Showing 195001 words to 198000 words out of 216282 words

Chapter 66 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

da mulkin sa cikin aminci da lafiya, Allah ya bawa Aliyu lafiya" ta fad'a muryar ta rawa sosai sabida kuka da yake so ya kwace mata.

Mama ta Mike tace, "Na gode sosai. Ki huta lafiya" ta fad'a tana tashi ta fita itama ta biyo bayan ta har k'ofar waje sukayi sallama ta shiga wajan Ammi. Nan ma dai maganar d'aya ce Ammi tace bata rik'e ta ba sukayi sallama tace da Suhaima ta koma zata je b'angaren mahaifin su haka akayi ita ta koma ita kuma ta nufi b'angaren kai tsaye.

Babban falon ta shiga baya nan kai tsaye ta shiga d'akin da tasan yana nan, nan ma baya nan ta fito ta shiga d'ayan nan ta ganshi zaune kusa da Aliyu yana bashi magani. Sallamar ta ya saka shi ya juyo tare da amsawa ya d'auke kai ya cigaba da bashi maganin ta tako a hankali ta tsaya tana kallon Aliyu.

Yana zaune yana binta da ido ya rame yayi wani iri sai ido kawai da yake binta dashi kamar ba Aliyu d'an gayu mai ado ba, kusa dashi taje ta rik'e hannun sa shima ya rik'e alamun ya ganeta tace, "Sannu Aliyu." Kallon mahaifin sa tayi sai taga ya tashi ya fita ta zauna a gefen Aliyu ta rik'e fuskar sa tace, "Haba Aliyu meyasa ka aikata dukkan abinda kayi? Meyasa neman duniya ya rufe maka ido kake k'okarin cutar da d'an uwan ka?."

Kamar yana jin me take cewa ya sunkuyar da kansa k'asa sai ta fara kuka tunawa da tuni Asad ne a cikin halin da hakan ta faru bata san ya zatayi ba. Bacci taga yana neman yi ta kwantar dashi tayi masa addu'a ta rufe shi ta kashe mishi haske ta nufi d'akin mahaifin sa.

Waya ta samu yanayi da governor Kano ta samu waje kusa dashi a k'asa ta zauna har ya kammala wayar suka had'a ido ya d'auke kansa tace, "Barka da dare."
"Ya jiki?" Ya fad'a a tak'aice ba tare da ya kalle taba.? Ta goge idanunta tace, "da sauk'i." Daga nan yayi mata banza bai sake magana ba ta gyara zama tace, "Dan Allah kayi hak'uri."

Kallon ta yayi yace, "Me kikayi min?." Ta ja numfashi tace, "Komai ma." Tab'e baki yayi yace, "kome kika aikata ai kanki kika cuta Rabi'atu, yanzu ba gashi y'ay'an naki da kike taqama dasu? meye amfanin su yanzu?. Ace jinina wanda na haifa d'an cikin gidan nan shine ya dinga Zina da matar aure matar auren kuma matar k'anin sa, shi kuma d'ayan har d'akin nan yazo kashe mahaifin sa sabida son zuciya da bak'ar aniya. Yanzu meye amfanin wad'annan guda biyun?."

Ta goge idanunta tace, "Babu, ina rok'on Allah ya d'auki ransu dukka na huta domin ganin su kawai bak'in ciki yake k'aramin."
"Ganin kanki baya saka ki bak'in ciki? Kin manta kece silar jefa Aliyu da Jiddan wannan hali?, ko kina tunanin ban san aikin da kika yiwa Asad lokacin da yana Cairo dan kawai kar yayi auratayya da matar sa?."
Gaban Mama ya sake fad'uwa ta runtse ido bata ce komai ba yayi murmushi yace, "Alhakin abinda suka aikata yana kanki, da ace Asad d'in a lokacin da lafiya a tare dashi da bata bawa Aliyu had'in kai ba amma kin dakushe lafiyar tasa sabida kawai nufin ki Mara kyau akan y'ar mutane, dan haka kanki zaki fara tsana ba su ba."
"Ina jin haushin kaina domin na cutar da kaina da y'ay'ana. Asad da ya kasance mai yi min biyayya nafi cutar dashi sama da komai."

