Showing 150001 words to 153000 words out of 216282 words

Chapter 51 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

"Kina so na farka ne daman?." Yadda ya kafe ta da ido sai ta kasa magana ta diririce ta rasa me zatace ta sunkuyar da kai ta d'ago ta rasa me zata ce, ganin hakan sai yayi murmushi yace, "tashi ki koma inda kika fito, sannan umarni nake baki kar wani ko wata yasan da wannan labarin koda wasa, in kuma akasin hakan ya faru ranki ne zai b'aci dan nasan ke kad'ai kika sani."

"Mijina ina zanje?." Ya kalle ta yace, "Inda kika fito nan zaki koma, bana son sake ganin ki a wajan nan har sai lokacin da kowa zai san na farka zaiyi. Asad, Aliyu, Hydar ban amince dukkan su su san da wannan maganar ba, in kuma naji a bakin su na tabbatar ke kika fad'a." Sai ta fashe da kuka tana kallon sa murya na rawa tace, "Mijina dan Allah ka yafe min nasan nayi abubuwa da yawa a bayan idanun ka, nayi ne sabida...."
"Son zuciyar ki ko?" Ya katse ta da fad'ar hakan yana kafe ta da idanun sa masu kwarjini.

Shiru tayi ta sunkuyar da kanta tana kifta idanu yaja dogon tsaki yace, "baki fara ganin komai ba Rabi'a, baki ga komai ba a cikin abubuwan da kika shuka yanzu kika fara girbar su. Tashi ki bani waje bana son ganin ki gabad'aya." Jiki a sanyaye ta mik'e tana tafiya kamar mara laka ta juyo ta kalle shi taga bama ita yake kallon ba tace, "Dukkan abinda na aikata nayi nadama bazan sake aikata makamancin su ba."

Bai amsa ba dole ya saka ta fita yaja tsaki ya lumshe idanun sa dukkan abinda ta aikata suna dawo masa cikin kansa ya cize baki shi kam bai tab'a ganin mace makira kamar ta ba. Uncle ne ya shigo d'akin ya kalle shi yace, "Mubarak taya aka bar Rabi'a ta shigo a wannan lokacin?." Uncle yace, "Ranka ya dad'e na fita ta shigo su kuma masu tsaron k'ofa baza su tab'a iya hanata shigowa ba, da ace ina nan ne zan san yadda zanyi na dakatar da ita to bana wajan."

Mai martaba yace, "Bana tunanin zata iya shiru da bakin ta ba tare da ta fad'awa y'ay'anta ba, fad'a musu daidai yake da lalacewar komai." Uncle yace, "Babu abinda zai faru in sha Allah mai martaba, Allah ya wuci zuciyar ka." D'auke kai yayi kana yace, "Ina Asad yaje?." Uncle yace, "Babu wanda yasan inda ya tafi." Abba ya sauke numfashi yana girgiza kai yace, "komai yazo k'arshe."
Uncle ya amsa da fad'in, "Da izinin Allah."

? ? ? ? B'angaren Mama kuka take sosai a kan gadon ta, bata tab'a jin dana sani akan abubuwan da ta aikata ba sai a wannan lokacin da ta tabbaatar mijin ta yasan duk wani target d'inta nasan ganin bayan kowa akan burinta.? Tunawa da wani abun sai ta zabura ta fara zagaye d'akin tana girgiza kai tana fad'in, "A'a bazai san ni na aikata wannan laifin ba, bazai sani ba, in ya sani na shiga uku na lalace" ta fad'a tana d'ora hannun ta a kanta tana cigaba da zaga d'akin hankalin ta a tashe tsoro ya bayyana a tare da ita.

Sai ta koma kan gadon ta zauna tana kuka tayi tagumi, "shin ina y'ay'a mazan da nake alfahari dasu?" Ta tambayi kanta dan dukka su uku bata san inda suka suke ba balle ta neme su. Kai ta dafe zuciyar ta na farbawa da sauri-sauri zazzaSi yana neman rufe ta tunda mai martaba ya farka bata da kwanciyar hankali dan tasan daidai yake da tonuwar dukkan asirin ta wanda ta jima tana b'oyewa.

