Showing 99001 words to 102000 words out of 216282 words

Chapter 34 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

take ta samu mafita amma ta rasa inda zata samu ta d'auki waya ta kira babar yayar su amma wayar a kashe ta ajjiye wayar ta dafe kanta da duka hannayen ta.

"Ni Rabi'a Jidda zata yiwa wannan wula?ancin? Inaaaa bata isa ba wallahi ba kuma zata isa ba har abada" ta fad'a tana sake naushin iska cikin tashin hankalin da bata san iyakar adadin sa ba.

Bata san ina adadin lokacin da ta d'auka tana a? haka ba ita dai tasan bata jin bacci ko kad'an ga abinda ya kuma tsaya mata a rai rashin kiran ta da Mum bata yi hakan ya sake tauar mata da hankali matuk'a. Bacci b'arawo ne ya sace Mama shima tana yi tana mafarkai tana farkawa.

Washe gari.

*&&*

? ? ?? "Rauda!" Umma ta fad'a tana tab'a ta tayi firgigit ta kalli Umma tare da sauke tagumin fuskar ta tace, "Na'am Umma, yaushe kika shigo?." Umma tace, "ta ya zaki san na shigo bayan kin shiga duniyar tunani?. Anya Rauda kina son samawa zuciyar ki salama kuwa? Kin mayar da tunani abokin ki koda yaushe kuna tare dan k'addara ta fad'o rayuwar ki?, meyasa baza kiyi tawakkali bane?."

Ta sunkuyar da kai Umma ta kuma cewa, "da k'aracin shekarun ki zaki jawowa kan ki ciwo sabida d'a namiji, son sa kike har haka ne?." Ta kalli Umma ta sake sunkuyar da kai Umma ta kuma cewa, "kinyi gangancin bari soyayyar sa ta shiga zuciyar ki, kin sani ba tsarar ki bane daman akwai dalilin da ya saka shi auren ki ya samu abinda yake so kuma ya barki, kina saka damuwa a ranki shi yana can yana walwala yama manta da shafin ki a rayuwar sa ke kuma kina nan zaki kashe kanki da tunani. Ina rok'on Allah da na sanki da shi Rauda? Ina karatun alkur'anin da na san ki dashi duk ina suka tafi?."

? ? ? Rauda ta share idanun ta tace, "Umma bawai ina sonsa bane kawai in na tuna ni a yanzu bazawara ce sai naji zuciyata ta karye."
"Rashin karb'ar k'addarar kenan Rauda, dole ki damu amma bana tunanin zaki kaini damuwa domin nice mahaifiyar ki, addu'ar da nake yi babu dare babu rana shine ya sa kike ganin kamar ni abun bai dame ni ba amma na fiki damuwa. Ki cigaba da addu'a da rok'on Allah komai zai wuce ya zama tamkar ba'a yi ba, duk kin bi kin rame kin sake yin bak'i kamar ba ke ba."

Rauda ta sauke numfashi tace, "In sha Allah Umma zanyi."
"To yayi kyau. Kizo ga Habiba da Walida sun zo wajan ki" tana fad'a ta fita daga d'akin Rauda ta sauke numfashi ta tashi ta fito daga d'akin zuwa falo.?

A zaune ta same su suna shan ruwa ta k'araso tana fad'in, "manyan manya maganin k'ananu yara." Dariya sukayi bayan ta zauna Habiba tace, "kodai kece manyan ba, ai wallahi baki da kirki gabad'aya bakya neman mutane ko a waya ma an daina samun ki. Nifa ban san ma kin dawo daga gyaran k'afa ba sai jiya."

Rauda tayi y'ar dariya tace, "Bari kawai, wallahi kaina ne ya cushe ni ko fita bana yi, tsohuwar wayata kuma a can na cillar da ita ban sani ba. Ya kuke ya kwana biyu?." Walida tace, "lafiya lau, k'afa tayi kyau Allah ya kiyaye gaba."
"Amin ya Allah. Ya su Gwaggo dasu Umma?."
Habiba tace, "Gwaggo tana gidan sarki yanzu ma daga wajan ta nake."

