Showing 72001 words to 75000 words out of 216282 words

Chapter 25 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

Eman ta kalle su tace, "yace dare yana yi kuzo in an je can ayi hotunan."

Jidda ta tako ta bud'e gaban motar ta shiga k'awayenta suka gyara maza zaman mayafin nata suka kalle shi suka ce, "Ango harda sha mana khamshi? Duk da yadda bikin naku yazo without mun shirya komai muka zo akayi abu kamar an jima ana shiri amma shine baza ka fito ba?." Kallon ta yayi kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa yayi murmushi kawai da ya tafi da hankalin su dukkan su.

Kulle k'ofar sukayi ko wacce ta shiga tata motar ya fara juya motar ya fita suka biyo bayan sa. Kallon sa Jidda take yi kawai cikin zallar mamakin ta yadda akayi ya amince har ya fitar da ita kunya haka amma ta kasa magana sai murmushi da take yi cikin farin ciki.? Shi kuma gabad'aya khamshin turaren ta ya addabe shi nema yake ya dagwagwala masa lissafi hakan ya saka baya kallon ta driving kawai yake hankali kwance.

? ?? Kallon sa ta?kuma yi sanye yake da shadda fara sai maiko take tana d'aukar ido hular kansa brown kalar aikin jiki yayi kyau sosai ba kad'an ba kamar ka sace shi ka gudu.? Juyowa yayi suka had'a ido ya d'aga mata gira d'aya ya kyalkyale da dariya kana yace, "Amaryar Prince Asad ko nace his princess, kinyi kyau fa sosai ba kad'an ba but turaren ki yayi yawa" ya fad'a yana cigaba da tuk'in sa.

Ras ras rasss gaban Jidda ya fad'i yadda yayi maganar ya tabbatar mata da Aliyu ne ba Asad ba ta dafe k'irji tana binsa da kallon mamaki tace, "Aliyu!." Ya kalle ta yace, "Yeah Jidda."
"Daman kaine ba Asad ba?."
"Yeah nine, kema kin san ko za'a sake haifo ki ne Asad bazai zo ba dalilin da ya saka Mama tace kiyi hak'uri kenan."

Kai ta dafe fuskar ta ta canja gabad'aya ta kalle shi tace, "kai kuma shine ya turo ka kenan ko kai ka turo kanka?." Ya d'aure fuska kamar ba shi ba shine ya gama dariya ba yace, "ni na turo kaina dan na taimake ki, kamar ki ace anyi bikin ki dinner babu ango akwai disgracing da yawa a cikin lamarin, time d'in da kuke waya da Mama naji komai na kuma yi niyar taimaka miki but in bakya so zan k'yale ki ne."

Jidda ta sauke numfashi tace, "Na gode ka taimake ni amma yau sak ka koma min Asad har acting din rashin maganar sa kayi." Yayi murmushi yace, "Ina sane nayi hakan." Hannun ta ya rik'e yana murzawa kafin ya kai hannun sa bakin ta yayi mata kiss a hannun ta k'wace tace, "nifa matar k'anin kace ka dinga controlling kanka mana." Murmushi yayi mata kawai ya cigaba da tafiya har suka zo inda suke so.

A nan aka fito ya fito shima suka tsaya shida Jidda ana hotuna kamar daman hoton akazo yi, sai daga baya aka shiga wajan taro da ya cika da k'awaye da yayyen k'awaye Mum harda Suhaima tunda taga shigowar su tasan ba Asad bane sai dai Aliyu dan yanayin rawar kan kawai ya nuna mata hakan dan tasan ko za'a yi ruwa da kankara Asad bazai zo ba. Sun ci sun sha sun kuma sha rawa abinsu anyi hotuna kamar babu gobe kafin kace kwabo hotuna sun zaga duniya.

Sha biyu na dare suka tashi kowa ya koma gida Jidda taji dad'in bikin domin kuwa kaf k'awayen ta tasan babu wanda ya d'auko kyau da kud'i da mulkin Asad sai ita kawai, sunga Aliyu sun rikice gabad'ayan ina ga sun ga babbar giwar Asad? Duk da kamar d'aya ce amma akwai banbancin class.

