Showing 90001 words to 93000 words out of 216282 words

Chapter 31 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

yace, "karb'i."

Ta karb'a yace, "Ki tabbatar kin bashi wannan magani yasha in kikayi sa'a zai samu lafiya iya na yau in kuma bai samu lafiya ba shikenan sai dai kiyi hak'uri." Kallon sa take kamar bata yadda ba ya rik'e hannun ta yace, "trust me bazan cutar dake ba, ina sonki ke kin sani that's why nake nema miki duk abinda kike so." Ta sauke numfashi tace, "ta yaya zan amince?."
"U know bazan cutar Asad ba ko kad'an, I love him so much so bazan cutar dashi ba."

Kai ta girgiza kana tace, "Okay I will try it now." Yayi murmushi tare da yi mata kiss a goshi yace, "That's my friend." Ya kalle ta yace, "Jeki, zan saka a dawo da hasken." Ta juya ta tafi yayi murmushi yana sosa gemun sa yana hango yadda zai same ta a b'agas ba tare da wata matsala ba.

Tana dawowa inda take haske ya dawo ta nufi b'angaren Mai martaba ta hau sama ta same shi a zaune ya dafe kansa yayi shiru alamun akwai abinda yake damun sa, zama tayi kusa dashi tace, "akwai abinda yake damun sarkina?." Kallonta yayi ya girgiza kai alamun babu komai ta tashi ta kawo masa lemon da taga yana yawan sha wato five alive ta had'o da cup ta zuba masa tace, "take it pls."? Kamar bazai karb'a ba sai kuma ya karb'a yasha ya ajjiye cup d'in ta bishi da kallo sai taga ya tashi ya shiga d'akin karatu baice komai ba. Murmushi tayi ta girgiza kai ta tashi ta shiga d'akin sa ta shafe jikinta da turaren ta fito falo ta zauna.

Bai jima ba ya dawo ya wuce ta zuwa d'aki ya jima da shiga tabi bayan sa ta ganshi da laptop a cinyar sa yana dannawa ta k'araso ta d'auke laptop d'in ta zauna a cinyar sa ta sak'alo hannun ta wuyan sa ta kwantar da kanta a jikin sa. Khamshin turaren ta ya bugar dashi sosai ta fara kissing d'in sa a wuya da fuskar sa a hankali. So yake ya daure ya kawar da ita daga jikin sa but turaren yayi tasiri a jikin sa sosai lokaci d'aya ya fara fita daga hankalin sa yana jin kansa yana sarawa sosai.

? ?? Kamar wanda ya tuna wani abun sai ya firgita ya ture ta daga jikin sa ya mik'e tsaye ta rik'e hannun sa tace, "Please My king." Ya sauke numfashi yace, "I'm sorry" yana fad'a ya zame hannun sa ya fita daga d'akin ta cure waje d'aya ta fashe da kuka dan a wannan lokacin ta kai mak'ura. Ta jima tana kukan ta kafin ta share hawayen ta ta d'auki hijjabin ta ta fita daga d'akin ta sauka ta fita daga b'angaren ma gabad'aya dan ranta ya b'aci.

Gabad'ayan ta wani iri take jinta ta kasa jurewa tana shiga d'aki ta d'auki wayar ta hannu na rawa ta danna number Aliyu, ba jimawa ya d'auka tace, "i need your help Aliyu." Daga can b'angaren yayi kyakykyawan murmushi yace, "Zan taimake ki kar ki damu, ki nutsu zan miki duk abinda kike so ki daina kuka" yana fad'a ya yanke wayar yana bin wayar da kallo yana juyawa ta a hannun sa yana murmushi yace, "Lokaci ya fara Asad, bazaka iya yin komai ba duk abinda ka mallaka sai ya dawo tafin hannuna" yayi murmushi ya kwantar da kansa a jikin kujera yana murmushi zuciyar sa cike da farin ciki.


