Showing 24001 words to 27000 words out of 216282 words

Chapter 9 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

siyi waya ba, da ya siya ai gwara ya ajjiye kud'in yana kallon su." Umma tayi tsaki kad'an tace, "In ya siya sai ki kwace." Rauda tace, "Ina k'annena suke Umma?."
"Yanzu basa nan da sun dawo anjima sai ku gaisa."
"Toh shikenan Ummana, nayi kewar ku wallahi sosai."
"Muma munyi Rauda, Allah ya baki lafiya. A cigaba da biyayya banda rashin kunya Rauda banda tsiwa nasan halin ki."

"Umma wai wa zan yiwa rashin kunyar?, Tabd'ijam wannan mutumin ba sai naga fuskar yi masa bama, kofa magana baya min sai yaga dama shima sau d'aya kawai in yace ya jikin ki basai sake cewa komai ba" ta fad'a bayan ta gwada muryar sa tana yamutsa fuska zuciyar ta na karyewa kamar zatayi kuka.

Umma tace, "kina addu'ar dana fad'a miki? Duk da nasan ki bakya wasa da addu'a amma dai ki dage."
"Ina yi sosai Umma" ta fad'a murya na rawa."
"To meye kuma na kukan bayan alqwarin da kika yi min kin daina? Haba kodai daman alqawarin bai kai zuciya ba?." Ido Rauda ta goge bata ce komai umma tace,
"Kuma kina jin komai na barin zuciyar ki?."
"Eh Umma."

Umma tace, "to ki dage nan gaba sai dai ki bada labari. Baki ga abinda ya aiko mana dasu ba ga ginin gidan mu an kusa gamawa baki ga ginin da akayi ba kamar ba'a unguwar ba, bamu da bakin gode masa ai sai addu'a ko iya haka aka tsaya, balle shi da yaga jinin mu yace yana so duk da tazarar da take tsakanin mu dashi, dan Allah Rauda ki cigaba da hak'uri."

Rauda tayi murmushi bata ce komai ba kafin Umma tace, "ke ni na gaji sai anjima" ta Fad'a tana k'okarin yanke wayar da sauri Rauda tace, "Ina kewar ki Ummana, a gaida min dasu Khalil ace ina kewar su sosai, in Yaya Ummi tazo suyi min magana ta Whatsapp mu gaisa dasu."

Da to Umma ta amsa ganin Raudan ta fara hawaye sai ta kashe wayar itama ta ajjiye wayar a k'irjin ta ta jingina da bango ta lumshe idanun ta cikin kewar y'an gidan su da k'aunar iyayen ta.

Asad da yake jin ta duk abinda take yi yana kallon ta jin yadda take ta magana a kansa ta bashi dariya, wai baya magana daga ya jiki shikenan lallai da gaske ya jikin nan tana bata haushi. Murmushi yayi ya shafa kansa sosai ta bashi nishad'i da farin ciki sosai a zuciyar sa musamman in ya tuna yadda take kwaiwayon muryar sa sai ya sake yin dariya yana kallon ta dan yaga alama ta manta dashi a wajan shiyasa ta saki baki.

"Waya ta" ya furta a hankali yana mik'a mata hannu. Da sauri yaga ta firgita tana kallon sa ta wara idanun ta alamun ta tuna da b'aranb'aramar da tayi kunya ta kamata ta kasa koda motsi ta d'auke kai daga kansa ba kuma ta bashi wayar ba, godiya take yiwa Allah da yasa bata furta bata son sa gaban idanun sa. Ganin hakan sai ya matsa daf da ita sosai har tana jin numfashi sa da khamshin turaren sa ya kai hannu k'irjin ta inda wayar take yana kallon ta yana sake matsar da hannun sa zuwa jikin ta.
[17/12, 10:39 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*034.*

Hannu ya saka ya d'auki wayar sa a k'irjin ta yaja baya kamar bashi ba ya koma danna wayar sa hankali a kwance kamar ma bashi ne ya kalle ta ba, kunya ta da lullub'e Rauda tunawa da sakin bakin da tayi ta manta shaf yana zaune gefen ta sai ta kasa d'ago kai balle ta iya kallon sa. Bai kalle ta ba ya mik'e tsaye yace, "Byeee" abinda ya furta kenan ya d'aga k'afa da niyar fita sai kuma ya dawo da baya ya dawo kanta ya tsaya yana kallon fuskar ta da take a duk'e ya matso kusa da ita ya sunkuya a goshin ta ya sakar mata lafiyayyen kiss kafin?ya kai ga d'agowa aka shigo d'akin.

