Showing 45001 words to 48000 words out of 216282 words

Chapter 16 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

ta bita a baya suka shiga mota suka fita.

Tafiya suke har suka zo daf da gidan su Rauda daga can nesa ta tsaya ta kalle ta tace, "Karb'i wannan ki shafa a hijjabin ki ta baya." Karb'a tayi ta juyo da hijjabin tayi yadda tace ta kalle ta tace, "ki fita ki shiga gidan nan b'angaren haggu ki gaishe su kice dan Allah zaki gyara kanki ne kina hanya yazo miki baki sani ba, in sun baki hijjabi ko wani abun ki karb'a ki tawo ina nan ina jiran ki. In kika yi aiki mai kyau har suka baki kina da kyauta." Da to ta masa ta fita ta nufi cikin gidan Mum ta bita da kallo ganin yadda hijjab d'in ya lalace sai ka d'auka da gaske jinin ne.

Da sallama ta shiga b'angaren Umma tana zaune ita kad'ai Umma ta amsa Safiya ta durk'usa tace, "Ina wuni Hajiya." Umma ta murmusa tace, "lafiya lau."
"Taimako na shigo nema Hajiya, ina hanya ne naji zubar bak'on wata na ba tare da na shirya ba duk ya b'ata shine na shigo na gyara kaina in da hali." Umma tace, "Ayya, muje na kai ki band'aki" ta fad'a tana yin gaba tana binta a baya har d'akin su Rauda ta shigar da ita tace, "Ga band'aki nan ki shiga."
"Na gode Allah ya saka da alkhairi" Umma ta amsa da amin ta fita.

Kamar gaske Safiya ta shiga band'aki ta jika hijjabin jalaf duk a son ganin ta burge uwar d'akin ta ta fito ta saka shi a haka a wannan lokacin Umma ta shigo ganin haka ya saka tace, "Haba ke kuwa y'ar nan ina ke ina saka hijjabi mai danshi haka? Cire gana y'ata da bata nan kiyi amfani dashi yafi duhu koda wani abun ya zuba a jikin sa ma babu lallai a gane" ta fad'a tana bata maroon d'in hijjabi wanda tsahon sa ya wuce guiwa.

Safiya ta karb'a tana godiya tace, "Allah ya saka da alkhairi Hajiya ya biya ki. Zan dawo da hijjabin da na koma gida in sha Allah."
"Amin. Kar ki damu ki rik'e ma kema ai kamar y'ata kike. Ya sunan ki?."
"Allah ya saka da alkhairi. Suna na Safiya." Umma tace, "Ashe kakata ce shiyasa kike tsohuwa." Safiya tayi dariya daga nan sukayi sallama Safiya ta fito ta nufi motar Mum.

Tunda Mum ta hango ta da sabon hijjabin tayi ajiyar zuciya cikin farin ciki take kallon ta har ta shiga motar ta cire ta mik'awa Mum tace, "ga wannan ta bani tace na y'ar tane da bata nan." Mum tayi dariya ta karb'a ita kuma ta zauna babu hijjabin tace, "na gode Safiya, naji dad'in abinda kika yi min muna komawa gida zan baki kyauta ta ban mamaki." Safiya taji dad'i ta dinga murmushi a haka suka koma gida ta sauke Safiya ta sake buga motar ta sai gidan Sarki.

Mama na kashingid'e a falonta na ciki taga shigowar ta ta bita da kallo tace, "ya kika yo nan kuma bayan aikin da yake kanki?." Mum tayi dariya ta ware hijjab d'in tana nuna mata tace, "Har na kammala ai, kin sanni indai akace a kan abinda ya shafe kine ba wasa." Mama ta tashi zaune sosai tace, "ban fahimta ba me kike nufi?."
"Har na saka an kawo min hijjabin ta."
"Bana son wasa Sadiya." Mum tayi murmushi tana zama tace, "Wallahi ba wasa nake ba ranki ya dad'e wannan hijjabin tane."

