Showing 168001 words to 171000 words out of 216282 words

Chapter 57 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

gurbin kujerar ya mulki kowa son ransa."

"Duk soyayyar da yake nunawa yana yiwa Asad ta bogi ce a zuciyar sa babu wanda ya tsana sama da Asad, kullum b'acin ransa ta ya Asad ya kasance abin so a wajan iyayen su shi ya koma baya? Ta ya kowa yake zancen Asad bashi ba? Ta yaya za'a ce shida Aliyu suna da makusa shi bashi da ita...?."

Shiru falon babu mai motsin kirki a cikin su kowa yayi shiru yana kallon Hafiz Mama kam ji take zuciyar ta tana gab da bugawa. Mai martaba yace, "ko kun san jiya da daddare Hydar ya shigo har d'akin da nake da niyar kashe ni? Ko kusan ya zuba min poison a a.c dan kawai na shak'a na mutu na bashi waje yayi abinda yake so, bai so yau tazo ba badan tonuwar asirin sa ba sai dan bai shirya kowa yasan waye shi ba dan bai gama tsara abinda yake so ya tsara ba. Hydar yayi kwantan b'auna ya kuma cimma nasara akan abubuwa da yawa amma lokacin bayyanar komai yanzu yayi."

Hafiz yace, "shine master planer, shine yake tsara muku komai a duk sanda yaso shiyasa nace dukkan ku a k'asan sa kuke. Yana amfani da voice changer yana magana daku matsayin mace ku kuma da yake kowa ya saka cuta a zuciyar sa babu wanda ya kawo tunanin da wa kuke magana kawai kun amince dashi. Ku in ba na cikin gida ba taya za'a dinga kawo muku labaran cikin gida wanda na gidan ma basu sani ba?" Ya fad'a yana kallon su dukkan su suma kuma shi suke kallo.

"Mallake Aliyu da Jidda tayi tafi masa dad'i fiye da kowa shiyasa in Mama ta tura shi da magani?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
 ya kai mata sai ya zubar ko shi ya shanye amma bazai kai masa ba. Da ace Abba ya bar Hydar ya tafi da Aliyu wata k'asar a jiya tabbas da sai dai gawar Aliyu amma bashi ba, sannan ya dawo kan Asad domin kuwa dukkan ku sai yaga bayan ku harda ke Mama domin kina k'okarin bashi matsala zai kawar dake dan cikar burin Hydar yafi masa komai a duniyar nan."

"K'arya kake Hafiz! K'arya kake Hydar d'ina bazai tab'a aikata abinda kake fad'a ba, taya Hydar d'ina yaga lafiyar da zaiyi abinda kake cewa shida yake kwance cikin ciwo a ko wanne lokaci?. Hydar yana son Asad bazai tab'a cutar dashi ba, Hydar yana son mahaifin sa bazai tab'a aikata abinda kake fad'a ga mahaifin sa ba, Hydar yana sona bazai tab'a yun?urin yin abinda kake fad'a min ba. Na amince duk abinda kuka fad'a Aliyu zaiyi tabbas ya aikata shi amma banda Hydar K'arya kake bazai tab'a yin abinda ake cewa zaiyi ba" hawaye sharrrr daga idanun Mama sai kuma ta dafe kanta tace,

"Ta ya ma Hydar zaiyi haka? Ta wacce hanya duk abinda ka fad'a za'a ce Hydar ne shi kad'ai ya aikata ta yaya hakan zata kasance banda K'arya?!" Ta fad'a cikin kuka tana kallon Hafiz da take ji kamar ta bindige shi.

Hafiz yace, "Ya aikata fiye da haka domin kuwa har laya ya saka Asad a kujerar zaman a office duk dan yayi masa Farraqu daga gidan nan amma Allah bai bashi sa'a ba. Hydar ya wuce tunanin ki Mama a gaban sa nake fad'ar komai nasan kuma komai domin tare ake shirin dani. Duka wannsn tunanin naku akan sa shiyasa yake cutar daku domin dukkan ku kun amince dashi amma shi kuma ta b'angaren sa ba haka abun yake ba. Shiyasa yayi nasara akaan Asad sabida yasan dukkan lagon Asad yasan abinda yake so yasan wanda baya so, yasan abinda yake ci yasan wanda baya ci. Da ace maqiyin ka na kusa dakai gwara yana nesa dakai domin maqiyin kusa yafi na nesa sharri."

