Showing 132001 words to 135000 words out of 216282 words

Chapter 45 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

kusa kashe masa uwa su kwana lafiya ba. Dan shi kaf cikin plan d'in sa babu kashe Mama. Lokaci d'aya sai Mama taji dad'in jikin ta ganin addu'ar ta biyu ta karb'u har Allah ya biya mata saura guda biyu da take jiran tabbatuwar su. Basu jima sosai a asibitin ba tace sai an sallame su ganin taji sauk'i sai ciwon cikin kad'an-kad'an sai aka sallamo su suka dawo gida.

? ? ? ? Aliyu gida ya koma sai a ranar ya shiga cikin masarauta ya tattara gabad'aya ma'aikatan b'angaren Mama ya saka su a gaba yana kallon ko waccen su yace, "Wacece k'arshen aiki a kitchen d'in Mama jiya?." Suna durk'ushe dukkan su duk sun tsorata dan sun san hali ba kirki ne dashi ba d'aya tace, "Nice ranka ya dad'e."

Ya hard'e hannu a k'irji yana kallon ta sai ta sunkuyar da kai yace, "ke kika zuba ruwa a kettle d'in da ake dafa tea?." Kallon sa tayi suka had'a ido yayi mata mugun kwarjini ta sauke kai yace, "Duk wacce tayi min k'arya wallahil azimi saina hukunta, kun san halina."

"Ranka ya dad'e nidai na gama gyara kitchen d'in amma ban zuba ruwa a butar ba" ta fad'a kanta na k'asa ya kalle su yace, "Wacece ta zuba a cikin ku?." Duk sukayi shiru ya girgiza kai yana kad'a k'afar sa yace, "in na sake maimaitawa sai kunyi kuka." D'aya daga ciki tace, "Nice ranka ya dad'e, amma wallahi ban zuba komai a ciki ba ruwa kawai na tara a fanfo na zuba na ajjiye kuma bada niyar wani abun nayi ba."

"Nace daman an zuba wani abun ne?" Ya jefe ta da tambayar muryar sa a can ciki dan in baka nutsu nama baza ka san me yace ba yana kallon ta. Tayi shiru ya kuma cewa, "Bayan ku waye ya shigo?." Suka had'a baki suka ce, "Babu kowa."
"Kenan dai a cikin ku wata ta zuba gubar a ruwan."

Sun tsorata matuk'a jikin su sai rawa yake ya girgiza kai yace, "Better, zan saka a kulle ku yanzun nan then ayi muku bulala goma sannan ku share harabar gidan nan gabad'aya, in kun gama sai mu sake zama muji wacece tayi a cikin ku."

Kafin suyi magana yace, "kana ina!." A guje dogarai biyu suka shigo yace, "aje ayi musu hukunci kar a k'yale su har sai rana ta fad'i" yana fad'a ya tashi zai bar wajan suka rushe da kuka d'aya tace, "Dan girman Allah ranka ya dad'e kayi hak'uri kayi mana rai, nidai wallahi ban san komai ba ban aikata komai ba kuma."

Ko kallon su ma baiyi ba ya wuce abinsa aka tasa kewar su dan su karb'i hukunci ko wacce cikin su kuka take yi dan hukuncin da ya zayyana bamai sauki bane ba.

? ?? Ba jimawa su Mama suka dawo ta tarar b'angaren nata babu kowa hatta jakadiyar ta ladidi bata nan suna zaune a k'aramin falon Aliyu ya shigo ya zauna a kusa da k'afar ta kamar yadda Hydar yake a gefe tace, "Ina hadiman nan suke?." Aliyu yace, "na saka ayi musu hukunci sai sun fad'a min wacece ta zuba poison a tea."

"Aliyu meyasa?" Ta fad'a tana kallon sa. Shima kallon nata yayi ya rasa me ya canja maman nasa lokaci d'aya itace take cewa meyasa aka yiwa Hadimai hukunci...? Baice komai ba ya kalli Hydar yace, "Ina so na had'u da Asad." Hydar yace, "Yana k'aramin falon sa yana tare da bak'i."

