Showing 63001 words to 66000 words out of 216282 words

Chapter 22 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

irin nauyi yake ji a zuciyar sa karo na farko a rayuwar sa yayi alqawari bai cika ba nan take tashin hankalin sa ya sake ninkuwa. Wayar sa da take kusa dashi yaga kira na shigowa ya kalla yaga Khalifa ne yake masa waya ya sauke numfashi dan ya tabbatar maganar Rauda zaiyi masa shi kuma bai san me zaice masa ba haka ya share har ta katse.

Numfashin sa ya cigaba da janyowa da dak'yar kafin kansa yayi mugun sarawa k'irjin sa ya fara up and down daga zazzaSi ya rufe shi lokaci d'aya. Suhaima ce ta shigo ganin halin da yake ciki ta kwallawa Mama kira ta tawo a guje ganin kamar zai mutu ya saka su danna emergency bell nan take sai ga ma'aikatan hotel d'in sun bayyana aka d'auke shi zuwa asibitin hotel d'in.

A b'angaren Rauda lokacin da suka bar Four Seasons hotel a mota ya saka ta yaja suka wuce estate d'in ma'aikata y'an Nigeria wanda suke aiki a garin irin sa. Gida ne mai kyau plat mai d'auke da ado tun daga wajan sa har ciki, fita yayi ya bud'e gate d'in sannan ya dawo ya shiga da motar ya kuma fita ya sake kulle gate d'in kana ya zagayo ya bud'e bayan mota dan tana kwance a bayan motar yace, "Zaki iya fitowa?." Kai ta d'aga alamun eh dan bata so ya rik'e ta ta fito dak'yar ta iya tsayawa tana takawa a hankali har cikin falon gidan ya gyara mata waje ta zauna.

Fita yayi ya shigo da kayanta sannan ya ajjiye ya shiga cikin gidan Jim kad'an ya dawo da magani da allura a hannun sa, ajjiyewa yayi ya k'arasa fridge ya d'auko yogurt ya dawo ya mik'a mata yace, "karb'i kisha sai kin saka wani abu a cikin ki magani zai miki aiki." Kallon sa tayi tana so tayi magana sai kawai hawaye ya fara zubo mata sharr duk sai yaji ya damu yace, "Haba chocolaty wannan kukan da kike yi wai duk na meye ne? Koma meye yake damun ki ki adana shi a gefe kisha magani tukunna."

Mik'a mata ya kuma yi yaga ta kalla tana goge idanun ta sai tace, "kaina."
"Na san yana miki ciwo shiyasa na baki dan ki sha sai kisha magani."
"Bazan iya sha ba."
"Zaki iya, karb'i" ya fad'a yana sake mik'a mata ta karb'a ta kai bakin ta tayi kurba d'aya ta ajjiye shi a jikin ta bata kuma sha ba.

"Bazan cutar dake ba Rauda, ina miki kallon k'anwata duk abinda zan yiwa k'anwata da muke jini d'aya shi zan miki. Ki kwantar da hankalin ki ki nutsu in ma zuciyar ki na rawa a kaina kar ki damu wallahil azim bazan cuce ki ba. Asad ya sanni farin sani in koda na cutar dake zai nemo ni duk inda nake" ya fad'a cikin sigar kwantar da hankali yana kallon ta.

Bata tanka ba ta d'aga gorar nonon tana sha har ta d'an sha da yawa ta ajiiye ya bata magani ta sha ya kalle ta yace, "shiga wannan d'akin da yake kallon ki huta zan kira deaf d'in naji ina yaje ya barki security suka yi miki haka. Kayan ki suna ciki in zakiyi wanka. Matar gidan bata nan ne tana wajan aiki amma nasan tana hanya." B'oyayyiyar ajiyar zuciya tayi jin yana da aure sai hankalin ta ya kwanta daman tunanin ta ta inda zata zauna dashi a gida d'aya shi ba wani nata ba bata ma tab'a ganin sa ba sai da tazo k'asar.