Facebook, whatsapp, Instagram, Twitter da sauran su kafin kace kwabo hotunan sun yad'u kana bud'e wayar ka ka shiga da abinda zaka fara karo kenan hotunann Aliyu da Jidda a jikin ko wanne an saka prince Asad and his princess Jidda. Mum ma kafin su dawo a nan taga hoton tun da ta gani itama tasan sai dai aikin Aliyu bana Asad ba ranta ya b'aci matuk'a jira take Jiddan ta dawo tayi mata fad'a.
Lokacin da suka dawo kamar jiya kwaliyya aka goge ana cire kaya ita dasu Eman da sauran cousins d'insu da suka tawo tare Mum ta shigo d'akin ta kira Jiddan ta fita.

A d'aki Jiddan ta same ta tana fad'in, "Mum na gaji bacci zanyi fa." Mum tace, "ashe bki da hankali ban sani ba Jidda?." Da mamaki tace, "me nayi Mum?."
"Baki san ma me kika yi ba kenan ko? Dan baki da hankali an fad'a miki halin Asad akan kishi amma kika gayyato Aliyu yaje ya tsaya a gefen ki kamar shi zaki aura ko? Kalli wannan hoton har hannun ki ya rik'e, meyasa bakya gudun matsala ne kewai?, kin san da yadda auren nan zai yu kuwa?."

Jidda ta turo baki gaba tace, "Nifa Mum bani na gayyace shi ba shine yazo da kansa kuma da farko na d'auka Asad ne sai daga baya na gane shine, kuma Mum banda ku ai babu wanda yasan ba Asad bane ba." Mum ta sake fusata tace, "Amma nida ke na fad'a miki Asad bazai je ba, mahaifiyar sa ta fad'a miki bazai je ba meyasa zaki tunanin shine yazo? Ke yanzu in yaga wannan hotunan yace ya fasa auren naki Aliyu zaki aura ko wa?."

? ? ?? "Mum meya kawo maganar fasa aure? Kin san dai bazai yi magana ba dan nayi hoto da Aliyu tunda Yayan sane jinin su d'aya."
"Dan jinin su d'aya sai kije ki aikata wannan haukan? Me ya shiga kanki ne?." Shiru tayi tare da turo baki Mum taja tsaki tace, "in zaki nutsu ki nutsu gobe zaki zama matar aure kuma matar sarki kuma dole ki shiga hankalin ki in ba haka ba wallahi zaki sha wahalar da bakiyi tunani ba. Matar sarki da nutsuwa aka Santa da aji da nuna mulki na irin ki ba" tana fad'a mata haka ta barta wajan itama ta koma d'aki dan ita bata ga laifin data aikata ba.

*&&&*

? ? ? ? ?? "Bana so yau ya kwana a raye duk yadda za'ayi a tabbatar anyi Asad ya bar duniya, bana so ya wayi garin gobe da rai da lafiya a tabbatar an kashe Asad, kada Asad ya rayu rayuwar sa barazana ce ga tawa rayuwar, a tabbatar an kashe shi har lahira!."

Cak Asad ya tsaya daga wucewar da zaiyi ya dawo da baya kasancewar dare yayi sosai yake jin me ake cewa yana kallon inda yake jiyo maganar duk da dare ne akwai haske sosai a wajan amma baya ganin wanda yake a tsaye a wajan. Motsi yaji a bayan sa ya waiga yaga mage ce ta gifta ya dawo da hankalin sa inda yake jin maganar amma babu kowa.

Bin wajan yayi har indai ya hango inuwar mutum a wajan amma bai ga kowa a wajan ba, k'irjin sa bugawa yake yi bai san dalili ba yaji tsoro ya dabaibaye masa zuciyar sa k'in k'aunar mulkin na sake shiga jikin sa ya juyo jikin sa a sanyaye ya nufi b'angaren Mama zuciyar sa cike da saqe-saqe yana sake tuno muryar yana so ya tabbatar da muryar wanda yaji yana maganar.