Baice komai ba kawai ya mik'e ya fita Mama ta bishi da kallo zuciyar ta tana mata rawa a kansa dan gani tayi gabad'aya ya canja kamar ba shi ba kamar kuma shi ta girgiza kai tace, "Akwai alamar tambaya akan sa, meya canja Ali haka?." Hydar yace, "Mama ashe bani kad'ai na gani ba, tabbas Aliyu ya canja kamar bashi ba." Kai take girgizawa ta koma ta kwanta a jikin kujera dan har lokacin cikin ta ciwo yake yi mata.

A k'aramin falon cikin gida kamar yadda akace Asad ya gama ganawa da bak'i yana kashingid'e yana duba wani littafi a hannun Aliyu ya shigo da sallama, amsawa yayi yana kallon sa shima shi yake kallo Asad bai san ya mik'e tsaye ba sai murmushi yaga Aliyun yayi yace, "Our king surprise" ya fad'a yana bashi hannu alamun su gaisa. Sai kuma ya janye hannun yace, "Oh sorry ba haka ake gaida ku ba" sai ya duk'a kamar yadda ake yiwa sarakuna yace, "Allah ya taimaki sarki ya k'arawa sarki lafiya."

Asad ya saka hannu biyu ya d'ago Aliyu ya mik'e tsaye yana kallon sa da farin ciki a kan fuskar sa ya mik'a masa hannun alamun su gaisa, Aliyu daman abinda yake so kenan da sauri ya bashi hannu suka gaisa yana kallon Asad yana wani irin murmushi mai d'auke da ma'anoni da dama a cikin sa.........



*karfa muje ya shafawa Asad maganin hauka Fans....*=?(?
[17/12, 10:41 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*066.*

? ? ? ? ? ?? Kallon kallo suke dukkan su baza ka iya fassara yanayin su ba duk da akwai murmushi akan fuskar ko wannen su amma yadda suke kallon juna hakan zai baka tabbacin akwai wani abun a k'asa a dinne wanda ba kowa yasan dashi ba. Asad ne ya fara janye hannun sa Aliyun ma ya janye Asad ya sake fad'ada murmushin sa yace, "Yaushe ka dawo?."

? ? ? ? Jin yadda maganar Asad ta fita cike da iyayi ana bawa ko wanne harami na kalmomin hakkin sa sai abin ya bawa Aliyu dariya ya dara kad'an yace, "Ba'a jima ba ranka ya dad'e." Asad ya murmushi ya koma ya zauna Aliyu ya zauna shima a k'asa kamar yadda Asad d'in ya zauna kana Asad yace, "Barka da zuwa." Murmushi ya kuma yi yace, "Na gode."

Shiru wajan yayi babu mai magana ko wanne da abinda yake sak'awa a ransa Aliyu ka katse shirun da fad'in, "In mai martaba yayi min izini zan shiga wajan Abba naga yanayin jikin sa." Asad ya kalle shi yace, "A fito lafiya." Tashi yayi yace, "A tashi lafiya our king" ya fad'a yana niyar tafiya har yaje gab da k'ofa sai kuma ya juyo yaga Asad d'in ma kallon sa yake yi sai suka saki murmushi a tare Aliyu ya fita.

? ? ? ? Da wannan murmushi a fuskar sa ya shiga b'angaren mai martaba ya samu an zaunar dashi idanun sa a buWe Uncle ya bashi alkur'ani yana karantawa, sallamar Aliyu ya saka shi kallon k'ofa Aliyu sai ya saki murmushi ya k'araso kusa dashi ya kalli Uncle yace, "Uncle barka da safiya." Uncle yace, "Aliyu yau kaine a k'asar tamu?." Murmushi yayi ya shafa kansa kafin ya kalli Abba da yake kallon sa shima ya rik'e hannun sa yace, "Ina farin ciki da naga mahaifina lafiyar sa tana samuwa, Allah ya tashi k'afadun mai martaba nan bada jimawa ba."

Uncle ya amsa da amin sai mai martaba ya murmusa ya cigaba da karatun sa bai kuma kallon sa ba, Aliyu kallon gefen drawer yayi yaga allurai a ajjiye da yawa ya kalli Uncle yace, "wannan fa?." Uncle yace, "itace wacce ake masa duk sati." Aliyu ya girgiza kai ya d'auki allurar ya d'auka a waya ya ajjiye sai suka had'a ido da Uncle sai yace, "zan nunawa wani Dr ne naji ya ingancin ta." Uncle yace, "ba laifi."

