Showing 12001 words to 15000 words out of 216282 words

Chapter 5 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

san komai na kuma shirya komai Deaf. A karo na babu adadi bazan bari ka rasa abinda kake so ba musamman wannan da ta kasance abokiyar rayuwar ka."
Ya sauke numfashi yace, "But ita bata sona."
"Mahaifin ta da kansa yace ta amince kaga kenan tana sonka."
"Bana tunanin da gaske ne."
"Mahaifin ta ai bazai mata k'arya ba, ka ajjiye abinda kake jin tsoro babu abinda zai faru sai alkhairi."

Ya sauke numfashi ya kulle idanun sa kana ya bud'e yace, "Rayuwar ta tana cikin hatsari a lamarin auren nan, u forgot abinda ya faru right?."
"Ban manta ba Asad amma a wannan karon babu abinda zai faru, lokaci kad'an ma da zaku wuce Cairo Mama bata san anyi ba." Kai yake girgizawa cikin sanyin jiki alamun bazai iya aikata hakan babu sanin Maman sa ba, nan take yaji auren ya sake fita a ransa komai baya yi masa dad'i dan sai Mama nasan abu shima yake ji yana so.

"Kar ka damu dan Mama bata sani bafa tunda Abba ya sani kuma shine ya yanke hukunci ai komai ya k'are." Asad ya sauke numfashi ya d'aga kai sama kamar mai son gano wani abun a saman.

Hydar ya kalle shi yace, "Ka kira ta for the first tym as your lovely wife." Kai ya sake girgizawa alamun a'a Hydar yayi murmushi kawai ya daki kafad'ar sa yace, "kurma nawa, ina ji da kai sosai, zan iya yin komai dan samuwar farin cikin ka, zan iya barin komai da farin cikin ka" yana fad'ar hakan ya tashi ya bashi waje yana dariya zuciyar sa fess karon farko Asad ya mallaki abinda yake so ba tare da takurar Mama ba.

Bayan kwana biyu.

Ranar da akayi addu'ar ukun mai martaba sarkin Kano su Asad suka d'auki hanyar Bauchi suka bar Mama ita kad'ai a gida sai anyi addu'ar bakwai zata dawo ita,? bata san me ya faru ba har lokacin tana cikin alhinin rashin mahaifinta ba ta kan komai take bi hakan ya saka bata cika d'aukar waya bama balle a samu wanda zai sanar da ita bak'in labari a wajan ta.

Bayan sun huta da daddare Asad na zaune a d'akin sa yanaa karatu Hydar ya kira shi a waya, bai d'auka ba sai da ya kira sau uku sannan ya d'auka baiyi magana ba ya kashe ya fito zuwa falo.? A tsaye ya tarar da Hydar d'in ya kalle shi alamun lafiya yake neman sa?.

Hydar yace, "Takawa ya bada umarnin kaje gidan su matar ka yanzun nan shiyasa na sanar da kai" yana fad'ar hakan ya wuce ya barshi tsaye yana tunanin abinda ya kamata yayi. Yasan shirin Hydar ne sarai amma tunda ya ambaci mahaifin sa dole yaje babu yadda zaiyi.
Shi bawai baya sonta bane yana sonta har lokacin kawai wasu abubuwa ne suke caja masa kai har yaji komai y???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ana fice masa a rai shiyasa baya wani zumud'in hakan kwata-kwata. D'akin sa ya koma ya d'auki makullin mota a kan madubin d'akin har ya gota sa ya dawo yana kallon kansa a madubin, kayan jikin sa yake kalla riga da wando ne dogaye marasa nauyi a jikin sa sai yaji a zuciyar sa bai kamata yaje da kayan jikin sa ba.

Ajjiye key d'in yayi ya shiga band'aki ba jimawa ya fito ya shirya cikin yadi fari mara nauyi mai shara-shara ya saka hula bak'a kalar aikin jikin yadin ya fashe jikin sa da turare masu sanyi ya tsaya yana kallon kansa a madubin bayan ya gama shiryawa.