? ? ? ?? Duk da bashi da walwala da kuzari zuciyar sa cike take da tsoro da fargabar abinda zai faru komai cikin takun isa da nuna tsantsar jinin sarauta na yawo a jikin sa yake takawa ya shiga apartment d'in mahaifiyar sa ya wuce falon farko ya shiga na biyu ya same ta zaune tana kallon wayar ta tana murmushi jin sallamar sa ya saka ta amsa ta d'ago ta kalle shi tace, "Asad zo kaga wani abu." Ba musu ya zauna a k'asa kusa da ita ta mik'a masa wayar ta tace, "Kalli kaga." Karb'ar wayar yayi ya kalli screen d'in ya kalle ta ya sake kallo alamun shi bai fahimta ba tace, "Jidda ce fa matar ka ta gobe ita da Aliyu amma kowa d'auka yake kaine, nasan baza kaje ba shiyasa ma ban sanar da kai ba gaahi Aliyu ya fitar da ita kunya."

Jin an kirata da matar sa ta gobe ya saka shi yake kallon hoton baice komai ba ya mik'awa Mama wayar ta karb'a tace, "Jidda tana da kyau sosai? shiyasa na zab'e ta matsayin matar ka." Nan ma bai tanka ba amma a zuciyar sa cewa yake, _kyau fuska kawai kika gani babu kyawun hali. Kuma baki nuna b'acin ranki akan abinda Aliyu yayi ba sai ma murnar hakan kikayi, ta ko wanne b'angare bata dace dani ba._ Kallon sa tayi tace, "Ya shirye-shiryen goben? Bak'i sun iso daga Kano a naka b'angaren fa?." Numfashi ya sauke kana yace, "Banyi inviting kowa ba Mama tunda kinyi gayyaar ki nima tawa ce."

Murmushi tayi tace, "Haka ne, Allah ya nuna mana goben da rai da lafiya." Ya amsa da amin kafin ta kuma cewa, "Akwai maganin da aka kawo maka daga Kano na ajjiye maka a d'aki ka tabbatar kasha maganin tsari ne da Abie yake bamu kafin ya bar duniya. Kasan yau akwai wanda suke fatan kar ka kai gobe nima kuma na shirya musu, kasha maganin akwai coal da kasko kayi turare akwai na wanka duka kayi amfani dasu kafin ka kwanta." Kai ya d'aga kana yace, "in sha Allah." Tayi shiru shima yayi shiru yana jiran ta bashi umarnin tafiya dan dare yayi sosai? ita kuma bata ce komai ba sai danna wayar ta da take yi.

? ? Agogo ta kalla kana tace, "kaje ka kwanta dare yayi sosai kana da hidima gobe." Kamar jira yake yace, "A tashi lafiya" ya fad'a yana mik'ewa ya wuce hanyar sabon d'akin da ta bashi yana tunanin sabuwar rayuwar zai fara gobe mai cike da sark'akiya da tarin qalubale da kuma wad'anda suke k'okarin ganin bayan sa.

*&&&*

? ? ? ?? A daren ranar Rauda gabad'aya bata jin dad'in jikinta tun safe haka ta wuni duk da yayyen ta sun zo ana ta hira amma bata sake ba haka har dare yayi ta k'ule a d'aki tana aikin tunanin da ya cushe mata zuciyar ta. Numfashi ta sauke ta d'auki wayar ta ta shiga contacts din wayar tata tana duba numbers d'in wayar gabad'aya basu fi goma ba daga ta y'an gidan su sai Khalifa da matar sa sai kuma number Asad da yayi mata saving da Husband.

Numfashi take saukewa tana kallon number kafin ta danna ta goge ta gabad'aya daga wayar tare da goge hawayen idanun ta. Datar wayar ta kunna wacce tunda ya bata wayar akwai ta akai har lokacin bata san kuma taya zata duba ba balle tasan yaushe zata k'are ko zata expire, Whatsapp ta shiga kasancewar dare yayi babu jama'a online ta fita ta shiga Instagram tana scrolling.

Gabanta yayi mugun fad'uwa karo da tayi da hoton Jidda da Aliyu a caption an rubuta prince Asad and his Princess, zaune ta tashi tana kallo tana zooming ganin da gaske shi d'in ne ta cigaba da kallon hotunan a nan ta tabbatar biki ake yi gashi yana ta walwala kamar bashi ba. K'irjin tayi yana zafi kamar ana soya mata zuciyar ta tayi saurin kife wayar tana zare idanu jikinta yana rawa ta sake fashewa da marayan kuka mai tsuma zuciya da gangar jikinta.

