Showing 39001 words to 42000 words out of 216282 words

Chapter 14 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

ya sake kallon ta ya sake d'auke kai alamun tunanin wani abu yake yi wanda yake son aiwatarwa amma kuma yana jiran umarnin zuciyar sa kafin ya tashi tsaye ya tasar da ita itama yace, "can we pray?." Kallon sa tayi yadda yayi maganar a hankali ta shige ta sosai ta tab'e baki ta d'aga masa kai alamun eh domin so take taga iya gudun ruwan sa kana ya bata amsar tambayar da tayi masa.

? ? ?? Sallah sukayi raka'a biyu kamar yadda addini da al'ada ta tanadarwa ma'aurata bayan sun idar ta tashi daga kan sallayar ta zauna a gefen gadon ta kalle shi muryar ta a sanyaye sosai tace, "baka bani amsa ta ba, ina so na sani domin nasan matsayina a wajan ka, duk da amsar a bayyane take amma ina so naji daga bakin ka zanfi amincewa." Tsam ya tashi ya d'auke sallayar ya ajjiye a mazaunin ta ya dawo kusa da ita ya zauna zuciyar sa na sake fad'a masa abinda zaiyi tana sake ingiza shi ga aikata abinda bai kawo shi a ransa kusa ba ya kalle ta yace, "meyasa kika tambaya?."

"Ina so na sani na fad'a maka, ban dace dakai ba meyasa ka zab'e ni? Ban dace da rayuwar gidan ku ba meyasa ka d'auko ni? Ban dace da zama a cikin iyalan ku ba meyasa ka saka ni?. Ni ba kowa bace face k'ask'antacciya a cikin ku domin bazan had'a kaina daku ba ta ko ina kunyi min zarra wacce bazan kamo ku ba har abada. Sannan gani ni ba kyau gare ni ba sai......." d'uf bakin ta ya kulle sakamakon abu mai sanyi da khamshi tare da taushi da taji ya kulle mata bakin ta, ta zaro idanu waje ganin abinda take karantawa a novel take gani a American film da sauran finafinan k'asar waje ya faru a kanta.

Cak numfashin ta ya fara k'ok'arin tsayawa jin abinda bata tab'a ji ba a cikin bakin ta yana yawo tamkar tafiyar maciji yana zaga ko wanne sak'o na cikin bakin ta yana tab'a duk wata halitta da Allah yayi a cikin sa. Shiru ya ratsa a wannan lokacin baka jin sautin komai a d'akin motsin kirki babu wanda yake yi a cikin su idanun su dukka a lumshe suna karb'ar bak'untar bak'on yanayin da yazo musu bazata ba tare da tsammanin zuwa sa ba.

Dukkan su basu da nutsuwa wannan lokacin jikin su da zuciyar su tayi nisa cikin lokaci kad'an ba tare da sun shiryawa hakan musamman ga Rauda. Rauda bata farga ba taji sabon yanayi yana ratsa ko wanne sassa na halittar da Allah yayi a jikinta nan take jikin ta ya sake saki lokacin da ta tabbatar babu riga a jikinta, har lokacin bai cire bakin sa daga cikin nata ba sai ma tallafar kanta yayi da hannu guda d'aya yana cigaba da abinda yake yi zuciyar sa na sake k'arfafa guiwa.

? ? ? ? Lokacin da hannun guda d'aya ya fara zagawa a kan fatar bayan ta sai da ta sauke b'oyeyayyiyar ajiyar zuciya jin hannun sa yana tab'a fatar bayan ta hakan ba k'aramin sake rud'a tunanin ta yayi ba, ba zato babu tsammani taji yana k'ok'arin kwantar da ita a kan gadon hankalin ta ya fara dawowa jikin ta ta yunk'ura cikin rashin k'arfin jiki zata tashi ya mayar da ita ta kwanta sai a lokacin ta sake tabbatar babu suttura a jikinta. Hasken d'akin taga ya kashe d'akin yayi duhu sosai daidai lokacin da ya cigaba da zagawa da hannun sa ko ina na jikinta ta sauke numfashi ta kulle idanun ta tana ji kamar ta kurma ihu sabida yanayin da take ji a jikin ta bana wasa bane.