Shi kansa yasan yayi kyau sosai ya murmusa sai kuma ya cize baki ya d'auki key d'in motar ya fita a sanyaye. Da Aliyu suka had'u a falon har ya gifta Aliyu sai kuma ya dawo da baya ganin irin kallon da Aliyun yake masa ya wara idanun alamun kallon na meye?.? Aliyu yayi dariyar shak'iyanci ya cize bakin sa kamar yadda Asad d'in yake yi yace, "na tsaya ina kallon angon talakan yarinya, wow u look very beautiful deaf" ya fad'a yana tasowa yazo kusa dashi yana kallon sa.

Asad baice komai ba ya fita shi kuma yayi dariya yana cize baki cike da mugunta sai da ya tabbatar Asad ya hau mota ya fita sannan ya shiga d'akin Asad d'in da yake a bud'e.

K'arewa d'akin kallo yake yana girgiza kansa ganin sa tsaf dashi khamshin turaren Asad d'in ya cika d'akin wanda indai kasan Asad ka sanshi da wannan turare, a jikin bango ya jingina yana bin d'akin da kallo kamar me neman wani abun kafin ya girgiza kansa ya fita.

Asad kuwa a sanyaye yake driving d'in motar gabad'aya jikin sa ya saki kansa take ji yana rasa masa sosai ga tunanin ta yadda zai tunkari gidan su Rauda as sirikin gidan duk sai yaji wani iri a jikin sa wallahi, Dak'yar ya iya kawo kansa k'ofar gidan ya faka motar yana kallon gidan amma ya rasa abinda zaiyi shiyasa ya zauna a motar kawai yana kallon gidan.

Kamar wasa ya ganta tana nufar gidan ita da wani saurayi suna ta murmushi ita dashi har tayi tuntub'e zata fad'i yayi saurin rik'o ta ya gyara mata zaman sandinan nata suka cigaba da takawa har suka shiga cikin gidan da alama wani nata ne ta san shi sosai.

Wani irin zafi Asad yaji yana taso masa daga zuciyar sa yana mamaye dukkan jikin sa har cikin idanun sa, cize bakin sa yake yana bin su da kallo har suka shiga gidan ya runtse ido ya kai hannun sa ya rik'e wuyan sa da duka hannayen sa biyun nan take yaji har fatar wuyan tayi zafi sabida zafin zuciyar sa har ya huda ya fito ya mamaye fatar sa. Ya sani yana da kishi Allah ya yishi cikin maza masu zafin kishi ko kad'an baya so yaga an rabi abinda yake so koda kuwa takalmi ne balle kuma matar sa.

Idanun sa har sun fara canja launi daga fari zuwa ja ciwon kansa ya k'aru fiye da wanda yazo dashi dana sanin zuwa wajan ya mamaye masa zuciyar sa da ruhin sa ji yake ina ma baizo ba da baiga abinda zai d'aga masa hankali haka ba. Knocking d'in glass d'in ake yi amma bai iya kalla ba sai akayi kusan sacan ashirin sannan ya kalli gefen tagar ganin mahaifin ta ya saka shi daurewa ya bud'e motar ya fito waje.

Baba ganin sa sai ya washe bakin sa yana jin farin ciki a zuciyar sa ganin kamar Asad ya kasance siriki a wajan sa me zaiyi in ba farin ciki ba?. Kafin Asad ya gaishe shi Baba ya riga shi furta, "Barka da Dare Asad." Sai Asad yaji wani iri ya dawo da nutsuwar sa jikin sa ya duk'a ya gaishe shi ya amsa baki a wangale kana yace, "ya karin hak'uri kuma?." Asad ya amsa da fad'in, "Alhamdulillah."
"Allah ya jikan sa ya gafarta masa ya duba abinda ya bari."
"Amin" Asad ya amsa a tak'aice domin baya jin dad'in yanayin sa gabad'aya.