Aliyu yace, "Ina dawowa" ya fad'a yana fita daga b'angaren ya wuce tsohon b'angaren su wanda suke da d'akuna a can. Har zai gota b'angaren Jidda sai kuma ya tsaya cak ya kalli b'angaren nata yaga dogarai maza biyu masu gadin ta a tsaye a k'ofar da zata shigar da kai wajan nata, ba tare da wani tunani ba ya nufi wajan hango shi da sukayi sai suka mik'e suka zube a k'asa yana zuwa bai bi ta kansu ba kai tsaye ciki ya shiga.

? ? ?? A cikin falon kuwa Jidda na zaune ita kad'ai ta kori kowa na b'angaren nata waya na hannun ta kamar ko yaushe suna waya da Mum tana fad'in, "Mum naga Aliyu wallahi na ganshi ya dawo!, na shiga uku na lalace Mum komai zai lalace." Daga can b'angaren Mum tace, "Dallah malama ki nutsu, me Aliyun zai miki kika bi kika tsorata da dawowar sa haka? Mukayi maganin Asad sa balle shi karan kad'a miya."

Jidda ta rausayar da kai tace, "Mum baza ki gane ba, Aliyu ya wuce duk inda kike tunani wallahi tsaf zai lalata mana shirin da muka jima munayi. Dawowar sa ba alkhairi bace ba a rayuwar mu meyasa ba'a kashe shi a can k'asar b......." cak maganar ta maqale baki bud'e ta mik'e tsaye tana kallon inda ta ganshi a tsaye ya hard'e hannayen sa a k'irji yana kallon ta fuskar nan tasa a tamke babu alamun fara'a a cikinta.

? ? ? ?? A hankali yake takawo hannun sa na cikin aljihu yana Isowa kusa da ita ya saka hannu ya zare wayar hannun ta ya saka a speaker yaji Mum na cewa, "Waye Aliyu nayi maganin Asad da uwar su ma balle wani shi jiki duk neman mata...?. Ki? nutsu Malama ina so na gama da babar sune sannan na juyo kansa amma tunda naga kin tsorata sosai zan dawo da aikin kansa ko ba'a kashe shi ba za'a kulle bakin sa ko meye ma ya kasa fad'a. Nayi maganin Asad ma mai k'arfin ibada balle shi karan kad'a miya, ita kanta Rabi tana tsalle rijiya da baya ne amma gab nake da kawo k'arshen ita da yaran nata gabad'aya."

? ?? Jidda ta k'ame babu damar magana sai kallon sa da take yi yana sauraron abinda Mum take cewa da hannu yayi mata alama da ta bata amsa Jidda ta had'd'iye yawu murya na rawa tace, "Toh Mum." Mum tace, "Yauwa ki kwantar da hankali babu abinda zai faru ina tabbatar miki da hakan. Naji ya saka an kama hadiman babar sa akan yana zargin an zubawa babar sa guba zan gargad'i Ladidi kar ta bari sunana ya fito a cikin tuhumar su kome zai faru kar tace nice na saka ta dan Aliyun nan ba hankali ne dashi ba sai yayi min hauka." Mum tana gama fad'ar hakan ta yanke wayar Aliyu wayar da kallo suka had'a ido da Jidda ya saukar da idanun sa zuwa cikinta yaga ciki ya fito ya tab'e baki yana girgiza kai bace komai ba ya dire mata wayar ya fita.

? ? ?? Hannu Jidda ta d'ora a ka tace, "Na shiga uku! Shikenan ta faru ta k'are!" ta fad'a hannun ta na rawa sosai zuciyar ta a tsorace tana sake kiran Mum amma bata samun ta sai kawai ta d'auki wayar ta shiga d'aki ta saka babban hijjabi ta fito ta saka aka kira jakadiyar ta suka rufa mata baya zuwa inda mota take ajjiye driver ya shiga yaja su sai gidan Mum jikin ta har rawa yake sosai.

