Showing 138001 words to 141000 words out of 216282 words

Chapter 47 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

ganin Asad ya haukace har sun hak'ura in suka yiwa Aliyu maganar sai yace yana sane kuma yana sane d'in akwai abinda yake shiryawa wanda yafi nasu.

Hajiya Mama an fara farfad'owa ginin da take so ayi mata an gama cikin sati d'aya har ta tare a cewar ta ba matsayin ta d'aya da ragowar matan gidan ba duk da girman kan ba kamar baya ba. Jikin mai martaba ana ta samun cigaba sosai duk da akwai wanda basa son farfad'owar sa.

*&&&*

? ? ? ? Bikin Rauda ya rage saura sati biyu an kawo lefe akwati goma sha hud'u ko wacce cike taf da kaya komai akwatin sa akayi masa y'an uwa da abokan arzuk'i sai murna kawai ake yi. An ta jeren gidan amarya a unguwar Tatari Ali quarters?? gida d'ankarere mai kyau da tsari kowa yaje sai ya dawo yana santin gidan.

? ? ? ? ? Suna zaune ana ta shara yadda shagalin kamu zai gudana duka matan gidan ana zaune ana hira ita tana gefe tayi shiru domin mugun zazzaSi take ji a jikinta, Yaya Fariha ta kalle ta tace, "Wai amarya lafiya kike ana hira kin yi shiru?."
Rauda tace, "wallahi zazzaSi nake ji sosai ga ciwon kai." Yaya Shamsiyya tace, "Muda muke da Fariha kun manta ta kusa magana karatun ta? Duba mana ita ki bata magani bana son wannan zaman nata shiru wallahi."

Yaya fariha ta k'arasa kusa da Rauda tace, "Kodai malaria ko typhoid shine yake damun ta, abinda zai faru ina jin ina da sabon sring a aljihun jakata dana siya a makaranta muka gwada wani abu bara na d'auki jinin ki aje a gwada dan mu san meye" ta fad'a tana d'aukowa daga Jakarta.

? ? ? Jinin Raudan aka d'iba ta yago takarda daga Jakarta tace, "Maza Rahma jeki nan baya ayi wannan test d'in" ta fad'a tana rubutu ta bawa Rahma da kud'i wacce take zaune.? Rahma ta karb'a ta mik'e ta fita tace, "kifa yi sauri kar jinin ya daskare."

? ? ? ? Rahma na fita Baba ya shigo yace, "Ah lallai yau an zo za'a cinye min abincin gida, ko wacce ta kwaso yara an tawo zaman hira kawai." Da yake sun saba da halin mahaifin nasu dukkan su dariya sukayi kawai aka gaisa ganin su tare shima sai ya zauna ana hirar dashi.

"Ke kuma lafiya?" Ya fad'a yana kallon Rauda. Yaya fariha tace, "ZazzaSin nan dai, na bayar dai yanzu ayi mata test na malaria da typhoid yadda zamu gane wanne ne yafi yawa sai ayi maganin sa kai tsaye."
Baba yace, "Yau dai naga amfanin karatun ki." Ummulkhairi da take gefe tace, "Baba nima in mukayi waec wannan shekarar shi nake so nayi."
"Sai kiyi ai" ya bata amsa yana tab'e bakin sa kafin yace, "Itama mijin tane yake biya ki jira kiyi aure kema mijin naki ya biya miki."

Yaya Shamsiyya tace, "Ai ko mijin ta bai biya ba Baba mu zamu biya mata, Allah yana rufa mana asiri dukkan mu yanzu Alhamdulillah." Baba yace, "Masalaha mai kyau." Umma da Inna dai kanzil basu ce ba suna dai zaune suna jin me ake yi.

? ? ? ? Rahma ce ta shigo da sallama ta mik'awa Yaya Fariha takardar tace, "Ashe gwajin ba wahala, nan da nan akayi ashe ma uku yayi wai ya manta ya had'a da gwajin ciki." Yaya Fariha tayi dariya tace, "Yo ina ruwan mu da gwajin wani ciki ana zaune lafiya" ta fad'a tana warware takardar tana dubawa.