Yace, "Yanzu me gari ya waya? Da kin bar son mulkin da kike a zuciyar ki duk da ba haka ba, amma ji kika dinga yi kamar ki kunna min huta na k'one dan cikar burin ki. Baki tab'a addu'ar in Mulkin Asad bazai haifar da alkhairi ba Allah kar ya bashi baki tab'a ba kawai ke son kanki da yadda zaki wula?anta abokan zaman ki shine kawai a gaban ki. Akwai jinin sarauta a jikin ki na sani amma duk abinda kike ji dashi nima ina ji dashi dan ni nayi mulki ke kuma baki yi ba iyaye ki da mijin kine sukayi; amma yadda nake zaune da Jama'ar gidan nan ke ba haka kike ba. Kika d'auki burin duniya kika saka akan Asad akan burin ki har kokarin kashe wacce yake so kika yi, akan burin ki tsallake umarnina kinyi kin tafi Cairo kin saka ya saki matar sa dan akwai bani da lafiya. Da farko na zarge ki a rashin lafiyata domin nasan zaki iya indai akan burin kine amma daga baya sai naga anyi amfani da damar da kika bayar ne dan ace kece."

"Abun kunya kuma d'an cikin ki shine ya aikata hakan dan ki fad'a ramin da ya hak'a kuma kin fad'a dan kaf mutanen gidan nan duka ke suke zargi akan rashin lafiya ta hatta d'anki Asad. Kin aura masa wacce kike so sai gaahi suma suna k'okarin kashe ki har sai da kika je gidan su wacce kika saka ya rabu da ita d'in kika nemo alfarmar Kawunta. Kin jawo min abubuwa da yawa wanda bazan manta ba Rabi'a, kin saka anyi cikin shege a cikin gidan nan bayan kin san tun farko yarinyar ba tarbiyya ce da ita ba kika nace sai ya aure ta, kin saka an aikata min abubuwa da dama wanda har k'asa ta rufe idanuna bazan manta dasu ba."

Ya sauke numfashi yace, "Amma ta dalilin Asad na yafe miki kamar yadda na yafewa Yahuza dalilin Suhail, amma ki jawa Hydar d'anki kunne wallahil azim idona idon sa sai yayi zaman prison, ya bar ganin na k'yale shi ya d'auka yaci bulus ina nan sane dashi sai na saka an masa hukinci daidai da abinda ya aikata. Shi Aliyu Allah ya hukunta shi saura shi."

Kuka Mama take yi sosai muryar ta har dashewa take sabida kuka tace, "Nayi nadama, wallahi nayi nadamar dukkan abinda na aikata. Na nemi yafiyar Raudan ita yafe min domin na cutar da ita cuta mai yawan gaske. Duk abinda ya faru tabbas nice silar komai, ya Allah ka yafe min" ta fad'a tana sake fashewa da kuka yayi mata banza bai kula ta ba.

Sai da ta gama kukan ta son ranta sannan ya kalle ta yace, "Kije ki huta nima zan huta." Kai ta d'aga ta mik'e tsaye ta dafe kanta tayi baya kamar zata fad'i yayi hanzarin rik'e hannun ta har ta tsyaa daidai yace, "Kiyi a hankali." Kai ta d'aga ta nufi k'ofar fita ta fita ya sauke numfashi yana jin ciwon abubuwan da suka faru a zuciyar sa.

Washe gari.

Rauda koda ta tashi girki abinci tayi masa duk da ranta a b'ace bayan ta gama tana shirin kaiwa Suhaima ta shigo ita da Khaleesat da sallama, tana tsaye da tray akan table ta amsa da murmushi tana fad'in, "Barkan ku da zuwa." Sukayi dariya Suhaima tace, "Khamshi muke ji ya cika ko ina na gidan nan shiyasa muka shigo muci girki." Dariya Rauda tayi kad'an tace, "Bismillah ku."