FitattuBiyar
Nana Haleema.
[17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*053.*

? ? ? ? ?? A zaune yake a k'asa kusa da k'afafun ta kamar koda yaushe in ya kai mata ziyara ta d'ora k'afa kan d'aya da file a hannun ta tana shan khamshi ji take kamar bazata iya magana ba sabida izzar da take ji da ita a wannan lokacin, file d'in ta mik'a masa tace, "Saka min hannu akai." Asad ya karb'i file d'in yaga akwai biro a ciki yana karanta takardar daki-daki har ya fahimci ta maye ya d'ago zaiyi magana tace, "Abinda na saka ka nace kayi ba magana ba."

Ya d'an gyara zaman sa zuciyar sa cike da tunanin sanya a hannu a takardar amma babu damar musu, kallon sa take yi ganin yana juya biron tace, "baza kayi bane?." Ba yadda ya iya haka ya saka hannu ya rufe ya mik'a mata ta karb'a tana murmushi kana tace, "Sai abu na gaba, ina so filin can na baya a tasar min gini a cikin sa bazai yu ina matsayin babar ka na zauna waje mai iri d'aya da sauran ba, ya zama dole a banbanta ni."

Asad yace, "in sha Allah za'ayi." Mama tace, "Sai batun bawa Aliyu da Hydar sarauta banji kace komai bafa." Asad yace, "Aliyu yace baya so Hydar kuma baya nan shiyasa ba'a yi komai ba."
"To yanzu meye a gaba?."
"Ina da meeting da shugaban k'asa gobe a Abuja, then zan wuce Germany wajan Abba daga nan zan shiga madina akwai taron da aka gayyace ni."

Mama ta yatsine fuska jin yayi maganar mahaifin sa ita sam bata son ma abinda zai dawo da mahaifin sa kar yazo ya takura mata ya hanata rawar gaban hantsi gwara yaje can ya k'arata tace, "da matar ka zaka tafi?." Asad ya girgiza kai alamun a'a tace, "Meyasa bazaka tafi da ita ba?." Ya lumshe ido ya bud'e kana yace, "Bazan jima ba."
"Allah ya kiyaye."
"Amin. Godiya nake Allah yaja da rai" ya furta a tusashe cikin girmamawa matuk'a.

Shiru ya ratsa tsakani kafin tace, "Zaka iya tafiya."
"A huta lafiya" ya furta yana mik'ewa yana takawa a hankali ya fita daga falon aka take masa baya mutane sama da goma yana gaba ana binsa a baya ko tsuntu baya giftawa ta wajan sai in ya wuce sabida tsabar girmamawa.
Mota ya shiga aka saki jiniya aka d'auki hanyar Bauchi kai tsaye airport suka nufa har gaban private get motar taje ya fito ya shiga jirgi shida shamakin sa da Uncle suka wuce Abuja.

? ?? A kan idanun Aliyu Asad ya fita yayi murmushin farin ciki ya fito zuwa b'angaren Mama ya same ta a zaune da file d'in a kusa da ita ya zauna a inda Asad ya tashi ta kalle shi tace, "Ya dai?." Ya saki murmushi bai ce komai ba ta kuma cewa, "Kamar akwai magana a bakin ka."
"Babu komai Mama, tafiya zanyi shiyasa nazo na sanar dake zan jima sosai kuma in na tafi." Ta yatsine fuska tace, "Allah ya dawo dakai lafiya."
"Amin Mamana, ina godiya."

File d'in gefen ta yabi da kallo kana yace, "Wannan file d'in....." ya fad'a yana niyar d'auka ta d'auke bata bari ya d'auka ba tace, "Bana son bincke, tashi ka bani waje." Murmushi yayi kad'an yace, "A tashi lafiya" yana fad'a ya tashi ya fita yana dariya farin ciki na cika zuciyar sa domin akwai abinda zai aiwatar.

A ranar Asad suka gama da president a ranar jirgin su ya d'aga zuwa Germany dan Allah ya sani ya k'agu yaga jikin mahaifin sa shiyasa ko hutawa ma baiyi ba suka wuce. Lokacin da suka sauka ko masauki basu je suka wuce asibitin direct ba tare da sanin Hydar ba.

