Showing 87001 words to 90000 words out of 216282 words

Chapter 30 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

yace, "kace mace ta biyu a duniya dana bawa hak'uri because nasan na cutar dake, forgive me please." Numfashi ta sauke a hankali sai taga ya saki hannun ta ya juya gefen sa ya d'auki wata k'aramar leda ya ajjiye mata yace, "Is for u."

Dafe kai taga yayi ya zauna yana runtse idanu alamun maganar da yayi da yana tana affecting d'insa ya lumshe idanu yana sauke ajiyar zuciya.? A nan ta tabbatar Asad ne domin kuwa yadda yake yatsine fuska da zanen hannun sa da yadda yake magana ya tabbatar mata shine, babar shaidar ma itace zanen hannun sa. "Na sake ki saki biyu!." Abinda taji ya furta kenan ta sake kallon sa a gigice taga ya mik'e tsaye yana mayar da abubuwan da suka hana fitowar fuskar sa gabad'aya yace,

? ? ? ? "Na yiwa Mama alqawarin zan rabu dake gabad'aya har abada that's why na yanke duka igiyoyin aurena a kanki. Ki yafe min banyi dan na cutar dake ba sai dan na barki ki huta ki auri wanda kike so yake sonki. Ina sonki har gobe amma nafi son Mama akan komai, kiyi ha?uri" yana fad'a yana gifta ta zai wuce k'unar zuciyar ta na k'aruwa tayi sufa ta sha gabansa tana binsa da banzan kallo cikin tsanar data mayaye mata zuciya lokaci d'aya tace,

"K'arya kake wannan ba alqawarin da ka yiwa Maman ka bane iya ita kad'ai harda zuciyar ka, na dad'e da sanin wannan ranar zata zo a cikin rayuwata, na jima da sanin za'a zo wannan gab'ar da saka wula?anta ni dan na kasance kaskantacciya a wajan ka."

"Kayi abinda kake so ka mayar dani bazawara da k'aracin shekaruna, kasan babar ka bata sona meyasa ka aure ni? Kasan Babar ka bata sona meyasa ka b'ata min k'uruciya ta?." Kallonta yayi yace, "Ba'a san shugaba da sakin aure ba a wata masarautar an haramta hakan amma ya zama dole a wajena shine kwanciyar hankalina da naki."

"K'arya ne wallahi, burin kane kawai kuma ka cika sai kaje ka k'arata daman Allah ya sani tun farko ba son auren ka nake ba k'addara ce ta had'a kuma ta raba, ban damu da kai waye ba amma ina so ka sani sai Allah ya saka min." Runtse ido yayi ya kalle ta ganin kamar an canja ta kamar zaiyi magana sai ya fasa ya cize bakin sa ya fita daga falon zuciyar sa na zafi shi kansa inda tasan abinda yake ji baza tayi masa wannan zargin ba, amma ya zaiyi umarnin zuciyar sa kawai yake bi maganar da yayi mata ma ya daure ne amma bala'in haushin ta yake ji.

? ? Zubewa tayi a wajan tana kuka sosai zuciyar ta nayi mata ciwo ranta na suya haka take zubar da hawaye masu zafi, ta jima a wajan bata san adadin lokacin data d'auka a wajan ba taji an dafata ta baya, bata d'ago ba bata daina kukan ba kuma sai da taji muryar Baba yana cewa, "ke kuma lafiya kike yiwa mutane kuka? Ina mai martaban yaje?." Ta sake k'ara kaimi wajan kukan ta sai a sannan take ji a zuciyar ta komai ya faru da ita Baba ne silar komai da bai bada auren ta babu sanin ta ba da duk hakan bata faru ba.

? ?? Umma tace, "tashi muje d'aki ki daina wannan kukan." Umma ta d'aga ta ta jinginar da kanta a kafad'ar Umma suka fita Baba yaga ledar da aka ajjiye ya d'auka yabi bayan su jikin sa na rawa tsoro duk ya dabaibaye masa zuciyar sa.

