Showing 189001 words to 192000 words out of 216282 words

Chapter 64 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

bai rarrashe ta ba babban tashin hankalin sa Hydar dan yasan zai dawo kuma wajan ta zaizo ba wajan shi ba. Tablet d'in ta buWe a hannunta tace, "Ban sha ba, ya d'auka nasha a lokacin hankalin sa ya tashi yaji ana buWe gate alamun kun dawo sai na neme shi na rasa."

Tablet d'in ya d'auke daga hannun ta ya mik'ar da ita tsaye tak'i barin jikin sa har lokacin ya kaita d'akin sa ya zare hijjabin jikinta ya ajjiye a gefe ya kwantar da ita yace, "Ki huta." Zai fita ta sake rik'e shi tana girgiza masa kai ya sauke numfashi dole ya zauna a gefen ta tana rik'e da hannun sa tana sauke numfashi alamun taci kuka ta k'oshi.

Wayar sace tayi k'ara ganin sunan mahaifinsa ya saka shi ya d'auka ya saka a kunne daga can b'angaren yace, "Asad da gaske Hydar yana gidan nan?." Asad ya girgiza kai kawai kamar yana gaban sa dan bazai iya magana ba b'acin ran da yake ji a zuciyar ba bazai barshi magana ba.

Jin yayi shiru Abba ya sake cewa, "Kayi magana Suhail ya sanar dani kace a bincika yana nan, kenan shine ya saka aka kashe wutar gidan?." Asad ya sauke numfashi yace, "Abba yazo har wajan ta." Jin yadda maganar Asad d'in ta fita yasan akwai tarin b'acin rai a tare dashi alamun wani abun ya faru Abba yace, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Amma dai lafiya ko?."

Asad yayi shiru yana runtse idanun sa ya kalle ta yaga itama shi take kallo ya d'auke kansa yana girgiza kai kana kallon sa kasan ransa b'ace yake. Jin bai amsa ba ya saka Abba yace, "In zaka iya sauko kasa Uncle ka zai zo kuyi maganar sabida a san abinda za'ayi kar abun yayi nisa."
Datse kiran Asad yayi ya mik'e zai fita ta kwab'e fuska tana kallon sa tare da girgiza kanta ya zauna ya dafa goshin ta yana kallon ta amma baice komai ba kafin ya zame hannun sa ya tashi ya fita.

K'asa ya sakko tun daga nesa da Uncle da Suhail suka hango shi suka san ran maza ya b'aci domin kuwa fuskar sa har ja tayi sabida b'acin rai annuri kona sisi babu akan fuskar sa yana k'arasowa ya kalli Suhail yace, "An same shi?." Suhail ya tsorata da yanayin Asad yaja baya yace, "ranka ya dad'e an duba ko ina amma ba'a samu Hydar a gidan nan."

"Meye amfanin ma'aikatan gidan nan har da Hydar zai shigo har nan har sama babu wanda zai ganshi? Meye aikin su?" Ya fad'a cikin fad'a sosai yana kallon Suhail har sai da ya tsorata dan bai tab'a jin muryar sa da amo haka ba.

Suhail yace, "Allah ya wuci zuciyar ka ranka ya dad'e tuba nake, dukkan su hankalin su ya tafi tunanin abinda ya d'auke wutar gidan a yadda akayi bincike an tabbatar shine ya kashe wutar gidan."

Uncle da yake kallon Asad yanayin b'acin ransa ya tabbatar da an yiwa matar sa wani abun ya kalli Suhail yace, "Meya amfanin cameras gidan din gidan nan da aka saka? Meyasa basu mayar d ahankali wajan kula da duk wanda zai shigo gidan ba?."

Asad ya murza yatsun sa na tsakiya da babba suka bada sauti ya kalli Suhail yace, "Aje a duba a tabbatar an gano ta hanyar da ya shigo nan" yana fad'a ya juya ya koma Suhail ya fita ya kalli Uncle yace, "Gaskiya akwai abinda ya faru da ya b'ata ran mai martaba haka, dole a nemo inda Hydar yake nan gaba ba'a san me zaiyi ba."
Uncle yace, "Ya kamata."

