Showing 210001 words to 213000 words out of 216282 words

Chapter 71 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

Mama ta yafe min, ki cewa Asad ya yafe min dan Allah nasan babu lallai na kuma ganin su dan yau d'in nan zan kai kaina inda za'a jefe ni na mutu." Eman tana kuka matuk'a itama haka. Mum da take gefe tana kuka tace, "Kwarai son zuciyata ne ya jawo min, tabbas nice na jefa ki a wannan hali Jidda kiyi ha?uri ki yafe min dan Allah."

Jidda tace, "Babu yafiya tsakanin mu Mum, sai Allah yayi mana hisabi nida ke." Eman tace, "haba Jidda meyasa kike cewa haka? Yanzu kike cemin na fad'awa su Asad su yafe miki meyasa ita bazaki yafe mata ba?." Jidda tace, "Haka ne kuma, na yafe mata Eman amma ta cuce ni wallahi."

Tari Jidda ta fara tana dukan k'irjin ta ganin yadda idon ta yake k'afewa ya saka Eman fita a guje ta kira likita ya shigo a guje aka fitar da Eman aka rufu akan Jidda dan ganin a ceto rayuwarta dan yanayin nata yayi muni sosai ba kad'an ba amma abin yaci tura rai yayi halin sa lokaci ya riga yayi tafiya ko baka shirya ba sai kaje.

Fad'a musu ta rasu Eman ta zube a sume Mum ma bata sake sanin inda take ba. Daddy aka kira aka sanar dashi duk da abinda yake ji a kansu sai da hankalin sa ya tashi rasuwar Jidda ta tab'a shi gama jana'izar abinda ta haifa kenan itama ta bishi, ya rud'e sosai haka akazo aka d'auki gawar ta a safiyar akayi jana'izar Jidda wacce ta tara mutane dama dan shi kansa Daddy bai san za'a cika haka ba aka kaita makwancin ta Mum bata sani ba Eman ma tana sume.

*&&&*

? ? ? ? ? K'arar wayar sace ta tashe shi ya tashi yana yamutsa fuska ya kai kallon sa kan agogo yaga k'arfe d'aya daidai na rana ya wara idanun sa ya sakko daga kan gadon ya zauna ya d'auki wayar ganin mai kiran ya saka shi ya d'auka ya saka a kunne, "Zaki ina ka saka waya haka?." Asad ya gyara murya yace, "Barka da safiya Abba."
"Safiya! Da alama yanzu ka tashi kenan."

Asad ya dafe kansa yace, "Na kwana bana jin daWi ban samu bacci da wuri ba. Ina fatan Abba ya tashi lafiya." Mai martaba yace, "Alhamdulillah. Ya zaman Abujan?." Asad ya shafa kansa yace, "Alhamdulillah."
"Ina ta kiran ka tun d'azu na sanar dakai rasuwar matar ka Jidda da ita da abinda ta haifa duka Allah ya karb'e su."
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Yau akayi jana'izar ta?" Ya furta cikin bugawar zuciya.

"Tun safe akayi ana ta mamakin rashin ganin ka." Asad yace, "Hasbunallahu wani'imal wakil! Allah ya gafarta mata ya yafe mata yasa tana aljanna. Abinda ta haifa yasa ya kasance mai ceton ta." Abba yace, "Amin ya rabbil alamin. Babar ta da K'anwar ta har yanzu basu farfad'o ba suna sume, ita kanta babar ka mutuwar ta tab'a ta sosai."

Asad yayi shiru yana girgiza kai kafin Abba yace, "In ka kammala abinda kake yi dai zuwa gobe ko jibi ka dawo akwai abubuwan da suka taru suna jiran ka dawo ka aiwatar dasu." Asad yace, "In sha Allah." Daga nan sukayi sallama ya kashe nan ya duba yaga missed call d'in Mama dana Suhail.

Mama ya fara kira ta d'auka yace, "Barka da rana Mama." Mama tace, "Barka Asad."
"Ina neman afuwa ban d'auki kiran Mama ba."
"Babu komai Asad. Ka samu labarin rasuwar Jidda ko?" Ta fad'a muryar ta na rawa sosai. Kafin yayi magana tace, "Asad duka abinda Jidda ta aikata nima ina da hannu a ciki gashi ta rasu bata yafe min ba ya zanyi?."

