Showing 120001 words to 123000 words out of 216282 words

Chapter 41 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

Baba yace, "Baba." Baba ya kalle shi yace, "A'a Anas." Ya duk'a ya gaishe shi kafin yace, "Waye babu lafiya a daren nan?." Baba yace, "Rauda ce ta samu k'aramin hatsari, amma Alhamdulillah komai yazo da sauk'i buguwa tayi a bayan ta kawai."

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, yaushe Baba?" Ya tambaya a gigice yana kallon Baba. Baba yace, "kwantar da hankalin ka, d'azu ne kuma da sauk'i dan yanzu dana biya kud'in nan ma tare zamu koma." Anas ya karb'i takardar yace, "Baba ka koma ka zauna zan gama komai." Baba yaji sanyi a ransa dan Allah ya sani baya son fitar da kud'i dan babu yadda zaiyi ne yasan shine yaja yace, "Ayi haka Anas?." Yayi murmushi kawai ya k'arasa inda ake biyan kud'in Baba kuma ya koma da baya zuciyar sa fes.

? ? ? Bayan ya biya kud'in aka siyi magani Umma suka fito da Rauda Anas ya gaida Umma ta amsa Raudan ta gaishe shi ya amsa yace, "Ya jikin naki?."
"Da sauk'i, maganin da suka bani nasha naji dad'in." Kallon da yake mata ya saka ta k'in had'a ido dashi murya a tausahe yace, "Sannu." A tare suka fito harabar asibitin Anas yace, "ku tsaya Umma bara na kawo motar nan."

Baba yace, "Ai da adaidaita sahu muke." Anas yace, "bara na sallame shi sai mu tafi tare." K'arasawa inda motar sa take yayi ya bawa mai adaidaita sahun kud'i yace ya tafi ya shiga mota ya kawo ta inda suke tsaye Baba ya shiga gaba suka shiga baya suka tafi gida. A k'ofar gidan suka tsaya suka fito Baba yace, "Allah yayi albarka Anas, mun gode." Murmushi yayi kawai suka shiga gida yabi Rauda da kallo har ta shige ya sauke ajiyar zuciya Allah ya sani yana son Rauda da wannan tunanin ya shiga mota ya tafi.

*Bayan wasu kwanaki.*

? ? ? ? An shiga watan Ramadan an fita an shiga na sallah, tuni an saka ranar auren Rauda da Anas ya rage saura sati hud'u kacal ana ta shirye-shirye daman akwai kayan ta duk da aka siya lokacin auren ta da Asad k'arawa kawai akeyi tunda Allah ya rufa asiri yanzu. Amarya Rauda tana ta karb'ar gyara daga wajan yayyen ta kai da ka ganta kasan ta kusa zama amarya khamshin da yake fita a jikinta kad'ai zai tabbatar da hakan. A cikin satin za'a kawo lefe can gidan su angon ma shirye-shirye ake sosai bikin Babban d'a ba wasa bane.

A bangaren gidan sarauta babu abinda ya canja anyi shagalin sallah yadda ya kamata mai martaba sarki Asad yayi hawan sallah fiye da wanda akayi a baya, yasha ado ya kashe kud'i dan dawakin da aka hau ma daga Germany aka zo dasu.

Mama har lokacin bata kai matsayin da Asad zai zo inda take ba har gwara ma yanzu ya kan lek'a wajan ta ya gaishe ta amma bata san komai ba duk abinda zai faru sai dai ta gani kawai ya faru amma bata san anyi ba. Kullum Mama cikin shan maganin hawan jini take domin ya riga yayi mata illa dole sai da suka d'orata akan magani. Mama ta rame tayi bak'i abubuwa sun tarar mata iskanci kala-kala jidda take shinfid'a mata musamman yanzu da cikin Jidda ya tasa kana iya ganin sa a cikin riga sai iskanci yayi gaba dalilin samuwar ciwon ta kenan.

Hydar ya warke ya cigaba da kula da mai martaba wanda ake samun cigaba a rashin lafiyar sa dan a yanzu yana motsawa sosai sai dai baya magana har lokacin kuma baya tashi.

