in saurare. D'ana Hydar yaso kashe ni da d'an uwan sa, ya aikata abubuwa masu muni, ya mutane zasu kalli wannan?."

Asad yayi shiru zuciyar sa babu dad'i sosai ya lumshe ido ya bud'e yaji Mai martaba yana cewa, "Amma baza'a bar Hydar ba yayi ta'asar da yaga dama ba, kuma in aka kyale shi yaci banza kenan, in za'a kyale kowa baza'a k'yale Hydar ba dole ayi maganin sa domin har yanzu babu nadama a tare dashi. Shi kuma Aliyu za'a yi masa ma???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?gani in sha Allah duk sihirin da yake cikin sa zai warware."

Asad yayi shiru mai martaba ya kalle shi yace, "Soyayyar da mahaifiyar ka take yi maka itace ta jawo maka tsana a wajan y'an uwan ka." Asad ya girgiza kai yace, "Allah ya k'ara maka lafiya Mama tafi son Hydar a kaina, tana son Hydar matuk'a shiyasa abinda ake fad'a ya saka ta suma. Burin ta take so na cika mata amma bawai tafi sona bane."

Mai martaba yace, "Kuma ka kasance mai biyayya shiyasa take tauye ka a koda yaushe, bata duba abubuwan da ka bari sabida ita burinta kawai kayi abinda take so."

Mai martaba ya mik'e tsaye shima dole ya mik'e yana binsa a baya Mai martaba yana cewa, "kaje duba maman naka in ka dawo kazo dai ina neman ka." Ya amsa da girmamawa Mai martaba ya tafi shi kuma ya koma da baya dan ya shirya.

Shigar buzaye yayi riga da wando da babar riga ya nad'a rawani kalar kayan ya fito ya sauka k'asa nan ya tarar da masu zaman jiran sa ciki harda Suhail ya bada umarnin mota biyu kawai yake so banda kuma jiniya haka akayi kuwa ya shiga mota suka nufi asibitin.

Lokacin da suk shiga d'akin Suhaima na zaune hannun ta da canular ta dafe kanta, sallamar da akayi ya saka ta d'ago suna had'a ido dashi ta taso a guje ta fad'a jikin sa ta rik'e shi gam sai ta fashe da kuka. Kallon Suhail yayi da yake gefen sa ya kalli Suhaima zuciyar sa ta karye ya saka hannun sa a bayan ta ya bubbuga kad'an yace, "Ki daina kuka Suhaima."

Ta d'ago ta kalle shi tace, "Mama Yaya Asad, har yanzu bata farka ba ko motsi batayi. Babu kai babu Yaya Aliyu babu Yaya Hydar a kusa da ita,in ta farka taga haka zuciyar ta bazata yi mata dad'i ba." Yadda take kuka sosai ya saka shi ya rik'e kafad'ar ta yace, "calm down Suhaima! Babu abinda zai samu Mama Ina tare da ita a ko ina, relax please" ya fad'a yana wuce ta ya k'arasa gaban gadon Mama yana kallon ta.

Gani yayi gabad'aya ta canja kamar ba ita ba ya rik'e hannun ta da babu ruwa a jiki ya zauna a gefe yace, "I'm sorry Mama." Likita ne ya shigo ganin Asad ya saka ya k'araso yana fad'in, "Barka da zuwa ranka ya dad'e." Asad ya kalle shi yace, "Me yake damun Mama?."

Ya kalli Mama yace, "jinin tane ya hau sosai har yanzu bai sauka ba, sannan zuciyarta na bugawa sosai har bugun yayi yawa har yanzu bai daidaita ba hakan kuma matsala ne ga zuciyarta. Akwai firgici sosai a tare da ita shiyasa dole aka yi mata allurar bacci dan ta samu hutu" ya nuna Suhaima yace, "Itama sai da aka bata magani dan ta firgita sosai sai da tayi bacci ta samu lafiya."

Asad ya girgiza kai yace, "in aka fita da ita outside country fa?."
"Ranka ya dad'e ban tari numfashin ka ba, amma duk inda akaje hutu zasu bata dan shi take buk'ata a halin yanzu."
Asad ya girgiza kansa yana kallon Mama da take bacci ya kalli Suhaima yace, "Zauna." Ba musu ta zauna Dr yace, "tak'i zama yadda ya kamata, tana buk'atar hutu itama sosai amma tak'i zama ta huta d'in." Asad ya kalle ta alamun meyasa hawaye ya zubo mata tace, "Bazan iya kwanciya na huta Mmaa tana cikin wannan yanayin ba, zuciyata bugawa take in na tuna abinda aka fad'a d'azu akan Yaya Hydar da Yaya Aliyu. Bazan iya jurewa ba" ta fad'a tana fashewa da kuka.