Suhaima da take rik'e da Mama tace, "dan kai kana aikatawa hakan ba yana nufin ka yiwa Yaya Hydar wannan mummunan kazafin ba, wallahi K'arya kake Yaya Hydar babu ta inda zai iya aikata abinda ake fad'a, yana son yaya Asad karen Yaya Asad Bobby Yaya Hydar bazai iya cutar dashi ba balle kuma shi."

"Mama, Suhaima ya kamata ku daina rantsewa duk abinda kuka ji an fad'a ku amince dashi domin kuwa Hydar zai iya aikata abinda yafi haka ma. Kuna yiwa Hydar kallo a baibai ne amma Hydar ya wuce duk inda kuke tunani, dukka abinda aka fad'a yanzu kad'an ne daga cikin shirina kuma har gobe ina kan bakata ban sauka ba!" Muryar sa ta karad'e falon cikin kaushin murya mai fita a zafafe da nuna tsantsar isa da izza da kuma zallar mugunta a cikin ta.


Hydar!>?? @&?
[17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*081*

Dukkan su juyawa sukayi suna kallon sa ya d'aga gira guda biyu yayi murmushi mai kama da dariya kafin ya sauke numfashi ya kalli kowa na falo sai kuma ya tab'e baki har lokacin murmushi yake yi ya mik'e tsam ya zuba hannu a aljihu yana kallon su d'aya bayan d'aya yace, "Ki daina rantsewa Mama kar azumin kaffara yayi miki yawa a kanki, k'anwata ki bar kuka" ya fad'a yana kallon Suhaima kafin ta taka zuwa tsakiyar falon yana kallon kowa.

Mama suman tsaye tayi ta kasa motsi sai kallon Hydar da take yi da ya juye mata ya koma tamkar wani cikakken d'an ta'adda a kamannin sa. Hydar ya kalle su yace, "Eh duk abinda kace nayi na aikata gaskiya Hafiz yake fad'a ba k'arya ba" ya fad'a yana kallon Hafiz d'in yana murmushin rainin hankali.

"Nine master planer, kun jima kuna so ku ganni yau gani a tsaye a gaban ku kunyi murnar ganina?" Ya fad'a yana kallon su tare da wara musu hannayen sa. Ganin duk sun kasa magana sai ya kyalkyale da dariya ya dafa hannun sa sai ya kalli mahaifin sa yace, "Ina so mahaifina yasan AliyuHydar baiso kashe shi ba, inda yaso ganin bayan sa tamkar yadda zan take kiyashi haka zan take duk wanda naso. A wannan tafiyar babu nufin kisa sai dai za'a sha wahala."

Ya kalli Asad da yake kallon sa yace, "Ina sonka Asad kamar yadda nasan zuciyar ka tana zafi a wannan lokacin kana ji inama mafarki kake ba gaskiya ba, yadda kake qaunar Hydar baza kaso hakan ta kasance ba amma ta kasance domin ba mafarki kake yi ba. Kai kana tunanin a banza na goya maka baya ka auri wannan?" Ya fad'a yana nuna Rauda da yatsan sa ba tare da ya kalle ta ba har lokacin Asad yake kallo.

Sai kuma ya sake yin ya cize bakin sa yace, "Nayi ne sabida mafita tawa badan wai kana sonta ba sai dan ta silar soyayyar ta Mama ta tsane ka tayi maka baki ta daina fighting akan baka kujerar mulkin garin nan. Amma sai naga Mama bata saduda ba hukuncin ta akan yarinyar ne a kanka ba shiyasa na canja shiru. Tun dawowar ka nasan waye ya dawo kake raina min hankali wai matsayin kaine Aliyu baka san Aliyun ma a tafin hannuna yake ba balle kai, ka tuna yar da wayar ka da kayi a Cairo? Koda yake a yanzu nasan kasan nine na cire ta daga jikin ka dan nisanta ka da Mama."