Mama ta kalleta ta kalli Hijjabin tace, "ta yaya har kin samo ko cikakken mintina talatin bamuyi da maganar ba?." Nan Mum ta warware mata komai Mama tayi dariya tace, "Shiyasa a koda yaushe nake sonki Sadiya, basirar ki bata yara bace." Mum tayi murmushi tace, "da zafi zafi ake dukan k'arfe."
"Gaskiya ne. Yanzu za'a kaiwa malam shi kuma ya aiwatar da aiki a kawar da ita har lahira."
"Shikenan magana ta k'are mu huta da tashin hankali" Mum ta fad'a da murmushi Maman ma murmushi take na farin ciki kafin tace, "Wa zan samu ya mik'a masa yanzun nan?."

Mum tace, "meye amfanina ranki ya dad'e? Bara kiga" Ta fad'a tana d'aukar hijjabin ta fita da sauri Mama tayi shewar farin ciki maganin matsalar ta yazo kusa-kusa.



*Hajiya Mama kenan*=?
?
[17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*040.*

? ? ? ? ? Tunda Asad ya fita daga d'akin da take bayan an yanke kiran sa da Mama bata kuma ganin sa ba har akayi sallar i'sha, bayan ta tashi daga bacci wanka ta kuma yi kamar yadda Yaya Ummi take yawan fad'a mata akan yawan yin wanka, sosai taji dad'i zazzab'in jikin ta ya sauka sai ciwon kai kad'an ta kuma shan magani tayi sallah ta zauna a d'akin ta kira y'an gidan su suka gaisa. Bayan ta gama wayar ta gaji da zaman d'akin hakan ya saka ta fito falon ta zauna tana kallon tv.

Remote ta d'auka tana dubawa dan ba sanin kan TV tayi sosai ba duba da bata taso da ita a gidan su ba ta canja ta mayar mbc bollywood suna haska film d'in kalank. Film din ya burge ta ganin na sarauta ne kuma ba'a jima da farawa ba ta fara gani tana fahimtar wasu abubuwan kad'an a ciki. Jingina tayi da kujerar dan gabad'aya bata jin dad'in jikinta sakayau take jin ta kamar an cire wata garkuwar da take tokare ta a jikinta.

? ? ? Film d'in ya d'auki hankalin ta ganin an yiwa yarinyar labarin auren dole an kaita gidan sarauta tana kuka bata so, ji tayi kamar itace jikinta yayi sanyi ta cigaba da kallon film d'in yadda mijin baya nuna mata wata kula sai matar sa hakan ya sake karya mata zuciya amma bata fasa kalla ba ta cigaba da kallon bayan tayi tagumi. Ba zato taji an cire tagumin da tayi ta d'ago ta kalle shi suka had'a ido ta d'auke idon ta ya zauna a gefen ta ba tare da yace komai ba itama haka ta cigaba da kallon.

Shiru ya ratsa tsakanin su babu wanda yace komai kafin ya bud'e abincin da yazo dashi ya tura mata pack d'in shinkafa da kaza da kuma ice cream da burger da roll d'in shawarma, kalla tayi ta d'auke kai tace, "Bana jin yunwa" ta furta tana cigaba da kallon ta ba tare da ta kalle shi ba. Pack d'in shinkafar ya bud'e ya d'auki spoon d'in ciki ya cika shi ya kai bakin ta, kallon sa tayi ya d'aga gira idanun sa a cikin nata sai ta sauke kai k'asa Allah ya sani bata son kallon idanun sa bari ma yanzu da take jin kunyar sa.

? ? ?? "Na k'oshi fa" ta fad'a da shagwab'a idanun ta a k'asa. Bai janye abincin ba ta sake kallon sa taga still ita yake kallo ta sauke k'aramin numfashi ta bud'e baki a hankali ya zuba mata a baki tana taunawa a hankali gabad'aya bata jin d'andano daman kuma ga abincin larabawa babu isashshen maggi a cikin sa. Dak'yar ta had'd'iye ya sake debowa ya sake kai bakin ta ta sake karb'a tana yamutsa fuska kwata-kwata abincin baiyi mata ba.