Likitan ya fita Asad ya rik'e hannun Suhaima duka biyun yace, "Ki daina kuka ki kwantar da hankalin ki komai zai wuce." Kai ta d'aga yace, "wipe your tears." Ba musu ta goge hawayen ta yayi murmushi dan shi yaga k'okarin tama in shine a matsayin ta gani yake sai ya suma sau goma.

Suhail ya kalle shi yace, "Ranka ya dad'e sai nake ganin kamar akwai matsala barin Mama ta kwana da Suhaima tunda dukkan su babu lafiya." Asad ya girgiza kai dan tabbas gaskiya ya fad'a amma bai amince da kowa ba balle ya d'auko hadima d'aya ta zauna dasu, ga y'an uwan Mama duka a nesa balle ya nemi wata a cikin su.

Suhaima ta kalle shi tace, "Babu abinda zai faru zan iya." Asad ya kalle ta yace, "kin tabbatar?." Kai ta d'aga alamun eh yace, "duk abinda ya faru ki kira ni." Ta amsa da to shi kuma ya yi waya aka kawo security mata da maza wanda zasu kula da Maman ya yiwa Mama addu'a suka fita zuciyar sa duk babu dad'i musamman halin da ya tarar da Maman a ciki.

Tunda ya shiga mota ya dafe kansa baya ganin inda suke nufa kawai yayi shiru zuciyar sa na sake hargitsewa in ya tuna abubuwan da suka faru sai yaji kamar ya d'auki bindiga ya harbe kansa, yadda yaga Mama ya sake dagula masa lissafi kuka kawai yake son yi amma babu dama.

Tsayawa yaji anyi duk da hakan bai d'ago ba sai ji yayi Suhail yana fad'in, "Allah yaja da ranka Hydar ne ya tare hanyar." Jin hakan ya saka Asad d'ago kai ya kalli kan titin duk da baya ganowa sosai amma yaga mutum a tsaye ya tare musu hanya. Suhail yace, "Ranka ya dad'e zan ji dashi."

Asad yace, "K'yale shi yazo." Suhail ya tsorota yace, "Amma ranka ya dad'e....." ya d'aga masa hannu dole yayi shiru ya fita yaje inda Hydar yake sai gashi ya tako yazo inda Asad yake zaune ya bud'e motar ya shiga ya zauna kusa da Asad d'in shi kuma ya bada umarnin kowa ya basu waje sannan ya kalli Hydar?shi kuma yace, "Kasan sai ana neman izinin ganin ku, ranka ya dad'e" ya fad'a yana yiwa Asad jinjina yana kallon sa ido cikin ido.

Kallon sa Asad yake yi shima haka sai Hydar yayi dariya kad'an yace, "oga deaf." Asad ya basar ya b'oye raunin kan fuskar sa yace, "me yake tafe dakai?." Hydar ya wara hannayen sa yace, "kashe ka." Asad ya murmusa yace, "gani gaka." Hydar yace, "Ina so kisan ya zama na musamman ne gaskiya, kamar yadda nida kai muke na musmaman ko a gidan mu haka nake so komai ya kasance."

"Gani gaka duk abinda kake so zaka iya." Hydar ya kalli Asad yace, "Ina sonka har gobe Deaf amma nafi son kujerar katagum a kanka, naga yanzu ai ka koyo magana ba kamar da ba" ya fad'a yana dariya sai ya kuma cewa, "banfa yi niyar kashe ka bane tun farko da ba maganar ake yi yanzu ba, to lamarin ne naga sai an had'a da kisan sannan za'ayi nasara. Wannan matar taka ma cikin jikinta yana da kyau ace babu shi dan bana so ka bar baya."

Asad ya kalle shi sai ya kyalkyale da dariya yace, "Har face d'in ka ta canja na ambato Muwadda a lamarina, karka damu cikin tane kawai bana so ba ita ba kar ka manta nine na bada support d'in auren ta bazan mata komai ba."

Asad ya kalle shi yace, "Babban kuskuren da zakayi a duniya shine tab'a ta ko abinda yake jikin ta." Hydar ya girgiza kai yace, "Woww! Deaf fa ya koma mai magana yanzu ta dole ya koma Aliyu" sai kuma ya d'aure fuska yace, "In na tab'a ta d'in akwai abinda za'ayi min ne?."