? ? ? ?? Dummmmm gabanta yayi mugun fad'uwa a gigice tace, "Ke anya jinin dana baki ya gwada kuwa? Kodai anyi had'e dana wani?." Rahma tace, "A'a Yaya, babu kowa ma fa a lab d'in ni kawai aka yiwa gwajin." Yayar mu tace, "Lafiya?."

Shiru tayi ta sake kallon takardar hannun ta yana rawa tace, "Ba lafiya ba, bara na sake d'aukar sample d'in naje da kaina a sake yi na gani." Baba yace, "Fad'a mana abinda kika gani har ya tayar miki da hankali haka." Tace, "bara dai a sake yi Baba wannan bai nuna daidai ba."

Yayar mu tace, "Dalla Malama ki? fad'a. Wani ciwon ne Raudan!?" Ta fad'a cikin tsawa tana kallon ta. Umma da take gefe tace, "K'anjamau ce ko me Fariha?." Duk sai suka rud'a ta tace, "Gwajin da akayi mata ne ya tabbatar akwai ciki a jikin ta na sati biyu......!"
[17/12, 10:41 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*068.*

? ? ? ? ? A tare dukkan su k'irjin sa ya bada sauti mai k'arfi da hakan ya saka wasu daga cikin su dafe k'irji tare da runtse ido firgici ya mamaye fuskar su da zuciyoyin su nan take suka ji abinda basu tab'a ji ba. "Kee Fariha wanne irin ciki ana zaune qalau? Gwajin jinin Rauda nefa ba naki kona Ummi ba" Yayar mu ta fad'a tana kallon ta itama da alaamun tashin hankalin a tare da ita.

? ? ? ?? Yaya fariha idanunta ya fito waje sabida tashin hankali ta sake kallon takardar ta kalle su tace, "Abinda sakamakon ya nuna kenan shiyasa nace anyi kuskure wajan yin gwajin, gwara a sake daukar sample d'in a sake yi sai a tabbatar." Baba da ya kasa cewa komai sai baki da ya buWe zuciyar sa kamar ana doka ganga yace, "Ya dai kamata a sake yi amma har na cikin a sake gwadawa."

Umma da taji hawaye masu d'umi suna sakko mata daga idanunta ta girgiza kai tace, "Basai an sake yin gwajin nan ba abinda aka gani tabbas hakan ne, na fukanci hakan a yanayin ta daga jiya zuwa yau gudun kar zagi ya shiga zuciya ta sai na watsar da abin na barshi a rashin lafiyar da take fama da ita ne kawai. Amma sakamakon ku gaskiya ne Rauda nada ciki!."

"Wannan wacce irin maganar banza ce Binta? Da bakin ki kike cewa Rauda nada ciki?" Baba ya fad'a a fusace yana kallon ta kafin yaja tsaki yace, "Fariha sake d'aukar jinin muje tare a sake yin gwajin mu gani." Rauda da take zaune kamar an dasa bishiya sai idanu da take binsu dashi amma ko kad'an ta kasa fahimtar ma abinda suke cewa,? tunda aka furta kalmar ciki shikenan sai kwakwalwarta ta tsaya cak ta daina aiki gabad'aya, tana ji dai suna ambatar ciki amma bata san me suke cewa ba.

? ? ? ? Har aka huda fatar ta aka saka k'arfe cikin jijiyar ta aka d'auki jini bata sani ba wani wajan kawai take kallo zuciyar ta kamar ana kid'an kwarya sabida duka. Baba da Fariha suka fita falon yayi shiru baka jin motsin kowa sai sautin kukan Umma kawai da ya cika falon dan ita zuciyarta ta tabbatar mata da gwajin da akayi gaskiya ne ba k'arya ba.

Inna tace, "Haba Binta kin bani mamaki wallahi, na d'auka kece mace ta farko da zakiyi shaida halayen Rauda na kamun kai amma sai gashi kece kika fara furta kalma mara dad'i a kanta. Gaskiya baki kyauta ba bai kamata ki d'auki zugar shaid'an ba har ki furta wannan kalamai akan Rauda." Yaya Shamsiyya duk da k'irjin ta da yake bugawa tace, "Abinda na gani kenan Inna, Umma bai kamata kiyi saurin yadda da abinda akayi kuskure wajan yin sa ba."