Hydar yana tsaye kusa da likitan da yake duba Abba ana saka masa ruwa har loakcin yana kwance baya ko motsin kirki suka ga an bud'e k'ofa a shigo, Hydar wara idanun sa yayi ganin d'an uwan nasa cikin kamala da shigar da in ka kalle shi sai ya kuma kallo kana ganin sa kasan ba k'aramin mutum bane ba, kana kallon sa kaga basarake mai ji da sarauta da isa da kuma ilimi. Hydar ya washe baki farin ciki ya cika zuciyar sa yace, "Barka da zuwa Ranka ya dad'e, bismillah ranka ya dad'e" ya fad'a yana bashi kujera yana kallon sa shima shi yake kallo.

Zama Asad yayi ya kalli Dr cikin harshen turanci yace, "Likita ya jikin sa? Me yake damun sa?." Likitan ya kalle shi yace, "An rasa actual d'in abinda za'a ce yana damun sa, anyi scanning ba'a komai ba har yanzu, mu kan mu baza muce ga abinda yake damun sa ba." Asad ya sauke numfashi ya kalli Hydar yace, "In haka ne why ake ajjiye shi a nan? Meyasa baza mu koma India ba?."

Hydar ya sosa kansa cikin girmamawa yace, "Ranka ya dad'e hakan naso yi sai mukayi waya da Uncle yace in bari yazo in anga abinda bazai yu ba sai a koma gida ayi na hausa a had'a da addu'a. " Asad ya kalli mahaifin sa ya tashi ya k'arasa inda yake yana kallon sa idanun sa a kulle ko ina na jikin sa ya saki ga rama yayi sai haske gashin fuskar sa kamar wanda aka fito dashi daga prison. Numfashi Asad yayi ya d'ora hannun sa a goshin mahaifin sa ya kalli Uncle sai Uncle yace, "Ranka ya dad'e yana dakyau aje a huta in yaso sai mu kamo bakin zaren."

Asad bai iya magana ba ya sauke numfashi ya kalli Dr yace, "Ina so na gana da babban likitan asibitin nan." Likitan yace, "yana office, muje na raka ka." Asad yayi gaba likitan yabi bayan sa uncle ma yabi bayan sa haka Hydar zuwa office d'in. Abinda wancan likitan ya fad'a shi wannan ya maimaita haka suka fito suka tafi masauki gabad'aya jikin Asad a sanyaye yake zuciyar sa cike da nazarin mafitar da ya kamata ya samo.

? ? ? ?? A masauki shi kad'ai ne a d'akin ya yayi wanka tare da sallah ya zauna domin a gajiya yake sosai daga Abuja bai huta ba suka yo nan daga zuwan su kuma suka wuce asibiti, buga k'ofar akayi ya bada umarnin shigowa Uncle da kansa ya shigo hannun sa rik'e da babar leda yace, "Ranka ya dad'e ga abinci." Asad ya saunke numfashi yace, "Uncle bana tunanin zan iya cin wani abu." Uncle yace, "daurewa? za'ayi."
"Yanayin jikin Abba ya dame ni musamman yanzu dana ganshi."
"Dole a shiga damuwa ranka ya dad'e, amma ni a gani na a huta in yaso sai mu kamo bakin zaren." Asad yace, "have a seat Uncle."

? ?? Uncle ya zauna yana kallon Asad da ya dafe jijiyoyin kansa da suke harbawa kusan minti biyar kana yace, "I feel like basu iya aiki bane, ta yaya za'a ce an rasa abinda yake damun sa har tsahon wannan lokacin?." Uncle yace, "Ranka ya dad'e da alama an manta a inda muke, Germany ce fa cinbiyar da suka k'ware wajan duba marasa lafiya da k'wararrun likitoci." Asad kamar zaiyi kuka yace, "But why suka kasa yiwa Abba komai? Ka tuna yadda ya koma fa."

"Abinda mamaki gaskiya, sai nake ganin mu koma gida dashi ayi masa maganin hausa da addu'a a ganina hakan zaifi. Tunda har akazo nan akace an kasa ganewa da alama ciwon nasa bana asibiti bane yana buk'atar maganin mu na gida da kuma addu'a." Asad yayi shiru baice komai ba ya cize bakin sa zuciyar sa cike da tunani Uncle ganin ya shiga tunani sai ya bashi waje Asad ya jingina da jikin gado yana aikin tunanin ta inda zai b'ullowa lamarin.