"Duka abinda yake faruwa na sani, ka dawo ka koma Aliyu kake fita daga gidan nan matsayin Aliyu wasu suna d'auka da gaske Aliyu ne dan ko sarkin mota ya d'auka Aliyu yake d'auka yake fita dashi har yake kai masa wannan" ya fad'a yana sake nuna Rauda da yatsan sa sai yayi murmushi yana cize bakin sa yana binsu da kallo d'aya bayan d'aya.

"Duka ku kwnatar da hankalin ku ai yanzu aka fara kuna tunanin wai komai yazo k'arshe ne? Hmmm hatta wannan zaman da akayi yau yana daga cikin plan d'in master planer akwai na gaba wanda zai gigita ku gabad'aya ku. In har Hydar bai zauna a kan kujerar katagum ba babu wanda zai zauna ya kwana lafiya, ku rubuta wannan ku ajjiye!. Wannan yana nan tafe kuma zai zo in bai zo ba kuma ba sunana Hydar ba" Yana fad'a ya fita da baya kamar walqiya basu sake ganin koda kalar rigar jikin sa ba.

Luuuuuu Mama tayi ta zube a wajan a sume Suhaima tayi kanta a guje Asad ya taso shima da sauri ya rik'e ta amma ina ta suma ko numfashi bata yi, Fulani Rukayya da take zaune tana hawaye ta girgiza kai tace, "Dole ki suma Rabi'atu, abin suma ne ya same ki. In ma da abinda yafi suma kyayi abubuwan sun wuce tunani." Asad da yake hankali a tashe ya tara yatsun sa a kofofin hancin ta yaji bata numfashi hankalin sa ya kuma tashi sosai yace, "Muje asibiti" ya fad'a yana tallafo Mama.

"Asad ka bar Suhaima da Suhail su kaita asibitin ina buk'atar zaman ka a wajan nan, sannan a bincika inda Jidda take a ji ya yanayin jikin nata" Mai martaba ya bada umarni jin hakan Suhail Asad da Suhaima suka kai Mama mota suka tafi shi kuma ya dawo duk jikin sa a sanyaye da zai samu dama ya keb'e kansa babu abinda zai hana bai fashe da kuka ba.

Dawowa yayi ya zauna mai martaba ya kalle shi ya kalli Aliyu da yake a kwance idanun sa a kulle yayi murmushi yace, "Asad ka zama namiji ka danne zuciyar ka bana son ganin rauni a tare da kai ko kad'an." Mutanen falon ya kalla gabad'aya yace, "Ban amince wani hadimi ya samu wannan labarin ba dalilin da ya saka nace kowa yazo nan kenan, bana so maganar nan ta fita in kuma ta fita na samu labarin wanda ya fitar da ita akwai mummunan mataki a kansa. Yadda kowa yake d'auka Asad ne yake mulki aje a hakan bana so kowa yasan da canje akayi, bana so!" Ya sake fad'a da kakausar murya.

"Sa'adatu dake da Yahuza da Hafiz babu abinda zance muku haka zalika babu abinda zan yi muku, kowa ya aikata alkhairi ya sani haka kowa ya aikata akasin sa ya sani. Aliyu da yake kwance a k'asa yanzu hankalin sa yana barazanar barin jikin sa ya zamar muku abin kallo da darasi domin tare kuke shirya komai ga kuma abinda ya same shi nan, abinda ake kira qaiqayi koma kan masheqiya kenan anyi zalincin da Asad sai kuma ya k'are a kanku. Shi Allah haka yake ikon sa baya cutar da wanda bashi da hakki yana bayan mai gaskiya a koda yaushe yana kuma bashi kariya daga mutane irin ku. Kai kayi abinda kayi sabida kanka ita kuma tayi ne sabida kawai ra'ayin tane, ina so ku jira sakamakon ku wajan Allah domin bazai barku ba, hakkin cutar da wannan bawa da kuka yi sai yayi masa sakayya ko yanzu ko nan gaba. Ta inda Allah ya taimake ku babu ran wanda aka d'auka da wallahil azim babu abinda zai hana ban saka an yanke muku hukuncin kisa ba."