'Kin sakar masa jikin ki yana niyar mallakar ki har abada ba tare da kin tabbatar da sonki da yake yi ba, ya gama abinda yane so dake k'arshe ya sake ki shikenan ya cuce ki ya mayar dake bazawara mai lasisi, baki da hankali ko?' Zuciyarta ta fad'a mata ta bud'e idanun ta tunawa da hakan tayi k'ok'arin kwace kanta a hannun sa amma ina ta makara a wannan lokacin babu wanda zai iya kwatar ta daga hannun sa domin yayi nisa baya jin kira kome zatayi a wannan lokacin tunda yayi niya sai dai ta jira ya kammala sannan ta aikata nata domin yadda yake jin zuciyar sa babu mai tsayar dashi a wannan lokacin.

Ba zato babu tsammani ba tare da shiryawa hakan ba taji bak'on abu wanda bata tab'a jin irin sa ba tunda Allah ya kawo ta duniya yana shiga cikin jikin ta sai a sannan take jin muryar sa a hankali amma bazata tantance abinda yake cewa ba sabida ita kanta ba'a cikin hankalin nata take ba.

(fan's kar ku manta fa Asad a cikin labarawa yake so akwai soyayya?&
@&?>?#?=??)


*After some minutes.*

? ? ? ?? Kuka take sosai wanda b'ata tab'a yi irin saba muryar ta har dashewa tayi sabida yadda take ware murya tana kukan sai ka d'auka iyayen ta ta rasa a lokaci guda. Tun bayan lafawar komai take wannan kukan har ta lallab'a tayi sallar asuba ta kwanta kuka take bata daina ba babu kuma niyar tsayawar tasa. Bawai kukan ciwon da take ji bane kukan tausayin kanta takeyi domin bata da tabbacin matsayinta a zuciyar sa gashi ya gama mallakar jikinta gabad'aya a cikin lokaci kad'an ta zama shi ya zama ita, ko a yanzu ya sake ta sunan ta bazawara ta k'arfi da yaji.

Abinda yake tab'a mata zuciya take kuka kenan duk da tana jin ciwo a jikin ta ba kad'an ba amma bai dame ta ba dan tasan ciwon gado ne a wajan duk wata mace da takai mutuncin ta kan gadon mijinta, abin alfahari ne ciwon za'a kiran sa na alkhairi shiyasa bai dame ta sosai ba abinda ya dame ta matsayin ta a wajan sa.

Asad tun yana rarrashin ta da kwayar idanun sa har ya zuba mata ido ya rasa abinda zaiyi mata gashi baya so yaji kukan nata ko kad'an amma kuma ya rasa me zaiyi. Kallon ta yake a cukwikuwiye cikin bargo sautin kukan ta kawai ake ji a d'akin ya runtse idanun sa yadda yake jin ta a ransa a wannan lokacin matsayin ta ya ninka na baya sau adadin da bai san iyakar su ba, yanayin da ya kasance da ita a lokacin da suka wuce ya saka shi sake bata wani babban matsayin da babu macen da take dashi a wajan sa, shiyasa kukan ta yake d'aga masa hankali gashi shi ba bakin magana sosai ba balle ya zauna ya fad'a mata kalaman da zasu kwantar mata da hankali.

Jin kukan nata yayi yawa ya k'arasa kan gadon ya yaye bargon ds take ciki ya shiga ciki shima ya jawo ta jikinsa gabad'aya a kunnen ta yake furta, "Shiiiiii is okay please." Bata daina kukan ba sai ta kifa kanta a k'irjin sa tana cigaba da zubar da hawaye.

Fatar jikinta yaji tayi zafi ya zare k'aramar rigar da ya saka a jikin sa yayi sallah ya had'e fatar jikin sa da tata kodan ta samu sauk'in zafin jikin nata, "I'm sorry Muwaddaty, ki daina kuka bana so naji ko kad'an!" Ya furta cikin sabuwar muryar da ya samo a lokacin yana shafa bayanta a hankali.