_Kukan me kike Rauda? Kukan dan ya sake ki ya auri daidai shi kome? Kishin sa kike?._ Da sauri take goge idanun ta amma hawayen sunk'i tsayawa ga k'irjinta da yake mugun zafi maimakon hawayen ya tsaya sai kwanciya da tayi ta kuma fashewa da sabon kuka ta kasa tsayar dashi ta dinga kuka mai tsuma zuciya ita kad'ai a kwance a kan gado tana birgima.

Sai da tayi mai isar ta ta dinga sauke numfashi kafin dabara tazo ranta ta tashi ta shiga band'aki tayi alwala ta dawo ta tayar da sallah ko dan taji dad'in zuciyar ta. Ta jima tana sallah a kan sallayar bacci ya kwashe ta ba tare da tasan lokacin ba.

? ? Haka ta tashi washe gari bata da wata walwala lokacin da ta farka duka yaran sun tafi makaranta tayi wanka ta saka riga mara nauyi ta fito falon nan ta tarar da Umma a zaune a akan carpet tana cin d'an wake. K'arasawa tayi ta zauna kusa da Umman tace, "Ina kwana Umma." Da kallo Umma ta bita ta tsayar da cin d'an waken tace, "lafiya lau, lafiya naga fuskar ki haka kamar wacce ta kwana tana kuka?." Ajiyar zuciya tayi tace, "na jima banyi baccin bane ba shiyasa."
"Meya hana ki baccin?" Ta fad'a tana kallon ta.

"Haka kawai na kasa baccin." Umma tace, "Zaki ci d'an waken ne ko shayi zaki sha?. Tashi nayi da sha'awar cin sa shiyasa nayi in zaki ci akwai ragowa." Rauda tace, "Bana jin yunwa ma Umma sai anjima." Umma ta bita da kallo kafin ta fuskance ta tace, "Rauda akwai abinda kike b'oyewa a zuciyar ki tun dawowar ki, fad'a min me kike b'oyewa har yake saka ki damuwa haka?." Gaban Rauda yayi mugun fad'uwa tsoro ya bayyana a akan fuskar ta ta daure ta cize tace, "Babu komai fa Umma."

Umma tayi murmushi tace, "Labarin zuciya a tambayi fuska Rauda, yadda kika rud'e tsoro ya bayyana a tare dake hakan ya tabbatar min akwai wani abun a k'asa. Meya faru a can Egypt d'in? Meyasa har yanzu Asad baizo ba kuma bai yi miki waya ba? Na lura damuwar da kike ciki ta tattara ta dalilin sa ko wani abun da ya shafe shi." Hawaye suka fara sakko mata tayi saurin gogewa amma ina Umma ta gani kafin ta goge tace, "Babu komai Umma."

Jikin Umma yayi sanyi sosai tace, "K'arya kike Rauda akwai wallahi kawai baza ki fad'a min ba gashi nan kina kuka. Kodai wani abun yayi miki kafin ki dawo?."? Rauda zatayi magana Baba ya shigo ya k'araso ya zauna Rauda ta goge idanun ta tace, "Baba ina kwana." Baba da murmushi yace, "Lafiya lau Raudan Baba, lafiya naga fuskar ki haka?." Rauda tace, "ciwon kaine yake damuna Baba."
"Ki sha magani gajiya ce bata gama sakin ki ba."
"Toh Baba zan sha."
"Asad d'in shiru na d'auka jiya zai shigo amma ban ganshi ba, ya kamata ace yazo ai an gaisa kuma munji maganar tarewar ki kunyi waya?."

Girgiza kai tayi alamun a'a sai kuma ta d'aga kai alamun eh Baba yace, "to meya ce miki?." Rauda tace, "Akwai abubuwan da suka tsayar dashi amma zaizo kayi hak'uri." Baba yace, "Ai shikenan sai yazo, in na kira shi bana samun sa a waya yanzu; ni da in mukayi magana hankalina yafi kwanciya." Shiru tayi bata amsa ba Baba ya tashi ya fita kafin Umma tayi magana Rauda ta mik'e da sauri ta shiga d'aki.