Asad ya jingina sosai da kujera yace, "Baka sanin abinda zai faru sai ka aikata abinda aka hane ka." Hydar yace, "Zan kuwa so naga abinda zai faru gaskiya dan haka zan aikata kodan na gani d'in, kai kasan ni akwai son rigima. amma fa sai na fara kashe ka sai na koma kan d'anka daman na hannun jidda ba naka bane bani da damuwa da wannan" ya fad'a yana zaro bindiga daga aljinun sa ya saita ta ya kalli Asad sai ya sake fashewa da dariya yace, "Deaf nawa, ina ji da kai har yanzu, kayi hak'uri wannan zata ratsa zuciyar ka ta fasa k'aunar Rauda ta fito daga ciki ta tsiyaye a k'asa tabi rariya."

Asad yayi murmushi mai kyau ya gyara zaman sa yace, "Go ahead Hydar, kashe ni in zaka iya."
"Me zai hana na iya? Indai akan kujerar katagum ne zan iya yin komai."
"Bismillah!."
Hydar ya saita bindiga a daidai zuciyar Asad yace, "silences gun ce babu wanda zai san ka mutu dan ba k'ara zasu ji ba. Ka fad'i abinda kake so na fad'awa Muwadda kafin ka mutu ina so nayi mata baban albishir."

Asad baiyi magana ba bai motsa ba kallon sa yake yi ganin hakan ya saka Hydar yaja kunamar bindigar yace, "Baka da abin cewa kenan Oga deaf? Say goodbye" ya fad'a yana? dariyar mugunta tare da harba bindigar.

#NanaHaleema
#FitattuBiyar
[17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*084.*

? ? ? ? Kallon idon Asad yayi sai kuma ya kyalkyale da dariya ya jiya bindigar a hannun sa yace, "Relax our king babu bullet a cikin bindigar, taya zan kashe ka Abba yana raye? Ai kamar na kashe maciji ne ban sare kai ba. Sai na gama da Abba na gama da babyn cikin Rauda then sai na dawo kanka" ya fad'a yana kallon bindigar yana dariya.

Asad yayi murmushi shima ya kalli taga kafin ya dawo da kallon sa ga Hydar yace, "Hydar babu abinda zaka iya yi min, wani nawa ma baza ka iya yi mashi komai ba balle ni." Hydar ya sake yin dariya yana girgiza kai yace, "Asad d'in Mama, babu dalilin da zai saka na kasa ganin bayan ka, burina shine na d'auki ran kowa ciki harda naka ran" ya fad'a yana kallon sa.

Asad baiyi magana ba Hydar yace, "Ya jikin Mama? In ta farka kace ina gaishe ta ka kuma sanar da ita ina kan cika burin ta ne dan naga kai babu abinda zaka iya" ya fad'a yana kallon idanun sa. Kallon sa shima yake yi Hydar ya d'aga riga ya sake yin dariya yace, "Asad nasan kana jin Hydar a zuciyar ka" ya dafa kafaWarsa yana bubbuga ta yace, "Hydar ina son Asad amma kuma yafi son mulki a kanka."

"Lokacin da na dawo Nigeria zan yi swapping sim card me ka bani abinci naci?" Asad ya tambaya yana kallon sa. Dariya Hydar ya sake yi yana tafa hannu kana yace, "Y'ar dabara ce irin tamu ta k'ananun yara ba wani abun bane ba" ya fad'a yana kallon sa har lokacin fuskar sa da murmushi.

Asad baiyi magana ba Hydar yace, "kana da yarda da yawa shiyasa a ko yaushe ake cutar dakai, nasan tun a Germany ka gano ni musamman lokacin da ka dage akan a kai Abba India nak'i tun a sannan nasan ka saka min question mark baka nuna min bane ba amma kar ka manta harara Asad yayi nasan me yake nufi, shiyasa tun a lokacin nayi maganin ka."

Ya sake kallon Asad d'in suka had'a ido sai ya d'an yi k'aramin tsaki yana runtse ido yace, "idon ka yana saka ni jin wani iri a jikina ka daina kallona haka bafa sata nayi maka ba."? Kafin Asad yayi magana ya kuma cewa, "in kuma ba haka ba a juya akalar auren ka da Rauda ya dawo kaina, cikin sauk'i zan raba ku na aure ta daman can tawa ce. Kaga sai ayi 2_0 Aliyu ya rik'e Jidda ni har da albarka an samu ni kuma na rik'e Rauda" ya fad'a yana d'agowa ya kalle shi.