Jin tana kuka sosai sai hankalin sa ya tashi ya sassauta murya yace, "Kiyi ha?uri Mama ki mata addu'a" ya fad'a dan bai san me zaice ba kuma. Kuka take sosai yana jinta sai da tayi kusan mintina bakwai tana kuka a waya shi kuma yayi shiru bai kashe ba yana jin kukan har zuciyar sa kafin yace, "Kiyi ha?uri Mama haka Allah ya rubuta abinda zaiyi silar rasuwar ta kenan." Yana ji ta sauke ajiyar zuciya kafin tace, "Ka gaida Rauda" tana fad'a ta yanke wayar yabi wayar da kallo zuciyar sa tana bugawa sosai.

Mutuwar yaji ta a jikin sa sosai bazai manta lokacin da suka je dubata ba duk da abinda ya faru yana yi mata fatan samun rahamar Allah, Rauda da tunda ya fara waya ta tashi tana jin duk abinda ake cewa tace, "Waye ya rasu Sultan?." Kallon ta yayi ya sauke numfashi yace, "Jidda ita da yaron ta." Rauda ta mik'e zaune tace, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, yaushe?."
"Yau" ya bata amsa a tak'aice.
"Allah ya gafarta mata yasa yaron ya zama mai ceton ta."

Numfashi ya sauke yace, "Amin. Mama tana gaishe ki" ya fad'a yana mik'ewa tsaye.
"Ina amsawa" ta fad'a jin wani iri wai Mama tana gaishe ta lallai duniya ta ishi kowa riga da wando harda babbar riga.

Agogo ta kalla ganin d'aya ta wuce sai ta sakko daga kan gadon ta tsaya itama kamar yadda yake a tsaye bai motsa ba sai k'asa da yake kallo, numfashi taga ya sauke ya juyo ya kalle ta ya mik'a mata hannu yace, "Wanka." KafaWar ta nok'e tace, "Zanyi ni a wani d'akin kayi kai a nan."

Duk da babu walwala a fuskar sa haka ya tako inda take ya rik'e hannun ta bai magana ba ya jata har cikin band'akin babu yadda zatayi dan babu fuskar musawa a tare dashi. Tare sukayi wankan suka fito ta zauna gefen gado tana kawar da fuska har gobe kunyar sa take ji shi kuma taga ya sakawa idanun sa toka baya jin kunyar ta ko kad'an kamar ba shine sarkin Katagum ba.

Sabuwar doguwar riga taga ya d'auko mata a leda irin mai laushi da babban mayafi ya mik'a mata ta kalli doguwar rigar tace, "Bani da undies fa." Tab'e baki yayi baice komai ba ya k'arasa inda take ya zira mata doguwar rigar ta sama ya zame towel d'in jikinta yace, "Sallah."

Shima doguwar rigar ya saka suka tayar da sallar azahar, bayan sun idar ya kalle ta yaga sai yanutsa fuska take ganin yana kallon ta tace, "Wallahi bana jin daWin zama haka babu komai a jikina, ni zan koma gida kawai yau." Bai tanka mata ba taga dai ya d'auki waya bata san me yayi ba taga ya ajjiye sai kuma ya kuma d'auka ya kira Suhail.

Yana d'auka yace, "Allah yaja zamanin mai martaba, Allah ya kiyaye mai martaba ya kare shi."
"Suhail" shine abinda ya furta kawai. Suhail yace, "Allah yaja zamanin ka ina cikin gidan tun safe na kawowa mai martaba abinda yace a kawo." Kai kawai ya girgiza kafin ya yanke wayar ya kalle ta yace, "Ina zuwa." Ya tashi tsaye itama ta tashi tana kallon sa tace, "tsoron gidan nan nake ji fa bazan iya zama ni kad'ai ba, nidai zan bika muje inda zaka gaka."

Kallon ta yayi sai yaga kamar ana ganin komai na jikin ta dan yadda ta motsa komai na jikinta motsi yake tunda babu komai a jikin nata, d'aure fuska taga ya sake yi amma duk da hakan bata hak'ura ba zai wuce ta tace, "Wallahi tsoro nake ji." Ganin a tsorace take sosai sai ya kira Suhail yace ya k'araso falon ya fita ita kuma ta zauna a d'akin.