A falon Umma ya tarar dasu a zaune daga ita sai Umma tana ta kuka har lokacin Baba ya zauna kusa da ita yace, "meya faru ne wai?." Cikin kuka gabanta yana fad'uwa tace, "Baba tun a Egypt ya sake ni saki d'aya, yanzu kuma......" Sai kuma ta kasa k'arasawa ta sake fashewa da sabon kuka. Murmushi Umma tayi tace, "Daman nasan za'a rina ai, yanzu da yazo ya k'arshe guda biyun ko?." Rauda ta d'aga kai alamun eh tana sake cigaba da kukan ta.

Baba cikin tashin hankali yace, "ban fahimta ba, mayar dake yayi sannan ya kuma sakin ki?." Kai ta d'aga alamun eh tana jikin Umma tana kuka tare da jan numfashi Umma tace, "Shine ya had'o ki da kud'i a jaka da yake ga kwad'ayayyiya wacce take neman kud'in hannun sa ko?."

Baba ya buWe jakar nan yayi karao da takardar doguwa fara ya d'auka ya warware yaga abinda ta fad'a a rubuce???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? harda tambarin masarauta yaja tsaki yace, "K'arya kike wallahi kece kika yi silar da ya saka shi ya sake ki tunda daman tun farko ba so kike yi ba. Na tabbatar wani abun kika fad'a masa wanda ya b'ata masa har ya kai ga aikata abinda ya aikata. Kin cuce ni keda uwar ki kun gama dani gabad'aya, ina sirikin sarki guda fad'ar sirikin sarkin nan a baki ma dad'i ne dashi sai da kika saka k'afa kika b'arar da wannan sunan hankalin ki ya kwanta, kun kyauta ai keda babar ki burin ku ya cika sai ku zuba ruwa a k'asa kusha, gaki nan sai ta jika tasha ai. Ke ni ban ma amince ya sake ki d'in ba sai naji da kunnena domin shugaba baya saki."

Umma tayi murmushin takaici tana kallon Baba tace, "ka duba takardar ka gani ka karanta ka tabbatar anyi sakin kace baka yarda ba?." Baba yace, "Nidai Allah ya isa ban yafe ba, dukkan wanda yake da hannu a cikin wannan lamarin bazan yafe masa ba wallahi, sai Allah yayi mana hisabi domjn an cuce ni an gama dani an b'arar min da duk wata dama da nake da ita."

? ? ? ? ? Ran Umma ya b'aci matuk'a ta mik'e tsaye tace, "Nida itafa mu ya kamata muyi Allah ya isa ba kai ba domin mu aka cuta, son kud'in ka shine ya jawo ka bada y'arka badan tana so ba sai dan kawai kwai kud'i da mulki. Da Anas kake goyan bayan ta aura amma tunda kaga wanda ya fishi ka tsallake shi kace baka san zance ba duk tarin kyautatawar da yayi maka. Ka bayar da Rauda aure aka d'aura auren duk da abubuwan da suka faru a baya akan maganar auren ka manta ka shafawa idanun ka toka kana ji a ranka koda zasu kasheta indai kai zaka samu kud'i zance ya k'are. Har cikin gida akazo za'a kashe ta akan auren wanda ba komai ba tunda ba annabi bane ko sahabi amma duk da haka baka gani ba ka take kayi san ranka baka duba halin da zata shiga ba ta inda zaka fita kawai kake nema. To dan yanzu sakamakon abinda ka aikata ya bayyana sai kazo kana yi mana Allah ya isa? Ita yarinyar dan bazata iya bud'e maka zuciyar ta kaga abinda yake ciki ba shiyasa kake ce mata haka!?" Umma ta fad'a cikin d'aga murya tana kallon Baba da b'acin rai k'arara akan fuskarta.

? ? ? Da mamaki Baba yake kallonta dan zai iya cewa karon farko kenan da ta d'aga masa murya a zamantakewar su ta aure su,ranar farko kenan da ta tsaya a gabansa yana fad'a tana fad'a har tana yi masa magana cikin fad'a kamar zata dake shi, "Binta ni kike yiwa magana kina d'agawa murya? Ni kike kallo kike cewa na siyar da y'ata sabida son kud'i?."