Muhibba da ta shigo taga abinda akayi amma bata kawo komai ba dan tasan Sister d'insa ce da yayi mata kiss a goshi ba komai bane ya d'ago ya sake tamke fuskar sa ta kalle shi da murmushi tace, "Morning Prince." In ya kalle ta ma ta gode Allah ya kalli Rauda suka had'a ido tayi saurin d'auke kanta ya fita ba tare da ya sake cewa komai ba. Muhibba ta bishi da kallo tana lumshe idanun ta Allah ya sani yana burge ta sosai jan ajin sa yana d'aya daga cikin abinda yaja hankalin ta gare shi.

Rauda ta kalla tayi mata murmushi tace, "ya jikin ki?." Rauda ta kalle ta tace, "Da sauk'i." Daga haka bata ce komai ba ta juya ta fita Rauda ta bita da kallon mamaki kafin ta tab'e baki ta saka hannu ta shafa saman goshin ta har lokacin tana jin sanyin lips d'in ta a kai sai abin ya bata dariya.

*Nigeria*
*3:00pm.*

A wannan lokacin jirgin Asad ya sauka a Nigeria yana fitowa ya samu Hydar yana jiran sa ya k'araso ya shiga motar yana duba wayar sa, Hydar ya kafa masa ido yana kallon sa har ya tsargu ya kalle shi yayi masa alama da lafiya sai Hydar yace, "gani nayi kayi kyau kwana biyu kawai ga wani annuri akan fuskar ka."
"Mtswww!" Shine abinda Asad ya furta kawai Hydar yayi dariya yaja motar bai tsaya a ko ina ba sai a mtn office.

Suka shiga ciki shida Hydar direct wajan manager da suka wuce emergency akayi masa swapping na layin sa ko cikkaken mintina ashirin basuyi ba suka fito, zai shiga mota kenan yaji ance, "Prince Asad." Cize baki yayi ya dafe kai baiso a gan shi ba ya juyo a hankali ganin wacece takaicin sa ya k'aru sai ta saki murmushi tace, "Ashe dai na gane ka."

Hydar ya kalle ta yace, "Jidda sauri muke kwa had'u a gida" ya fad'a yana shiga mota shima ya shiga suka ja motar suka bar wajan. Asad yaja tsaki kafin yace, "Mama bata dawo ba?." Hydar yace, "Ta kusa."
Hotel mafi kusa da airport d'in suka samu Asad ya sauka yayi wanka yana hutawa dan jirgin safe zai hau ya koma Egypt.

Awa d'aya na cika da yin swapping ya d'ora layin a kan wayar sa ya sauke Whatsapp d'in sa ya danna number Mama ya kira ta, bata tsinke ba ta d'auka daga can b'angaren tace, "Asad ina ka shiga kwana biyu wayar ka a kashe?." Asad yayi shiru ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?shi ba ma'abocin k'arya bane hakan ya saka ya rasa abinda zaice mata jin shiru ya saka tace, "baka ji bane? Ko gurguwar ce ta d'auke maka hankali har ka manta dani?; ba kayi min alqawarin ka barta ba Asad?, ashe zaka iya yi min alqawari ka sab'a?."

Mama ta d'aure Asad ya rasa me zaice komai nasa ya tsaya cak ya cize baki kana yace, "Barka da yamma Mama, ya karin hak'uri?." Jin ya canja maganar sai itama ta canja tace, "Alhamdulillah, amma zaku zo ranar Friday d'in ko? In yaso sai mu dawo tare." Asad ya girgiza kai kamar tana gaban sa yace, "Mamaa Abba ya sani aiki bazan samu dama ba."
"Okay, dana dawo maganar ka da Jidda zata taso cikin watan nan nake so ayi bikin a gama."