A karo na uku kafin ya debo tace, "dan Allah ka bari wallahi bana jin dad'in sa baki na babu taste ga kaina ciwo yake" ta fad'a idanun ta na kawo hawaye ta mayar da kanta cinyar ta hawaye na sakko mata. "Ohh Muwaddat! Meye na kukan?" Ya fad'a a sanyaye yana kallonta ta tashi ta goge idanun ta tace, "Ba kaine ba nace na k'oshi kana sake bani, bana jin dad'in bakina" ta fad'a cikin shagwab'a. Ture pack d'in yayi alamun shikenan an bari. D'an shiru yayi kafin yace, "muje kiga Dr" ya fad'a yana niyar tashi tayi saurin rik'e hannun sa ya kalle ta tace, "Basai munje ba."

Da kansa yayi mata alama da meyasa tace, "Bana so ne kawai, kuma naji sauk'i." Komawa yayi ya zauna na wani lokaci kafin ya saka hannun sa ya rik'e kanta yaji ba sosai yake harbawa ba ya dawo da hannun sa wuyan ta yaji babu zazzab'i a jikinta ya kalle ta yace, "What do u want? Fad'a min ko meye I will give it to you." Lumshe ido tayi hak'ik'a in yayi magana kome girman ka da ajin ka sai kaso ya sake maimaitawa sabida yadda maganar take fita daki-daki da wani salo ba hayaniya sai kwantar da hankali da saka nutsuwa a zuciyar mai sauraron ta musamman ita da zuciyar ta take da rauni a kansa, bud'e ido tayi ta saukar k'asa bata ce komai ba itama.

? ? ?? Kallon ta yayi kamar zai kuma magana sai ya fasa sai yaga ta tashi ta shiga d'aki ta d'auko maganin ta ta dawo ta zauna, k'afar ta yake bi da kallo sai yaga kamar tafiyar ta ba daidai take yi ba hakan ya saka shi binta da kallon har ta zauna kana yace, "Are you okay?." Kai ta d'aga alamun eh kafin yace, "but bakya tafiya daidai ko k'afar ki na ciwo?." Sai gaban ta ya fad'i ta bata ce komai ba domin bata san me zata ce masa ba.?
"Answer me." Rauda tasha maganinta bata kalle shi ba sai da ta shanye kamar zatayi kuka tace, "Babu komai."

Yadda ya kafe ta da idanu ko kiftawa bayayi hakan ya bata tabbacin bai yadda ba ta kalle shi sai ta kwab'e fuska tana shirin yin kuka tace, "Babu komai, dan Allah ka bar kallona kunyar ka nake ji wallahi" ta fad'a tana sake mayar da kanta cinyar ta. Sai yayi murmushi amma baiyi magana ba ya k'yale ta kusan mintina biyar yaga ta cigaba da kallon ta amma bata kalle shi ba.

"Kina jin zafin still?."
"Oh my god!" Ta furta a bayyane sai kawai ta fashe da kuka. Hankalin sa ya tashi ya jawota jikin sa gabad'aya ta dawo kan cinyar sa yana so yace wani abun amma kukan da take yi ya hana shi magana. "Please!" Shine abinda ya furta kawai yana shafa bayanta a hankali.
"Ni ka daina min maganar kunya nake ji." Murmushi yayi ya mata kiss a kumatu yace, "is okay, sorry."

Nishad'i yake ji a zuciyar sa in ya ganta a gefen sa sai ya rasa me yake masa dad'i kamar yayi ta kallon ta haka yake ji hakan ya saka shi cigaba da kallon ta kafin yace, "kina son zama y'ar jarida still?." Sai ta d'ago ta kalle shi ganin ba ita yake kallo ba ta wara idanun ta waje kafin tace, "ta ya akayi kasan ina son zama y'ar jarida?." Baice komai bai kuma kalle ta ba sai kallon tv d'in shima da yake yi.

Tace, "Ina da tantama daman ina so na tambaye ka tun ranar nan da naga katin magani na a d'akin ka. Kenan ranar da muka had'u ka d'auka? Kaine ka siya min magani kenan har ka biya bashin maganin da ake bina. Ya akayi kasan Baba yana son keke napep ka siya masa?, yama akayi kasan gidan mu?, meyasa ka b'oye kanka a lokacin?" Bata kallon sa take maganar dan bata so su had'a ido yana jinta amma kuma baiyi alamun da zata gane ma yaji ba balle ta saka ran zai amsa mata.