Bayan ta shiga d'akin kwanciya tayi wai ko zatayi bacci amma ina bacci ya k'auracewa idanun ta sai tunanin da tasan zai damu zuciyar ta, babban tashin hankalin ta in ta koma gida me zata cewa iyayen ta? Auren da bai cike sati hud'u ba ya mutu ko mutu ko kuma shiru zatayi da bakin ta?, sanar dasu zatayi ta zama bazawara ko kuma shiru zatayi?. Da wannan tunanin bacci ya d'auke ta dan a maganin da ya bata harda na bacci dan ta huta.

Ta jima sosai tana baccin bata farka ba sai dare ta kuwa tashi ciwon kan ya tafi sai kad'an ta kalli agogo ganin sallah ta wuce ta sai ta mik'e ba shiri ta shiga band'akin tayi wanka tare da alwala ta fito ta bud'e kayanta, gabad'aya sababbin kayan aka zuba mata a cikin akwatin wanda taje dasu guda d'aya ce. Hawaye taji suna niyar zubo mata tayi saurin mayar dasu dan bata ga amfanin kukan ba ta d'auki wacce taje da ita d'in ta saka ta tayar da sallah.

Bayan ta idar tayi addu'a kamar ko yaushe ta tashi ta koma gefen gado tana yamutsa fuska ji take gefen marar ta yana ri?ewa, d'an k'aramin tsaki tayi dan tasan hakan yana nufin period d'in ta yana gab da zuwa.

Tagumi tayi hannu biyu da tunanin abinda ya fad'o mata zata kawar dashi ta koma wani amma ta kasa sai da ta tuna.
_i promise you I will never ever leave you no matter what!._ kalmar sa k'arshe kenan tsakanin su ta mayar da kwallar idanun a lokacin aka fara k'wank'wasa k'ofar d'akin.

Sai da ta nutsu sannan ta amsa bai shigo ba yace, "In zaki iya ki fito ku gaisa da Madam." Ba musu ta tashi ta yafa mayafin ta ta fita falon ta same su a zaune suna cin abincin ta zauna da murmushin yak'e a fuskar ta kafin tayi magana matar tasa tace, "Sannu Rauda, ya jikin naki?."
Ganin matar ta sakar mata fuska sai taji dad'i tace, "Da sauk'i. Ina wuni."
"Lafiya lau, ya zaman bak'unta?." Rauda tayi murmushi bata ce komai ba tace, "kiyi hak'uri yau aiki ya min yawa shiyasa ban dawo ba kina ta zaune ke kad'ai. Ga abinci kici ko zaki samu k'warin jikin ki" ta fad'a tana tashi ta zuba mata dankali mai Romo da naman kaza a cikin sa an yanka shi k'ananu.

Rauda tace, "da kin barshi bana jin yunwa." Ta kalli Khalifa tace, "kaji fa Dear wai bata jin yunwa" ta fad'a tana mik'a mata tana fad'in, "kici Rauda mara lafiya sai da abinci." Ba yadda zatayi ta fara ci a hankali bata jin d'andanon abincin gabad'aya dan tayi loosing appetite. Matar tasa ta koma kusa dashi ta zauna suka cigaba da hira harta ci iya yadda zata iya ta ajjiye.

Khalifa ya kalle ta yace, "Rauda na kira shi bai d'auka ba nayi masa message still bai reply ba, kin gwada kiran sa ke?." Shiru tayi bata amsa ba ya kuma cewa, "Halin Asad ne sai shi wallahi, wata?ila yana can ya keb'e kansa yace baya son magana amma duk da baya baici ya barki ke kad'ai ba." Rauda ta kalle shi idon ta na kawo ruwa tace, "ni dan Allah kasa na koma Nigeria basai kayi magana dashi ba."

Da mamaki yace, "meyasa zaki koma ba tare da sanin sa ba? Naga tare kuke kuma yayan kine yana dakyau yasan halin da kike ciki kafin ki tafi." Rauda idanun ta yayi rau-rau tace, "basai ka sanar dashi ba ko kayi masa maganar ma bazai saurare ka ba, dan Allah ka saka ni na koma gida na gaji da zaman nan ina son ganin Ummana." Kallon Ramla matar sa yayi itama ta kalle shi Khalifa yace, "kar ki damu zaki tafi Nigeria in sha Allah. Amma ina shi Asad d'in yake? Meyasa ya tafi ya barki?, ke ba k'anwar sa bace ba?."