Rage sautin kukan nata tayi sai kad'an-kad'an da take yi a k'irjin sa yana jin hawayen ta akan fatar jikin sa yana sauka ya sake cewa, "Kina so nayi kuka nima?." Bata motsa ba balle tayi magana hakan ya skaa shi yace, "So please ya isa, I'm sorry" ya sake fad'a mata a cikin kunnen ta yana matsa mata jikin ta a hankali.
Yadda yake matsa mata jikinta sai take jin dad'in hakan domin tana buk'atar a matsa mata jikinta dan ko ina a sage yake kamar an mata dukan tsiya haka take ji.

Lokaci kad'an bacci ya d'auketa kukan ya tsaya sai hawayen da yake fuskarta har lokacin, ya kalli fuskar ta ya saka harshen sa ya lashe hawayen fuskar ta ya mata kiss a goshi ya lumshe ido yana jin sa daban a kamar ba Asad na kwanakin baya ba. Sake matse ta yayi a jikin sa ya sake kallon fuskar ta ya sake mata kiss a lips d'inta yayi murmushi yana shafa kanta qaunar ta na sake yin nitso a cikin sa da zuciyar sa.


*&&&*

? ? ? ? ? Haka kawai ta ta tashi da fad'uwar gaba da ta motsa sai Asad yazo mata ranta ta rasa dalilin faruwar hakan gashi gabad'aya kanta ya kulle ta rasa wanne irin tunani ma zatayi a kan abinda yake faruwa da ita taji dad'i. Waya ta d'auka ta kira shi a karo na babu adadi amma bata shiga ta cillar da wayar kan kujera tana dukan goshin ta cikin b'acin rai da takaicin rayuwar ta a wannan lokacin.

Wayar ta sake d'auka ta kira Malamin ta ya d'auka da sallama ta amsa suka gaisa kana tace, "Malam aikin nan an gama shi kuwa?." Daga can b'angaren Malam yayi shiru bai bata amsa ba domin a zahirin gaskiya baiyi aikin da ta saka shi ba sabida rashin lafiyar da yayi fama da ita sai a yau yake da niyar yi amma sanin halin ta ya saka shi yace, "Kwarai ranki ya dad'e anyi aiki tun ranar da kika zo. Zancen da nake miki mun lalata komai babu macen da zai iya sani a wannan lokacin har sai mun karya shi."

Mama tayi ajiyar zuciya cikin jin dad'i tace, "Naji dad'in hakan sosai ba kad'an ba,?a cigaba da bincika min da zarar an samu damar da za'ayi aiki na biyu kawai ayi bana son b'ata lokaci ne ka sani."
"In Allah ya amince za'a yi ranki ya dad'e."
"Ka turo account number na saka maka na goro" tana fad'a ta yanke wayar tayi murmushi ko babu komai ta gama da wannan matsalar babu Asad babu sanin yarinyar da ta tsana matsayin y'a mace.

? ? ?? Hydar ne ya shigo d'akin da sallama ta amsa a ciki ba tare da ta kalle shi ba ya k'araso jikin sa a sanyaye ya zauna a k'asan ta yace, "Ban san laifin da na aikatawa mahaifiyata bata amsa sallama ta, hakan yana raunana min zuciya ina jin kamar na zubar da hawaye dan fushin Mama a gare ni ba k'aramin abu bane. Ina so Mama ta tuna bafa nine Asad ba akan me laifin sa zai shafe ni?."

Mama ta kalle shi tace, "sabida bakin ku d'aya duk abind zai aikata ka sani, kaine kake bashi goyan baya akan duk abinda yake yi sabida kafi k'aunar sa a kaina. Hydar matuk'ar baka dawo min da Asad ba bazaka sake ganin farin cikina akan komai naka ba, nan gaba hatta magana sai ta daina had'a mu."