Baba yace, "ka k'araso ciki mana Asad kamar wani bak'o ka tsaya a waje." Babu yadda ya iya dole yabi bayan sa zuwa ciki , a k'aramin falon dake wajen cikin gidan ya zauna yana kallon sa yace, "Bara na turo maka ita ku gaisa" Baba ya fad'a da nishad'i yana kallon sa. Murmushi yayi kawai baice komai ba Baba ya fita shi kuma ya d'auko waya yana dannawa ko zai rage masa abinda yake ji a zuciyar sa.

Ba jimawa yaji motsi tare da sallama a sanyaye ya d'ago ya kalle ta ya amsa shima a sanyaye, fuskar ta a tamke take babu alamun walwala ta k'araso ta zauna ta d'ago ido ta kalle shi tace, "Barka da dare." Bai iya amsawa ba sai zuba mata ido kawai da yayi yana k'arewa fuskar ta kallo ganin yadda fuskar tata tayi fresh duk da batayi kwalliya ba ko kad'an amma fuskar ta tayi kyau sosai bai sani ba ko shi kad'ai yaga hakan.

? Jin shiru bai amsa ba ta d'ago ta kalle shi suka had'a ido sai ya d'age gira guda d'aya ya basar kamar ba kallon ta yake ba muryar sa a ciki yace, "Ya jiki?." Rauda ta tab'e baki tace, "Alhamdulillah, ya hak'uri."
"Alhamdulillah" ya furta daga nan yayi shiru itama tayi shiru.

Shiru k'aramin falon yayi babu wanda ya kuma magana a cikin su kusan mintina uku suna a haka kafin yace, "waye shi?." A sama taji maganar ta d'ago da mamaki tana kallon sa kafin tace, "Wa kenan?." Bai bata amsa ba sai ido da ya zuba mata tayi saurin d'auke nata idanun ta kalli gefe amma batayi magana ba.
"You're my wife ya kamata ki sam da wannan, I can't tolerate any kind of relationship tsakanin ke da wani" ya furta a sanyaye duk da maganar a kausashe take zuwa kuma a ciki alamun ba son maganar yake yi ba.

Rauda da take jin sa ta kalle shi jfin kallon kama raina min hankali d'in nan tace, "ikon Allah, wai kana so kace kishi kake?, daman ana kishi without soyayya ne?" Ta fad'a cikin rainin hankali tana kallon sa. D'ago idon da yayi suka had'a ido sai ta sauke nata k'asa sai ya samu kansa da yin murmushi baice komai ba ya mik'e ya wuce ta kana yace, "Good night" abinda ya furta kenan ya fita ya barta zaune a wajan kamar wacce aka dasa a wajan.

Idanun Rauda suka ciko da kwalla a bayyane ta furta, "Rainin hankali, Baba ga abinda ka jawo min nan na fara gani tun yanzu" Kafin ta mik'e hawayen ya zubo daga idanun ta tana k'okarin takawa da abinda yake taimaka mata take tafiya k'afar sandar ta zame zata fad'i ba tare da zaton ta ba taji an rik'ota ta fad'a jikin abu mai laushi da khamshi mai d'aukar hankali, sai da ta sauke numfashi sabida dad'in khamshin da taji kafin ta kalli abinda ya tare ta d'in ta ganshi tsaye yana rik'e da ita kamar bashi ba.

Hawayen idanun ta yake kalla da mamakin abinda ya sakata kuka daga fitar sa haka yana so ya tambaya amma baya tunanin zai iya yin hakan sai ya cika ta ya kalle ta yace, "Be careful" yana fad'a ya k'arasa inda ya zauna ya d'auki key d'in motar sa ya fita daga falon bai kuma kallon ta ba. Jikin ta take bi da hancin ta gabad'aya khamshin turaren jikin sa take yi ta cize bakin ta takaicin ta ya k'aru ji take kamar ta rufe kanta da duka amma babu damar hakan ta fito tana hawaye ta nufi cikin gidan.

Bata ga Umma a falo ba ta shiga d'aki ta zauna ta fashe da kuka mai tsuma zuciya da tausayin kanta da rayuwar ta a gidan wanda baya sonta yayi amfani da k'arfin mulki da son kud'in Mahaifin ta ya aure ta.