K'wankwasa k'ofar da akayi ya saka ta kalli k'ofar bata bada umarni ba aka shigo ganin Hydar ne ya saka ta mik'e ya k'araso inda take da sauri ta rik'e shi tana fad'in, "Mahaifin ku ya farka Hydar, naje na same shi a zaune yana magana har yana tafiya. Meyasa zai farka yanzu? Meyasa sai da komai ya lalace min zai tashi?" Ta fad'a tana rik'e Hydar shima ya rik'e ta dan yaga kamar bata hankalin ta.

Gaban sa ya fad'i jin abinda tace ya zaro idanu yace, "Mama da gaske ya farka? Abbana ya tashi har yana tafiya?. Zanje na ganshi Mama" ya fad'a zai fita tayi saurin dawo dashi tace, "karka sake kaje inda yake, koda wasa kar ka nuna kasan ya tashi bana so yasan na fad'a maka ka rufa min asiri" ta fad'a tana kuka sosai ya rik'e ta hankalin sa duk ya tashi ya zaunar da ita yace, "Shikenan Mamana kwantar da hankali ki babu abinda zai faru, ki daina kuka dan Allah" ya fad'a yana rik'e da ita gabad'aya jikin sa yayi sanyi.

Kuka take sosai yana rik'e da ita har sai da yaga kukan nata ya tsaya Suhaima ta shigo yace ta kula da ita shi kuma ya fita. Har zaije inda mahaifin na yake sai ya tuna mai tace masa sai ya fasa dan baya son abinda zai haifar mata da matsala kamar yadda tace.

*&&&*

? ? ? ? "Inna da gaske fa ni ina sonshi zan aure shi indai kin amince" Rahma ta fad'a tana kallon Inna. Inna tace, "kin amince fa kika ce Rahma? Kuna jin abinda take cewa ko?" Inna ta fad'a tana kallon Yayar mu da Yaya Nafisa da Yaya Fariha da kuma Yaya Shamsiyya.

Yayar mu tace, "To Inna tunda tace tana son sa shima kuma yace zai aure ta basai ayi ba. In kika duba Inna samari wahala suke yanzu, y'ay'an masu kud'i ma da kyau da komai suna zaune babu mijin aure ina ga mu y'ay'an talakawa?. Tunda har ya furta a bashi d'in kar mu bari ya sub'uce mana kinga har yanzu fa babu wanda yake zuwa wajan ta."

Yaya Shamsiyya tace, "Nima dai abinda na gani kenan. Tunda kowa yasan asalin yaron nan me zai hana baza'a barta ta aure shi ba tunda dai yana so itama tana so?, mun san sai yafi son Rauda da ita tunda tun farko ita yake so amma duk soyayyar da yake mata in Allah ya rubuta Rahma ce matar sa babu wanda sai canja hakan."

Yaya Nafisa tace, "Inna kawai a amince ayi abin nan, sai mu cigaba da mata addu'a Allah yasa hakan shine mafi alkhairi." Inna ta sauke numfashi tana kallon su tace, "dukkan ku kun goyi bayan ta aure shi kenan?."
Yaya fariha tace, "To meye aibun hakan Inna?."
"Amma kun san Rauda yake so ba ita ba, bakwa tunanin gori wata rana?."

Yayar Mu tace, "Allah zai kiyaye babu abinda zai faru in sha Allah Inna." Inna tayi shiru kafin tace, "Yanzu dukka sai na fito na cewa y'an uwana zan aurar da Ita nan da kwanaki kad'an masu zuwa? Hakan ai abin kunya ne."
"Babu kunya a ciki Inna, wacece bata da budurwa a cikin y'an uwan naki Inna? Ko wacce kuma burin ta taga ta kawar da ita daga gaban ta tayi aure; mu mun samu meyasa zamu watsar da samun gefe?."

Inna tace, "Shikenan Allah yasa hakan shine mafi alkhairi." Suka amsa da amin Yayar Mu tace, "Zan sanar da Baba ta amince kema kin amince ayi komai a gama." Inna bata ce komai ba suka cigaba da hira kafin su je wajan Umma.