Umma tace, "Na fad'a! ai ba k'arya nayi ba na sake fad'a ka bada auren ta sabida son kud'i irin naka. Har cikin gidan su yaro yazo ya sake ta sabida baka bata mahimmaci ba a lokacin daka ce ana sonta da ka nuna musu tana da daraja da abin zaizo da sauk'i. Yanzu kuma kake bud'e baki kake cewa baka yafe mata ba sabida ta rabu da wanda zai yanke maka talauci, ai ga kud'in nan ya sake had'o ta dasu sai ka d'auka ka rik'e tunda shine mutunci a wajan ka. Ya nuna maka y'arka iya matsayin ta kenan ya aureta ya saka bawai don ta zama matar sarki ba iya matsayin ta kenan; wacce take da wannan? matsayin tana gida a zaune da ita ya dace ba yarka ba, kud'i shine abinda take so gashi nan kuma ya bata tunda haka ka nuna musu."

? ? ? ? ? Rauda hankalinta ya tashi karona farko kenan da taga iyayen nata suna cacar baki musmaman Umma da taga tana d'aga murya tana yiwa Baba fad'a kamar ba ita ba, rik'e Umma tayi tana kuka tace, "Dan Allah Umma kiyi hak'uri kiyi shiru, Baba kayi hak'uri dan Allah" ta fad'a tana kallon su idanunta na zubar da hawaye har lokacin. Kyakykyawan mari Baba yayi mata a fuska ta dafe kuncin tana kuka yace, "Duk ba kece sila ba? Da baki aikata abinda kika yi ba za'a zo wannan gab'ar ne?. yau a kanki uwar ki take kallon idanuna take cewa na siyar dake sabida kud'i, a kanki take d'aga min murya tana k'okarin tara min jama'a."

? ?? "Ni ya kamata ka mara ai ba ita ba tunda nice nayi maka laifin ba itace tayi ba, koda yake ai haushin sarki ya sake ta shine dalilin da ya saka ka mare ta to ka koma kaje kayi bikon sa mana in yaso sai ka had'a ta da wani suyi auren kisan wuta sai ka mayar da auren, ko kuma ka mayar haka sai ta koma can ta zauna" Umma ta fad'a cikin fusata sosai tana kallon Baba shima yana kallonta.

Kuka sosai Rauda take yi ganin tashin hankalin da bata tab'a gani ba a gidan su kuma a kanta ake wannan fad'a tsakanin iyayen ta shiyasa hankalin ta ya tashi, zuciya ce take d'auka Baba in ya tsaya a wajan zai iya aikata komai abinda baiyi ba tun da zai iyayi a wannan lokacin a yadda yake jin zuciyar sa, yayi k'wafa ya juya ya fita ransa a b'ace yana wuci. Umma d'aki ta shiga Rauda tabi bayanta tana kuka tace, "Dan Allah Umma kiyi hak'uri, ki yafe min nice silar komai da ya faru" ta fad'a tana sake fashewa da sabon kuka.

Umma tace, "ni baki min laifin komai ba ke aka yiwa laifi kuma ake tauye miki hakkin ki, dan nayi shiru kwanaki da suka wuce yanzu bazan yi shiru ba in yaga dama nima ya sake ni d'in sai na d'auke ki mu tafi gidan ubana na tabbata can zasu nemo miki mutuncin ki baza su siyar dake sabida kud'i ba. Dan ina yin shiru akan lamarin y'ay'ana ba hakan yana nufin bana son ku bane ko ban damu daku ba sai dan kawaici, to na lura bai san shi ba san anyi fito na fito."

"Dan Allah Umma ki daina fad'ar haka tun tasowa ta ban tab'a ganin haka tsakanin ki da Baba ba meyasa yanzu zakuyi kuma sabida ni?."
"Hmm" shine abinda Umma tace bata ce komai ba sai Rauda da take kuka tace, "badan Allah yasa Khalil da Khairi suna wajan inna ba da a gaban su hakan zata faru? Haba Ummana kamar ba ke ba?."