Aliyu kuwa har lokacin babu labarin sa tun ana samun a sa waya yanzu ta kai ta kawo an daina samun sa a waya har Maman ta gaji ma ta daina gwada kiran nasa, tayi addu'a a watan azumin da ya wuce taje umra zuciyar ta tana fad'a mata Allah ya masa dukkan abinda ta rok'a sai dai ta jira sakamako.

*&&*

? ? ? ? "Nifa na kasa gane abubuwan nan da suke faruwa, tun kwanakin baya kace min zaka san yadda za'ayi da Asad za'a haukatar dashi ya dawo daga England lafiya lau ya cigaba da mulkin sa babu abinda ya canja har kawo yanzu saima cigaba da yake samu. Kace min bazai tab'a iya haihuwa ba yanzu ga matar sa da ciki har ya fito ana ganin sa. Abu biyu ka fad'a ka cika shine b'atar da Aliyu da kuma gurb'acewar raywuar Rabi'atu bayan wannan shiru har yanzu ni na gaji. Kaida mastar d'in kun kasa komai lokaci yana ta tafiya da zarar yarinyar nan ta haihu shikenan abu ya sake dawowa baya" Hajiya ta fad'a tana kallon waziri da yake zaune.

Yace, "kwantar da hankalin ki ni kaina nasan an d'auki lokaci amma me kika ce a maganar ki? Abubuwa biyu sun tabbata sauran ma zasu tabbata ne."
"Yaushe? Kusan shekara ana abu d'aya ace har yanzu an kasa cimma komai."
"Zamu cimma daman dole sai munyi hak'uri, in kuka tuna waye Asad ta b'angaren addini dole sai mun sha wahala. Suhail da muka tura shi jikin sa matar Asad bata yadda dashi ba tana k'okarin raba su ne kin san yanzu sai abinda tace shine nak'asun da muka fara samu tun farko."

"Batun mai martaba fa? Kace bazai tab'a warkewa ba sai gashi yanzu ana samun cigaba har abinci yana ci." Ya dafe kai yace, "Baki amince dani bane?."
"Da na amince amma yanzu amincewar tawa k'asa take yi sabida ka kasa yin komai kullum sai magana, itama master planer ta kasa komai. yar ficiciya Jidda ace ta gagare ku? Wannan ai abun kunya ne."
Ya sauke numfashi yace, "wallahi sai munyi galaba akan Asad, babar matsalar a nan wanda zai shiga jikin sa shi muke so ta hanyar da zamuyi amfani dashi wajan tarwatsa shi to bamu dashi."

"Gagarumin aiki za'ayi masa wanda zai saka shi yaso Suhail koda baya so, itama jiddan a saka ta so shi koda bata son hakan, sannana a zubar da cikin jikin Jidda, a sake kwantar da mai martaba kar a bari ya tashi in ya tashi komai ya dawo baya." Ya mik'e yace, "Abinda ya kamata ayi kenan kuma za'ayi." Itama ta mik'e tace, "in wannan damar ta kuma cewa gaskiya na fita daga tafiyar ku, bazan sake tafiya da ku ba zanyi tafiya ta ni kad'ai kawai" tana fad'a ta fice ya bita da kallo yayi murmushi yace, "A tunanin ki zaki fita daga cikin mune kuma mu barki da rai salon ki tona masa asiri Sa'adatu...? Lallai an gaishe ki" ya fad'a yana d'aukar wayar sa shima ya fita.

*Bahrain.*

? ? ? ? Kwanakin da suka gabata yake jin son komawa gida yana shiga zuciyar sa amma bai tab'a tasiri ba. Tunda ya farka yau yake jin zuciyar sa na sassautawa a hankali a hankali yake jin tunanin Nigeria yana dawo masa cikin kansa cikin mintina da basu wuce goma ba ya tuna komai, ya dafe kansa ya runtse ido yace, "me nake yi a nan ne? Ina mulki na? Kenan yana hannun su? Daman cin amanata suke yi...?" Ya fad'a yana tashi zunbur yana kalle-kalle.