*Bayan kwana biyu.*

Biki ya gabato ya rage saura kwana biyu kacal d'aurin aure amarya tana ta shagali abinta tunda suka had'u da Anas sau daya bai sake zuwa ba dan jinyar kansa yake dauriya kawai yake yi yana zuwa amma bawai don son ransa ba. Da ya saka addu'a da neman zab'in Allah a kan gaba sai komai yake barin zuciyar sa a hankali yaji yana karb'ar Rahma matsayin mata a gare shi.

A cikin kwanakin dai suna waya kuma babu laifi yana jinta a ransa yana k'ok'arin nuna mata yana son auren nata yana nuna mata ya karb'i k'addarar da Allah ya k'addaro musu itama kuma tana nata k'ok'arin.
Rauda ta tattara komai nata Umma ta tura ta Bauchi gidan yayar ta tace sai an gama komai na biki ta dawo.

Ana ta shagalin biki dangin Umma dana Baba dana Inna kowa yana nuna tasa bajintar daman gidan Amarya an gama zuba komai dan Umma bata ce uffan akan kayan Rauda da suke gidan ba tace dukkan su d'aya ne ita da Raudan.

Ranar lahadi da misalin k'arfe sha d'aya na safe a masallacin cikin gari dubban jama'a suma shaida daurin auren Anas da Rahma akan sadaki naira dubu d'ari. Bayan d'aurin aure ya watse ango yazo gidan su amarya kamar yadda al'ada ta tanada yayi namijin k'ok'ari wajan kawar da komai a zuciyar sa duk da Raudan bata nan.

Anyi shagali sosai kamar ba gidan Baba dan abinda Asad ya aiko dashi a bikin kad'ai ya isa ayi komai na bikin harda canji, aljihun Baba cike yake taf shiyasa da ance babu abu kaza zai bayar a haka aka gama taron biki aka kai amarya gidan ta kowa ya watse.


*Matar mutum kabarin sa.*>?u?>?u?
[17/12, 10:42 pm] Nafisat Alwasa: *Arewabooks @nanahaleema11*
*73*

Kallon Baba Anas yake yi bakin sa yana rawa alamun yana so yayi magana amma bashi da k'arfin guiwar yin maganar sai kallo da yake bin Baba dashi idanun sa kamar zasu fad'o kasa sabida tashin hankali da firgici. Ganin yanayin da ya shiga ya saka Baba sake tausasa murya yace, "Anas nasan dole kaji babu dad'i akan abinda na fad'a maka amma ina so ka fahimce ni wallahi bamu yi maka haka da wata manufa ba, Allah ya sani badan wannan maganar ba auren ka da Rauda yana nan babu fashi. K'addara ta riga fata Anas dukkan mu babu wanda yaji dad'in wannan abinda ya faru, amma babu yadda zamuyi da ikon Allah. Kayi ha?uri bamu yi dan mu wula?anta ka ba Anas."

Runtse ido Anas yayi jin abinda Baba ya sake fad'a ya tabbatar masa da ba mafarki yake ba da gaske ne abinda yake faruwa, da gaske ne Raudan sa tana da miji babu damar ya aureta ya sake rasata a karo na biyu. Shiru yayi ya kasa magana jikin sa har rawa yake yi kansa na k'asa idanun sa sun cika da ruwan hawaye ya rasa abinda yake masa dad'i.

Ba k'aramin tausayi ya bawa Baba ba zuciyar sa ta karye dan Allah kad'ai yasan abinda yake ji a cikin zuciyar sa a wannan lokacin hakan ya saka yace, "Sai hak'uri Anas. In kaga abu ya tunkaro bawa gadan-gadan zai same shi sai ya kubce to ka tabbatar ba alkhairi bane a tare dashi,? in kaga kana kaucewa abu Allah yana sake mayar dakai wajan koda baka so to tsaya a inda Allah ya kaika wata?ila alkhairi ne a gare ka. Kayi hak'uri nasan akwai ciwo kasancewar ka jima kana son Rauda amma Allah bai rubuta kai mijin ta bane shiyasa ake ta samun akasi a ko wanne lokaci."