Rauda tayi shiru bata amsa Khalifa yace, "ko ke ba k'anwar sa bace?." A hankali tace, "k'anwar sace."
"To ina yake? Kin kira shi ke da kanki?." Sai kawai ta fashe da kuka Ramla ta kalle shi ta girgiza masa kai alamun ya k'yaleta sai yace, "Yaushe kike son komawa Nigeria d'in?."
"Gobe" ta fad'a murya na rawa.

Khalifa yace, "Allah ya kaimu sai ki tafi." Ramla matar sa tace, "Ba jibi daman zaka tafi ba? Ta bari sai jibin sai ku tafi tare kaga ba wani sanin kan garin nan tayi ba bai kamata ta tafi ita kad'ai ba. Kema a bauchi kike?." Kai ta girgiza alamun a'a tace, "Katagum." Ramla tace, "bauchin kenan ai, shima a can yake abokin Yayan kine zai mayar dake har gida kinga ba saba tafiya kikayi ke kad'ai ba gwara ki bari in Allah ya kaimu jibin sai ku tafi."

Rauda ta d'aga kai alamun to sukayi shiru dukkan su Ramla ta lura a takure take sai tace, "ki shiga d'akin ki huta." Kamar jira take ta mik'e ta shiga ciki tana goge idanunta. Ramla ta kalle shi tace, "Shine yace maka k'anwar sace?." Khalifa ya girgiza kai alamun a'a yace, "Nine dai nake ganin hakan amma bai fad'a min ba gaskiya."
"Ni sai nake ganin kamar ba k'anwar sa bace."
"To wacece d'in sa da zasu zauna waje d'aya shida ita? Kin san waye shi kuwa wajan kamewa?."

"Ka sani ko matar sa ce?." Wara idanu yayi yana kallon ta yace, "Dan sarkin Katagum ne fa ta yaya zaiyi aure ba tare da an sani ba? Koma ace ba kowa bane ta yaya Asad zaiyi aure bamu sani ba?." Ramla tace, "to ka sani ko baya buk'atar a sani d'in ne? Kayi tunani yanayin ta bai gwada k'anwar sa bace in ba kuma ta tabbata ba k'anwar tasa bace wacece d'in sa? Budurwa sa kenan zamu ce?."

Ya girgiza kai yace, "A'a Asad bazai tawo da budurwa wata k'asa ba nasan halin sa."
"To kaga kenan indai har ba k'anwar ba bace ba to matar sace, yanayin yadda take magana kamar sun samu matsala ita dashi ne." Ya girgiza kai cikin gamsuwa yace, "na dai fi tunanin k'anwar tasa ce, abinda ya d'aure min kai ina yaje ya barta?. In ya kasancewa matar sace babu ta yadda za'ayi ya tafi ya barta ita kad'ai domin kishin sa bazai barshi ya iya barin ta ba. Shine fa wanda nake fad'a miki in ya nuna takalmi yace yana so tofa duk yadda kuke dashi kar ka saka wannan takalmin yadda yace yana so nasa ne shi kad'ai, in kuma ta faru ya bar maka shi baya so kiyi tunani ace matar sace ya abin zai kasnace?."

Ta girgiza kai tace, "akwai dai wani abun a biye Dear amma ni ban yadda k'anwar sa bace ba kallon matar sa nake mata, matsala suka samu har hakan ta kasance amma bazai bar k'anwar sa inda ka ganta ba. Tunda ya kasance mai kishi dole yayi kishin k'anwar sa. Kuma k'anwar sace zai tawo da ita k'asar nan su biyu kawai har ayi mata aikin k'afa ba tare da mace ba? Ka tuna suna da kud'in da za'a tawo da masu jinyar ta bama guda d'aya ba amma aka had'o su su biyu kawai, in ba matar sa ba babu wacce zai zauna da ita daga shi sai ita."