Khaleesat tace, "Dole ai mu zauna muci wannan khamshin bazai bar mu ba." Suhaima tace, "A haka ma fa wai dan mai martaban baya nan ne da ace yana nan abincin da zamu samu sai yafi wannan." Khaleesat tace, "ashe fa ya tafi Abuja d'azu, ai naga alama Fulanin mu akwai iya girki ga iya kula da yayan mu kuma shugaban mu.:

Murmushi tayi kawai amma bai kai zuci ba zuciyar ta cike da zallar b'acin rai da kuna jin wai ya tafi Abuja kenan ya mayar da ita banza kenan a gidan bata da wani amfani tunda har zaiyi tafiya bata sani ba. Daurewa tayi tace, "Bismillah kuci zanje wajan Mama na kai mata nata" ta fad'a tana kiran Hadimar ta ta shigo a guje ta d'auki tray d'in tayi gaba tana binta a baya.

Suhaima ta bita da kallo tace, "Yayan mu yayi sa'ar mace ki kalla abincin ma ba y'an aiki ne zasuyi ba itace zatayi" ta fad'a tana tashi ta k'arasa kan table d'in Khaleesat ma ta taso tana fad'in, "Gaskiya dai tana da kirki gashi tana son Mama." Suka zauna suna cin abincin.

Rauda lokacin da suka shiga Mama tana zaune ita kad'ai tasha magani ganin Rauda da abinci ya saka ta yin murmushi aka ajjiye abincin hadimar ta fita Rauda ta zauna tace, "Barka da safiya Mama."

Mama ta bita da murmushi tana kallon ta tace, "Barkan ki, ya k'arfin jikin k?." Rauda tace, "Alhamdulillah. Ya jikin Maman?."
"Naji sauk'i sosai. Wannan aikin duka ke kikayi?." Rauda ta girgiza kai tana murmushi Mama tace, "Allah yayi miki albarka ya baku zaman lafiya me d'orewa."

Rauda tayi murmushi ta amsa da amin kafin Mama tace, "Yace min zaki bishi Abuja anjima gwara kije ki shirya kar azo ana jiran ki." Rauda ta kalli Mama da mamaki amma bata da bakin musawa ko babu komai bata nunawa Mama bata san ma baya nan ba. Rauda tace, "a tashi lafiya." Daga nan ta fita Mama ta bita da kallo tana jin kamar ta wanke zunubai masu yawa cikin wanda ta aikata.

? ? ? ?? A fusace Rauda ta koma b'angaren ta sai da ta shiga falon ta tuna dasu Suhaima a zaune suna ganin ta Khaleesat tace, "Fulanin mu wallahi abinci yayi dad'i sosai, da ace mai martaba yana nan yaci abincin nan yau kin gama dashi, daman Yaya Asad da son abu mai dad'i." Murmushi tayi tace, "Santi kuke yi kawai. Ina zuwa" ta fad'a tana shiga d'akin da sauri tana jiyo Suhaima tana fad'in, "Mun wuce wajan Ammi."

Mayafin jikinta ta cillar a kan gado cikin zallar b'acin rai tana zaga d'akin tana fad'in, "Rainin hankali mai lasisi kenan, ni zai yiwa irin wannan rainin wayon dan kawai ya raina ni ya raina yadda ya d'auko ni? Wato harda fad'awa Maman sa zan bishi bayan ban san ma yayi tafiyar ba? To wallahi bazan je ba sai dai duk abinda zai faru ya faru."

Wayar ta taji tana k'ara kamar bazata duba ba sai ta kalla taga sunan Umma ta d'auka ta zauna a gefe ta saka a kunne tace, "Umma barka da safiya." Umma tace, "Barkan ki Rauda, ya naji maganar ki wani iri haka?." Rauda tace, "Babu komai Umma. Ya mutanen gidan?."

"Alhamdulillah. Daman sanar dake zanyi y'ar wajan kawun ku Lawan ta haihu sai ki kirata kiyi mata barka kafin kije."
Rauda kamar tana gaban ta ta d'aga kai kafin tace, "in sha Allah Umma, Allah ya raya." Umma tace, Amin. Amma akwai abinda yake damun ki fad'a min ina jinki kar kice min babu." Rauda ta fashe da kuka jin hakan sai Umma tayi shiru gabanta yana fad'uwa kafin tace, "Nutsu kiyi min bayani, meya faru?." Rauda murya na rawa tace, "Umma na gaji da gidan nan gabad'aya."

Umma tace, "Meya faru?."
Rauda tace, "Umma baya sona gabad'aya sai a kwana biyu ban ganshi ba shima bai ganni ba kuma hakan bai dame shi ba, yau tafiya yayi zuwa Abuja amma ban sani ba sai a bakin k'annen sa nake ji Umma."