Asad lokacin da ya ya same ta a tsaye a falon ta kasa nutsuwa ganin sa ya saka hankalin ta ya kwanta ya rik'e hannun ta suka koma ta kwanta ya kalle ta kamar zai magana sai ya fasa ya cize bakin sa. Ya jima a haka kafin ya dawo nutsuwar sa yace, "Ki nutsu babu abinda zai faru." Kai ta girgiza yana zaune a gefen ta har bacci ya d'auke ta ya d'auki waya ya fita yana neman Suhail.

A daren sai da aka tabbatar da ta inda Hydar ya shiga b'angaren sa da ta inda ya fita sannan hankalin sa ya kwanta aka tara meeting na ma'aikatan duk a dare aka yiwa kowa warning akan kula da aikin sa duk suka amsa da zasu dage Suhail ya sanar dashi sai a lokacin yake jin nutsuwa a zuciyar sa.

Yana zaune bayan sun gama waya da Suhail kawai yaga kiran Hydar yana shigowa ba tare da tunanin komai ba ya d'auka ya saka a speaker kafin yayi magana Hydar yace, "To dan ka saka an nemo ta inda na shiga apartment d'inka ai ba wani abu bane mai wahala, ka sani masu tsaron ka ina da yaran da in nazo zan shiga zasu bar wajan suyi kamar wani aikin ne ya taso musu. Ina da mutane da yawa a gidan nan ko me naso yi zanyi lafiya lau babu damuwa."

Asad baiyi magana ba hakan ya saka ya kuma cewa, "Na samu matar taka ai a zab'in da na bata na d'auka zata ce a kashe kane sai naji gwara ta bar babyn ta ya salwanta da dai kai ka bar duniya, amma fa naso ta amince dani mun kasance yau d'in nan kasan ance mace mai k'aramin ciki sirri gare ta" sai ya kyalkyale da dariya yace, "Kwantar da hankalin ka ko hannunta ban rik'e ba tunda dai tasha maganin shine burina, zan juyo kanka daga baya."

Asad ya runtse ido ya buWe murya a kausashe yace, "Ka kiyayi had'uwar mu Hydar!" yana fad'a ya yanke wayar ya cillar akan kujera ya dafe kai da duka hannayen sa.
Bai jima a haka ba ya tashi ya shiga d'akin yayi wanka ya saka kaya ya kwanta a gefen ta amma ko kad'an bacci yak'i zuwa idanun sa sabida b'acin rai, tsaki yayi ya d'aura alwala ya tayar da sallah.

Washe gari da wuri Rauda ta bar b'angaren ta koma nata dan ita take son dinga yi masa abinci ba ma'aikata ba, duk da akwai kitchen a saman nasa amma bata tsaya yi a can ba ta sauko k'asa. Da kanta tayi duk abinda ya kamata sannan ta saka aka d'auka suka tafi tare aka kai har lokacin bai fito ba kasancewar asabar ce babu zaman fada.

Hadimar ce ta koma ita kuma ta tuna wayar ta na saman sai ta hau saman da sallama ta shiga falon ya amsa ta ganshi a zaune amma bai kalle ta ba, k'arasowa tayi ta zauna tace, "Barka da rana." Kai kawai ya d'aga mata ta tab'e baki ta duba wajan da wayar ta fad'i ta hango ta a can k'arshen kujera har chajin ya k'are saboda fitila da take a kunne tama manta ita.

Kallon sa tayi taga ya wani d'aure fuska yana zaune da manyan kaya kansa babu hula yana ta aikin kad'a k'afa ya d'ora d'aya kan d'aya, "Breakfast yana k'asa" ta fad'a tana niyar mik'ewa kallon da yayi mata ya saka ta fasa tashin ta koma ta zauna ta kawar da kanta gefe itama ta d'aure fuska ta fara kad'a tata k'afar.