Hankalin Hydar ya tashi yace, "ta yaya zan fifita a Asad a Mamana? Mamana itace komai nawa bani da wacce ta kaita ta wanne yanayi zanfi son Asad a kanta?."
"Gashi a bayyane kafi son ya rayu da wacce na tsana a duniya, kafin son ya rayu da yarinyar da ta kalli cikin idanuna tace min sai ta auri d'ana koda zan mutu. Kuka munafurce ni kai da mahaifin ku kukayi abu ba tare da sani na ba sannan yanzu kazo kana cemin ba haka ba?."

Yadda yaga ta fusata sosai hankalin sa sai ya kuma tashi ya durk'usa guiwa biyu a k'asa yace, "Ina neman afuwa ina rok'on Mama dan Allah ta yafe min, duk abinda mahaifiyata take tunani a kaina ba haka bane dan Allah ta daina fushi dani bana so naga ranta ya b'acia kaina" ya fad'a kamar zai zubar da hawaye. Ta kalle shi tace, "tashi tsaye Hydar" ba musu ya mike tace, "matuk'ar Asad bai dawo gidan nan ba wallahi baza ka sake ganin walwala ta ba, fushi kuma yanzu na fara yi da kai nan gaba zan iya sallama ka daga cikin y'ay'ana tunda abinda kake so kenan."

Wara idanu yayi kamar zai zubar da hawaye yace, "Haba ya Mahaifiyata take fad'ar haka a kan d'anta Hydar? duk abinda ya faru ba yin Hydar bane umarnin Mai martaba ne babu abinda Hydar zai iya a kai, dan girman Allah ina rok'on Mama da ta yafe min." Tsaki taja ta kalle shi tace, "kanka ake ji kuma. Inda kasan abinda nake ji a zuciya ta baza ka aikata min abinda kayi ba Hydar, kaine kake bada goyan baya a koda yaushe badan kai ba da yanzu ba wannan maganar ake yi ba dan kaine silar had'uwar shi da yarinyar badan ka d'auki mota ka fita ba tare da sanina na ka buge ta da hakan bai faru ba. Kaine ka jawo komai ka kuma bada goyan baya a kan komai, ka tashi ka bani waje bana son ganin fuskar ka."

?? A hankali ya tashi tsaye daga durk'uso d'in da yayi yana kallon ta ita kuma ta kawar da fuskar ta gefe har zai fita tace, "Tsaya." Ya juyo da sauri har da murmushin sa ta kalle shi tace, "Kira min Asad da wayar ka." Hydar gaban sa yayi mugun fad'uwa ya kalle ta yace, "in na kira shi bata tafiya."
"Gwada na gani."
Ba musu ya d'auko wayar sa a aljihu ya fara neman number Asad a zuciyar sa yana ta jan salati ya kira, a speaker ya saka ta jima batayi magana ba kafin ta katse ta rubuta call ended.

Ganin hakan sai yaji dad'i a zuciyar sa da hannu tayi masa alama da ya bata waje ya fita jikin sa gabad'aya a sanyaye yake amma b'angaren zuciyar sa yaji dad'in rashin samun wayar Asad.

*&&&*

? ? ? ?? Kuka take sosai cikin d'aga murya take fad'in, "Bazan jure ba Mum, bazan iya jurewa ba. Ke kika cusa min son Asad a zuciya ta meyasa yanzu kika kasa yi min komai game da hakan?. Yau kwana nawa da zancen auren nasa amma kin kasa komai a kai, zuciyata bazata jure ba Mum zata iya bugawa na mutu" ta k'arasa fad'a tana kifa kanta a cinyar Mum tana kuka sosai.

Shafa kanta Mum take yi cikin sigar rarrashi da kwantar da hankali tace, "Haba Jidda ke kin san wahalar da aka sha kafin ta ambace ki matsayin wacce d'anta zai aura...? Ke kin san irin kud'in da na kashe kafin faruwar hakan? dak'yar aka sawo kanta ta ambace ki. Na san dole kina jin babu dad'i amma ya zamuyi? Ita kanta babar tasa kanta ya kulle sabida mai martaba da yake a tsakiya badan shi ba wallahi da yanzu ya yiwa yarinyar saki uku."