Umma tayi shiru kafin tace, "Tsayar da kukan tukunna." Rauda taja numfashi ta goge idanunta sannan Umma tace, "Shine zai neme ki kenan ba kece zaki neme shi ba ko Rauda? Wato kece mijin shi kuma shine matar ko?." Kafin tayi magana Umma tace, "duk irin qalubalen da ya tsallake da rijiya da ya tsallake da baya duk baki gani ba sai kin sake d'ora masa wata damuwar? Zuwan ki gidan wacce gudunmawa kika bashi wacce zata kore masa damuwar da yake ciki?."

Rauda tayi shiru kafin tace, "Tsakani da Allah Umma ni banyi komai ba, hasalima ni bana zuwa inda yake indai ba abinci zan kai masa ba." Umma tace, "Baki da hankali ashe ban sani ba Rauda?." Rauda tace, "Umma haushin sa nake ji kin sani, ta dalilin sa fa kika......" Umma ta katse ta tace, "Dake da haushin nasa da kike ji kunci uban ku, shi baice yana jin haushin ki ba sai kece zaki ce kina jin haushin sa?. Ki tuna mahaifiyar sa kwanciya rashin lafiya tayi, ya rasa soyayyar y'an uwan sa guda biyu dukkan su suna son ganin bayan sa, ya rasa lafiyar mahaifin sa a baya, ya rasa komai hatta ke ya rasa, a wannan gab'ar yana neman wacce zata share masa hawaye ta yaye masa damuwa ta taushi zuciyar sa ta rarrashe shi kodan ya rage zafin da yake ji a zuciyar sa. Ki tuna Hydar ke kanki da Hydar kika sanshi amma me Hydar yayi masa? Ke wannan an fad'a miki abu ne mai sauk'i? Kin san zafi da k'unar da zaiji a ransa ace k'anin sa uwa d'aya uba daya shine yake neman kashe shi?. Ki tuna yayan sa da suke ciki d'aya shine ya dinga Zina da matar sa har tayi ciki wannan ma ba damuwa bace? Ke wacece da zai saurare ki yana cikin wannan yanayin bayan baki taimake shi wajan ganin an kawar da damuwar ba?."

Yadda Umma take mata fad'a sai taji fad'an yana shiga zuciyar ta abinda take fad'a kuma gaskiya ne sai ta sake nutsuwa taji tana cewa, "Ke kad'ai ce zaki d'auke masa damuwa kuma kin share shi to me kike so yayi miki? Zuwa zaiyi ya durk'usa akan guiwar sa yace miki Rauda ki rarrashe ni?."

Nan ma Rauda tayi shiru Umma tace, "Zaki ragewa kanki matsayi da k'ima a wajan sa, duk soyayyar da yake miki wannan banzar dabi'ar taki zata d'auke ta cillar da ita a gefe domin baki da amfani a wajan sa indai baza ki wanke masa damuwar da take ransa ba. Na tabbata yana buk'atar ki a kusa dashi ko in kula d'in ne da kike nunawa ya saka shima ya watsar dake, to dan yayi tafiya bai fad'a miki ba kuma sai kiji haushi? Naga ke kika zab'arwa kanki hakan ai ko?. Ai sai kije ki tayi Rauda tunda haka kika zab'a Allah ya bada sa'a kina zaune zai k'ara aure daman sarakuna basu zama da mata d'aya" tana fad'ar hakan ta yanke wayar bata jira Rauda tace komai ba.

Rauda tabi wayar da kallo k'irjin ta yana bugawa matuk'a cikin tashin hankali da gano zallar laifinta da kuma wautar da ta tafka a cikin lamarin, babban abinda yafi d'aga mata hankali bai wuce kalmar kishiya da Umma tace ba nan take hankalin ta ya sake tashi matuk'a......
[17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*090.*

? ? ?? Da kallo tabi wayar jikinta kamar an zare duk kuzarin jiki ta ajjiye ta a gefen ta ta sauke numfashi ta tallafi hab'ar ta da duka hannayen ta ta lumshe idanu tare da jan numfashi ta sauke sannan ta buWe idanunta tana jin babu dad'i a zuciyar ta.