Sai ta bashi dariya ma amma baiyi ba ya danne ganin yadda ta wani basar ta d'aure fuska itama ya jinjina kai yana girmama k'arfin hali irin na mace, in ba ita ba waye yana zaune a kan kujera zai zauna? Waye zai wani d'ora k'afa kan d'aya yana kad'awa a gaban sa?, lallai ba'a yiwa mace mulki in taso nata mulkin sai yafi na ko wanne shugaba.

D'auke kai yayi daga kallon ta ganin yayi mata banza ya skaa ta kalle shi taga bama ita yake kallo ba waya yake dannawa suna chart da son MD d'in sa na company akan sabon aikin da suka samu. "Ina da abin yi fa" ta fad'a ba tare da ta kalle shi ba. Sarai ya jita sai yayi kamar ma baiji ba ta sake cewa, "Ina da bak'i ni zan tafi."

Kallon ta yayi sai ya d'auke kansa daga kallon ta ya sake yi mata banza. Ganin hakan kawai sai ta mik'e zata bar wajan taji yace, "Dawo." Sai ta fara yi mata dara tana buga k'afa a k'asa kamar zatayi kuka tana cewa, "Nace maka ina da bak'i kana ji kuma ina magana kayi banza dani."

Nan ma banza yayi mata kafin ya d'ago ya kalle ta ya hard'e hannu a k'irji ya juya kansa yana k'are mata kallo kafin ya mata alama da hannu taje. K'aramar harara ta sakar masa yana kallon ta ta juya ta sauka shi kuma yayi dariya kad'an dan ta bashi dariyar sosai.
Tunda ta bar wajan sa basu sake had'uwa ba tana wajanta tana ta amsar bak'i daga waje daban-daban na gidan har Habiba da Walida kawayen ta yadda suke mata sai ta dinga jin nauyin su.

Waya sukayi da Umma take ce mata taje ta duba Mama kar abinda ya faru a baya yayi tasiri a zuciyar ta duk abinda zatayi ta dinga tuna Asad d'in. ta gamsu da abinda Umma tace bayan sun gama waya ta kira number Asad, bai d'auka ba har ta katse bata sake kira ba ta ajjiye wayar.

Kusan mintina ashirin da kiran ya kirata ta d'auka ta saka a kunne tayi sallama bata jira ya amsa bama tace, "Ammmmm daman ina so naje duba Mama ne." Shiru yayi kamar bai ji ba itama tayi shiru dan tasan yana jinta sai da aka d'auki lokaci sannan yace, "Suhail zai kaiki" yana fad'a ya datse kiran tabi wayar da kallo tana harara kamar shi take harara.

Ba jimawa hadimar ta ta shigo ta sanar da ita zuwan Suhail ta bada umarnin ya shigo ya shigo yana fad'in, "Allah yaja da ran Fulani." Dariya kawai tayi dan bawai ta iya wad'annan abubuwan bane tace, "na taso ne?." Suhail yace, "zamu iya tafiya."
Ita da Jakadiyar ta suka tafi Suhail yaja motar suka je asibitin har lokacin Mama bata farka ba taga jikinta suka gaisa da Suhaima da kannen Maman kafin ta dawo gida dan da fitar da dawowar ba'a yi mintina talatin ba.

Da daddare Hydar ya kaiwa Mama ziyara a lokacin babu kowa a wajanta sai security ya shiga har gaban gadon da take kwance ya zauna yana kallon ta kafin yace, "Mama nasan wata?ila kina jin abinda zance; nazo dan naga lafiyar ki na kuma shaida miki abubuwan da suke raina."

"Wato Mama nasan kaf cikin y'ay'an ki kinfi sona tabbas nasan da wannan amma kinfi nuna k'aunar Asad a kaina tunda shi kike yiwa burin zama shugaba bamu ba, baki tab'a tunanin hakan zai k'ona mana rai zai kuma iya sakawa mu dauki mataki ba, kawai abinda yake zuciyar ki kike fito dashi bakya duba da yanayin da hakan zai jefa mu tunda muma jinin sarauta ne. Kullum zancen ki Asad ya mulki garin nan ko kara baki tab'a yi mana ba shin mu babu jinin sarautar a jikin mu ne? Ko kuma Asad ne kawai ya gaji sarauta banda mu?."