Kai Anas yake girgizawa nan take ruwan da ya taru a idanun sa ya sauko kan kuncin sa, hawaye yake wani yana bin wani kansa a k'asa har lokacin Baba ya zuba masa ido kawai shima ji yake kamar yayi masa kukan sabida tausayi zuciyar sa ta karye. Baba yace, "Abinda yasa banyi magana da wakilan ka ba na neme ka kai tsaye ina dan na sanar dakai da kaina kar kaji maganar a bakin iyayen ka kaga kamar an yaudare kane. Amma kayi hak'uri wallahi ita kanta Raudan tana sonka so mai tsanani, auren wani da yake kanta ya saka dole take k'ok'arin cire ka a zuciyar ta kodan gudun fad'awa fushin ubangiji."

Muryar sa na rawa yace, "babu komai Baba, haka Allah ya tsara babu wanda ya isa ya canja faruwar sa. K'addarata kenan zanyi......." ya kasa k'arasawa muryar sa ta sark'e ya sake saukar da kansa k'asa sabbin hawaye suka sake wanke masa fuskar sa. Baba yayi shiru yana kallon ikon Allah ganin namiji mai kyau da kud'i kamar Anas yana kuka da ya rasa y'ar talakawa Rauda. Lallai lamarin soyayya sai dai a barshi, duk wanda kaji yana cika baki a kan soyayya tabbas bai tab'a d'and'ana d'acin sa bane. Duk wanda yasan so yasan ya zafin sa yake, kana tare da wanda kake so d'in ma rad'ad'in sa yana damun zuciyar ka ina ga ka rabu dashi?.

Sai da ya tsaigata kuka sannan ya share idanun sa yace, "Baba babu komai na d'auki hakan matsayin jarabawar ubangiji ina rok'on sa da kyawawan sunayen sa da ya bani ikon cinyewa." Baba yace, "Amin Anas. Kayi hak'uri haka Allah yake tsarin sa, babu ta yarda za'ayi jarabawar wanda ya halicce mu tazo mana da sauk'i dole sai ta tab'a mana zuciya da gangar jiki kodan mu k'ara imani dashi nan gaba. Jarabawar duniya ma wacce wani ne a duniya zai baka sakamako in ka shige ta hankalin ka yake kai kololuwa wajan tashi ina ga wacce mahaliccin kane zai baka sakamakon da kansa?. Kayi hak'uri!" Baba ya sake fad'a a tausashe yana kallon sa.

Shiru yayi yana murmushin k'arfin hali kafin yace, "Babu komai Baba na d'auki k'addara." Baba yace, "Haka ake son dukkan mu'umi ya kasance Anas. Yanzu ya za'ayi da iyayen ka? A sanar dasu?." Anas yace, "A'a Baba, bazan so ace an sake fasa aurena ba a karo na biyu hakan bazai wa mahaifiyata dad'i ba, in na jure ita babu lallai ta iya jurewa. Na amince da tarbiyyar y'ay'an ka da kuma ilimin su Baba, tunda na rasa Rauda ina so a bani k'anwar ta guda d'aya."

Baba ya washe baki farin ciki ya bayyana a tare dashi ya gyara zaman sa yace, "Banda abinka Anas wannan ai abu ne mai sauk'i, na kuma ji dad'in wannan kalami naka har sosai ba kad'an ba. Rahma k'anwar Rauda ce jinin tace sai ta maye gurbin y'ar uwarta a gare ka, wata?ila daman can Allah ya riga ya rubuta itace matar ka ba Rauda ba tunda dukkan lalube muke a cikin duhu."

Anas ya girgiza kai yace, "Haka ne Baba" Sai kuma yayi shiru ya sake sunkuyar da kansa k'asa ya danne raunin da yake ji a zuciyar sa baya so ya bayyana amma ya kasa, Baba yace, "Na baka Rahma halak malak Anas, za'a cigaba da shirye-shiryen biki kamar babu abinda ya faru in Allah ya amince. Kayi hak'uri nasan har abada baza k daina jin ciwon da kake ji ba; amma ka jure wata rana sai labari."