Rauda tayi murmushi kawai Walida ta kalli Habiba tace, "Sai da kika ce gidan sarki na tuna ina cewa zan tambaye ki, ance yanzu gidan ya sake damalmalewa ko?." Habiba tace, "Uhum bari kedai kawai. Asad d'in da muke ganin in ya karb'i sarauta zamu ji dad'i mu da muka rab'i aiki a gida yanzu ya canja gabad'aya,? da farko ya fara taimako da sadaka kamar yadda kowa ya san shi da ita, ba wula?anci sai girmamawa amma yanzu....." ta k'arasa fad'a tana rik'e hab'a.

"Yanzu me?" Rauda ta samu kanta da tambaya ba tare da tayi niyar hakan ba. Habiba ta kalle ta tace, "Baya ganin k'imar kowa sai matar sa kawai wata shegiya kyakykyawar gaske kamar aljana, fatar ta har yellow take sabida haske gata bata da kirki ko misqala zarratun wula?anci a cikin ta kamar me. Duk soyayyar mai martaba Asad da Maman sa wallahi ta raba su."

Walida tace, "ni naji dad'in hakan ai maganin babar tasa akayi dan ba kirki ne da ita ba." Habiba tace, "ke kin san ba'a binne sirri a gidan sarauta, jiya ita matar tasa gimbiya Jidda kun san Gwaggona tana daga cikin hadiman ta ita take fad'a min d'azu tace ko babar Mai martaba d'in ce tazo shiga wajanta indai batayi izinin a barta ba duk wanda ya barta ta shigo a bakin aikin sa."

Walida ta bud'e baki tace, "Tooo! Lallai bata da kirki lamarin nata babba ne." Habiba tace, "duk inda kike tunanin rashin kirkin ta ta wuce haka. Amma fa itace daidai ita daman y'ar aminiyar tace farkon sarautar tasa sai abinda tace akeyi sabida tsantsar biyayyar da yake mata, yanzu kuwa an saka ta a gefe sai abinda matar take so akayi, babar tasa ma bata ma san meke faruwa bafa dan baya zuwa wajan ta."
Walida tace, "Ikon Allah, amma dai asirce shi sukayi ko?."
"Daman sai dai asirin ai ko nace tsafi ma dan yadda abun ya faru lokaci d'aya ke bakya ce zai faru ba."
"Amma na d'auka asiri baya kama masu sarauta sabida dafa'in da yake jikin su."

Dariya Habiba tayi tace, "Rauda kiji min walida dan Allah, akwai wanda asiri baya kamawa ne a duniya?. Ya kama annabin Allah ma balle wani sarkin katagum...?. Yana da ibada dan ibada kaf gidan babu mai ilimin addinin sa to abubuwan ne sunyi masa yawa, wannan ya jefe shi wancan ya jefe shi dan cikin y'an uwan sa ma ba kowa yake goyan bayan sarautar ba balle kuma y'an uwan mai martaba mai murabus. Ni wallahi har tausayi yake bani wani lokacin."

Walida tace, "wata?ila silar hakan sai babar sa tayi hankali nan gaba ai."? Habiba tace, "To gata nan dai. bata da kirki fa baki ga sai da tasan yadda tayi ta raba tsakanin Rauda da Asad d'in ba?." Gaban Rauda ya fad'i ta kalle su Walida tace, "Shiyasa nace Allah ya k'ara."
Habiba tace, "Shine abin tausayin daman ai ba ita ba, bata tab'a yi masa abinda yake so ba komai zab'in ta yake bi babu yadda ya iya, ta ya zata bar shi da Rauda..? Wallahi daman sai ta raba su ke matar nan shaid'aniya ce, ita ake zargi a rashin lafiyar mai martaba dan zata iya yin komai akan sarautar d'anta gashi ya karb'a kuma tana neman ta zamar mata masifa, shi Aliyun tunda ya bar k'asar sun kafe shi a can yak'i dawowa, shi kuma Hydar yana kula da mahaifin su shi kuma mai martaba an juyar da tunanin sa."

Walida ta ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?kalli Rauda tace, "ni nama ji dad'i da Allah bai k'addara kin aure shi ba da Allah kad'ai yasan me zai faru tunda babar sa bata da imani." Habiba tace, "Wallahi fa,? hakan ma dan Rauda tana da rik'o da addu'a ne da sai tayi mata wani gib'i a rayuwar ta ko a halittar ta." Walida zatayi magana Rauda da take jin su tace, "Dan Allah mu bar maganar gidan sarautar na can suje da matsalar su muma muji da tamu. Bara na dafa mana taliya koda manja ne muci" ta fad'a tana tashi ta shiga kitchen.