Jikin sane yake rawa tunawa da abubuwan da suka faru yayi k'wafa gano wanda suka yi masa wannan abun ya fara shirye-shiryen baro Bahrain ya dawo Nigeria a ranar. Sai da ya had'a kaya kaf sannan ya fita ya yanki ticket akayi sa'a ya samu jirgin da zai dawo Nigeria a ranar k'arfe goma na daren can jirgin sa ya taso zuwa Nigeria.

*&&&*

? ? ? ? Ji yayi kansa yayi mugun sarawa lokaci d'aya ya dafe kai ya tashi zaune ya kalli Jidda da take gefen sa tana bacci ya tashi ya fito zuwa falo yana jin jinin jikin sa ana tafasa masa shi. Ji yake kansa yana juyawa hakan ya saka shi tsayawa gaban taga ya yaye labulen yana kallon k'asan gidan da haske ya haske ko ina ga bishiyu da suke kad'awa amma babu kowa sai maguna da suke yawo.

Numfashi ya furzar zuciyar sa na bugawa da sauri jin sa yake kamar bashi ba sannan kuma ji yake kamar akwai abinda yake shirin faruwa dashi a b'oye ko a bayyane. labb'a ya taune ya kalli agogon bango falon yaga k'arfe uku na dare ya sauke numfashi ya shafa fuskar sa ya saki labulen ya koma kan kujera ya zauna tare da dafe kansa.

Ji yake kamar ya jawo safiya haka yake ji gabad'aya hankalin sa ya gama tashi da ya rufe ido abinda ya jima da mantawa shi yake hangowa ya k'agara gari ya waye yaje ga abinda zuciyar sa take hasko masa a cikin daren, numfashi ya fesar ya kwanta da baya ya kulle idanun sa sai kuma ya mik'e zubur ya shiga d'aki jim kad'an ya fito ya hau carpet ya tayar da sallah.

? ? ? ? *&&&*

Washe gari.

? ? ? ? ? ? "Umma! Umma!! Kin san me?" Rauda ta fad'a tana shigowa d'akin ta da farin ciki akan fuskar ta. Umma tace, "Sai kin fad'a zan sani." Rauda tace, "Anty Ramla ce tayi min waya matar Dr nan da ya taimaka min har na raka su wajan Baba malam....." Umma tace, "na gane ta, meya faru?."
"Umma yanzu take fad'a min tana da ciki na wata biyu, Umma sai kuka take tana gode min kamar nice na bata maganin."

Umma taji dad'i a zuciyar tace, "Kai amma na taya ta murna sosai, Allah ya iganta yasa na gari ne, yasa kuma shine silar bud'ewar haihuwar ta." Rauda tace, "Amin Umma. Tace da zasu shigo Nigeria dole su koma suyi masa godiya sun jima suna shan magani amma babu wanda yayi musu sai na Baba, tace nace miki ta gode Allah yasa da gidan aljanna. Umma baki ji bafa yadda ta gigice kamar wacce aka bawa aljanna."

Umma tace, "Amin. Shi Yaya Malam ai bashi ne ya bata ciki ba Allah ne, kawai ya taimaka mata ne cikin Ilimin da Allah ya bashi kuma akayi sa'a aka samu waraka. Murna kuma dole tayi murna ai Rauda, Allah kad'ai yasan tashin hankalin da take fuskanta a wajan dangin mijin ta dalilin rashin haihuwar nan, shi kansa mijin da an cigaba da tafiya a haka tabbas aure zai k'ara a hakan ma yayi mata adalci sosai."

Rauda tace, "haka ne Umma, Baki ji yadda naji dad'i ba wallahi kamar nice." Umma tayi dariya kawai bata ce komai ba Rauda ta mik'e tace, "Zan tafi gidan Yaya Ummi d'in, ina sak'on da kika ce?." Umma tace, "gashi can a leda ki kai mata" Rauda ta k'arasa ta d'auka sannan ta fita.

Shiryawa tayi cikin doguwar rigar da aka siya mata a Cairo, tunda suka dawo bata sake kallon kayan ba amma yau taji tana son sakawa ta saka wacce ta saka a can ranar da suka ci uwar soyayya ita da Asad. Tsaf ta shirya tayi mata kyau ta tsaya tana kallon kanta sai ta shafa cikin ta ta tuno yadda ya rik'e ta gam waka na tashi kad'an-kad'an. Saurin kawar da tunanin tayi taja tsaki ta d'auki waya da sak'on Umman ta shiga wajan Umma tayi mata sallama ta fita.