Muryar Umma taji a kanta tana cewa, "Meye na kukan kuma bayan kinyi min alqawarin baza ki kuma kuka akan wannan ba?, kince min kin amince da k'addara meyasa kike zubar da hawayen ki haka Rauda?."

D'ago kai tayi tana goge idanun ta kafin tace, "Umma baya sona ban san wanne irin zama zanyi dashi ba ga tarin qalubalen dake cikin aure na dashi." Umma tace, "Ki daina cewa haka yana sonki Rauda in baya son ki bazai aure ki ba, in baya son ki bazai zo inda kike ba a yau, in baya son ki bama zaki sanshi ba Rauda. kita addu'a wannan kukan bazai amfane ki da komai ba." Dak'yar Umma ta rarrashe ta tayi shiru zuciyar ta cike da tausayin ta.

Asad kuwa da farin ciki ya koma gida duk da fuskar sa bata gwada hakan ba amma zuciyar sa kamar an wanke ta da ruwa mai sanyi haka yake ji, abinda yake bashi tsoro sai ya tuna Mama sai taji fad'uwar gaba da tashin hankali a zuciyar sa.

Lokacin da ya gama shirin sa zai kwanta sai ya tuno da kalaman Rauda sai ya murmusa a bayyane yace, "ko ta yaya zan tabbatar mata da ita son ta ban sani ba." Murmushi ya kuma yi ya kwanta yana jin nishad'i a zuciyar sa da kuma tashin hankali a wani b'angaren na daban.

Aliyu yana tsaye a tagar d'akin sa yana kallo yaga dawowar Asad ya murmusa yana girgiza kai domin yafi kowa jin dad'in yin auren Asad da Rauda da akayi domin Allah kad'ai yasan abinda zai cimma da wannan auren shiyasa yake cikin farin ciki dashi yake kuma jin dad'in sa dari bisa dari. Dariya yayi mai sauti kana yace, "Zaku tafi Cairo amma kai baza ka dawo ba Asad ita zata dawo wajena matsayin kaine, zan cigaba da zama da ita a matsayin kai zuwa lokacin da zan kore ta daga cikin rayuwar gidan nan gabad'aya, sai na tabbatar na d'and'ana mata bak'in ciki a rayuwar ta sai tayi dana sanin kiran Aliyu da mahaukaci. zan cigaba da amsa sunan kai har abada kai kuma zaka kasance matattace a idanun duniya a yayin da ka koma Aliyu ni kuma na koma Asad. Ina godewa Allah da ya kasnace da kai nake kama bada Hydar ba zanyi duk abinda nake so da sunan Asad ne ba Aliyu ba, zan mallaki Jidda matsayin matata a matsayin kaine ba Aliyu ba, zan mallaki karagar katagum matsayin Asad ba Aliyu ba. Saura kiris hak'a ta ta cimma ruwa, wannan shirin nawa shi nake yiwa take da Kwantan b'auna" ya furta yana shafa sajen sa cikin tsantsar farin ciki da walwala.

Dariya ya kuma yi ya tafa hannun sa lokacin da ya tuno dasu waziri ya cize baki ya girgiza kai domin shi kad'ai yasan makomar da ya tanadar musu da zarar komai ya dawo hannun sa zasu gane kuran su, zasu gane sunyi kuskuren bari yasan dukkan sirrkan su bama su kad'ai ba duk wanda ya kasance a k'ark'ashin garin Katagum sai ya san Aliyu yana mulki.........


Tofa Aliyu ya k'ulla k'ullalliya>?? @&? @&?
[17/12, 10:39 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*031.*

Washe gari ta kama ranar Talata akwai zaman fada da safe duk wani mai muk'ami a masarautar katagum ya hallara anyi gaisuwa kowa ya watse wanda zasu nufi office sun nufa.
Bayan an tashi daga fada mai martaba ya nemi ganin Asad lokacin har ya tafi company ya dawo ya amsa kira, shi kad'ai ne a zaune kusa dashi kamar koda yaushe dan in zai gana dashi bai cika zama da wani ba ya kalle shi yace, "Asad akan batun matar kane anjima jirgin ku zai tashi zuwa Cairo ya kamata ka fara shiri."