Jim kad'an ta fito tace, "Habiba wai ina saurayin ki?." Habiba tace, "yana nan yana min wasa da hankali, dana ce ya fito sai ya fara kawo min zancen da ba shikenan ba."
"Ahh to ba son ki yake yi ba" Rauda ta fad'a tana zama.

"Assalamu alaikum! Asslamu alaikum!!" Aka fad'a sau biyu daga tsakar gida Rauda ta amsa tare da tashi ta nufi tsakar gidan, yaro ta gani yace, "Ana sallama da mai gidan a waje." Rauda ta kalli saman Baba tace, "To bara nayi masa magana" ta fad'a tana komawa ciki ta sanar da Umma ta fito dan taje wajan sa.

Zama tayi suka cigaba da hira jim kad'an suka fara jiyo hayaniya a waje ga kuma muryar Baba, Rauda ta saka mayafi suka fita su uku nan suka ga motar rushe gidaje da ta d"ibar k'asa ga dogarai sama da biyar a wajan alamun daga gidan sarauta suke.

Muryar Baba taji yana fad'in, "Ban fahimta ba? Wanne irin filin talakawa anyi gini dashi?." D'aya daga cikin su yace, "tun bayan kwana biyu da suka wuce mun kawo muku notice na tashi daga gidan nan baku tashi ba, masarauta ta bada umarnin a rushe gidan nan yau domin fitarwa da talakwan da aka kwace filayen baya hakkin su."

"Kamar ya kenan?" Rauda ta fad'a tana kallon sa. Ya kalle ta yace, "kamar yadda kuka ji na fad'a. Wannan gidan zamu rushe shine yanzu bamu damu da kun kwashe komai na ciki ba tunda an sanar daku ku tashi."
"Akan wanne dalilin za'a rushe mana gida?" Ta fad'a tana kallon sa.
Cikin tsawa yace, "umarnin masarauta ne!." Itama cikin tsawa tace, "Masarauta ai ba gwamnati bace, Gwamnati ce take da wannan ikon amma ba masarautar da take k'asan gwamnatin ba. Dan tsabar rainin hankali kawai ku kwaso mota kuce zaku rushe mana gida? Shi sarkin da ya turo ku gwamna ne shi kome?."

? ? ? "Ke y'ar talakawa ki iya kalaman ki akan mai martaba" wani daga baya ya fad'a yana kallon ta. Ta kalle shi tace, "in nak'i na iya bakin nawa akwai abinda zakuyi min ne?. Dan kawai mu aka raina gida a lungu zaku zo kuce wai anyi gini a filin talakawa?. Banga wanda ya isa ya rushe gidan nan ba koda shi kansa sarkin ne zaizo wajan nan." Baba ya kalli Rauda yace, "Nutsu malama, uban me ya fito dake wajan nan?." ya dawo da kallon sa ga mutanen yace, "ta ina gidana ya zama filin talakawa bayan gidan nan nawa ne shekara da shekaru ina zaune a cikin sa?."

Anas da ya faka daga baya mamakin mutanen yake yi ya fito daga motar ya k'araso wajan yaga Baba da Rauda a wajan ya k'araso yace, "Baba lafiya?." Rauda tace, "wani rainin hankali suka zo mana dashi wai zasu rushe gidan nan wai akwai filin talakawa, kuma wai daga masarauta dan tsabar sun mayar damu wanda basa fahimta." Anas ya kalle su yace, "wanne irin filin talakawa ana zaune lafiya?."
"Masarauta ce ta bada umarnin hakan."
"Masarauta ai ba gwamnati bace bata da wannan hurumin, gidan nan yafi shekara ashirin a wajan nan gyara shi kawai akayi tun lokacin ba'a ce akwai filin talakawa ba sai yanzu?."