? ? ? ?? Aliyu yana fita b'angaren nasu ya nufa a kan hanyar sa ta tafiya yaga ana yiwa su Ladidi hukuncin da yace ayi musu duk sun galabaita sai kuka suke da hannu yayi musu alamun da su kawo masa su ya shiga falon ya zauna, a lokacin aka shigo dasu duk suka zube a k'asa dogaran suna baya yayi musu alama da su koma su suka fita yabi su da kallo dukkan su kuka suke yi har ita Ladidin.

"Allah yaja da ranka kayi mana rai, wallahi ban aikata komai ba bazan iya cutar da Fulani ba ko sau d'aya" wacce take kula da kitchen d'in ta fad'a tana kuka. Da yatsa ya nuna su yayi musu alama da su fita su jiki na rawa suka mik'e duk da gab'ob'in su duk sun gashi suka ce, "Mun gode, Allah yaja da ranka yasa kafi haka."

Sai da suka fita ya kalli Ladidi da take raba idanu rashin gaskiya ya bayyana a tare da ita yace, "Bana son cin amana in na kama mutum da cin amana ina sakawa a b'atar dashi daga duniya ne ma'ana a kashe shi!" Ya fad'a yana kallon ta sai jikinta ya cigaba da rawa dan ta tabbatar ya gano ta ta rushe da kuka tace, "Allah ya taimake ka wallahi sharrin shaidan ne ban san kuma guba bace, Hajiya Sadiya ta bani tace maganin da zai ragewa Fulani zazzaSi ne ni kuma ganin alaqar su sai na amince na zuba kamar yadda tace. Ka yafe min ranka ya dad'e nasan na aikata babban laifi amma bazan sake ba."

"Ai sai kina raye zaki sake" ya bata amsa ba tare da ya kalle ta ba yana danna wayar sa tana sharb'ar majina tace, "Dan Allah annabi Muhammad S.A.W kayi hak'uri ka yafe min ranka ya dad'e, kuskure ne kuma baza'a sake ba wallahi anyi na farko anyi na k'arshe. Nabi Allah na bika ranka ya dad'e ka taimake nj." Aliyu ya sauke numfashi ya kalle ta yace, "Zan k'yale ki amma da sharaWi d'aya."

Jikin ta na rawa ta nutsu taji yace, "yadda na gano ki cikin sauk'i kin san duk abinda kika kuma aikatawa bazai min wahalar gano ki ba ko?." Ta d'aga kai tace, "Kwarai ranka ya dad'e." Ya gyara zama yace, "bayan wannan Sadiyan ta tab'a baki wani maganin ki bawa Mama?."
"Bata tab'a ba wallahi, jiya ne rana ta farko."
"To ki nuna mana aiki kike mata har yanzu, duk abinda ta baki ki karb'a ki amsa kice zakiyi in kun rabu sai kizo ki bani duk abinda ta baki."

"Na amince ranka ya dad'e, na amince wallahi zanyi." Ya girgiza yace, "Nawa ta biya ki?." Jikin ta rawa yake da hannu yyi mata alama da tayi magana tace, "dubu dari."
Ya d'aure fuska tamau yace, "Akan dubu d'ari kika so kashe mana uwa?." Kuka take yi sosai tace, "Ban san na kisa bane, ban san kashe ta za'ayi ba wallahi."

"K'arya kike Ladidi zan k'yale ki ne kawai. Zan ninka miki abinda ta baki sau goma matuk'ar kika yi abinda nace."
"Ko baka bani komai bama zanyi ranka ya dad'e." Ya kwanta a jikin kujerar yace, "Kiyi abinda nace in naga yanayin aikin naki sai muga abinda zai faru" da hannu yayi mata alama da ta tashi ta bashi waje ta mik'e tana godiya sosai.

? ? ?? Bayan fitar ta ya tashi ya nufi d'akin sa har zai shiga sai ya fasa ya nufi k'ofar d'akin Asad ya murd'a handle d'in ya jishi a buWe, "A'a bro yau kuma d'akin deaf zaka shiga?" Hydar ya fad'a daga bayan sa ya juyo ya kalle shi ya d'aga kai yana tura k'ofar d'akin yana kallon d'akin yace, "nasa zan dawo tunda ya wuce matsayin wannan yanzu."