Asad ya lura so yake ya hasala shi ransa ya b'aci sai yayi murmushi yace, "Hydar!." Hydar ma yayi murmushi yace, "Asad! Sai fa kayi ha?uri na shirya wasu abubuwan da yawa za'a rasa rai za kuma a rasa lafiya. Tabbaci nake baka akan cikin jikin matar ka sai ya zama babu shi dan in zan k'yale komai bazan k'yale cikin ba, ka shammace ni ban san za'ayi ciki da sauri haka ba dan ban bari an zo wajan ba. Duk d'auka nake har yanzu abin sautin ya daina d'aukar sauti ashe ya gyaru har amo yake fitarwa ba iya sauti ba" ya fad'a yana kallon sa shima shi yake kallo.

Hydar yace, "Ashe sitiyarin motar ya dawo da aiki yadda ya kamata na d'auka tunda Mama ta lalata shi bai dawo daidai ba ashe nine nake haukan banza tunda gashi harda ciki."

Asad ya sau ke numfashi yace, "Ko a mafarki kar ka d'auka wannan abinda kake fad'a zai kasance." Hydar ya hard'e hannu a k'irji yace, "to muyi deal mana, in na zubar da cikin ta me zaka bani? Ni kuma indai ban zubar da cikin ba ka saka a kashe ni."? Asad yace, "bani da lokacin da zan tsaya yin deal dakai Hydar, bana da lokacin da zan saurari shirmen ka mai kama da tatsuniya. In kayi nasara a kaina a kwanakin baya tabbas yanzu ni zanyi nasara a kanka."

Hydar ya murmusa yace, "Kana nan yadda na sanka confidence d'inka yana nan, to in ban tabbatar da shirina a kanka ba ai ba sunana AliyuHydar ba." Asad yace, "fitar min a mota." Hydar yace, "Daga na ambaci Rauda sai a kore ni daga mota? Ayi ha?uri tuba nake ranka ya dad'e ba wani abun nace zanyi da ita ba ai" ya fad'a yana yi masa jinjina kafin ya sake kyalkyalewa da dariya yace, "Zan fita Asad koda baka ce ba, amma ina so kasan zan dawo gare ka bazaka tab'a zama lafiya ba matuk'ar ina raye sai na raba ka da komai da ka mallaka ni na mallake shi ciki kuma harda matar ka da kake so. Zamu had'e nan bada jimawa ba, ina nan zuwa gare ka" yana gama fad'ar hakan ya fita daga motar ya shiga tasa motar yaja a guje.

A lokacin escorts d'in sa da Suhail suka dawo Suhail ya shiga motar uana fad'in, "Ranka ya dad'e fatan komai lafiya? Naga bindinga a hannun sa." Asad ya masa alama da su tafi kawai driver yaja motar kai tsaye gida suka wuce.

Shiru Asad yayi suna tafiya tunani yake yi ta ko ina Hydar ya gama gano lagon sa, ta ko wanne b'angare ya karance shi sosai shiyasa cutar dashi bazai yi wahala ba. Tambayar da yake yiwa kansa itace anya Hydar zai iya kashe shi? Yasan har yanzu Hydar yana sonsa anya zai iya kashe shi?. Bai gama nemo amsar tambayar ba suka iso cikin gidan kai tsaye b'angaren sa ya wuce.
Suhail yana bayan sa bayan sun shiga falon yace, "Suhail a tabbatar an sake k'ara tsaro a kaf gidan nan, inda babu camera ina so a saka" ya fad'a yana dafe kansa.

Suhail yace, "An gama ranka ya dad'e. Allah yaja zamanin ka Fulani Hajiya ce take neman izinin ganin ka." Asad ya sauke numfashi a wahale yace, "Suhail bana jin zan iya ganin kowa. Suhail na gaji sosai."
"To ranka ya dad'e sai a sanar da ita" ya fad'a yana juyawa zai koma.

"Tazo" ya fad'a a hankali Suhail ya amsa ya fita. Zama yayi a kan kujerar da take mallakin sa ba jimawa Hajiya ta shigo da kaf y'ay'anta mata da namiji ganin hakan sai ya mik'e tsaye suka k'araso yace, "Hajiya da an sanar dani da nazo da kaina."

Hajiya tace, "Mune ya kamata muzo da kan mu ranka ya dad'e." Zama yayi ya nuna musu waje su zauna duk suka zauna Hajiya tace, "Ranka ya dad'e nazo da kaina ne neman afuwa akan abubuwwan da suka faru a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login