Kasancewar da rana suka shiga bacci Asad yayi sai dare ya farka bai ma iya cin abincin ba sai bayan yayi wanka yayi alwala ya saka manyan kaya da babar riga wacce taji aikin sarakai ya saka hula mara girma ya kawo hirami ya d'ora a kai ya fito sak a babban malami. A sannan ya d'anci abincin kad'an ya fito suka shiga masallaci sallah daga nan suka koma asibitin.

A nan suka sake tarar da Hydar kamar koda yaushe Asad baiyi ta kansa ba yaje ya nemi transfer daga asibitin zuwa asibitin madina, bayan ya dawo d'akin Hydar ya kalle shi shima shi yake kallo kamar zaiyi magana sai ya fasa ya fita shi kad'ai ya tsaya a harabar asibitin daga ciki Hydar ya biyo bayan sa yace, "Amma da ka barshi a nan a ganina zai fi samun kula duba da yanayin likitocin su." Asad ya sauke numfashi ya kalli Hydar kana yace, "can yafi safe."
"Ta yaya yafi nan bayan su na can d'in ma nan suke kawo marasa lafiyar su?."

Asad yayi shiru kamar bazai yi magana ba kafin yace, "Can akwai albarkar garin addu'a sai ta bashi lafiya." Hydar yace, "Haka ne. Wai Mama ko Hajiya babu wanda zaizo ya kula da Abba ne? Sai dai suyo waya itama sai sunga dama kamar farin ciki suke da ciwon nan nasa. Har gwara ma sauran akan Mama ita kamar ma abin bai dame ta ba."

Asad yayi murmushin takaici ya cize bakin sa shi kansa yana yiwa kansa addu'ar Allah kar ya jarrabce shi da mata irin su Mama gabad'aya babu wacce ta damu da rashin lafiyar mijinta abinda yake gaban su kawai suke yi musamman ma Mama da kawai burin ta yayi abinda take so a k'arkashin mulkin sa.

? ? ? ? "Kai baza ka iya kula dashi ba?." Hydar ya kalle shi yace, "Akan me bazan iya ba? Gani nayi ya kamata ace koda sau d'aya ne sunzo sunga jikin sa tunda har gobe miji yake a wajan su, har su Yaya sunzo sunga jikin sa amma su basu zoba. Aliyu shi kam ko waya, hakan yana k'ona min rai."

Asad ya kawar da kai gefe baice komai ba Hydar yace, "Allah ya kyauta." Ya k'arewa Asad kallo sai yayi murmushi yace, "Asad ka koma babban mutum kamar ba kai ba, ka sake yin kamala kamar mai shekaru da yawa, fuskar ka ta koma ta manyan mutane ta k'aro kwarjini da sanin ya kamata."
Bai bashi amsa ba kawai ya juya ya bar wajan Hydar yayi murmushi yana girgiza kansa shima ya juya yabi bayan sa.

*&&&*

? ? ? ? ?? "Amma dai bashi da kirki bashi da mutunci bai san mutunci ba, har gida dan tsabar ya raina mu yazo yayi mata saki uku! Haba dan Allah" Yaya Ummi ta fad'a kamar zatayi kuka tana kallon Rauda. Umma da take jinta ta tabe baki tace, "To ya za'ayi ne wai? Wannan cacar bakin da kuke yi nida ku babu wanda ya isa ya canja k'addarar nan Allah ya rubuta faruwar ta kuma ta faru."

Yaya Ummi tace, "Amma dai duk da hakan akwai ciwo Umma, kwata-kwata nawa Raudan da take da za'a ce ta koma bazawara? Kalle ta fa sabida Allah bai cutar da ita ba?. Daman cana akwai manufar da ta kawo shi gidan nan neman aurenta ba soyayya ba." Umma tace, "kuma dai, sai yanzu kika fahimta ai da kema idanun ki ai rufe k'anwar ki zata shiga gidan sarauta." Rauda dai tana zaune bata ce komai ba tayi shiru kanta ciwo yake mata matuk'a bazata iya magana ba.