Babban cikin su yace, "Kaga malam umarni aka bamu dole kuma mu cika shi." Anas yace, "Ina plan d'in filin talakawan?." Ya mik'a masa ya karb'a ya ware yana dubawa Anas ya kalle shi yace, "ko zamu iya magana a gefe?." Ba musu yabi bayan sa sun jima suna tattaunawa kafin Baba yaga sun shiga mota sun bar wajan Anas ya dawo wajan Baba yace, "Baba mu shiga ciki." Ba musu suka shiga Habiba da Walida suka tafi cikin mamakin wannan lamari.

A harabar gidan yace, "Baba sun k'i amincewa sunce umanini ne daga masarauta na lallab'a su sun k'ara kwana biyu."
Rauda ta kalle shi tace, "Wai ban gane kwana biyu ba? Kana so kace sai an rushe gidan kenan?." Ya kalle ta ya d'aga mata kai ta wara idanu tace, "Akan wanne dalili kenan? Filin wa akayi gini dashi?."

Baba ya kalle ta yace, "Shiga gida Rauda." Ba musu ta juya ta shiga gida Baba ya kalli Anas yace, "abinda ban gane ba meye had'in masarauta da ginin gidan nan? Filin me ake magana akai?." Anas yace, "Baba a ganina kawai wannan wata manak'isa daga masarautar, ana so a wulak'anta ahlin gidan nan ne kawai ba wani abun ba. In ba haka ba babu ta yadda za'ayi ace wai sunzo zasu rushe gida, ko gwamnati bata rushe gida sai bisa ka'ida balle su."Baba ya girgiza kai alamun gamsuwa da maganar Anas yace, "babu damuwa Anas, ina zuwa" ya fad'a yana shiga cikin gidan.

Ba jimawa ya fito ya wuce Anas ya biyo shi yana cewa, "Baba duk inda zaka je zan ka basai kaje titi ba." Baba ya kalle shi yace, "Na sani Anas, ina so naje a motar hayan ne." Ya nufi kan titi ya hau abin hawa ya tafi gidan sarkin kai tsaye.

Lokacin gab da sallar azahar ya shiga har cikin gidan masallacin cikin gida ya zauna yasan indai mai martaban yana gari tabbas zai fito sallah.
Hakan ce ta kasance kuwa ana yin kiran sallah ya aka sanar da isowar sa bayan an tary gabad'aya, bayan an idar mai martaba ya fita Baba yabi bayan sa ya shiga cikin makarrban sa ya k'arasa gaban sa yana fad'in, "Barka da rana ranka ya dad'e." Cak ya tsaya ya kalli gefen da Baba yake sai kuma ya d'auke kansa bai amsa ba sai yayi ciki Baba duk da haka bai daina bin bayan sa ba.

? ?? K'aramar fada ya shiga Baba yana tsaye sai ga dogari yazo yace ya shigo suka shiga Baba yana baya shi yana gaba, a k'asa ya zube yana yi masa jinjina yace, "Allah yaja da ran sarki, Allah ya k'arawa sarki lafiya da tsahon rai, Allah yasa afi haka." Lumshe ido yayi ya bud'e shamakin sa da sauran dogarai suna amsawa da amin kafin wani dogari yace, "Fad'i matsalar ka."

Baba ya gyara zama duk sai yaji wani iri ganin yanayin Asad din shima sai yasha jinin jikin sa yace, "Ranka ya dad'e kwana biyu da suka wuce aka kai mana takarda akace wai notice ne umarni daga gare ka mu tashi za'a rushe inda muke zaune, ban d'auki abinda mahimmaci ba amma sai gashi yau anje da motar rusau za'a rushe, shine nazo gare ka duba da ban san dalilin hakan ba."

Asad yayi shiru zuciyar sa na bala'in harbawa amma kuma haushin Baban yake ji gabad'aya a zuciyar sa ba tare da ya shirya ba yace, "Ba iya gidan ku kawai bane, duk gidan da ya shiga hurumin talaka zamu rushe shi."

"Wannan gaskiya ne, dan sarki kake jikan sarki kuma sarki" aka fad'a daga zaune cikin kirari. Baba jikin sa yayi sanyi ya kuma cewa, "Amma ranka ya dad'e gidana yafi sama da shekara ashiriin a inda yake gyare-gyare kawai aka samu ba samon gini bane, a duba lamarin ranka ya dad'e" ya fad'a a sanyaye zuciyar sa na bugawa.