Dukkan su sunyi shiru suna jin abinda yake cewa Fulani Hajiya kuka take sosai nadama tana shiga zuciyar ta a yanyin da Waziri ya d'auko wayar sa jin kiran da ake masa yayi yawa, mai martaba ya kalle shi yace, "Amsa kira, ka kuma sakata a amsakuwa." Ba musu kuwa yayi yadda yace daga cikin wayar akace, "Ranka ya dad'e tun d'azu muke neman wayar waziri bamu samu ba, gida ne babu lafiya Mai sunan Hajiya mai babban d'aki da mai sunan mai martaba aka same su a kwance a falon Waziri dukkan su kumfa na zuba daga bakin su. Labari mara dad'i ranka ya dad'e dukkan su Allah karb'i rayuwar su."

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!" Dukka jama'ar falon suka fad'a shi kuwa katse kiran yayi ya kulle idanun sa a daidai lokacin aka kwalla kiran sallar la'asar. Bud'e idanun sa keda wuya ya fara zubar da hawaye kamar k'aramin yaro yana kuka sosai mai had'e da hawaye jin lokaci d'aya y'ay'an sa guda biyu wanda yafi so a duniya sun mutu.

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, muna rok'on Allah ya jiqan su ya gafarta musu ya sa sun huta ya kuma karb'i baquncin su. Abinda ya kamata ayi yanzu in an idar da sallar la'asar za'a kai su makwancin su. Taron nan dole ya tashi a yanzu" Mai martaba ya fad'a cikin maganar mai d'auke da taushi a cikin ta.

Zabura Waziri yayi ya fita da sauri duka mutanen d'akin kowa ya fita ya bada umarnin a tafi da Aliyu gida Uncle suka fita dashi dan zuwa lokacin ko motsi ma bayayi sai numfashi kawai da yake fitarwa. Falon ya rage daga Asad sai Abba sai kuma su Baba da suke zaune suna jin abu kamar almara kansu duk ya kulle.

Abba yace, "Malam Adam da iyalan ka ina yi muku godiya akan dukkan abubuwan da suka faru, ina fatan kuma dukka ku kun fahimci abinda ya faru an kuma tabbatar babu hannun Asad a dukkan abinda ya faru. Hakika naji dad'in yadda kuka karb'i k'addarar nan hannu biyu na sake tabbatarwa a zuciyata itace matar Asad ta cikin mafarkin sa. Y'ata Rauda ina fatan kin tabbatar da har gobe kina matsayin matar sa ne ko?." Rauda hawaye take yi sosai a lokacin ta kasa magana mai martaba yayi murmushi yace, "Kar ki damu ki daina kuka ita daman rayuwa haka take, wanda ka bawa amanar kanka da rayuwar ka shine yake cutar dakai a wani lokacin. Shiyasa amana tayi karanci ba kowa ne yake tamk'a amanar wani abu nasa hannun mutane ba balle kuma rayuwar sa. Asad yaso Hydar sosai har gobe yana son sa kaf y'an uwan sa yafi son Hydar yanzu ga abinda Hydar yayi masa. Kuyi ha?uri dukkan ku abubuwan da suka faru a baya yanzu komai ya wuce in sha Allah."

"Ta silar ki komai ya bayyana y'ata shiyasa dukkan su baso son dawowar ki domin ke tamtar Inuwa kike a gare shi tun a mafarki ya sanki yake kuma rayuwa dake. Ke alkhairi ce a cikin gidan nan ta silar ki abubuwa da yawa sun bayyana wanda ba'a yi tunanin bayyanar su ba. Allah yayi muku albarka dukkan ku ya albarkaci rayuwar ku yasa kufi k'arfin dukkan maqiyan ku."

Baba ya gyara zama ya amsa da Amin kafin yace,"Allah ya taimake ka babu komai, komai ya wuce sai dai muyi fatan alkhairi nan gaba."
"Ma sha Allah. Yanzu abu na gaba da zamu fuskanta shine dawowar ta cikin gidan sarauta matsayin matar sa, ina so ayi gagarumin biki da dukka jama'a zasu shaida matar sarkin katagum ce. Ba kuma naso a d'auki lokaci nan da kwanaki uku zuwa hud'u nake so ayi komai a gama dan ina so a dawo da martabar katagum da aka rasa. Ina fatan babu takura a cikin lamarin."