"Mama a duk sanda kika fad'i haka ina jin kamar na bawa Asad guba yasha ya mutu sabida banbancin da kike nunawa k'arara a kanmu, bakya tunanin komai sai shi kawai bayan muma y'ay'an kine muna da hakki a kanki ko sau d'aya ki ambace mu dukkan mu babu wanda baya son sarautar amma maganar d'aya ce kullum Asad!" Ya fad'a cikin fusata yana dafa gadon da take kai kafin ya cigaba da fad'in, "Na shirya abubuwa da yawa akan ganin bayan duk wanda zai hanani mulkar garin nan koda kece Mama, ina nan akan baka ta duk abubuwan dana shirya a baya baza su zama a banza ba sai na aiwatar da kudurina. Jiya na bawa matar Asad maganin zubar da ciki amma na fahimci tayi min wayo ne bata sha maganain ba to ai in tasan wata bata san wata ba zanyi maganin ta cikin k'aramin lokaci."

"Mama ban hak'ura da mulkin nan ba ina nan ina shirin yadda zan ga bayan Asad da mijin ki, koda kece zan iya ganin bayan ki a duk sanda naso indai burina zai cika. Kiyi ha?uri Mama amma bazan iya hakura ba sai na tabbatar da burina ya cika hankalin kowa zai kwanta. Ina baki hak'uri in kika farka kika samu bak'in labari ba laifina bane laifin kine."

BuWe k'ofa akayi aka shigo ya kalli wanda ya shigo yaga Suhaima ce kawai sai ya mik'e ya fita bai mata magana ba a daidai lokacin da Mama ta fara wani irin numfashi k'irjin ta yana sama da k'asa.
Hankalin Suhaima ya tashi ta fita a guje suka dawo da likita aka yiwa Mama allura? amma har lokacin numfashin baiyi daidai ba dak'yar aka samu numfashin ya tsaya tana kuka ta kira number Asad ta sanar dashi halin da ake ciki.

A daren suka fito shida Suhail suka tawo hankalin sa a tashe, lokacin da suka zo ta koma bacci likita yake sanar dasu an fad'a mata maganar da ta tayar mata da hankali ne shiyasa hakan ta kasance in aka cigaba da hakan kuma zuciyar ta zata iya bugawa. Nan take Asad ya saka dokar ko waye kar a sake barin sa ya shiga sai Suhaima kawai da kannen Mama in basu ba kar a sake barin wani yazo inda take.

Ransa a b'ace ya koma gida yaga Rauda a saman sa ko ta kanta baibi ba ya wuce itama bai isheta kallo ba balle ta kalle shi ta tab'e baki ta cigaba da hira da Yaya Ummi a wayar ta domin tayi alwashin nuna masa itama fa bazata d'auki wulak'anci ba sai dai duk abinda zai faru ya faru.


Bayan kwana biyu.
[17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*088*

? ? ? ? Cikin ikon Allah a cikin kwanakin duk wani abu da Aliyu ya b'ata da ya shafi masarauta Asad ya gyara shi da taimakon Abba, duk wata sadaqa da aka daina yanzu an dawo da ita komai yana tafiya bisa tsari Asad yna k'okari ganin komai ya tafi bisa tsarin addinin musulunci. Ma'aikatan gidan su kansu sun san an samu canji sosai kowa farin ciki yake yi don sakaqa da taimako ya dawo.

A cikin kwanakin Rauda da Asad babu abinda yake had'a su magana ba sai anga dama tun tana zuwa ma b'angaren sa har ta share ta daina daman sabida mutane take yin wani abun to ta gaji da wula?ancin itama ta watsar dashi sai a kwana a wuni ma a sake tashi basu had'u dashi ba balle magana.