Tana tsaye a kan titi ga rana babu abinda duk ta gaji ji take ma kamar ta koma gida taga mota ta tsaya a gabanta, sauke glass akayi ta kalli na ciki sai tayi murmushi yace, "ki shigo rana." Ba musu ta shiga gaban motar yaja suka fara tafiya ya kalle ta yace, "Ina amarya ta zata je haka ta tsaya rana tana dukar min ita?" Ya fad'a cikin kalar tausayi yana kallon ta.

Murmushi tayi kad'an tace, "Zanje gidan Yaya Ummi ne fa, tun jiya take kirana."
"Shine ko ayi min waya nazo nayi rakiya aka tsaya rana dan kawai ta saka min mata tayi ciwon kai ko?."

Bata ce komai ba sai murmushi ya kalle ta yace, "kinyi kyau matata, ashe haka Abaya take miki kyau? Lallai dole a k'aro miki su a zuba a lefen ki." Had'a ido sukayi nan take sai gaban ta ya fad'i ta sauke ido k'asa tace, "Kaima kayi kyau sosai." Sai yayi y'ar dariya yace, "Ina kyaun a nan? Kina ganin duk nayi bak'i sabida zarga-zargar auro ki..? Sai yanzu na tabbatar auren matar manya yana da wahala sai ka jure, ki duba yadda na koma fa yanzu haka ma cafe zan wuce zasu buga min iv."

"Wai matar manya, kodai mijin manya?." Ya kalle ta yace, "ni awa? Matar manya dai my love."
"Har zaka buga Invitation? Ai yayi wuri naga."
Ya wara ido kad'an yace, "Waye ya fad'a miki yayi wuri? Kin san irin adadin mutanen da zan gayyato ne..? Tabd'ijam ai in ban fara rabawa yanzu zan manta da abokaina da yawan gaske."
Ta girgiza kai tace, "in ka raba yanzu su kuma zasu manta ba dan yayi wuri sosai."
"In sun manta su suka jiyo babu wanda zai min k'orafin ban gayyace shi ba. Shima kuma nasa yazo banje ba."

Tayi dariya kad'an ya kalle ta yace, "Rauda Allah ya sani na k'agu na mallake ki matsayin matata, gani nake sati hud'u yak'i zuwa dan yaga ina so yak'i yayi sauri. Sai zuciya take bani kamar akwai wata katanga da zata sake shigowa tsakanina dake shiyasa kawai nake so ayi a wuce wajan." Tayi murmushi tace, "babu wannan katangar in sha Allah, bata da gurbi a tsakiyar mu." Yayi murmushi ya dafe zuciyar sa yace, "Har naji dad'i wallahi, shiyasa akace kalma d'aya ta matar ka ta isa ta kwantar maka da hankali. Ina sonki matata."

"Nima ina son ka mijina." Yayi murmushi ya kalle ta tace, "ka kalli gaban ka fa." Ya kalli glass d'in motar yace, "Ina ma kin zama mallaki na kika furta wannan kalmar, da babu abinda zai hana ban rungume ki a jikina ba My love" ya furta muryar sa a sanyaye yana kallon ta ta kasan idanun sa.

Bata amsa ba daman yasan bazata amsa ba sau da dama in irin maganar nan ta fad'o tsakanin su bata bashi amsa har mamaki yake domin yasan yadda yawancin zawarawan yanzu suka lalace amma ita ba haka take ba dalilin da yake k'ara masa k'aunar ta kenan.

"Kinyi shiru." Ta kalle shi tace, "to me zance?." Sai yayi murmushi jin me tace ya kai hannun sa ya rik'e hannunta zata kwace yace, "Rana ta farko dan Allah, ki bani dama na ro?i hannun ki kawai." Ta rausayar da kai tace, "Amma kasan babu kyau ko?."
"Na sani My love, na kasa sarrafa kaina ne ina so naji dumin jikin ki a fatar jikina, ki bani wannan damar kawai dan Allah."

