Showing 129001 words to 132000 words out of 216282 words

Chapter 44 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

biyo bayan ta tace, "Akan me za'a k'yale ta? Kenan in ta kashe ki shikenan taci riba?." Mama tace, "bamu da hujja Jamy, dan Allah ku bani waje ina so na huta." Ba musu ta fita tana k'wafa ranta duk ya b'aci matuk'a.

Bayan kamar awa biyu Suhaima ta shiga wajan Mama ta ganta a zaune batayi magana ba sai ta fita zuwa? kitchen ta had'o mata shayi mai zafi dan tasan bata ci komai ba ta tawo kawo mata.
Hydar ta samu a wajanta ta zauna tace, "Allah yaja da ran Mamana, baki ci komai ba tun safe ki daure kisha tea d'in nan ko zaki ji dad'i." Hydar ya karb'i cup d'in yace, "Mama dan Allah kisha." Ta yamutsa fuska tace, "Hydar bana so."
"Please Mahhh!" Ya furta a sanyaye yana kallon ta ta mik'a hannu ta karb'a ta rik'e a hannunta amma bata sha ba.

Shiru basuyi mata magana ba ta kafa kai a kofin tasha ta sauke sai taji yayi mata dad'i yaji kayan khamshi hakan sai ya saka tasha da yawa ta ajjiye ragowar tayi tagumi, Hydar ya cire hannun ta yace, "Dan Allah Mama." Idanun ta ya ciko da kwalla tace, "Aliyu baya nan, Asad ya guje ni sai yaga dama yake zuwa inda nake, Sadiya tana so ta kashe ni, Jidda tana yi min wula?ancin da take so, mutanen gidan nan gabad'aya sun raina nj ya kuke so nayi?. Bani da uwa bani da uba y'an uwana suna nesa dani me kuke so nayi in ban damu ba?."

Shiru sukayi ganin tana hawaye Suhaima tace, "Amma ranki ya dad'e damuwar ciwo take saka miki, likita yace damuwar da kike sakawa tayi yawa ya kamata ki rage kodan lafiyar ki." Ta sauke numfashi tace, "Nafi buk'atar mutuwa ta a yanzu." Shiru sukayi jin abinda tace ko wanne kansa a k'asa zuciyar su duka a raunane.

Cikin ta taji yana juyawa sai taji tana jin amai ta yamutsa fuska tace, "Hydar bani maganin ciwon ciki a cikin drawer." Ba musu ya juya yana neman maganin yaji ihun Suhaima tana cewa, "Yaya Hydar Mama!" Ta fad'a tana yin kanta suka ga tana shak'uwa idanun ta na juyewa suna komawa farare babu alamun bak'i a cikin farin abu na fita a bakin ta kafin Hydar ya k'araso tuni Mama ta zube akan gado babu numfashi.

*&&&*

? ? ? ? ? ? "Ashe zaku iya cin amanata ban sani ba?" Aliyu ya fad'a yana kallon Waziri da hajiya idanun su sunyi fik'i-fik'i alamun marasa gaskiya. Gyara tsayuwa yayi jin sun kasa magana yace, "baza kuce komai ba?." Waziri yace, "Aliyu ka saurare ni."
"Kace min me?."
"Abinda kake tunani sam ba haka bane ba, mu kan mu bamu san meyasa ka maqale a wata k'asar ba."

Ya harde hannayen sa a k'irji yana bin su da kallo yace, "Shine baku tab'a nema na ba?."
Fulani Hajiya tace, "Na kira ka bana samun ka." Yayi murmushi mai kyau ya taune lips d'in sa yana jin d'aci a zuciyar sa yana girgiza kai.

"Amma yanzu tunda ka dawo zamu d'ora daga inda muka tsaya ko Fulani?" Ya fad'a yana juyawa ya kalle ta ta d'aga kai tace, "Daman mun rasa wanda zai shafawa Asad maganin da zai bar karagar nan baki d'aya tunda ka dawo mu abin murnar mune ai."

"Da ban dawo bafa? In kuka yi nasarar shafa masa maganin waye zai hau karagar kenan?." Alamun rashin gaskiya ya bayyana a tare dasu suks kalli juna Hajiya tace, "Ai bai ma farun ba, ka daina tuna baya dan Allah muyi abinda yake gaban mu yafi mana alkhairi."