Umma tace, "Tun zuwan ku Egypt d'in ya sake ki?." Rauda ta girgiza kai alamun a'a tace, "Sai ana saura kwana biyu zamu tawo, Maman sace tazo a gabana ta saka ya sake ni ta kuma kore ni daga hotel d'in badan abokin sa likitan da sukayi min aiki ba da yanzu ban san a ina nake ba. A gidan sa na zauna na kwana biyu matar sa ta d'auke ni kamar y'ar uwar ta shine ya dawo dani."

Umma tace, "ba wani uwar sa da ta saka ya sake ki daman can shima akwai manufar da ya saka ya aure ki ba don Allah ba, daman can ban amince da wai yana sonki ba ina ke ina shi? Kwantan b"auna yayi ya lallab'a ya aure ki wata?ila sirrin? wani aikin ne akan sarauta akace sai ya auri budurwa mai irin suffar ki shiyasa ya nemo ki dan yasan halin mahaifin ki, yanzu da buk'ata ta biya ya zama sarki kuma ya dawo ya warware abinda ya rage dan kar ma wani tunani ya d'arsu a ranki nan gaba.'

Shiru Rauda tayi bata ce komai ba sai kuka da take sharewa, Umma ta kuma cewa tace, "In kin kammala idda Allah ya baki miji kiyi auren ki kowa ya huta, ni ina jin ma na tura ki gidan Yaya Bilki can bauchi kije can ki huta da bala'in mahaifin ki, ko ki tafi gidan Baba Malam kiyi zaman ki."? Kallon Umma Rauda tayi itama ta kalle ta tace, "Nasan akwai idda a kanki Rauda tun dawowar ki idanun ki sun tabbatar min da kin zama cikakkiyar matar aure Rauda, kada ki damu k'addarar kice a haka komai zaizo da sauk'i nan gaba in sha Allah, wata rana sai labari zai wuce kamar bai faru ba."

Rauda tayi shiru Umma ta kuma cewa, "Tun dawowar ki nasan akwai abinda kike b'oyewa zuciyata ta hasoso min hakan amma kika ce babu komai."
"Umma ban san ta yaya zance muku an sake ni ba, ban san ta yadda zance miki auren satittika ya mutu ba shiyasa nayi shiru."
"K'addarar ki kenan ki kwantar da hankalin ki."
"Umma ki bawa Baba hak'uri dan Allah." Umma ta Harare ta har zatayi magana sai kuma ta fasa ta tashi ta shiga band'aki.

Jikin Rauda a sanyaye ta tashi ta fita daga d'akin ta shiga nata d'akin tana, jingina tayi da bango ta lumshe ido hawaye suka sakko mata ta share a bayyane tace, "Tabbas Asad kayi min bazata, ka illata min k'uruciyata, ka jawo sa'insa tsakanin iyayena, ka raunana min zuciya, kayi wasa da hankalina, ka saka min ciwo a raina, ka lalata duk wani shirina, ka barmin tabo a zuciyata. Allah sai ya saka min" ta fad'a tana durk'ushewa a wajan ta fashe da sabon kuka tana dana sanin amincewa dashi har ta fara sonsa.

_nayi miki alqawarin bazan barki ba ko meye zai faru._ kalaman sa da suka fad'o mata kenan ta runtse ido ta zube a wajan tana kuka sosai babu mai rarrashin ta. Tashi tayi tana kallon hannunta taga zoben da ya bata ta zare shi daga hannun ta ta buWe kayan ta ajjiye dan k'ona shi zatayi da safe dan bata son tunawa da komai da ya shafe shi.

Kama wacce ta tuna wani abun sai ta zabura da jajayen idanun ta ta fita zuwa saman Baba gabanta yana fad'uwa, a zaune ta ganshi yayi shiru alamun ransa a b'ace yake tayi sallama taga ya d'ago ya kalle ta bai amsa ba ta k'arasa ciki ta zauna akan carpet tace, "Dan Allah Baba kayi hak'uri, wallahi Allah ban cewa Asad ya sake ni ba shine ya sake ni tun muna Egypt sannan kuma ya dawo yau ya k'arashe saki biyun da suka rage na rantse da Allah babu laifina balle laifin Umma, kayi hak'uri ka yafe mana" ta k'arasa fad'a cikin kuka sosai dan zuciyar ta tayi rauni.