Khalifa girgiza kai yace, "to Allah ne dai masani, zan jira naga zai kira ni daga yau zuwa gobe in bai kira ba kawai sai na mayar da ita Nigeria d'in mayi magana dashi daga baya." Daga haka suka cigaba da hira kafin Khalifa ya fita.
[17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*045.*

? ? ? ?? B'angaren Asad yayi baccin sosai mai cike da sabbin mafarkai kafin ya farka dan sai da aka amsa allurar bacci sannan baccin ya d'auke shi. A gadon asibiti ya ganshi ya kalli hannun sa yaga ruwa yana shiga ya dafe kansa yana sauke numfashi a sannan Mama da Suhima suka shigo.
Mama ta kalle shi tace, "Sannu Asad, kaji dad'in jikin ka?." Kai ya d'aga alamun eh sai ga likita ya shigo ya k'araso inda yake ya zare masa ruwan jikin sa ya sake auna bp sa ya kalli Mama cikin turanci yace, "bp nasa ya sauka saura kad'an, daman ya firgita ne dalilin da ya saka jinin ya hau kenan but yanzu in ya samu nutsuwa zai dawo daidai."

Mama ta girgiza kai kawai bata ce komai ba tana binsa da kallo jin wai harda hawan jini akan kucakar yarinyar da bata wuce mai goge masa takalmi ba. A sannan suka koma cikin d'akin su ya shiga d'aki yayi alwala yayi sallah dan sosai yaji dad'in kansa ya rage ciwo sosai.

Bayan ya idar da sallah Suhaima ta shigo ta zauna kusa dashi tace, "Kayi ha?uri Yaya Asad na bata passport d'in ta da wayarta da kuma kayanta in sha Allah zata koma Nigeria. Sai dai kuma babu kud'in ticket" Suhaima ta daki kanta tace, "na manta ban bata ba Yaya, yanzu da wanne kud'i zatayi amfani ta siya?." Asad sai murmusa ya cize bakin sa ya lumshe ido ba tare da yace komai ba. Suhaima tace, "kazo falo inji Mama" tana fad'a ta Mike ta fita jikin ta a sanyaye.

Bai jima ba ya fito tunda ya fito daga d'akin take kallon sa har ya k'araso ya zauna a kusa da k'afafun ta bata daina kallon sa ba tace, "Asad kaga yadda ka rame lokaci guda kuwa?." Shiru yayi baice komai ba kafin ta share zancen itama tace, "gobe zamu koma Nigeria akwai abinda kake so ka siya ne? In akwai ka siya yanzu dan jirgin safe zamu bi." Dak'yar ya fizgo maganar yace, "Babu."

"To yayi kyau, in muka tafi da safe nasan zuwa azahar zamu je bauchi mu shiga katagum zuwa jibi dai nake so sarautar ka ta dawo hannun ka a had'a shagalin da bikin auren ka da Jidda a huta." Baice komai ba ko d'agowa ma baiyi ba balle yayi magana. Kamar ya tuna wani abu sai ya kalli mahaifiyar tasa yace, "Ya jikin takawa?." Mama tace, "Bamu samu Hydar a waya ba har yanzu." Ya kalli Suhaima yace, "Wayana."

Tashi tayi ta shiga d'akin ta kawo masa ya karb'a yana dannawa yaga message d'in Dr Khalifa a notification hannun sa na rawa ya danna ya bud'e yaga abinda yace kamar haka, _Prince ina kaje ne ina ta kiran baka picking call d'in?, sister ka tana gidana nazo hotel wajan ka na tarar da ita security suna neman arresting d'in ta. Ka kira ni in kaga message d'ina bata da lafiya ma._

_Tana gidana._ abinda ya sake dawo masa kansa kenan ya runtse idanun sa yayi saurin fita daga message d'in ya shiga wajan kira yana nemo Hydar zuciyar sa na zillo ya danna kiran wayar Hydar. Bai d'auka ba ya sake kira nan ma bai d'auka ba sai ya k'yale shi Mama tace, "Bai d'auka ba ko?." Kai ya d'aga alamun eh tace, "muma baya d'auka in mun kira, Allah yasa ba jikin nasa bane babu dad'i."
"Wanne County suka tafi?" Ya tambaya muryar sa na shaking.
"Germany" Suhaima ta bashi amsa da tausayi.