"Ai bazan kuma amincewa daku ba domin dukkan ku munafukai ne, kunce min matar Asad baza tayi ciki ba sai gata da ciki har ya bayyana ko bamuyi haka daku ba?." Waziri yace, "Sammatsi aka samu ne ranka ya dad'e amma yanzu zamuyi iya bakin k'ok'arin mu koda yaron yazo duniya zamu kashe shi dan baza mu bari y'ay'an sa su Shura ba."

Ya murmusa kana yace, "Ita mamana me tayi muku kuke son kashe ta?." A tare suka wara idanu suka ce, "Kisa? Mu din?." Banzan kallon da yayi musu ya saka waziri yace, "bamu tab'a k'okarin kashe Rabi'atu ba, to akan me ma zamu kasheta muda ba ita muke hari ba?." Aliyu yayi murmushi mai kyau ya d'an sosa goshin sabaice komai ba waziri yace, "Yanzu ina tare da maganin da za'a shafa masa ayi maganin matsalar mun tura Suhail amma ya kasa yin komai, kai kad'ai ne zaka kawo k'arshen matsalar nan."

Aliyu ya zuba hannu a aljihu yana kallon su d'aya bayan d'aya yayi shiru baice komai ba duk suka tsargu ganin irin kallon da yake musu yana murmushi wanda yake basu tsoro dan basu san shirin sa ba sun kuma san halin sa akwai dan bazan wayo, "well, ku kawo mu gani." Waziri ya washe bakin sa ya saka hannu a aljihu ya d'auko shi a kwalba ya mik'a masa ya kalla ya kalli wazirin sannan ya karb'a Waziri yace, "Kana shafa masa wannan an tabbatar mana da awa biyu bazata cika ba zai haukace kaga shikenan babu sarauta a hannun mahaukaci."

Aliyu ya jinjina kai yana girmama mugunta irin tasu amma yafi su kaifin tunani dukkan su buga su zai dinga yi kamar ball shi kad'ai yasan mai ya tsaya da kuma abinda zai aiwatar yace, "Da an shafa masa shikenan an gama ka tabbatar?." Waziri yace, "An gama na tabbatar da wannan." Aliyu ya juya ya bar wajan ya shiga mota yaja ya tafi ba tare da yace komai ba.

Hajiya ta kalle shi tace, "Ni nasan za'a yi haka sai da nace ka kashe Aliyun tun ba yanzu ba kak'i, wayon jaraba ne dashi zai iya lalata mana komai, dawowar sa barazana ce ga sarautar ka domin bazai bari kayi ba sai shi." Yayi murmushi yana kallon inda Aliyu yabi yace, "Barshi ya gama yi mana wannan aikin ya shafawa Asad d'in tukunna kiga yadda zanyi dashi, ai yadda ya shafawa Asad shima haka zan saka a shafa masa an fad'a miki k'aramin kaine dani?, duk wannan marairaicewar da kika ga ina yi ina sane tarko ne. Haka na tsara ko master planer da taji wannan sai da tace tsarin yayi ko ita iya abinda zata iya kenan."

Fulani tayi ajiyar zuciya tace, "Har naji dad'i domin na tsani Rabi'atu tsana maimunin gaske,? haka na tsani y'ay'anta." Yayi murmushi yace, "Yanzu aka fara wasan fa, barni dashi kawai."

Aliyu da yake tafiya ya saka bt a kunnen sa yana sauraron duk abinda suke fad'a ta cikin bt d'in ya murmusa ya daki sitiyarin motar yace, "Naku wasa ne tunda na dawo komai yazo k'arshe" ya fad'a yana sake take speed d'in motar? yana k'warara gudu akan titi.

*&&&*

? ? ? ? ?? Yadda babu wanda yasan ya fita haka babu wanda yasan shine ya shigo sai masu gadin k'ofar sa yana hawa sama bai nemi Jidda ba ya shiga d'aki ya kulle kansa abubuwa sun cushe masa kansa yama rasa wanne kalar tunani zaiyi yaji fad'i. Zama yayi a gefen gado yayi tagumi yana kallon wani wajan daban yaji ana buga masa k'ofa.