Umma dai kanzil bata ce ba Yaya Babba kuma Yaya Ummi da Yaya Nafisa sunyi shiru basa iya cewa komai kowa zuciyar sa cike da tsoro jiran dawowar Baba kawai akeyi.
"Tana ina dan Ubanta!" Baba ya fad'a da k'arfin gaske yana shigowa hannun sa rik'e da zarbad'ed'iyar bulala ya k'arasa wajan Rauda da ta rasa hankalin ta na wucin gadi.

? ? ? ? K'arfi ya saka ya finciko ta babu zato babu tsammani ya ta fara jin saukar bulala, dukan shine ya dawo da ita hankalin ta ta fara kuka yana dukanta duk ta inda yaso amma ta daure hawaye kawai take yi bata ihu. "Ni zaki tonawa asiri Rauda? Me kike nema kika rasa a gidan nan da zaki bari wani yayi miki ciki?. Bikin ki saura kwana goma sha hud'u ki rasa abinda zaki zo mana dashi sai ciki Rauda?" Ya fad'a yana dukan ta da iyakacin k'arfin sa ta ko ina ita kuma tana kuka.

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!!" duka matan suka fad'a suna mik'ewa tsaye Umma kuwa kukan tane ya k'aru Inna na zaune kusa da ita dan ta rasa ma bakin magana.? Sautin bulalar Baba kawai ake ji a falon ganin dukan da Baba yake mata yayi yawa zai iya jawo mata matsalar Yaya Fariha ta k'arasa ta rik'e bulalar tana kuka tace, "Dan Allah Baba ka bar dukan ta haka, zama ya kamata muyi muji taya aka samu cikin duka ba shine mafita ba."

Baba yana wuci muryar sa na rawa yace, "Fariha ko ki sakar min bulalar nan kona had'a dake" ya fad'a yana fincikar bulalar ya cigaba da dukanta zuwa lokacin fatar hannun Rauda da bayan ta da k'afafun ta duk sun fashe suna jini amma bai daina dukan ta ba. Sai a sannan ta fara kuka sosai har muryar ta ta dashe sabida kuka Yaya Fariha ta shiga tsakiya wai ko Baba zai daina dukanta amma sai ya had'a da ita dole tayi tsalle ta koma gefe taga ya ajjiye bulalar ya rik'e fuskarta yana marin ta ta ko wanne b'angare.

Bakin ta da hancin ta suka fashe amma Baba bai daina dukan ta ba ganin hakan ya saka matan tasowa a guje suka janyeta suka tura ta d'aki suka kulle k'ofar dukkan su kuka suke har babar Yayar su, Yayar mu ta kalli Baba tana kuka tace, "Kayi hak'uri dan Allah mu zauna da ita aji waye yayi mata cikin, wannan dukan zaka iya kashe ta."

Umma da take zaune tace, "in ta mutu sai me? Mutuwar itace ta dace da rayuwarta a yanzu. Bikinta sati biyu fa kacal ya rage da wanne ido zamu kalli Anas muce masa ciki ne da ita? Me muka yi mata tayi mana wannan sakayyar? Me ta nema ta rasa a gidan nan da zata je ta bawa wani kanta?. Duk lokatun baya da suka wuce batayi ba sai yanzu da yake tana son......." kasa k'arasawa Umma tayi sabida kuka da jirin da take ji duk da a zaune tane.

? ? ?? A guje Yaya Nafisa tayi kan Umma ganin kamar zata kifa ta rik'e ta tace, "Dan Allah Umma ki daina kuka, k'addara ce ta same mu muyi rokon Allah ya bamu ikon cinye jarabawar."? Umma tace, "So take ta kashe ni kawai Nafisa so take taga an fita da gawata daga gidan nan, in ba haka ba me take so wanda bata dashi a cikin gidan nan?, ina tarbiyyar da ilimin nata suke?. Tsakanina da Rauda Allah ya......." da sauri suka dakatar da Umma wajan fad'in, "Kar ki furta Umma dan Allah kiyi hak'uri, ku tsaya muji uzurin ta wata?ila fyad'e akayi mata."