? ? ? ? Shiru ya sake ratsawa a tsakanin su tana jiran amsa shi kuma bashi da alamar bata amsa sai ya murmusa kad'an har taji sautin murmushin nasa ta kalle shi sai taga ya d'auki waya yana dannawa alamun bazai bata amsa ba kenan. Rauda ta d'auke kai bata ce komai ba amma zuciyar ta cike take da son ya bata amsar tambayar ta hakan ya saka tace, "Ka amsa min please, a lokacin da hakan ta faru mun d'auka Anas ne ya bayar sabida shine kawai yake taimaka mana musamman a........" shiru tayi ta kalle shi taga kuwa kallon nata yake kamar yadda taji a jikinta bayan ya had'e fuskar sa waje d'aya kamar ba shine yake murmushi ba.

? ? ? ? "Don't call his name again please" ya fad'a yana kallon ta. Kai ta sunkuyar tana mamakin yadda yake nuna yana kishin ta amma a bayyane ya kasa nuna mata soyayyar da take so, dan ita Allah ya sani macece da take so a nuna ana sonta a kula da ita kamar kwai. Shiru tayi bata kuma magana ba amma taci alwashin sai ya bata amsar tambayar ta ko yaushe ne.
"I'm sorry" ta furta a tak'aice tana cigaba da kallon ta.


Wayar sa tayi k'ara ya kalla yaga sunan Aliyu ya sauke numfashi a bayyane yace, "Aliyu!." Har ta katse bai d'auka ba aka kuma kira sai ya saka a speaker ya d'auka daga can b'angaren yace, "Hii Asad baka nema na ko?." Asad ya sauke numfashi yace, "how was your day?."
"I'm fine, ina missing d'inka ne shiyasa na kira ka."
Asad yayi murmushi yace, "thanks you." Aliyu yayi y'ar dariya yace, "kar ka damu. A gaida Madam" yana fad'a ya yanke wayar shima ya ajjiye tasa.

Ta kalle shi taga ba ita yake kallo ba amma sai taji yace, "What up?." Kai ta sunkuyar ya juyo yayi y'ar dariya amma baice komai ba.
"Maganar ku ma tana iri d'aya da Aliyu, ta yaya ake gane ku?" Ta furta ba tare da ta kalle shi ba. Ya shafa fuskar sa ya lura akwai ta da magana a haka ma wai bata da lafiya ya cize baki kamar bazai magana ba.

Kallon ta yayi suka had'a ido sai ya mik'a mata hannu ta saka nata a ciki ya dawo da ita jikin sa gabad'aya ya hade hancin su waje d'aya yana goga nasa a akan nata idanun sa a buWe ita kuma nata a kulle. Wuyanta ya yiwa kiss sannan yace, "Akwai different between Aliyu and i." Har lokacin hancin sa yana kan nata bai d'ago ba a haka yake magana khamshin vanilla flavor d'in da yasha na ice cream yana dukan hancin ta.

Fuskar ta ya rik'e yace, "open your eyes please." Kai ta girgiza tace, "I can't." Murmushi ya sake yi baice komai ba ya kwantar da ita a k'irjin sa ya mayar da hannun sa ya kulle ya lumshe idanun sa. Bugun zuciyar sa take ji a k'irjin ta ta saka hannu ta dafe saitin zuciyar sa taji muryar sa yace, "sabida ke take beating very fast." Ya d'ago ya kalle ta suka had'a ido ya wara ido yace, "ana ahibbaki."

Tasan me kalmar take nufi da hausa ta sake mayar da kanta k'irjin sa tana ji kamar ita kad'ai ce mace a duniya. Kusan mintina goma suna haka har bacci yana neman d'aukar ta jinta a jikin sa taji ya d'ago ta ya zare agogon hannun sa ya nuna mata wani bak'in zane kamar ciwo ya zagaye tsintsiyar hannun sa yace, "wannan shine banbanci na da Aliyu, duk lokackn kika ga wannan it's me not Aliyu ko Mama bata san dashi a hannuna ba because...." Sai kuma ya dafe kansa tace, "Sorry."