Yasan Jidda ce domin shi bashi da lokacin ta a halin da yake ciki yana buk'atar kebe kansa amma yasan bazata gane ba, "My king pls ka buWe magana zamuyi."
"Jidda please leave, I need rest" ya fad'a a sanyaye yana kallon k'ofar.
"Pls my king magana kawai zan maka fa." K'aramin tsaki yaja daman yasan bazata tafi ba ya kwanta a kan gadon ya lumshe ido kafin ya tashi ya shiga wanka.

Yana ji tana dukan k'ofar yayi banza sai da ya gama shiryawa yayi sallah sannan ya buWe ya same ta a tsaye yana bud'ewa ta fad'a jikin sa tace, "My king nayi maka laifi ne kake share ni?."? Ji yayi tana bashi mugun haushi ya runtse ido gabad'aya baya son ganinta kwata-kwata ya dafe kai ya d'ago ta daga jikin sa ta sake komawa ya sake d'ago ta ta sake komawa ya fusata ya fincike ta yace, "I said leave....!" Ya fad'a cikin murya mai amo wacce ta saka ta gigicewa tana kallon sa idanu a waje cikin zallar mamaki da al'ajabi.
[17/12, 10:41 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*065.*

? ? ? ?? Kallon sa take da mamakin da ya cika mata zuciya ganin ita yake yiwa tsawa har cikin kanta kamar zai dake ta kuma yana kallon ta, sak tayi jiki yayi sanyi ta koma da baya shi kuma ya kulle k'ofar tabi k'ofar da kallo jikin ta a mace kawai ta sauka daga saman ta fita gabad'aya daga b'angaren.

Kamar zata kifa haka take tafiya bata lura ma da jakadiyar ta ba kawai tafiya take tana shiga d'aki ta kulle kanta hannu na rawa take neman layin Mum amma bata d'auka ba ta sake kira bata d'auka ba ta ajjiye wayar tana kallon mudubi gabanta yana fad'uwa.

Hankalin ta mugun tashi yayi ta rasa inda zata saka ranta zuciyar ta na bugawa ta dafe kai da hannun biyu tace, "Na shiga uku, me yake shirin faruwa ne? Yau My king shine ne yake min tsawa haka?" Ta fad'a tana zagaye a d'akin hankalin ta ya tashi sosai ji take kamar tayi tsuntsuwa ta tafi gidan su.

*&&&*

? ? ? ? "Dr ka saka mu a gaba baka ce mana komai ba, meya samu Mama wai?" Hydar ya fad'a yana kallon Dr Yasir shima yana kallon sa. Dr Yasir yace, "I'm sorry to say prince, guba Mama tasha."

A tare suka wara idanu waje Suhaima tace, "poison..!." Dr yace, "Eh, kuma poison din ma ba kad'an ba da an sha kashe mutum take kai tsaye dan kunyi gaggawar kawo ta nan ne da babu abinda zai hanata kashe ta." Hydar ya kalli Suhaima sannan yace, "Amma a me tasha gubar Dr?" Ya tambaya cikin tashin hankali yana kallon sa.

Dr yace, "Ba zallar ta tasha ba a wani abun aka zuba mata, inda zaku iya tuna abinda tasha na karshe ko zamu ga ragowar sa zamu iya duba shi wata k'ila a ciki gubar take."
"Tabbas tasha tea, tana gama sha take cemin cikin ta na ciwo na juya na d'auko magani sai na ganta a yanayin da muka kawo ta nan." Dr yace, "To tabbas a cikin tea d'in poison d'in yake, amma dan mu tabbatar zamu iya zuwa mu d'auko ragowa in akwai sai gwada mu gani."

Suhaima tace, "eh ta rage dan bata shanye ba ta ajjiye yana d'akin ta." Dr yace, "Zamu iya zuwa a d'auko mu gani." Hydar ya mik'e tsaye ya fita baice komai ba Suhaima tace, "Ina zuwa Dr" tabi bayan Hydar tana fad'in, "Yaya Hydar tare zaku je a d'auko?." Cak ya tsaya ya juyo yana binta da kallon tuhuma yace, "ta ya Mama tasha poison bayan kece kika kawo mata tea d'in?."