? ? ?? Baba ya cillar da bulalar yana wuci ya zauna a kan kujera ya hard'e yatsun sa waje daya yana kallon wani wajan daban yana maimaita kalmar ciki a zuciyar sa, "Rauda tana da ciki kuma cikin shege a cikin gidana, bikinta saura sati biyu taje tayo min ciki dan ta wula?anta ni a duniya" sai kuma ya zabura ya sake nufar k'ofar d'akin da suka saka ta da sauri sukayi saurin tarewa yace, "In baku bani hanya ba wallahi zan had'a daku na zane."

"Kayi hak'uri Baba in ka sake dukanta mutuwa zatayi" Yaya Ummi ta fad'a tana kuka sosai. Baba yace, "ta mutu d'in mana daman raywuata bata da amfani a yanzu, gwara ta mutu nasan mutuwa tayi da abinda zai faru nan gaba."

"Asslamu alaikum" aka fad'a daga k'ofa aka shigo duk suka kalli wajan aka amsa a ciki banda Baba da ko gezau baiyi ba balle ya juya, Kawu Badamasi ne da Kawu Mansur suka shigo Yaya Nafisa tace, "Gwara da kuka Baba zai kashe Rauda." Kawu Badamasi yace, "Adamu zo ka zauna ka bar wajan nan."

Baba yace, "in ba kashe yarinyar ciki nayi ba hankalina bazai kwanta ba."
"Kasheta ba shine mafita ba, kazo ka zauna kawai." Kai ya girgiza kai ya juyo da baya ya zauna akaan kujera suma duk suka zauna Kawu Mansur yace, "Nafisa ce ta kira mu ta sanar damu abinda yake faruwa shiyasa muka taso muka zo dan a kamo bakin zaren, duka ba shine magani ba a halin da ake ciki."

Kawu Badamasi ya kalli Umma da take kuka yace, "Haba Binta kiyi hak'uri mana ki daina wannan kukan komai zaiyi daidai in Allah ya amince."
"Meye zaiyi daidai d'in? Ciki fa tayi ba gwara a kashe ta d'in a huta ba."
"Haba haba, me kike cewa haka kamar ba ke ba? Dan Allah ki kwantar da hankalin ki."

Kawu Badamasi yace, "Adamu ba'a neman mafita da duka, ka sassauta zuciyar ka dan Allah a kira ta a tambaye ta wanda yayi mata cikin." Baba ya kalle shi yace, "Bikin ta saura sati biyu yau, da wanne ido zan kalli wanda zata aura nace masa ciki ne da Rauda dan Allah?" Baba ya fad'a muryar sa na rawa kamar zai yi kuka.

Kawu Mansur yace, "in kuma cikin nasa ne fa? Rauda tana da wanda take saurara ne in ba shi ba?." Dukkan su gaban su sai da ya fad'i Baba ya girgiza kai yace, "Anas bazai tab'a aikata wannan d'anyen aikin ba na tabbatar da hakan, sai dai wani daban amma bashi ba."

Kawu Badamasi yace, "Tana ina?." Yayar mu tace, "Tana cikin d'aki Baba yayi mata duka sosai."
"Kuje ku bata magani tasha in anjima zamu dawo sai ta sanar damu koma waye yayi mata cikin. Dan Allah kar wanda ya sake dukan ta, kar kuma wanda yayi mata wata maganar ku k'yaleta taji da abinda take ji itama dan na tabbata babu wanda a cikin ku ya kaita jin ciwon abinda ya faru."

? ?? Rauda da take jin duk abinda da ake cewa kanta ya sake yin nauyi hawayen ma sun tsaya cak tana kwance a kan tiles tana jan numfashi dak'yar kamar zai bar jikinta, kalmar Allah ya isa da Umma taso furta mata tafi komai d'aga mata hankali ta juya idanu bakinta duk jini haka hancin ta zuciyarta na rawa. Me zatayi me kuma zata ce? Da wanne ido zata kalli iyayenta?, da wanne ido zata kalli Anas?. Sai hawaye sharrr tuna yadda yake ta shirin zuwan bikin nan yanzu ashe maaa tana da ciki. "Na shiga uku!" Ta furta kanta na bala'in sarawa gefen idanun ta yayi ja jini ya taru a ciki sabida marin da tasha wajan Baba.