Da kallo Umma ta bita gabanta yana fad'uwa fargabar abinda ya faru wanda bata sani ba ya dabaibaye mata zuciya domin kuwa ta tabbatar akwai abinda ya faru b'oye musu take yi amma akwai abinda ya faru, to meye shi?. Babu mai bawa Umma amsa ta sauke numfashi ta cigaba da cin dan waken ta.

*&&&*

? ? ? ?? K'arfe d'aya da arba'in na ranar aka d'aura auren Jidda da Asad, d'aurin auren da ya tara manyan mutane sarakuna da y'ay'an su da jikokin su. Duk wani mai ji da kud'i da mulki yazo d'aurin auren domin kowa yasan mahaifin Asad haka mahaifin amaryar shima ba k'aramin mutum bane ba, bayan a gama aka fara watsewa kamar yadda aka tsara na jiki suka fara wucewa gidan gwamnati inda a nan ne Asad zai karb'o sarautar sa.

Gabad'aya bashi da walwala balle kwanciyar hankali fuskar nan tasa kadaran kadahan baza ka fassara yanayin sa kai tsaye ba a haka aka je dubban jama'a da kowa na garin da wajan garin duniya ta shaida Asad matsayin sabon sarki Katagum. Masu hotuna da y'an jarida nan da nan aka fara yad'awa cikin lokaci kad'an magana ta fita daga Katagum ta zaga ko wanne sashi na duniya domin ko wacce gidan jarida sun saka haka gidan radio da masu d'aukar hoto.

? ? ? Tunda aka tabbatar dashi matsayin sarki yaji kamar an d'ora masa wani abu a kansa mai nauyin gaske ga rawanin da yake kansa an canja masa ado zuwa na sarakai gabad'aya ya sake girma da kwarjini a cikin su ya sake yin kyau k'uruciyar sa ta b'uya mayyanta ta bayyana a a kan fuskar sa. Kid'a ake ana busa ana tambari aka nemi Asad yayi jawabi dogarai suka tawo a guje aka kare shi da zai mik'e ya tashi tsaye yana takawa a hankali da sandar girma a hannun sa ya k'arasa inda aka tanadar ya tsaya yayi shiru bai ce komai ba.

Harrrrr yake ganin mutanen duk da ya saba tsayawa gaban jama'a yayi magana amma ba kamar wannan da yake da wannan matsayin ba, ya lumshe idanun sa ya bud'e yayi gyaran murya a hankali kana yace, "A'uzubillahi minal shaidanir rajim bismillahir rahmanir Rahim. Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah ala kulli halin." Yayi shiru na wasu sacanni baka jin komai sai zallar kirarin da ake masa a wajan nan take yaji sabuwar izza na sake ratsa jijiyoyin jikin sa da gangar jikin sa, izzar da take banbance tsakanin d'an sarki da sarki ita yaji tana bin ko wanne b'angare na jikin sa ganin dukka mutanen da suke wajan a k'asan sa yake in aka cire gwamna.

"Mai girma gwamnan bauchi, kwamishinoni, sanatoci, da dukkan wanda suka samu damar zuwan wajan nan ina yiwa kowa barka da wannan lokaci, ina matuk'ar godiya da wannan damar dana samu aka zab"e ni a cikin dubban mutane aka d'ora min nauyin mutanen da suke cikin garin Katagum."

Ya sake yin shiru yana sauke numfashi tare da lumshe idanun sa yace, "In sha Allah a mulkin da zamu gabatar ko wanne mutum da yake zaune a cikin garin nan zaiyi alfahari da kasancewar sa a garin bazai yi dana sani ba, zai kuma yi farin ciki da zama a k'arkashin inuwar wannan mulkin." Dak'yar yake fizgo maganar ya sake yin shiru na wani lokaci kafin yace,

? ? ? ? "In sha Allah zamuyi iya bakin k'okarin mu wajan ganin bamu cutar da kowa ba ba kuma mu saka kowa zubar da hawaye ba, zamu tafiyar da mulki fiye da wanda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login