Bata kai ga yanke tunanin da zatayi ba wayar ta ta sake yin k'ara ta duba ganin sunan Yaya Ummi ya saka ta d'auka kafin tayi magana ta rufe ta da fad'a ta inda take shiga bata nan take fita ba hakan ya saka ta tayi shiru tana jin me take cewa.

"Wallahi Rauda ban d'auka shirmen ki ya kai haka ba, duk ina jin yadda kukayi da Umma kin bani kunya da mamaki wallahi. Duk abinda yayi miki wannan halin da yake ciki ai yaci ace kin ajjiye naki fushin ki taya shi korar nasa kodan samun sasauci a zuciyar sa. Wa yake dashi da zai rarrashe shi Hydar ne yanzu kuma yana ina?."

Rauda bata iya magana ba Yaya Ummi ta kuma cewa, "Kiyi gaggawar samun sa yanzu in da yadda za'ayi ki bishi inda ya tafi in babu hali kuma ki jira ya dawo ki gyara kuskuren ki in ba haka ba zakiyi dana sani" tana fad'ar hakan ta yanke wayar Rauda ta sake ajjiye wayar tana jin zuciyar ta na rawa sosai.

Duk sai hankalin ta ya tashi ta rasa inda zata saka kanta tunawa fa da duk abinda kace mata gaskiya ne gashi bata san ya zatayi ba,yanke shawarar kiran sa tayi a waya sai kuma ta fasa ta kira number Suhaima. Suhaima tana d'auka tace, "Babar Yayar mu." Rauda tace, "Sister number Suhail zaki tura min." Ta amsa da to ta kashe wayar jim kad'an sai ga number ta shigo ba tare da shawara ba Rauda ta kira number.

Bata jima tana ringing ba aka d'auka tayi sallama ya amsa kafin tace, "Dan Allah Suhail ne?." Ya amsa da fad'in, "Eh shine." Rauda ta sauke ajiyar zuciya tace, "Rauda ce take magana." Jin abinda tace sai yace, "Ranki ya dad'e,?da kanki Allah yasa lafiya?." Rauda ta d'anyi shiru kafin tace, "Ina so zaka kai ni inda Sultan yake dan Allah."

Suhail yayi murmushi yace, "Haba ranki ya dad'e umarni kawai zaki bani sai a aiwatar, yanzu zan k'araso in sha Allah."
"Na gode" ta amsa tana yanke wayar kafin ta tashi jikinta duka babu dad'i.

Rasa ma abinda zatayi tayi gabad'aya zuciyar ta babu dad'i ta koma ta zauna tayi tagumi kawai tana tuno fuskar sa a jiya da daddare yadda yake kallon ta da alamun maganar ta ta shige shi sosai. Furzar da iska tayi tana k'arewa d'akin nata kallo cikin rashin sanin abinda zatayi.

Tashi tayi ta shiga band'aki tayi sabon wanka ta canja kaya ta saka dogon wando ta saka vest mai k'aramin hannu ta zuba turare a jikinta kafin ta d'auko abaya cikin kayanta ta saka a jikinta ta nad'a mayafin tayi kyau sosai cikin shigar ta d'auki zoben da ya bata a Cairo ta cire ta saka a daidai lokacin da Suhail ya kira number ta.

D'aukar wayar tayi kafin tayi magana yace, "Ranki ya dad'e na iso, a ina zan same ki?." Rauda ta sauke numfashi tace, "Kazo kawai bakin apartment d'in nan zan fito." Ya amsa ta kashe wayar ta fito falon tare da kulle d'akin ta ta zare key d'in ta fito k'aramin falon ta dukka babu kowa ta fito babban nan taga hadiman ta ganin ta duk suka mik'e tsaye Jakadiyar tana fadin, "Barka da fitowa uwar gida ga mai martaba sarki katagum, takawar ki lafiya mara mai farar aniya, zuciyar ki wankakkiya fuskar ki wankakkiya. Allah yaja zamanin ki ya baki dukkan abinda kike so." Kanta taji ya fashe sosai tana jinjina dad'in mulki domin kuwa ba k'aramin girma taji ta k'ara ba fad'ar wad'annan kalaman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login