Jikin Mama yayi sauk'i sosai duk da batayi magana ba tunda ta farka amma jikinta ya warware sosai sai dai an kafa mata sharud'a akan ahiga damuwa da yawan tunani. A ranar da ta kasance ranar laraba da safe aka sallamo Mama ta dawo b'angaren ta bayan an gyara mata b'angaren nata. Tun safe ake karb'ar bak'i amma har lokacin batayi magana ba Asad kawai take son gani amma shiru bai shigo ba duk ta damu.

Shi kam bayan an tashi daga zaman fada kai tsaye wajan ta yayo tunda aka hango shi aka fara bada hanya ana kirari sosai saman sa da lema har ya k'araso k'ofar falon Mama. Sauke Lemar akayi ya shiga ciki su kuma duk suka tsaya a waje ya shiga ya same ta zaune ita da k'annen ta mata biyu wanda suke wajan ta.

Tunda yayi sallama ta mik'e har ya k'araso ya tsuguna a k'asa yace, "Barka da dawowa Mama." Sai a sannan bakin ta ya buWe bakin ta yana rawa tace, "Asad!." Kowa yayi mamakin jin maganar ta farin ciki ya cika zuciyar su har lokacin bai tashi ba. Zama tayi akan kujera shi kuma ya zauna a k'asa kusa da ita tana ta kallon sa kafin ta fashe da kuka.

Hankalin Asad ya tashi ya kalle ta yana kallon fuskar ta yace, "Zubar da hawaye bai kamaci mahaifiyata ba, dan Allah Mama ta daina kuka nima hakan yana cutar dani." Mama ta dinga kuka kafin ta share hawayen ta ta kalle shi tace, "Asad kayi ha?uri."

Kai ya dafe yana kallon ta kamar zaiyi kukan shima yace, "Subahanallah! Dan Allah mamana ta daina furta wannan kalmar dan Allah" ya fad'a yana dafe kansa da yake sarawa. Mama tace, "Dole na baka ha?uri Asad na cutar dakai akan abubuwa da yawa dan ka kasance me yi min biyayya na dinga tauye maka hakki, kayi ha?uri ka yafe ni" ta sake fad'a cikin kuka sosai.

Ya kasa magana sabida shi kansa sarawa yake yi Mama Jamila tace, "Haba Maman Suhaima, dan Allah ki daina wannan kukan kinga kin saka Asad din cikin wani yanayi mara dad'i. Ga abinda likita yace" Ta kalle su tace, "Dole nayi kuka Jamila, na cutar da Asad iya cuta duk abinda ya nuna yana so sai na raba shi dashi bana duba halin da zai shiga kawai cikar burina nake so. Ban tab'a addu'ar in mulkin nasa ba alkhairi bane Allah ya hana shi kullum alkhairi nake hangowa ban tab'a fad'awa Allah yayi min zab'i ba. Na raba Asad da aikin sa, na raba shi da burin sa, na raba shi da duk wani abinda yake so hatta matar da yake matu?ar qauna na raba shi da ita kawai dan na samu cikar burina."

"Wacce nazo na tilasta shi ya aura sai gashi ita da babar ta suke so su kashe ni, daman yasha fad'a min Mama bata dace dani ba amma nak'i ji nace ko baya so dole ya aureta, ya aure ta d'in ya hak'ura ya zauna da ita ya fara mulkin da nake so na fara saka shi yana yin duk abinda nake so koda shi baya so koda kuwa ya sab'awa shari'a. In ban nemi yafiyar Asad ba me zanyi?. Ta silar mulkin da baya so aka masa kurciya ya bar k'asar nan ya koma wata k'asar amma da ya dawo sai ya cigaab da fafutukar neman ganin bayan makiya na" Ta fad'a tana sake fashewa da kuka.

Asad yayi shiru ya kasa magana Mama ta kuma cewa, "Hydar da Asad yake so sama da komai a duniya dashi kad'ai ya yarda ya kuma aminta amma shine yake cin dunduniyar sa yake neman kashe shi duk ta silata kuma, da ace ban

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login