"Zan iya siyan ticket naje Mama?." Ta kalle shi ya sunkuyar da kai tace, "A'a daga nan babu inda zaka je sai Nigeria, ka daina wani tunani in ba wannan ba." Ya girgiza kai kana yace, "Allah ya wuci zuciyar ki." Shiru ya ratsa tsakanin su kafin yace, "in an min izini ina so na sha iska." Mama ta kalle shi kamar baza tayi magana ba sai kuma tace, "jeka, amma in kayi abinda na haramta maka kasan sauran."

"Godiya nake" ya furta a hankali ya tashi ya fita daga falon ya sauka zuwa reception ya fita ya tsaya a kan titi kawai yana kallon mototoci hannun sa hard'e a k'irjin sa. Wayar sa tayi k'ara ya d'auko yaga sunan Hydar ya d'auka ya saka a kunne daga can b'angaren yace, "Sorry Deaf ka kira ni muna tare da Takawa ana bashi magani."
"Meyasa ba'a sanar dani bashi da lafiya ba?."
"Shi ya hana a fad'a maka shiyasa ban fad'a ba. Ya kake naji maganar ka wani iri kamar baka da lafiya."

Asad baice komai ba ya juya ya shiga hotel d'in ya zauna a reception kana datse kiran ya kira shi video call dan yana so yaga mahaifin sa, d'auka Hydar yayi fuskar sa ta bayyana a screen d'in wayar shima haka tasa fuskar tajewa Hydar daga can b'angaren Hydar yace, "Subahanallah! Deaf meya same haka? Naga ka rame sosai." Asad yace, "nuna min Abbana."

Ba musu ya juya Camarar ta baya ya haska mai martaba da yake kwance cikin wata na'ura kamar mai bacci, har kusa dashi Hydar yaje yana sake haska masa shi yana cewa, "tunda muka zo yake a haka sunce nan da kwana uku zai farfad'o in sha Allah kuma za'ayi nasara."

"Anya kunje asibiti mai kyau?" Ya furta a hankali cikin tashin hankalin ganin yanayin da mahaifin nasa yake ciki. Hydar yace, "kasan dai duk abinda zanyi dan ganin ya samu lafiya zanyi Deaf, likita har daga India munyo booking gobe zaizo, mun gayyato na nan? Egypt ma shima zai zo a had'u su a duba ko za'a gano matsalar dan nan har yanzu basu gano komai ba.
Asad yayi shiru baice komai ba Hydar ya kuma cewa, "ka sanar dani dalilin wannan ramar taka Asad, ina ita Raudan take?."

Shiru Asad ya kuma yi ya sauke ajiyar zuciya kana yace, "Komai ya k'are Hydar." Hydar ya kalle shi bayan ya dawo da camera front yace, "ya k'are akan me? Kar kace min Mama tayi nasarar raba ku?" Ya fad'a yana kallon sa da alamun tashin hankali. Asad yayi shiru baice komai ba yana kallon Hydar kafin ya janye idanun sa yace, "ka kula da Abba dan Allah, zanzo nan kusa in sha Allah" yana fad'a ya datse kiran ba tare da ya bashi amsa ba.
Shiru yayi na wani lokaci yana kallon wani wajan daban kafin yaja siririn tsaki ya tashi ya koma ciki.

Kamar yadda Mama ta tsara da safe suka dira a airport k'arfe bakwai da rabi na agogon Cairo jirgin su ya lula sama suka nufo Nigeria. K'arfe d'aya saura suka sauka tun kafin su taso an sanar da driver da zai d'auko su a airport d'in suka same su suna ganin fitowar su a guje suka k'araso aka karb'i kayan hannun su aka take musu baya, mota personal Asad ya shiga shi kad'ai Mama da Suhaima suka shiga aka d'auki hanyar katagum.

Gudu suke sosai nan da nan suka shiga katagum aka isa gidan sarki aka bud'e gate motar su ta shiga cikin gidan, da sauri aka fito aka bud'ewa Mama k'ofa shi kam Asad kafin a bud'e masa ma ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login