Suhaima ta buWe baki tana kallon sa da mamaki kafin tace, "Yaya Hydar zargina kake?."
"Meyasa kika yi saurin kama kanki bayan bance ke kika zuba mata ba?." Suhaima ta rud'e tace, "Amma kasan dai babu yadda za'ayi na bawa Mamana poison ko?."
"Shiyasa na tambaye ki ya akayi tasha poison bayan kece kika kawo mata tea d'in?."

Suhaima ta fara hawaye tace, "Wallahi ko magen Mama bazan iya bawa guba ba balle Maman da kanta." Hydar ya fusata yace, "bance miki ke kika zuba ba malama, tambayar ki nake ya akayi tasha guba?!" Ya fad'a a k'arfi yana kallon ta idanun sa a waje.

Kasa magana tayi kawai sai ta fashe da kuka yaja dogon tsaki ya barta a wajan ya fita ma daga asibitin gabad'aya zuciyar sa duka babu dad'i.? Suhaima d'akin da Mama take kwance ta shiga ta ganta a kwance an saka mata ruwa yana shiga jijiyar ta idanun ta a kulle farin abun ya daina zuba daga bakin ta, zama tayi a gefen ta ta rik'e hannun ta da babu allurar a jiki tana hawaye har lokacin d'aci take ji in ta tuna kalaman Hydar a kanta.

? ? ?? Bata san ya Hydar sukayi da Dr ba basu kuma had'uwa ba sai da safe sai da gari yayi haske ma Suhaima tayi sallar asuba duk ta k'agara ta koma gida sabida bata jin dad'in jikin ta ga makaranta zata je da azahar. Tana zaune a gefe taga Maman ta buWe idanunta ta k'arasa wajanta a guje tana fad'in, "Mamana kin farka." Mama ta buWe idanun ta sai ta fara tari da sauri Suhaima ta fita zuwa wajan Dr ta ganshi a tsaye dashi da Hydar tace, "Dr ta farka."

Tare suka shiga da Hydar d'in ya samu Maman tana ta amai a kwance Suhaima ta sake fashewa da kuka tace, "Dr amai take yi fa." Dr yace, "kwantar da hankalin ki aman shine samun lafiyar ta daman shi muke so tayi ta amayar da poison d'in gabad'aya."

Hydar ya kalli Maman ya kalli Dr yace, "yanzu ya aka gama binciken?."
"Kamar yadda na fad'a maka a cikin shayin aka zuba mata poison d'in tasha, yanzu abinda za'a mayar da hankali wanda ya zuba mata poison d'in." Hydar ya girgiza kai yace, "Yanzu ya jikin nata?." Dr ya k'arasa kusa da Ma?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
 ma da ta mik'e zaune idanun ta a kulle yace, "Ranki ya dad'e ya k'arfin jikin?." Kai ta d'aga kawai tana cize baki hannun ta rik'e da cikin ta.

Hydar ya kalli Dr yace, "Da alama cikin ta nayi mata ciwo." Dr yace, "Ai dole daman in ka duba a cikin ta poison d'in take, yanzu Suhaima ki taimaka mata ta tashi tayi wanka ta kuma sha tea mai zafi sosai." Kai kawai ta girgiza Dr ya fita ta share hawayen ta Hydar ya kalle ta yace, "Ga kayan Maman a jaka, a office d'in Dr sai ki karb'o mata tea" yana fad'a ya fita Suhaima ta bishi da kallo.

? ? ? ? Taimakawa Maman tayi ta tashi tsaye dak'yar ta suka k'arasa band'aki ta fito ta barta Maman tayi wanka ta wanke baki ta fito ta shirya ta zauna tayi sallar asuba a zaune bayan ta idar Suhaima taje office d'in Dr ya nuna mata kettle ta d'ora mata tea ta had'a a cup ta tawo mata ta karb'a tasha dan taji k'arfi a jikinta. Tana cikin sha Hydar ya shigo ya zauna kusa da ita yana kallon ta ganin ta samu lafiya sai yaji dad'i da abubuwan sun masa yawa shima ga mai martaba a kwance ga Mama ga Asad ya zama abinda ya zama ga Aliyu baya nan.