Suhail na ganin sa ya mik'e tsaye har ya k'araso ya zauna Suhail yace, "Barka da fitowa ranka ya dad'e. " zama Asad yayi ya nuna masa kujera shima ya zauna kafin Suhail yace, "Ina fatan mai martaba ya samu lafiya." Asad yace, "Alhamdulillah." Suhail yace, "Sai aka tashi da rasuwa, Allah ya jikan wanda suka rasu." Nan ma ya amsa da amin kafin Suhail yace, "Ranka ya dad'e ga abincin, ga kuma list d'in matan da aka kawo wanda za'a aurar babu kayan d'aki. Ga kuma yawan takardun masu neman aikin da muka samu. Na bibiyi gidajen y'an matan da za'a aurar kuma na tabbatar da gaske auren zasuyi wasu abincin gidan ma yana gagarar su balle kayan d'aki."

"Su kuma samari masu neman aikin na tabbatar dukkan su babu aiki babu kuma Sana'a, a cikin su wasu babu mahaifi sai mahaifiya da y'an uwa nauyi ya hau kansu amma babu halin saukewa."

Karb'ar takadar Asad yayi yaga sunayen mata sama da hamshin ya girgiza kai yace, "A siyi kayan ko a basu kud'in?." Suhail yace, "A siyi kayan ranka ya dad'e." Asad ya girgiza kai ya mik'a masa yace, "Duk abinda ya kamata ayi, a had'a da kayan abinci ga kowa a d'ora kud'i."
"Kamar nawa kenan ranka ya dad'e? Abincin kuma kamar ya za'a saka?."

Asad yayi masa alama da yayi komai Suhail yace, "In sha Allah. Allah ya k'ara arzuk'i yasa a d'auki alkhairin da ake a duniya a gidan Aljanna.

A zuciya ya amsa da amin kafin Suhail yace, "Su kuma masu neman aikin zan rarraba wasu a company mai martaba wasu kuma za'a basu jari." Asad ya girgiza kai alamun gamsuwa kafin Suhail ya kuma cewa, "akwai bak'i da suka zo suna son ganin mai martaba na sanar dasu mai martaba yayi tafiya sun kafe akan zasu jira shi ya dawo." Yayi k'aramin tsaki yace, "bazan koma yanzu ba." Suhail yayi murmushi Asad ya kalle shi ya d'aga gira sama yace, "Fad'i abinda yake ranka."

Suhail ya shafa kai yana murmushi yace, "ni na iya ranka ya dad'e? Babu abinda yake raina sai alkhairi."? Asad yayi murmushi shima dan yadda yaji dad'in kwana d'ayan nan bazai koma ba sai sun kwana biyar cif. Asad yace, "Hydar bai shigo ba?." Suhail yace, "tun kwanaki ban sake ganin gilmawar sa a gidan ba."

Ya girgiza kai kawai baice komai ba dan ya tabbatar akwai abinda yake shiryawa shiyasa yayi shiru kamar babu shi. Wayar Suhail tayi k'ara bai d'auka ba Asad yace, "pick it, akwai abinda za'a baka ka kawo min." Jin hakan sai Suhail ya d'auka ai kuwa masu delivery ne ya fita yaje ya karb'o kayan a leda babba ya shigo dasu ya ajjiye.

Suhail yace, "Ranka ya dad'e in anyi min izini zan iya tafiya?." Asad ya d'aga masa kai ya mik'e sai Asad ya kalle shi yace, "Wai yaushe zakayi aure ne?." Suhail bai sam dariya ta sub'uce masa ba shima Asad d'in dariyar yayi Suhail yace, "Ranka ya dad'e an kusa in sha Allah." Maimakon yayi magana sai ya sake yin dariya y???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ana cize bakin sa kafin yace, "yafi dai."

Suhail yana dariya suka had'a ido sai yaga Asad d'in ya d'aga masa gira ya sake yin dariya yace, "Zan zo wajan mai martaba a nema min mata dan naga giyar auren har saurin warkar da marasa lafiya su warke." Asad yayi dariya mai sauti amma baice komai ba.