? ? ? Shiru Baba yayi bai amsa ba ta kuma cewa, "Dan Allah Baba kayi hak'uri wallahi bani da laifi ko kad'an" sai ta fashe da kuka mai tsuma zuciya ta kifa kanta a cinyoyin ta tana kuka. Baice kanzil ba ta jima tana kukan kafin ta goge idanunta ganin kallon ta baiyi ba ta tashi ta sauka daga saman nasa ta koma d'akin ta tayi lamoo a kan gado babu alamun bacci a cikin idanunta.

? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?? *&&&*

? ? ? ? "Kin tabbatar kin zuba masa a cikin ruwan yasha?." Jidda rik'e da waya a hannunta tace, "Wallahi Mum yasha har na wankan ma dana zuba masa yayi wankan dashi, nayi mamakin yadda ya sauko lokaci d'aya haka." Mum tayi y'ar dariya tace, "k'yale Jidda tukunna ma kenan, ai na rantse da Allah sai Rabi tayi kuka da idanunta, sai ta gwammace bata bawa Asad kujerar sarautar nan ba."

"Shiyasa nake yin Mum wallahi, Allah yaja da ranki."
"Amin. Kedai kiyi duk abinda nace miki kar ya dame ki dan kinga baya neman ki akwai dalilin hakan sa kuma za'ayi maganin abun nan kusa."
"To Mum."
"To sai da safe ki tashi ki tafi b'angaren sa ki tabbatar ki shafe jikin ki da wad'an nan turarukan."
"Okay Mum, Bye" tana fad'a ta kashe wayar tana farin ciki.

? ? ?? Shiryawa tayi kamar ko yaushe ta d'ora hijjabi ta fito jakadiyar ta tana take mata baya zuwa b'angaren mai martaba ta k'ofar cikin gidan dan farin ciki take ji dashi tafi so kowa ya ganta bazata bi ta inda baza'a ganta ba. Sunzo tsakiyar harabar gidan wutar gidan gabad'aya ta d'auke d'uf duhu ya mamaye duka gidan a guje ma'aikatan gidan akayi wajan wuta dan a gyara dan kowa yayi mamakin d'aukewar ta.

Ba tsammani Jidda taji an jata wani waje an toshe mata baki zatayi ihu yace, "Shiiiii! Karki ce komai." Kallon sa take idanunta a waje tana so ta banbance Asad ne ko Aliyu ya kalle ta yace, "What are you thinking about?."

? ? ? ? "Aliyu?." Ya d'aga mata kai yace, "Yeah it's me." Ta kwace hannunta da yake rik'o tace, "Meyasa ka kawo ni nan? Sai wani ya ganmu?."
"Ki daina increase volume mana, i want to talk to you that's why na kashe wutar gidan."
"Daman kaine ka kashe wutar?."
"Yeah nine."
"For what reasons?."

Ya kalle ta yace, "stop shooting mana, ko ina kina so a ganmu ne?." Ta kalli bayanta taga babu wanda yayo wajan da suke tace, "Ina jinka."
"Asad yyi having sex dake?."

Idanun ta ta zaro tana kallon shima ya zaro idanun sa yace, "Answer me bana son wani kwana-kwana malama."
"To ina ruwan ka da wannan kake tambayata?."
"Because ina so na taimake ki ne in ba haka ba a haka zaki k'are a gidan nan babu wani cigaba sabida Asad yayi damage bazai tab'a yiwa kasancewa da wata ba; in fact bazai haihu ba."

"What?." Ya wara idanu yace, "yes ke kin san bazan miki k'arya ba, in kuma kina tunanin wasa nake ki gwada ce masa kina son ya baki hakkin ki kiga me zai faru."
"Wanne irin taimako kake fad'a zaka min?."
"Ki fara tabbatarwa then sai ki neme ni, and......" ya fad'a yana lalubo aljihun sa ya d'auko wani magani ya bata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login