Showing 192001 words to 195000 words out of 216282 words

Chapter 65 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

nuna k'arara Asad nake so yayi mulki ba da hakan duk bata faru ba. Ga Aliyu ma da yaso kashe Asad....Kai na cutar da Asad cuta mai tsanani" ta fad'a tana dafe kanta ta sake fashewa da sabon kuka.

Murya na rawa ta fara cewa, "Hydar! Aliyu!. Hydar d'ina shine yake so ya kashe Asad Hydar fa? Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un.? Duk abinda ake shiryawa ashe Hydar ne sila shine yake komai amma a zahiri sai ya nuna bai san komai ba, ya zanyi da rayuwata?. Y'ay'ana biyu duka babu na zab'e." Ta sake fad'a tana sake fashewa da sabon kuka ta kwanta a kan kujerar.

Asad ya tashi akan guiwar sa ya rik'e ta yace, "Mama likita yace kar ki shiga damuwa dan Allah ki kwantar da hankalin ki komai ya wuce."
"Ta ina ya wuce Asad? Bayan Hydar ya tabbatar da bai gama d'aukar fana a kanka ba yana nan zai dawo, in ya kashe ka ya zanyi Asad?. D'an uwanka jinin ka wanda kuka fito duniya lokaci d'aya ace shine yake neman d'aukar rayuwar dan uwan sa? Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un ina ma na mutu kafin wannan ranar. Meye amfanin maza ukun da nake alfahari ina dasu? Makisa, makirai, masu son kansu, masu son duniya akan D'anuwan su?, meye abin alfarahin da zanyi dasu? Basu da wani amfani dukkan su ina ma Allah ya d'auki rayuwar su gabad'aya na huta."

Mama Jamila tace, "bai kamata kina fad'ar wannan kalmar ba Mama, dan Allah kiyi ha?uri. Ya kike so Asad d'in yayi shida a lokaci d'aya ya rasa y'an uwan sa da babar sa suka juya masa baya? Ya kike so yayi lokacin da aka kwantar da mahaifin sa mai share masa hawaye?."

Mama ta tashi zaune ta dafe kai da hannun ta tace, "Duka ta silar Hydar wad'annan abubuwan suka faru, da kuma son tawa zuciyar badan na bayyana burina ba da duk hakan bata faru ba, da yanzu suna nan tare shida Hydar kamar da." Asad yace, "Dan Allah Mama ki daina kuka kodan lafiyar ki."
"Ka yafe min Asad, kace ka yafe min dan Allah."
"Mama dan Allah" ya fad'a a raunane yana kallon ta kamar zai zubar da hawaye shima.

Mama tace, "ku taya ni rok'on yafiyar sa dan Allah kar na mutu da hakkin sa a kaina." Asad yace, "Mama baki min komai ba, kina da iko dani har yanzu; ko yanzu kika ga abinda baki so a tare dani zaki iya cewa na hak'ura kuma na hak'ura domin kin isa." Mama ta girgiza kai tace, "A'a Asad, bazan sake hana ka abinda kake so ba har abada duk abinda kake so shi nake so, su wanda nake bawa abinda suke so d'in sune suke k'okarin ganin bayana kai da nake tauyewa kaine kake k'okarin ganin na rayu kake tsaye a kaina kana nema min lafiya. Naji dad'i da ya kasance Aliyu yana cikin yanayin hauka da lafiya saura Hydar shima Allah zai hukunta shi daidai da abinda ya aikata."

Mama ta kalli su Mama Jamila tace, "Ku kira min Suhaima tazo ta raka ni wajan matar sa na bata ha?uri." Asad yace, "Dan Allah Mama ki kwantar da hankalin ki baki da cikakkiyar lafiya fa."
"Nidai a kaini inda take na bata ha?uri nayi mata abubuwa da yawa a rayuwa wanda bazata manta dani ba." Mama jamila ganin yadda Mama ta rude lokaci d'aya sai tace, "Ranka ya dad'e a kira Fulanin taka tunda hakan take so ko dan sabida jikinta."

Asad ya kalli Suhaima da ta fito da kai yayi mata alama da ta kira Rauda ta amsa ta fita. Ba jimawa suka dawo tare da Rauda ta zauna akan k'asa kamar yadda Asad d'in yake tace, "Barka da dawowa Mama." Jin muryar Rauda sai Mama ta kalle ta tace, "Tun kina asibiti lokacin da Hydar ya buge ki ban tab'a ganin ki ba amma na d'auki tsanar duniya na d'ora miki, na saka aka kore ki daga asibitin ta silar hakan kika samu matsalar k'afa,? ta silar hakan abubuwa da yawa suka faru dake wanda na samu labari da wanda ban samu ba. Na saka akazo har gidan ku aka ci muku mutunci aka daki mahaifiyar ki, daga nan ban hak'ura ba na sake dawowa da kaina na sake ci miki fuska akan kud'urina wanda Allah ya riga ya rubuta ke matar sace. Na sake turowa har gidan ku a kashe ki Rauda, kisa nayi k'okarin yi a kanki a karo na farko a rayuwata" ta fad'a da kuka sosai ta kasa cigaba da magana.