? ? ? K'ofar aka bud'e daidai lokacin da take kwara amai tana daga kwance da sauri sakayo kanta suka kamata suka ga tana son kwacewa Yaya Ummi tace, "wayyo ciwon jikin ki ko? Sannu" suka kamata zuwa kan gado suka zaunar, Yaya Ummi ta cire mata hijjabin jikinta Yaya nafisa ta d'ebo ruwa aka goge aman da tayi ta jingina a jikin Yaya fariha tana sauke ajiyar zuciya.

Dukkan su kuka suke tausayin ta ya dirar musu a zuciya Yaya Fariha tace, "Jikinta yayi zafi fa sosai." Yaya Nafisa ta k'araso ta goge mata hancin ta da bakinta da suke a fashe tace, "Ki daina kuka Rauda komai ya faru da Allah jarabawa ce, Allah zai tona asirin wanda yayi miki fyad'e in sha Allah."

Yaya fariha tace, "A bata magani tasha ko zazzaSin zai sauka." Yaya Ummi tace, "Ina da sudrex a jaka ta bara na d'auko" ta fad'a tana mik'ewa. Yaya Fariha tace, "A'a Yaya Ummi in tasha sudrex zata iya yin miscarriage yayi k'arfi sosai sai dai normal p.c.m." Yaya Nafisa tace, "To ya zube mana, ni naso ma dukan nan da tasha ya zube wallahi kowa ya huta." Akan mudubi Yaya Ummi taga p.c.m ta d'auko aka bata tasha tana sauke numfashi jikinta duk ya fashe sabida duka.

? ?? Kuka ta fashe dashi ta kank'ame Yaya Fariha tana kuka sosai duk suma sai suka sake fashewa da kuka Yaya Fariha itama ta rik'e ta tace, "Ki daina kuka Rauda, ki daina kuka dan Allah." Kukan take sosai ta kasa magana sai kanta da yake harbawa tana jan numfashi kamar zai bar jikinta.

? ? Yaya fariha ta kwantar da ita suka suka zauna a gefen ta suna ta rarrashin ta duk da ta kasa magana, Yaya fariha ta mik'e tace, "Bara na bawa Ummulkhairi ta siyo mata maganin ciwon jiki" ta fad'a tana fita falon.
Kamar gidan makoki haka falon yake Umma na zaune zazzaSi ya rufe ta Inna ta kalli Fariha tace, "zo ki duba Umman taku." K'arasowa tayi ta tab'a jin Umma tafi zafi zau ta d'auke hannun ta ta d'auki biro da takarda ta rubuta maganin da za'a siyo har da allurar da zatayi Umma.

Ummulkhairi ta bawa tace taje ta siyo ta had'a su da Khalil tace ya rakata, jikin Ummulkhairi a sanyaye suka tafi suka je suka siyo a pharmacy da yake can bakin titi suka siyo duka abinda ta rubuta suka d'auko hanyar dawowa gida. Farar mota suka gani a ajjiye suka zo giftawa ta motar suka ji ance, "Khalil ko?." Juyawa sukayi dukkan su suka had'a ido da wanda yake zaune a ciki ya sauke glass kad'an ya kalle su da murmushi Ummulkhairi tace, "Ina wuni."

"Lafiya" ya amsa a tak'aice Khalil yace, "Kai ba wannan ne sarki ba?, wallahi shine, Anty Khairi sarki ne fa" ya fad'a a rud'e yana kallonta. Murmushi yayi kad'an yace, "shiii" alamun yayi shiru ya daina magana.

Khalil yana ta murmushi yaga sarki Asad ya sauke numfashi yana bin su da kallo kafin yace, "Ina kuka je?." Khalil yace, "Mun siyo magani za'a bawa Anty Rauda bata da lafiya, Baba yayi mata duka har bakinta sai da ya fashe. Kasan wai me akace?" Sai yayi shiru yana kallon sa.

Hankalin sa ya tattara gabad'aya akan Khalil ya girgiza kai alamun a'a Khalil yace, "Ance wai tana da ciki shine Baba ya mata duka jikinta duk ya fashe" ya fad'a kamar zaiyi kuka.
"Kai Khalil baka da hankali?" Khairi ta fad'a tana talle masa k'eya taja hannun sa tana fad'in, "Wallahi na sake ji ka fad'awa wani wannan maganar sai na fad'awa Baba ya zane ka kaima, banza mai surutun tsiya" ta fad'a suna yin gaba tana jan hannun sa.

"Duka!"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login