Baba ya sake cewa, "Duk abinda mai martaba yace shine daidai a wajan mu, Allah ya kaimu lokacin da rai da lafiya." Mai martaba ya amsa da amin ya kalli Asad yace, "banji kace komai ba? Ko na k'yale ka sai kaje can gidan?" Ya fad'a cikin zolayar Asad d'in. Murmushi ya kubce masa wnada baiyi niya ba ya shafa kansa yana jin nauyi da kunyar mahaifin nasa. Shima murmushin yayi yace, "Muje muyi sallah ayi jana'izar yaran da aka rasa" ya fad'a yana mik'ewa kowa ya mik'e ya kalli Baba yace, "Malam ya kamata a tsaya a samu ladan jana'iza in yaso sai su matan su tafi gida." Tare suka fito yana gaba Asad yana bayan sa har lokacin yak'i kallon inda Rauda take balle ma yayi mata magana.
Mota Umma da Rauda suka shiga aka tafi dasu gida su Baba kuma aka shiga masallaci akayi sallah.

*&&* A b'angaren Waziri lokacin da ya koma gida ya tarar har an musu suttura har lokacin kumfar bata daina fita daga bakin su ba, wani abu yaji mai nauyi ya tsirga masa ya tsaya a tsakiyar zuciyar sa ya fita da sauri zuwa falon nasa da akace a nan aka gansu. Shigar sa keda wuya yayi karo da kwalbar turaren da aka bashi wanda akace masa matuk'ar mai martaba da Asad ya shek'e su ya gama zaman gida kenan domin guba ne a cikin sa bana wasa ba.

Kai ya dafe yana kallon kwalbar dan yasan Y'ay'an sa guda biyun da suka rasu akwai su da son turare tabbas sun shigo sun ganshi sun buWe da nufin jin khamshin sa ya zama silar barin su duniya, zama yayi a kan kujera ya dafe kai maganar mai martaba ta fad'o masa inda yake cewa akwai sakayya ko yanzu ko nan gaba.

Bai san ya kuma fashewa da kuka ba zuciyar sa na k'una tashin hankalin sa ya nikku dan ya tabbatar shine ya kashe y'ay'an sa a dalilin son zuciyar sa. Bai san lokacin da ya d'auka a haka ba sai buga k'ofar yaji ana yi yana d'ago kai suka had'a ido da Suhail da idanun sa shima yayi ja alamun yasha kuka shima yace, "Ana jiran Abba dan gabatar da jana'iza" ya fad'a da girmamawa kansa a k'asa.

Haka ta taso jiki a salub'e badan yaso ba yayi gaba Suhail yana bin bayan sa limamin garin Katagum yaja sallar gawar aka sallace su daga nan aka wuce dasu gidan su na gaskiya.


_Son zuciya hausawa suka ce b'acin ta. Allah kasa mufi karfin zuciyar mu Amin._=?-?=?-?=?-?
[17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*082.*

? ? ? ? ? ? Tunda aka shiga da Jidda d'akin da za'a duba ta Mum take safa da marwa hankalin ta ya tashi abubuwa biyu sun cushe mata zuciyar ta a wannan lokacin, tunanin abinda ya faru da kuma rashin lafiyar Jidda sun d'aga mata hankali sosai ta kasa nutsuwa ko kad'an.

Daddy ne ya k'araso wajan ya kalli Mum d'in yace, "Sadiya lafiya? Meya faru da Jiddan haka?." Mum bata iya magana ba dan bata da nutsuwa a wannan lokacin nuna masa d'akin tayi yaja ya tsaya shima yana kallon d'akin zuciyar sa na harbawa cikin tsoron abinda zai biyo baya.

Tun suna tsaye sai da suka zauna jikin Mum har rawa yake yi so take ma ta zubar da hawaye ma ta kasa sabida bala'in rud'anin da take ciki. BuWe d'akin da aka shigar da Jidda akayi likita da nurses biyu suka fito Mum

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login