Mama tace, "Sannu Hydar, Allah yayi muku albarka." Suka amsa da amin Hydar yace, "Amin, Allah ya baki lafiya Mama." Mama tace, "Amin." Hydar yace, "Mama poison aka baki a tea fa kika sha."
Tayi murmushin takaici tace, "na san za'ayi haka Hydar, masu neman su kashe ni ai suna da yawa."
"Mama daman an san da hakan shine ba'a fad'a min ba? Da sun kashe mana ke fa shikenan."

Mama tace, "kwantar da hankalin ka nasan shirin bazai wuce na Sadiya ba, Suhaima daman taji Jidda tana waya suna cewa sai an kashe ni, ku barsu su kashe ni d'in kawai ma yafii min zaman duniyar."

Suhaima da Hydar suka kalli juna sannan suka kalli Maman Hydar yace, "Mama me kike cewa ne haka? Mun san da nufin ta a akan ki kuma mu zuba mata idanu?." Mama tace, "to muna da hujja ne?."
"Zamu nemo hujjar Mama tunda har ta furta zata iya aikatawa, wata?ila jiyan ma ita ta saka aka zuba miki guba a tea ni kuma ina zuwa na d'ebo ban sani ba" Suhaima ta fad'a kallon Maman.

Mama ta tab'e baki zuciyar ta na rawa tace, "a barshi dai kawai kome ya faru nice na jawowa kaina da ban bata dama ba da duk hakan bata faru ba. Asad baya son auren jidda na takura masa a kai wacce yake son zama da ita na raba su" ta dafe kanta da yake ciwo tace, "ku k'yale ta kawai abubuwan da suke gabana yafi wannan, burina Asad ya dawo hankalin sa, Aliyu ya dawo, mai martaba ya samu lafiya shine abinda na saka a gaba. Suhaima ina so ma zaki koma wajan Malamin nan da ya bamu maganin nan na k'arshe" ta fad'a tana dafe kanta cikin ta yana juyawa.

"Baza'a bar maganar nan ba Mama!" aka fad'a daga bakin k'ofa duk suka juya jin muryar wanda basuyi zaton jinta ba suka ganshi a tsaye cikin k'ananu kaya fuskar sa babu walwala. K'arasowa ya yake yi ya canja yanayin fuskar sa yana murmushi ya durk'usa a gaban Maman yana kallon ta itama shi take kallo yace, "Barka da safiya Mama, ya k'arfin jikin ki?."

Bakin ta rawa yake tana nuna shi da yatsa cikin mamaki da al'ajabi tace, "Asad ko Aliyu?." Murmushi yayi ta rik'e hannun sa yace, "Aliyun kine Mama, taya zaki ga Mai martaba da kansa da wannan shigar kuma shi kad'ai?."

? Mama ta bayyana farin cikin ta tace, "Yaushe ka dawo? Ashe zan kuma ganin ka a duniya?." Murmushi yayi yace, "Gani na dawo Mama. abinda nake ji kuma baza'a bar maganar nan ba, babu wanda ya isa ya bawa mahaifiyar mu guba ya kwana lafiya."

Ya kalli Hydar yana mik'ewa yace, "An tabbatar da tea d'in da tasha akwai poison?." Hydar da yaji dad'in dawowar d'an uwan nasa yace, "Akwai, bincike ya tabbatar akwai a ciki."
"Suhaima lokacin da kika shiga kitchen wa kika gani?."
"Babu kowa Yaya Aliyu, Amma ruwan a ajjiye yake a cikin kettle kawai dafasa shi nayi."
"You're not serious Suhaima, baki san wanda ya zuba ruwan ba kawai zaki d'auka ki bawa Mama.....?" Sai ya dafe kai yace, "Oh god" ya fad'a yana runtse idanun sa.

Suhaima tace, "Ina so naga taci wani abun ne a lokacin shiyasa." Aliyu ya kalle ta yace, "Duk abinda ya faru kece sila, kuma zaki shiga cikin wanda zan sakawa question mark." Mama da take ta kallon sa tana murmushi tace, "Sai kake min yanayi da Asad Aliyu, musamman yadda kake magana kana tsayawa kamar shine yake magana haka nake ji." Tausayin Maman nasu ya kama su dukkan su dan sun san tsananin kewar sa da take yi ne ya saka take jin hakan.

Aliyu bai magana ba ya tashi kawai ya fita dan bazai bar wanda suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login