Suhail yace, "Na barka lafiya, a gaida Fulani." Kai ya d'aga masa yana murmushi har lokacin Suhail yana jin farin ciki a ransa dan yaga shugaban nasa yana farin ciki shi kuma yana so yaga yana farin ciki domin yana da ciwo a zuciyar sa sosai farin ciki shine kawai maganin ciwon.
[17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*094.*

? ? ? ? Yadda ta rame ta lalace kallo d'aya in kayi mata sai ka sake kai duba a gare ta sannan zaka tabbatar itace, tayi bak'i babu gayu a tare da ita balle ado da kwalliya. Fuskar ta ta jeme kamar an saka sirinji an kwashe albarkar fuskar ta ta koma y'ar k'arama kamar wacce ta shekara tana jinya. Tana zaune kusa da Mama tana kuka wanda ya zamar mata abokin hira tun bayan rasuwar Jidda har ta hawaye basa tsayawa a fuskar ta ko yaushe cikin zuba suke.

Itama Maman kuka take amma bai kai na Mum dukkan su sun kasa magana ga Eman a gefe itama ta rame sosai idanun ta yayi bala'in ja. Dak'yar Mum ta iya had'a kalmomin a kan harshen ta ta kalli Mama tace, "Na rasa ta wacce kalma zanyi amfani na nemi afuwar ki Rabi'a, na rasa wacce irin kalma zan furta wacce zata nuna miki nayi nadamar cin amanar ki."

Sai ta sake fashewa da sabon kuka zuciyar ta nayi mata kuna da ciwo tace, "Kin amince dani na ha'ince ki, babban burina naga bayan ki na mallake dukkan abubuwan da kike taqama dasu ke na raba ki dasu badan komai ba sai don son zuciyata da rashin k'aunar Allah da kuma zallar cin amana. Gashi yanzu dalilin mugun halina na kashe y'ata da kaina domin badan na d'ora ta akan turba mara kyau ba da duk hakan bai faru ba."

Mama ta girgiza kanta tace, "Sadiya laifina ne, da ban nuna miki burina akan sarautar ba da kema baki saka ranki a kai ba, dan nuna miki tsantsar son kai ba da kema baki yi wannan tunanin ba, da ban nuna miki in y'ar ki ta shigo gidan nan zan mayar da ita tamkar baiwa ba da kema baki tunanin d'aukar mataki ba, da ban nakasa Asad akan banzan burina ba da bata kai kanta ga Aliyu ba, da ban nuna nice nake so nayi iko da komai ba da baku mallake Aliyu ba. Duka wad'annan abubuwan nice naja nice na bada k'ofar da aka shigo aka aikata su, nice na bada dama nice na bada lasisin aikita dukkan abinda aka aikata shiyasa kike k'okarin kashe ni. Ni ya kamata na nemi yafiyar Jidda domin badan abinda na saka aka yiwa Asad ba da yanzu tana matsayin matar sa."

Mum ta girgiza kai tace, "Duk da haka ban zauna dake da zuciya d'aya ba, tabbas nasan yawan cewa a kashe wane da wance da kike cewa shine ya d'arsa min son kashe ki shiyasa na? saka aka kwance burkin motar Suhaima ta yadda zaku mutu gabad'aya amma Allah ya tseratar dake. Na sake bada guba aka saka miki a shayi shima Allah ya kubtar dake. Dan girman Allah kiyi hak'uri Fulani naga sakamakon aikata sharri tun kafin naje lahira, naga sakamakon mugun nufi tabbas naga amfanin karin maganar da hauwasa suke cewa in zaka hak'a Ramin mugunta ka yishi daidai kai."

Kuka suke dukka su biyun kafin Eman tace, "Mama kafin Yaya Jidda ta rasu ta bani sak'o na sanar dake ki yafe mata abubuwan data aikata miki, dan Allah ki yafe mata ko zata samu salama a cikin kabarin ta." Mama ta kalki Eman da take hawaye tace, "Na yafewa Jidda, nima naso tana raye ta yafe min dan ina da hannu a halin da ta shiga." Eman tace, "Mai martaba da matar sa tace na nema mata afuwar su Mama, a ina zan gansu?."