Jidda tace, "yanzu shikenan ni sai dai na hak'ura ko?."
"Haba Jidda, ai ko zan mutum a tafe wallahi sai kin mallaki Asad matsayin mijin ki; wannan alqawari nayi miki kuma zan cika miki shi da iznin Allah."
"Allah yasa Mum, duk da jikina sai yake bani kamar bazan aure shi ba."

Mum tace, "Kar ki kuma fad'a zaki aure shi ke kad'ai zai zauna da ita a matsayin matar sa bayan ke babu wata. Ki kwantar da hankalin ki komai ya kusa dawowa hannun mu nan bada jimawa ba, nan da wani lokaci kad'an Asad d'in kansa hannun ki zai dawo ba babar sa ba." Jidda ta goge idanun ta ta d'ago kanta tana murmushi tana kallon mahaifiyarta ta domin kalaman ta sun kwantar mata da hankali ba kad'an ba shiyasa take alfahari da ita.

*&&&&*


A b'angaren Hydar tunda ya bar wajan Mama jikin sa yake a sanyaye gani yake kamar bai kyauta mata ba goyan bayan auren Asad da yayi tunda bata son hakan matsayin ta na uwa kamar bai kyautu yayi mata haka ba. Hydar ya shafa kansa yana kallon wani waje daban yace, "Ina so ta daina fushi dani domin tafi kowa sona a duniya."

Ya cize lips d'in sa yace, "Ta yaya zan dawo da Asad bayan yana tare da wacce yake so? Shima in nayi masa haka banyi adalci ba nafi kowa sanin waye shi, bashi da wanda yake so a duniya sama dani kodan na saka masa ya kamata nayi iya bakin k'ok'arina wajan ganin bai dawo yanzu ba." Yayi shiru kafin ya naushi hannun sa yace, "meya kamata nayi? Ya zama dole nayi wani abun kodan fushin Mama da yake a kaina, Yadda Mama bata son auren nan zata iya yi min baki akan cikar burin ta nasan babu abinda bazata iya ba balle babban burin ta da yafi ko wanne a duniya."
Ya sauke numfashi ya shafa kansa yana cize baki yace, "Dole nayi wani abun!."



_Tofa an shiga tsaka mai wuya._?&
@&??&
@&?
[17/12, 10:39 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*039*

? ? ? ? ? ? Bud'e idanun ta take yi wanda suka yi mata nauyi sabida kukan da tayi ba kad'an ba hakan ya haifar da nauyin idanun ta da kuma kunburi, Bud'e idon take a hankali kasancewar babu haske a inda take hakan ya taimakawa idanun nata wajan bud'ewa ba tare da wani abun ya kawo musu barazana ba.? K'arewa d'akin kallo take yi sautin agogo yana tashi a hankali, tik, tik, tik, hakan ya ja hankalin ta ga kai idanun nata kan agogon.

Dafe kai tayi ganin lokacin sallar azahar har ya wuce ta rutse ido tana jin rad'ad'i a jikinta ga kanta da yake ciwo ga k'afar ta da take yi mata suka kad'an-kad'an. Yunk'urawa tayi ta mik'e zaune tana share goshin ta tana furzar da iska abubuwan da suka faru suna yi mata yawo a cikin kanta. Runtse ido tayi tunawa da abinda ya wakana tsakanin su ta cize baki ta d'aki gadon tana ji kamar ta d'auki ruwa ta wanke abinda ya faru ta daina tunawa ko zata daina jin abinda take ji a zuciyar ta amma hakan bazai yu ba.

Idanun ta taji suna niyar kawo sabbin hawaye tayi aurin mayar dasu ta yaye bargon da ta rufa ta sauka daga kan gadon a hankali ta mik'e tsaye tana jin kamar ta kurma ihu sabida takaicin da take ji a zuciyar ta. A haka ta shiga band'aki ta watsa ruwan zafi a jikin ta ko zata ji dad'i ta gasa kanta sosai tayi alwala ta fito tana takawa a hankali sabida tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login