Ya had'd'iye saliva ya kasa furta komai kafin tace, "Ya gidan naku? Ba wani sabon abu?." Asad yayi shiru kafin yace, "Har yanzu dai."
"Shikenan mayi magana anjima, kar kaga bana nan Asad ka canja maganar da mukayi da kai akan yarinyar can, indai kana sona ka cire yarinyar nan a ranka in kuma baka sona Asad kayi abinda kake so" tana gama fad'ar hakan ta yanke wayar ya bi wayar da kallo kamar ya kurma ihu.

Dafe kansa yayi yana jin komai yana fita daga ransa tunawa da abinda ya cewa Mama sai yaji kamar yaci amanar tane da yayi abinda bata so bayan yace mata bazai yi ba. Shigowar Hydar d'akin bai saka ya d'ago ba Hydar ya zauna kusa dashi ya ajjiye masa ledar hannun sa yace, "Ya dai Deaf?."
"Mamaa!" Ya furta a hankali yana d'ago ido ya kalli Hydar. Hydar ya gyara zama kana yace, "Amma kamar kun gama maganar nan da takawa ko? Meyasa shi baka gudun b'acin ransa sai na Mama kake gudu?."

Asad ya d'auke kansa daga kallon sa ya d'auki ledar da ya shigo masa da ita yaga abinci ne da kuma kayan sa da zai saka ya d'auki ruwa a ciki ya sha ya jingina da kujerar yana kallon sama yace, "Ba haka bane but ina jin bazan koma ba." Hydar yace, "kenan baka jin maganar Abba ta Mama kake ji?."
"Ohhh Hydar ya zanyi ne?" Ya furta yana dafe kansa da duka hannayen sa biyu ya rasa zab'in wa zaibi na Mama kona Abba.
Hydar yace, "Kai dai ka sani, in kana ganin baza ka koma ba fine sai ka zauna kaga ka sab'a abinda Takawa ya nema a wajan ka a karo na farko, ni na tafi" ya fad'a yana tashi ta fita bai sake yi masa? magana ba.

Kasa motsin kirki Asad yayi daga inda yake domin shi kam ya shiga tsaka mai wuya ya rasa yadda zaiyi yaji dad'i gabad'aya komai ya tsaya masa cak ya rasa tunanin da zaiyi wanda zai ji zuciyar sa ta gamsu dashi.? Ko fita bai iya yi ba haka ya zauna a d'akin sallah ma a nan yake yi har dare.

Aliyu kuwa a lokacin suna tare da Waziri a falon gidan Wazirin Aliyu yana kallon sa shima yana kallon sa kamar bazai yi magana ba ganin hakan ya saka Waziri yace, "Kayi shiru baka ce komai ba, an tabbatar mana da maganin nan shine kad'ai zai ya manta dashi babar ku sai ya ganta hankalin sa zai dawo jikin sa kuma sai an shafa masa ina zamu ganshi?." Aliyu ya sake kallon sa ya d'ora k'afa kan d'aya sannann yace, "bani maganin."

Ba musu ya mik'a masa ya karb'a yana kallon robar maganin kana yace, "fatar jikin sa ake so kawai ta tab'a right?." Waziri yace, "Kwarai kuwa an tabbatar min......" Aliyu ya d'aga masa hannu kana yace, "Ba wannan na tambaye ka ba, naji amsar tambaya ta" ya fad'a yana mik'ewa ya saka bak'in glass ya kalle shi kamar zaiyi magana sai ya fasa ya fita daga falon.
Waziri ya bishi da kallo yace, "Allah ya tabbatar mana da nufin mu a wannan lokacin" ya fad'a yana binsa da murmushi.