? ? ? "Allah sai yabi miki hakkin ki Rauda wallahi sai yayi dana sanin abinda yayi miki sai kuma yayi kuka da idanun sa, aikin banza wanda ilimin sa bai amfana masa komai ba. Shine zai had'a ki da kud'i wato sune abinda kike so ko?." Rauda bata ce k'ala ba ta sunkuyar da kanta k'asa kawai amma batayi magana ba.


Umma tace, "Nida Bauchi zan tura ta ma gidan Yaya Bilki taje ta gama iddar a can sai ta dawo. Babban farin cikina ma ni da ba kowa ne yasan anyi auren ba da yawan mutane sun san ance yana sonta ya kuma biya mata kud'in aikin k'afa amma basu san an d'aura auren ba a wancan lokacin na jiki ne kawai suka sani, naji dad'in hakan sosai ba kowa ne zai san sun rabu ba."

? ? ? ? "A haka kamar mutumin kirki har ana yabon sa ace yafi kowa cikin y'ay'an mai martaba ashe shima da kashin sa a jikin sa, shiyasa aka d'aura auren a sirrance babu wanda ya sani kenan?. Kai ai bama iya shi kad'ai ne ya cuce mu ba har baban sa wallahi domin shine ya bada goyan baya." Umma tace, "wannan kumfar bakin da kike yi fa duk na banza ne, tunda Allah ya saka dai ta samu lafiyar k'afar ta shikenan mun gode Allah."

Shigowar Baba shine ya hana Yaya Ummi magana ya kalli Ummi yace, "Ki taya y'ar uwar ki da addu'a shine yafi ba wannan d'aga muryar ba dan ba amfani zatayi miki na. Rauda baki da lafiya ne?" Ya fad'a a tausahe yana kallonta. Kallon sa tayi cike da mamakin yadda yayi mata magana tace, "Kaina ne yake ciwo Baba."
"Dole kanki yayi ciwo kin kwana kina kuka, Kisha magani zai daina in sha Allah. Ki kwantar da hankalin ki kuma komai ya faru Allah ya k'addara faruwar sa tun kina ciki kafin kizo duniya, komai zai wuce tamkar bai faru ba.

Kai ta d'aga zuciyar ta cike da jin dad'in yadda Baban yake mata magana cikin taushin murya da kalamai masu kwantar da hankali ba kamar jiya ba sai taji hankalin ta ya sake kwanciya ko babu komai tasan yanzu Baba bazai ga laifin ta akan sakin ba. Baba yaa kalli Umma yaga fuskar nan tata a d'aure ta kawar da kanta gefe yace, "Binta kawo min ruwan sha sama." Kafin tace wani abun ya fita Umma da tasan babu wani ruwa da za'a kai masa badan taso ba ta mik'e bata d'auki ruwan ba ta fita.

Rauda tace, "Allah yasa su shirya, Yaya Ummi jiya naga tashin hankalin da ban tab'a gani ba Baba kamar zai daki Umma." Yaya Ummi tace, "da alama, a yanayin sa ai zaki ga ya gano bai kyauta ba shiyasa kika ga ya sauko har yana rarrashin ki. Daman banda abin Baba meye na fad'a?." Rauda bata ce komai ba tayi tagumi kawai tana kallon wani wajan daban.

? ? ? ? Lokacin da Umma ta hau saman a zaune ta same shi ta shiga ta zauna itama batayi magana ba yace, "Binta nasan ban kwanta ba jiya ni kaina sai yanzu na gano kuskure na tun farkon maganar sa da Rauda nine na bayar da goyan bayan ko meye ya faru nine na bada k'ofar faruwar sa. Kiyi hak'uri ki d'auka k'addara ce abinda ya faru jiya ma kiyi hak'uri."

Umma ta sauke numfashi tace, "Ya wuce." Baba yace, "itama Rauda ki bata hak'uri nasan ban kyauta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login