Dukkan su shiru sukayi kafin Mama ta cigaba da cewa, "Allah ya nuna min ikon sa akan aure ku akayi ba tare da na sani ba amma maimakon na hak'ura na d'auka haka k'addarata take sai na sake sakawa ana yi miki aikin da zaki bar duniya, har hijjabin ki an tura an samo a gidan ku dan ayi miki aiki a kashe ki amma Allah bai nufa ba duka ban hak'ura ba na skaa aka yiwa Asad aiki...." Sai ta sake fashewa da kuka Asad yace, "Dan Allah Mama ya isa haka duka komai ya wuce ki daina kuka Mama bana so" ya fad'a yana rik'e hannunta idanun sa sunji ja sosai.

Mama tace, "barni na fad'a, har abada bazan yafewa Sadiya ba dukkan abinda ya faru itace take shiryawa haka kawai bana iya tsallake maganarta komai tace sai nayi bana iya tsallakewa ban san meyasa ba. Nayi abubuwa da yawa akan ka da kuma matar ka Asad, inda ace nasan akwai idda a kanta da a lokacin da na saka ka sake ta bazan bari ta fita ba sai ka yanke igiyoyi biyun da suka rage ba, amma da yake Allah yana so ya nuna min in ya rubuta abu ban isa na goge ba sai gashi matar kace har yanzu ko a wannan yaci ace na fuskanci ikon Allah akan bayin sa."

"Duk wad'annan abubuwan da nayi miki keda iyayen ki baki rike shi ba kika tura min anniyata nazo har gidan ku neman alfarma maman ki ta tashe ki kika raka ni inda na samowa Asad da mahaifin sa da kuma Hydar, a kan hanyar dawowa akaso kashe ni kika cece rayuwata. Ban sani ba ashe kece kika kawo silar samuwar lafiyar mai martaba, tabbas kin turo min aniyata gata nan kuma ina gani tunda gani a zaune babu lafiya y'ay'ana biyu dukka sun zama y'an ta'adda. Ki yafe min Rauda dan Allah iya hakkin ki bazai barni na zauna lafiya ba dan nasan nayi miki abinda babu wanda ya tab'a yi miki shi a duniyar nan."

Rauda hawaye t??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ake yi ta girgiza kai tace, "Babu komai Mama ni komai ya wuce a wajena kin wuce neman alfarma a gare ni, ki yafe min in na tab'a b'ata miki rai nima." Mama tace, "Baki tab'a ba Rauda ba kuma zaki tab'a ba, babban burina kice kin yafe min dan Allah." Rauda tace, "Na yafe Mama."

Mama tace, "Na gode Rauda Allah ya saka miki da alkhairi ya raba ki da abinda yake jikin ki lafiya." Ta kalli Asad tace, "Na dawo kanka banji kace ka yafe min ba Asad, kaga y'ar albarkar matar ka ta yafe min saura kai." Asad yace, "Mama baki min komai ba dan Allah ki daina fad'ar haka, in ma kinyi na yafe miki Mama."

"Na gode Asad, tabbas zaka cigaba da ganin sakamakon biyayya a rayuwar ka, Allah yayi maka albarka ya kare ka daga y'an uwanka masu nufin ka da sharri a duk inda kake." Aka amsa da amin kafin ya tashi tsaye ya tasar da Mama ya kaita har cikin d'aki yana rik'e da ita ta zauna ya bata maganin ta da kansa ta kwanta yace, "Ki huta Mamana, dan Allah ki daina saka damuwa a ranki ina tare dake har abada."

Hannun sa ta rik'e yana zaune a gefen ta a haka bacci ya d'auke ta. Sai da ya tabbatar baccin yayi nisa ya fito bai samu Rauda ba sai kannen Maman ya kalle su yace, "Mama dan Allah a kula da ita." Tace, "in sha Allah ranka ya dad'e zamuyi iya bakin k'okarin mu." Daga nan ya fita dan baiga Rauda ba.

Kai tsaye b'angaren mahaifin sa ya wuce ana take masa baya kamar d'azu shi kad'ai ya shiga ya same shi zaune dashi da Uncle yana shigowa Uncle sai ya tashi ya shiga ciki Asad ya zauna a k'asa yayi ahiru baice komai ba, Mai martaba yace, "Fuskar ka akwai damuwa a tare da ita Asad, meye yake faruwa?."

Asad yace, "Abba dan Allah ka yafewa Mama, wallahil azim tayi nadamar dukkan abinda ta aikata yanzu har Rauda ta saka aka kira ta bata ha?uri. Dan Allah ka yafe mata Abba." Abba yayi murmushi yace, "Dole tayi nadama ai koda bata so na dan in ma batayi ta tsakani da Allah na duniya ta koya mata hankali, taga ishara akan Sa'adatu da Yahuza da kuma Aliyu, ta tabbatar itama ta cigaba da tafiya a haka irin wannan k'arshen zatayi. Kaf ma'aikatan gidan nan basa son ta sabida halin ta na wula?anta na k'asa da ita a ganin ta Allah ya fifita ta akan su, y'ay'an ta har biyu dukkan su y'an ta'adda masu bak'ar zuciya da bak'ar aniya da mugun nufi ai dole tayi nadama. Duk taqamar ta akan y'ay'an da take yi sai gashi dukan su samun su ba alkhairi bane in aka cire ka, Rauda kuma da take magana badan ita ba da yanzu har yanzu ina kwance har yanzu ana cigaba da yi min allurar karya garkuwar jiki, silar kawun ta komai yazo k'arshe ba dole ta bata ha?uri?."