Aliyu yana fita ya shiga mota bai wuce ko ina ba sai hotel d'in da Asad ya sauka ya tsaya yana kallon sa sai kuma ya fara tunanin a wanne room yake...?, waya ya d'auko ba tare da tunanin komai ba ya kira number Asad cikin sa'a ya d'auka ya kara a kunne yace, "Meye room number d'in ka gani nazo hotel d'in." Shiru yayi alamun ana bashi amsa kafin ya yanke kiran ya nufi ciki.

A bakin k'ofar ya tsaya ya d'auko man ya shafa a hannun sa sannan yayi knocking d'in k'ofar, Asad da yake zaune ya taso ya bud'e k'ofar suka had'a ido sai Aliyu yayi murmushi yana wara hannun sa yace, "Suprised" ya fad'a yana shigowa ciki yana kallon sa. Ya zare glass d'in idanun sa yana kallon Asad yace, "Har zaka shigo Nigeria kana niyar fita gobe without na sani Asad, a ganin ka hakan daidai ne?" Ya fad'a yana mik'a masa hannu alamun su gaisa.

Asad da mamaki yake kallon sa amma bai nuna ba ya bashi hannu suka gaisa kafin Aliyu ya zame hannun sa ya rik'e tsintsiyar hannun Asad kana yace, "Ban san me nayi maka ba deaf baka sona kafi son Hydar" ya fad'a yana sakin hannun sa. Asad ya kalli hannun sa sai yaga kamar shatin hannun Aliyu kamar dai a hannun Aliyun akwai wani abu mai maiko ya kalli Aliyu ya sake kallon hannun nasa kamar zaiyi magana sai ya fasa ya koma ya zauna kana yace, "Taya zan ki ka?."

Aliyu ya zauna a gefe d'aya yana kallon sa yace, "gashi nan kuwa baka nema na Hydar ne kawai naka." Asad baice komai ba daman shima Aliyun yasan bazai ce ba ya mik'e tsaye yace, "Shikenan ka gaida amarya in kaje" ya fad'a yana niyar barin wajan.

Asad so yake ya tambaye shi ya akayi yasan yana hotel d'in bayan yasan babu wanda yasan yana nan amma ya share baya son doguwar magana musamman da Aliyu shiyasa kawai Aliyu ya fita da farin ciki domin abinda ya kawo shi ya samu ya aiwatar ba tare da Asad d'in ya lura da hakan ba.

*Cairo*
*8:00am.*

Nurses masu kula da alhakin gyara ta sun mata komai hatta wanka an san yadda akayi tayi an canja mata uniform sun mata brush an kawo mata breakfast taci tana zaune tana charting da Yaya Ummi duk da zuciyar ta cike take da tunanin rashin ganin Asad awa ashirin da hud'u kenan. Sallama akayi aka shigo ta amsa tana kallon Dr da ya shigo tayi murmushi ta amsa ganin Dr Khalifa shima haka ya k'araso da tray na allurai a hannun sa yace, "Rauda ya jikin ki?."

"Alhamdulillah da sauk'i."
"Kina iya motsa k'afar taki?."
"Sosai ma, ni ji nake kamar ba'ayi min komai ba." Yayi murmushi yana had'a allurar da zai mata ta kalli tray d'in dake gaban sa taga wata k'atuwar kwalbar allura da bata tab'a ganin irin ta ba ta kai hannu ta d'auka da mamaki ta ajjiye ba tare da tayi magana ba.

"Mamakin girman ta kike ko?." Rauda tace, "eh, ban tab'a ganin kwalbar allura kamar ta ba." Dr Khalifa yace, "Wannan allurar da kike gani ana yiwa wanda ba'a so jikin su ya motsa ne kwata-kwata, kamar wanda za'a yiwa aiki haka duk dai ba'a amfani da ita sabida tana da hatsari sosai, in aka yiwa mutum ta kwana biyu tabbas jikin sa zai daina aiki har sai anyi masa wacce zata karya ta, itace wannan" ya fad'a yana nuna mata wata y'ar k'aramar kwalbar ta karb'a tana juyawa a hannun ta kamar wacce ta san ta kafin ta ajjiye tace, "Tabd'ijam, ita babba wacce zata karya garkuwar ta kuma k'arama."