Shiru tayi amma sai yaga ta d'aure fuska hakan ya saka shi ya saki hannun nata yace, "kiyi hak'uri." Bata amsa ba tana kallon titi har suka k'araso k'ofar gidan Yaya Ummi ya kalle ta yaga tana k'okarin bud'e motar sai ya saka mata lock ta juyo zatayi magana kenan taji saukar bakin sa a kumatun ta yayi mata kiss.

Runtse ido tayi kafin tayi magana kuma ya rik'e hannunta gam yana kallon idanun ta yace, "na kasa jurewa ne My love, ina kasa sarrafa kaina in muna tare daurewa kawai nakeyi yau bazan iya ba ki bani dama na rungume ki dan Allah."

Lallai ma ya raina mata wayo wato ta bashi dama ya rungume ta bayan ya rik'e mata hannu ta nuna bata ji dad'i ba shine zai k'ara gaba, zatayi magana yace, "Sau d'aya tak my love, sau d'aya kawai daga yau bazan sake ba sai kin zama mallakina." Kafin ta bashi amsa ma ya matso kusa da ita sosai ya jawo ta jikin sa kanta ya kwanta a k'irjin sa ya rik'e ta gam yana sauke numfashi a hankali.

"Kar ki rabu dani my love, sonki zai iya yi min babbar illa. Ki zauna tare dani har abada, Ina sonki ina qaunar ki" ya furta har lokacin tana jikin sa idanun sa a lumshe.? Jin tana k'ok'arin kwacewa ya saka ya sake ta suka had'a ido ta sakar masa muguwar harara yayi murmushi ya danna lock d'in motar ta bud'e zata fita yace, "zan dawo na d'auke ki." Bata bashi amsa ba ta wuce ta barshi yana kallon ta har ta shiga gidan yayi murmushi ya kunna motar yaja yana jin nishad'i a zuciyar sa.

? ? ? ? A zaune ta samu Yaya Ummi tana kallo ta shiga da sallama ta amsa tana fad'in, "Ga amarya, ga amarya." Dariya Rauda tayi kad'an ta zauna tace, "Yunwa fa nake ji." Tace, "to acici, sai kije ki zubo ai." Ba musu ta ajjiye ledar da mayafi ta fita ta shiga kitchen ta debo shinkafa da wake ta dawo ta zauna tana ci.

Yaya Ummi tace, "Yarinyar nan kyau kike k'arawa wallahi, Anas zai more aure."
"Kuma shine ya kawo ni fa."
"Lallai, amarya ta ango yana ji dake sosai, gaskiya kinyi dacen me k'aunar ki tun baki wayewar haka ba."

Yaya Ummi ta d'auki sak'on Umman ta bud'e kafin ta tashi ta d'auko wata leda ta dawo kusa da ita ta zauna tace, "ajjiye abincin ga kaza nan ki cinye ta tassss." Rauda jin ance kaza ta ajjiye tace, "Yaya meyasa baki fad'a min ba kika bari na fara cika cikina da shinkafa?" ta fad'a tana fara cin kaza ta lumshe ido tace, "Dad'i na da Yayata ta iya dahuwar kaza."

Tsaki tayi tana kallon ta tana ji kafin taga ga ajjiye tace, "na k'oshi wallahi." Yaya ummi tace, "Sai kin cinye tass Rauda dan ke aka yita ta gyaran amarya, maza daure ki cinye ki shanye romon."
"Wallahi Yaya cikina ne zai fashe na kuma ci na k'oshi, sai dai anjima." Yaya tace, "to anjiman kya shanye. Yanzu kora da wannan ruwan in kin gama ga zuma nan ki sha koda cokali biyu ne."

Daman tana buk'atar ruwan tasha ruwan zuma kuma abar kwadiyi ce tana ta lasa suna hira kafin ta ajjiye ta had'a mata a leda tace, "in kinje gida sai ki dinga sha, amma ko bari sai nan da kwana uku sai ki kuma sha kar yayi miki yawa. Kina shan kaninfarin dai ko?." Rauda tace, "eh."
"Yauwa maganin sanyi ne kar kiyi sake."

"To Yaya. Ni na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login