Gaban Asad ya fad'i dan baiyi tunanin abin zai zo da sauri haka ba ya furta, "Allah ya k'ara maka lafiya ni bani da visa Egypt." Mai martaba yace, "Na sani ai shiyasa na saka aka yi maka komai ta hannu Hydar, anjima da k'arfe hud'u zaku tashi kaje ka fara shiri itama ka sanar da ita na dai sanar da mahaifin ta amma yana da kyau kaima ka fad'a mata, gwara kuje a sama mata lafiya."

Asad k'irjin sa duka yake kansa na k'asa ya kasa d'agowa shud'ewar wasu sacanni kafin yace, "Abba Mamaaaa!." Mai martaba ya zuba masa ido yana kallon sa cikin burgewa, ya jima baiga yaro mai k'arancin shekaru kamar sa wanda yake da tsananin biyayya ga iyayen sa kamar Asad ba, yana gujewa b'acin ransu ko kad'an baya so ba kuma ya k'aunar hakan ta faru ko kad'an, yana iya hak'ura da farin cikin sa sabida nasu farin cikin, yana yin abinda suke so koda shi ba shi yake so ba shiyasa a wannan lokacin yayi alqawarin samar masa da abinda yake so a karon farko a rayuwar sa.

Cikin taushin murya kamar yace, "Zaki ka kwantar da hankalin ka komai zai zo da sauk'i Maman ka baza tayi fushi dakai ba, kaje kayi abinda nace kawai." Shiru yayi na wani lokacin kafin ya mik'e ya fita jikin sa a sanyaye matuk'a.


Azahar tayi lokacin ya shiga masallacin cikin gidan yayi sallah kana ya koma ciki ya tsaya gaban kayan sa yana tunanin wanda zai d'auka domin tafiya dasu, numfashi ya fesar ya lumshe ido ya rasa ma abinda zaiyi.

Kalaman Mama ne suke dawo masa cikin kansa ya koma gefen gado ya zauna ya dafe kai yana ji kamar ya kurma ihu sabida tsaka mai wuyar da yake ciki, Mama tace kar yayi Mai martaba yace yayi nawa zai d'auka nawa zai ajjiye?. Hydar ne ya shigo ganin a yanayin da yake bai kula shi ba ya jawo madaidaiciyar jaka ya fara zuba masa kaya da duk wani abun da zaiyi amfani dasu ya zuba a ciki kamar Asad d'in ne ya had'a ya zuge zip d'in jakar ya kalle shi yace, "ga automatic wheelchair a bayan boot d'in motar ka zaifi tayi amfani dashi sabida tafiyar Airport tunda ba private get zaku bi ba."

"Hydar ta ya zan iya tafiya Mama bata nan? Ka sani Mama bata sonta ba kuma ta goyan bayan auren ta meyasa zan zab'e ta na bar Mama?" Ya fad'a a raunane yana kallon sa. Hydar yace, "ita wacece da zaka zab'e ta ka bar Mama? Ba zab'in ta kayi ba ka bar Mama ba ka d'auki abinda kake so ne kawai a karo na farko na tabbata kuma Maman zata duba wanda ka bari sabida ita na baya zata yi maka adalci a karo na farko."
"U never understand" ya furta yana dafe kansa domin shi kad'ai yasan fitinar da hakan zai haifar.

Hydar yace, "yanzu kenan umarnin Abba ne baza ka iya cikawa ba?." Kallon sa yayi shima ya kalle shi yace, "Yeah gashi kana k'okarin bijirewa bayan shima umarni ya baka." Jin hakan sai ya sauke numfashi ya tashi jiki a sanyaye ya ahiga band'aki shi kuma ya fita ya k'yale shi. Ya jima sosai sannan ya fito yayi wanka ya shirya cikin k'ananun kaya suit black yayi kyau sosai kamar baturen America ya shiga d'akin karatun sa ya d'auki littafan da yasan zai nema ya zuba a jaka ya kalli agogo.

K'arfe uku na yamma ya rage aww uku kenan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login