Shiru yayi na wasu sacanni kafin yace, "Because ban jima sosai da samun shi ba, ciwo ne na same shi a madina shine banbancin kawai." Kallon hannun nasa take sai zanen ya masa kyau a hannu kamar irin mutum ya karce d'in nan wajan ya warke tace, "But voice d'inka dashi yana da banbanci wani lokacin." Ya girgiza kai ya sake mayar da ita jikin sa yace, "In yaso zai magana kamar ni ko Mama bazata gane ba." Rauda tace, "Ikon Allah! Ban tab'a ganin masu kama da juna kamar ku ba." Ya sauke numfashi kusan mintina biyu kafin taji yace, "Even me." Daga nan bai sake magana ba tana jikin sa kuma bai sake ta.

*After two days.*
*Nigeria.*

Rana d'aya aka tashi da rashin lafiyar Mai martaba sarki hankalin iyalan sa ya tashi domin lokaci d'aya jikin sa ya birkice yayi tsanani sosai. Kasancewar litinin ce ranar zaman fada ce da safe ko wanne mai rawani ya bayyana a fada an cika mak'il ana jiran isowar sa.
Ba jimawa ya bayyana Hydar yana rik'e da hannun sa suna takawa a hankali, take kowa ya mik'e tsaye masu kirari suna fad'in, "Barka da fitowa Dawisu sarkin ado, barka da fitowa dubu jiran mutum d'aya, barka da zuwa fari mai farar aniya. Allah ya watsa mak'iyan ka, Allah ya k'aro lafiya ya sake ninko ta fiye da wacce muke rik'a. Kauce ga inuwar alkhairi nan ya tawo manya da yara na gudu don shigar ta, kai kad'ai ne wallahi, wallahi kai kad'ai muka sani bayan kai babu wani. Wane mutum balle aljan? Aljan da kasa in kazo waje kaucewa sabida magana ake ta saurata da mulki da kuma k'asaita!" Da k'arfin gaske yake fad'a ko tsayawa baya yi har aka kare mai martaba ya zauna Hydar ya koma gefen sa ya zauna a kan carpet.

Kusan mintina biyar aka d'auka kafin liman ya bud'e taro da Addu'a mai margaba kawai ake jira yayi magana ya kalle su d'aya bayan d'aya yace, "Alhamdulillah, yau shekarar mu talatin har da wani abun akan karaga, muna yiwa Allah godiya da ya nuna mana wannan rana."
"Allah ya k'ara lafiya, yasa a gama da duniya lafiya. Ya jikan mai babban d'aki ya raya mana zuri'a!" Aka sake fad'a mai martaba ya amsa da amin kafin ya d'ora da fad'in,

"Shekaru sun ja k'arfi ya k'are ga ciwo da muke fama dashi, bamu san gobe ba amma Allah zai iya yin ikon sa a koda yaushe. Kamar yadda na ambata a kwanakin baya zan bayar da karaga mulki ga Asad a lokacin kuma duk kun bada goyan bayan hakan, ina fatan har yanzu kuna kan ra'ayi irin nawa?."

Kallon kallo aka shiga yi idanun waziri sukayo waje ya share gumin da ya fara tsatstsafo masa kowa ya d'aga kai alamun suna nan kan matsayin su mai martaba yace, "To ma sha Allah. Duba da shawara da mukayi da makusanta da kuma yanayin ciwon bana so a bar talawa cikin rashin shugaba mai lafiya dan haka, A yau litinin zan mik'a kujera ga Asad duk da baya nan zan bada rok'on kwarya ga kawun sa da ya dawo a mik'a masa abin sa koda bana raye." Jin an ambaci kawun sa Waziri ya fara washe baki jikin sa ya fara tsuma yace, "Allah ya k'ara maka lafiya duk abinda kace namu shine mubi."

Mai martaba ya d'aga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login