Mama ta share hawaye tace, "Asad da matar sa basa nan sunyi tafiya amma na tabbatar sun kusa dawowa. Allah ka yafe mana abubuwan da muka aikata dan tabbas duk cikin mu babu wanda baiga sakayyar Allah ba tun a duniya, shi waziri da ya tashi y'ay'a biyu ya rasa lokaci d'aya.....Allah ka yafe mana."

Mum tace, "Baki ce kin yafe min ba Fulani." Mama tace, "Na yafe miki, kema ki yafe ni."
"Na yafe miki nima. Allah ya saka da alkhairi" ta fad'a tana sake fashewa da kuka dukka su ukun kuka suke har Suhaima ta had'u da take gefen su.

*&&&&*

Cikin kwana hud'u da Asad da Rauda sakayi sun yishi cikin soyayya da nuna tsantsar kulawa ga junan su, ko gate basa fita ko yaushe suna cikin gida duk abinda suke so Suhail zai kawo musu ko yaushe suna tare da juna. Sunyi haske Asad har kib'a yayi dan ya samu mai kwantar masa da hankali bata barin sa cikin tunani da taga ya zauna shi kad'ai zata dawo kusa dashi tana bashi labari.

? ? ? ?? Tsaf ya shirya cikin manyan kaya shadda kalar ash colour babbar rigar har k'asa take tasha aiki kai da ka kalla kasan aikin bana k'ananun sarakuna bane, aka kawo alkyabba kalar shaddar aka d'ora akai aka saka rawani kalar aikin shaddar takalmi kalar shaddar da aikin da yake jikin ta. Ba sai ance yayi kyau ba kana kallon Asad kasan yayi kyau sosai yana tsaye a jikin madubi yana sake gyara rawanin kansa.

Rauda da take tsaye a bayan sa tana kallon sa tace, "Sulatan." Ta madubin ya kalle ta tace, "In ka saka kayan nan sai ka koma tamkar babba, kuruciyar ka sai ta b'uya sai manyanta ya bayyana akan fuskar ka. Kana kyau da kayan nan kamar daman dan kai aka yi su."

Yayi murmushi ya juyo yana kallon ta ta tako zuwa inda yake tana kallon sa itama kamar zai mata magana sai ya fasa ya juya yana cigaba da abinda yake yi amma har lokacin fuskar sa a sake take. Sai daga baya sannan yace, "Muwaddaty banso tafiya yau ba, amma ya zanyi dole na amsa kiran Abba in ba haka ba sai mun kwana bakwai a nan" ya juyo yama kallon ta yace, "Na jima ban samu farin ciki kamar na kwanakin nan ba."

Hannunta ta zaga dashi a jikin sa ta rik'e bayan sa tace, "Ai a can d'in ma muna tare ko yaushe." Yayi k'aramin tsaki ya girgiza kai yace, "ba kamar nan ba, can hayaniya tayi yawa."
"Abba yayi kira dole mu amsa, amma nima bana so mu tafi zaman nan yafi na can dad'i. Kasan ni ban saba da wannan kirari ga abubuwan da ake min ba sai naji wani iri" ta Fad'a tana kwanciya a jikin sa ya rik'e ta shima idanun sa a lumshe.

Jin yayi shiru ya saka tace, "Sultan baka ce komai akan makarantar tawa ba." Bai sake ta ba kuma bai magana ba yayi shiru suna tsaye a haka kamar baiji me tace ba jin yayi shiru itama sai tayi shiru.
"Kin tab'a ganin mace irin ki tana karatu a wata makaranta?." A sama taji maganar da bata d'auka ma zai sake maganar ba ta d'ago ta kalle shi tace, "To ai neman ilimi ne Sultan, kuma ina so shine burina a rayuwa."

"Badai a Nigeria ba sai dai in zaki iya a outside country" ya furta yana kallon ta sai yaga tayi murmushi tace, "Zan iya mana Sultan." Yayi murmushi baice komai ba ta bar jikin sa ya kalle ta yaga doguwar rigar jikinta bata nuna jiki ba kwata-kwata domin mai fad'i ce sosai ya rik'o

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login