Yayi dariya yaja kujera ya zauna ya fara k'ok'arin neman jijiyar hannun ta yayi mata tata allurar yace, "Haka abin yake; kuma duk girman ta da anyi k'aramar nan za'a fara ganin canjin indai ba anyi ta da yawa bane." Rauda tace, "ikon Allah" daga nan taja bakin ta tayi shiru bata kuma cewa komai ba.

Dr Khalifa yayi mata allurar kana yace, "Deaf bai dawo bane? Yace min jirgin safe zai biyo na d'auka by dis time ya iso." Rauda tayi shiru bata amsa ba domin bata san ma ita inda yaje ba.

K'ofar aka bud'e ya saka suka kalli wanda ya shigo suka ganshi yana takowa cikin k'asaita da izza fuskar nan a had'e babu walwala a cikin ta hannun sa zube cikin aljihun wandon sa yana kallon su ta k'asan idanu yana juya kwayar idon sa yana bin ko ina da kallo. Gaban ta ya fad'i ta daina kallon inda yake ta d'auke kai Dr Khalifa ya mik'e yana fad'in, "Welcome back Prince, yanzu nake tambayar ta baka dawo ba ashe kana hanya."

Hannu Dr ya bashi shima Asad d'in ya bashi suka gaisa kafin ya kalli Asad yace, "Sister nan naka tana da kirki sosai akwai saurin sabo ba irin ka bace." Banza Asad yayi masa shima kuma bai damu ba ya kwashi kayan sa ya fita Asad dake tsaye hannun sa cikin aljihu ya kalle ta ya kalli kujerar da Dr ya tashi ganin ta gab da Raudan ya sake kallon ta suka had'a ido tace, "Ina kwana."

Banza yayi mata bai amsa ba ya zagayo inda kujerar take kamar zai zauna ya tsaya yana kallon ta yace, "last warning kar na sake ganin hakan." Da mamaki ta kalle shi taga ya sake tamke fuskar sa sai ta kasa tambayar sa me yake nufi ta sauke kanta k'asa ba tare da tasan akan abinda yake magana ba.


Wayar ta taga ya d'auka yana juya ta a hannun sa kafin taga ya zare sim card d'in ciki ya raba shi biyu ya saka a shara ya d'auko sabuwar waya a aljihun sa ya ajjiye mata a kusa da ita ta hannun sa kuma yayi danne-dannen da zaiyi sannan ya saka a shara.

Rauda kallon ikon Allah kawai take yi gashi ya had'e fuska yayi mata kwarjini ta kasa kallon sa balle tayi magana, kamar a mafarki taji yace, "in akwai sauran abinda kika san ya baki throw it away" ya fad'a yana kallon ta.
Rauda tayi shiru cike da mamakin sa dan in ta fahimci me yake nufi kenan yasan Anas ne ya bata wayar shiyasa ya cillar?, yasan shine ya bata sim card d'in shiyasa ya karya?, kenan kishi yake da ita kome?.

Shiru ya ratsa tsakanin su kafin a shigo d'akin Rauda ta kalli wajan banda Asad da ya fara danna wayar sa, "morning beautiful face" Muhibba ta fad'a tana kallon sa da murmushi a fuskar ta. Tsaki yaja domin shi ya tsane ta gabad'aya baya son ganin ta amma ta nace masa duk inda yaje sai tayi masa magana ya rasa dalilin hakan, bai d'ago ba balle ya amsa ta k'arasa kusa dashi tana k'are masa kallo tace, "how was your day?." Nan ma yayi mata Banza ta sake yin murmushi tace, "I like your acting? prince, ko baka ce komai ba indai zan kalle ka is enough."

Tana fad'ar hakan ya fita daga d'akin ta bishi da kallo har ya b'ace ta kalli Rauda tace, "Ina son brother d'in nan naki Rauda, yayi min ta ko ina class d'in sa na burge nu over, I feel like naje nayi hugging d'in sa ko zanyi dad'i a zuciya ta." Kallon ta Rauda take yi itama ita take kallo tana murmushi Rauda taji babu dad'i a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login