Anas bai amsa ba dan kansa sarawa yake yi zazzaSi yana neman rufe shi bai san ya akayi bakin sa ya furta zancen k'anwar Rauda ba kawai taji ya fad'a ne hakan ya saka shi yin shiru bai ce komai ba. Baba yace, "Ya kake gani a sanar da iyayen ka abinda ya faru ko a'a?." Anas ya d'ago jajayen idanun sa ya kalli Baba yace, "A'a Baba, a cigaba da shiri kawai Allah yasa hakan shine mafi alkhairi." Baba yace, "A'a Anas in akayi haka kamar an mufurce su ne, kar nan gaba su samu labari suga kamar bamu kyauta musu ba."
"Babu komai Baba, basai an fad'a ba bazasu tab'a sanin ba ita bace" ya furta a hankali idanun sa a lumshe.

Baba yace, "To shikenan. Allah ya tabbatar da alkhairi yasa hakan ya samarwa da kowa farin ciki a zuciyar sa. Ya baka ikon jure abinda kake ji a ranka daga nan har lokacin da Allah zai kawo maka sassauci a zuciyar ka." Kai yake girgiza kai yace, "Amiin Baba."

Mik'ewa Anas yayi yace, "Baba zan koma." Baba ma ya mik'e yace, "Anas naga yanayin ka ya canja gabad'aya, Anya zaka iya tafiya kai kad'ai?." Anas ya murmusa yace, "Babu komai zan iya. Sai anjima Baba" ya fad'a yana fita Baba yabi bayan sa sai da ya tabbatar ya shiga mota ya tafi sannan ya koma cikin gidan jikin sa a sanyaye matuk'a.

Yana shiga wajan Umma ya wuce ya same ta ita da Inna ne a zaune Baba ya zauna yace, "Kamar kun san dukkan ku nake nema." Inna tace, "Lafiya na ganka a sanyaye haka?." Baba yace, "Yaron nan Anas shine ya karya min zuciya wallahi, kuka ya dinga yi k'aramar yaro k'arami jikin sa har rawa yake. Yana son Rauda amma Allah bai rubuta Rauda matar sa bace ba abin tausayi" ya fad'a a sanyaye yana sauke numfashi.

Umma tace, "Malam dan ka dage ne amma ni banga dalilin sanar da Anas ba tunda bamu da tabbacin sakin nan baiyu ba a kanta. Allah ya sani ni hankalina yafi kwanciya da Anas wallahi." Baba ya kalli Umma yace, "kina son maimaita magana guda d'aya, aure ne akwai shi akan Rauda dan babu yadda za'ayi mutum kamar Asad yazo yayi mana k'arya kawai dan cikar burin sa. Kina so muyi mata aure akan aure ne? Koda ma ace babu batun auren haka zamu bawa Anas auren ta da ciki a jikin ta?."

Jin Baba ya hasala sai Umma tayi shiru bata ce komai ba Baba yace, "Anas yayi tawakkali ya amimce da k'addara ni kuma na bashi Rahma a madadin Rauda dan haka biki baza'a fasa shi ba amma ya tashi daga kan Rauda ya koma kan Rahma" Baba ya fad'a yana kallon su. Inna ta bud'e baki tace, "Kamar ya kenan?."
"Kamar yadda kika ji na fad'a. Ya amince da maganar Rahma shine ya fara nema ni kuma na bashi, dan haka duk wani shiri da kuke akan Rauda ya tashi ya dawo kan Rahma dan yau saura kwana tara auren ta da Anas."

Inna ta kalli Umma itama ta kalle ta cikin mamaki tace, "Malam kenan auren cushe za'a yiwa Rahma kome?." Baba yace, "hukuncin dana yanke kenan babu ruwan ki dawai auren cushe ko akasin sa, Rahma Anas zata aura madadin y'ar uwar ta Rauda." Inna tayi dariya kad'an tace, "Ban damu da kud'in da Anas yake dashi ba abinda na sani shine wallahil azim babu wanda ya isa ya yiwa Rahma auren dole, in bata son Anas wallahi bazata aure shi ba dan ni ba ita bace da zan bari a d'auki y'ata a aurar ban sani ba sai dai kawai a kawo min sadaki" ta fad'a tana nuna Umma da take zaune tana kallon Baba da shima ita yake kallo.

Baba ya girgiza kai ya kalle ta yace,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login