Hydar yayi murmushi yace,? "Yadda kake so, but akwai kayan sa da littafan sa a ciki" yana fad'a ya shiga nasa d'akin Aliyu ya shiga d'akin ya turo k'ofar yana kallon d'akin yana tab'e bakin sa kamar yaga kashi.

Yana nan a gyare sai y'ar k'ura da yayi kad'an gadon a d'ame da alama babu wanda yake zama a cikin d'akin. Kamar an bashi umarni ya d'aga katifar gadon nan yayi karo da k'atuwar laya wacce bai tab'a ganin irin ta ba da wani bak'in gashi a nannad'e a jikinta ya saki katifar yana kallon layar.

A gefe ya ajjiye ya koma ya buWe kayan Asad yana kallon su a shirye sama da kala hamsin har sunyi k'ura sabida ba'a tab'a su. Murmushi yayi ya girgiza kai yace, "Allah sarki Deaf, dole abubuwa su canja" ya fad'a yana zura hannun sa can k'arshen wardrobe d'in ya zaro wata layar ya had'a da waccan ya jefa a drawer ya shiga band'aki domin bazai zauna da layoyi a d'akin ba dan shi yasan inda suke.

A nan yayi wankan sa ya shirya tsaf da kayan Asad ya tsaya yana kallon sa a madubi yayi murmushi ya shafa gemu yace, "Like deaf." Murmushi ya sake yi domin shi kad'ai yasan abinda yake shiryawa a zuciyar sa, bayan Allah da ya halicce shi babu wanda ya isa ya gano shirin sa sai shi kawai ya fita daga d'akin.

*&&&*

? ? ? ? ? "Ke Rauda tashi mana, wannan wanne irin bacci ne haka har azahar tayi baki tashi ba ko jikin ne?" Umma ta fad'a tana tashin ta daga bacci Rauda ta mik'e tana rausayar da kai Umma ta tab'a wuyan ta tace, "jikin ki babu zafi, tashi kiyi wanka kici abinci kiyi sallah bacci ciwo zai k'ara miki." Kai ta d'aga ta ziro k'afafun ta k'asa ta sakko daga kan gadon tana niyar mik'ewa sai tace, "Washh bayana."

Umma ta kalle ta tace, "meya samu bayan naki? Naga tun asuba kina rik'e bayan ki." Rauda tace, "Haka nan ya rik'e min" ta fad'a tana shiga band'aki sai kuma ta fito tace, "Bara na d'ora ruwan wanka babu mai zafi." Umma tace, "Zauna a kawo miki." Ba musu ta zauna tayi tagumi Umma ta fita ba jimawa da kanta ta shigo mata da ruwa a bokiti bata k'arasa band'akin ba ta ajjiye mata bata ce komai ba ta juya.

Tashi Rauda tayi ta d'auki ruwan ta shiga band'akin tayi wanka tare da alwala tazo ta tayar da sallar azahar, bayan ta idar tayi tagumi abinda ya faru da ita jiya yana yi mata yawo ba kamar irin kalaman da taji yana fad'a mata a lokacin da suke tsaka da sab'on Allah nan take tsigar jikinta ta tashi sai hawaye tayi saurin gogewa ta kwantar da kanta a guiwar ta.

? ? ?? Gudun kar Umma ta sake yi mata magana ta gano wani abun sai ta mik'e ta fito ta samu tasha tea kawai bata iya cin komai ba Rahma tazo suna hira da Umma ita kam bata saka musu baki tayi shiru tana kallon waje daya. Yaya Ummi ce ta shigo tana fad'in, "mara lafiya kin tashi ashe?." Ta daga kai tace, "Yaushe kika shigo?."
"Kina bacci, ya jikin?."
"Da sauk'i, Ina wuni."
"Lafiya lau, Allah ya k'ara lafiya."
"Amin Yaya."

Umma ta kalli Yaya Ummi tace, "Jiya wanne turare kika bata ta shafa mai d'aukar hankali haka?." Gaban Rauda ya fad'i ta kalli Yaya Ummi suka had'a ido ganin yadda ta rud'e lokaci guda sai Yaya Ummi ta d'auki haske tace, "Sabo ne,? Abban su Islam ya kawo min shine ta d'auka ta saka."

Umma tace, "Tunda ke ya bawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login