"Iya abinda zamu iya kenan" ya furta a hankali ba tare da ya kalli Baban ba fuskar Asad d'in a d'aure matuk'a. Baba ya kalle shi cikin mamaki ganin kamar bai gane shi ba hakan ya saka shi sake kallon sa cikin dunbin al'ajabi.
"K'asa da idanun ka, Hattara Dattijo kallon idanun mai martaba yafi k'arfin ka." Baba ya saukar da ido yace, "Allah yaja zamanin mai martaba bamu da inda zamu koma in hakan ta kasance, kuma a ina neman afuwa amma rushe gida a k'arkashin gwamnati yake ba masarauta ba."

"Hattara dattijo! Kasan a inda kake" aka fad'awa Baba cikin tsawa. Baba yace, "Tuba nake." Asad yayi shiru idanun sa a lumshe sam baya k'aunar ganin Baba ko kad'an a kusa dashi ya sunkuya ya rad'awa na gefen sa magana sai ya zabura ya mik'e yace, "Dattijo muje." Baba ya kalle shi ya kalli mai martaba ganin da gaske babu fuskar maganar sai yayi k'asa da kasa, "Tashi mana!" Aka sake fad'a da k'arfi Baba ya firgita ya mik'e ya fita jikin sa yana rawa zuciyar sa cike da zallar mamakin Asad da kuma tsoro........
[17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*057.*

? ? ? ? ? Mamaki ya gama dabaibaye Baba tafiya yake jiki a sanyaye kamar zai kifa kansa har juyawa yake sabida yadda lamarin ya cushe masa kai da kwakwalwar sa. "Baba!" aka fad'a daga gefe Baba ya kalli inda yaji an kira sunan sa yaga Hydar ne fuskar sa da murmushi yana k'arasowa inda yake.

Baba ma murmushin k'arfin hali yayi yace, "Ranka ya dad'e." Hydar yayi murmushi yace, "ziyara aka zo mana kenan?." Baba ya numfashi yace, "kusan hakan, matsala ce aka je mana da mota za'a rushe mana gida wai anyi gini a filin marayu, shine nazo da kaina wajan mai martaba naji abinda ya jawo hakan dan kowa yasan gidana yafi shekara ashirin a wajan da yake gyaran da kuka yi mana shine kawai ya sauya shi."

Hydar yace, "rushe gida kuma? To ya kukayi dashi?." Baba yace, "to bai ma saurare ni yadda ya kamata ba balle har yaji dalilin hakan, abinda yace min kawai iya abinda za'a iya kenan. Yanzu akan wanne dalili kenan za'a rushe mana gida? Mu ba'a kan hanya muke ba, ba'a kan titi muke ba rana tsaka azo ace za'a tashe mu ina zamu je?." Hydar ya furzar da iska zuciyar sa cike da bak'in cikin yace, "kayi hak'uri Baba, zan iya iya bakin k'ok'ari na wajan ganin hakan bata kasance ba in sha Allah. Ka kwantar da hankalin ka ya canja halayyar sane gabad'aya yanzu wani lokacin in yayi wani abun kamar bashi ba."

Baba ya girgiza kai yace, "to na gode, sai anjima" abinda yace kenan ya juya zai tafi, Hydar ya d'auko kud'i yace, "Baba ga wannan ka hau mota." Baba ya kalli kud'in ya girgiza kai kana yace, "na gode" yana fad'a ya nufi hanyar fita Hydar ya bishi da kallo zuciyar sa sam babu dad'i ko kad'an.

Fusata Hydar yayi ya nufi b'angaren Mai martaba yayi sa'a har lokacin bai tashi ba ya shiga kansa tsaye ya same shi shida makarraban sa kowa ya bishi da kallo har Asad d'in dan yadda ya ganshi yasan ransa a b'ace yake, ganin hakan Hydar yace, "Ina son ganawa da mai martaba ni kad'ai, ko zaka iya bamu waje?."

Suka kalli Asad ya d'aga musu kai alamun suje auka Mike suna fad'in, "A tashi lafiya." Hydar ya kalle shi yana zaune yayi zaman sarkai akan kujera cikin shigar da ya saba in ba zaman fad'a zaiyi ba yace, "Amma kasan abinda kake aikatawa ba daidai bane ba ko?." Bai bashi amsa ba yasan daman bazai amsa masa ba yace, "Ina ruwan gidan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login