"Ka manta har kisa ta aika aje ayi a gidan su? Duk tunanin ta wannan ranar bazata zo ba sai gashi tazo tana kuka da idanunta. Ta gode Allah ma tana da bakin rok'on bata mutu tun farko abin ba da sai a lahira Allah ya tsayar dasu yayi musu hisabi. Taje ta raba ku da yarinyar nan duk a tunanin ta taci riba bata san Allah ya riga ya kulla alaqar ku ba."

Asad yayi shiru baice komai ba har sai da mai martaba ya gana fadn sa sannan yace, "Yafiya nake nema mata Abba, nasan duka ta aikata amma sabida Allah sabida ni Mai martaba ya yafewa Mamana iya abinda take ji a zuciyar ta ma ya ishe ta." Mai martaba ya sauke ajiuar zuciya yace, "ni na yafe mata ai; na yafewa Sa'adatu ma balle ita? Na yafewa Yahuza ma balle ita? Na yafewa dukka ire-iren su balle ita?. Taci darajar ka na yafe mata."

Asad yace, "Na gode mai martaba, Allah ya k'ara lafiya da nisan kwana." Ya amsa da amin kafin ya kalle shi yace, "Akwai gajiya a tare dakai yana dakyau kaje ka huta." Asad yace, "zan duba jikin Aliyu ne."
"Ana samun cigaba sosai a rashin lafiyar tasa, basai ka shiga ba tafi kaje ka huta. Shi kuma Hydar da yak'i saduda Allah zai mana maganin sa." Asad baice komai ba ya fito aka rufa maaa baya aka raka shi b'angaren sa kafin kowa ya watse.

Zai hau saman Rauda zata sakko idanun ta yayi ja alamun kuka tayi ta dawo da baya ta bashi hanya ya wuce bata ce komai ba? ta sauka ta fita ya bita da kallo kafin ya wuce ciki shima.

? ? ?? Da daddare ta kawo masa abincin dinner har sama ta same shi zaune da k'ananun kaya masu laushi kalar milk yana aiki da laptop yayi shiru baka jin sautin komai sai na keyboard. Ajjiye masa abincin tayi ba tare da zatayi magana ba ta juya ya kashe laptop din yace, "Tsaya." Ba musu ta tsaya ta juyo tana kallon sa ya mik'e tsaye yazo kusa da ita yace, "Me kike ji dashi ne? Me kike d'aukar kanki?."

Rauda ta kalle shi itama fuskar ta kamar tasa fuskar a d'aure tace, "Abinda kake ji dashi nima shi nake ji dashi. In taqamar kai sarki ne ni matar sarki ce, in taqamar ka kai dan sarki ne nima sirikar sarki ce, in taqamar ka kai jikan sarki ne nima sirikar jikan sarki ce. Duk abinda kake ji dashi nima shi nake ji dashi" ta fad'a tana kallon sa shima ita yake kallo.

Kai yake girgizawa yana kallon ta kafin yace, "ba kece sarkin ba ashe matar sace?."
"Eh daidai nake da sarkin tunda nice matar sarkin!. Dan an kawo maka ni gidan nan sai ka dinga wula?anta ni kana yi min abinda kaga dama dan kaga kawai ina sharewa? In haushina kake ji nima ka sani haushi ka nake ji wallahi domin ta silar ka abubuwa da ya suka faru dani a rayuwata wanda bazan manta dasu ba har abada."

"Ta silar ka Ummana tayi min Allah ya isa" sai muryar ta ta soma rawa ta fara kuka tana fad'in, "Dukkan k'addara ta a kan kane duk abinda ya faru dani ta silar kane kaine ka jawo komai da baka shiga rayuwata ba da hakan bata faru ba. Ni banji haushin ka ba sai kai zaka dinga jin haushina kana share ni dan kawai kana taqama da wani abun kana ganin kamar power da kake dashi ne ya saka ni dawowa ko auren ka. To ba haka bane baza kayi min abu kuma ka fara fushi ba sannan ni na sauka k'asa ba bazai yu ba, a baya an dake ni an hana ni kuma amma a yanzu bazan lamunta ba wallahi, ina k'okarin sauke hakkin ka da yake kaina matsayin ka na mijina Allah yana gani in ka kula kanka in ma baka kula ba kanka" tana fad'a ta juya ta sauka ta barshi a wajan a tsaye yana kallon hanyar da tabi zuciyar sa na rawa sosai.



*Duk mulkin namiji bawan mace ne.*>???
[17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*089*

? ? ? ? ? Da kallo ya bita har ta sauka ya furzar da iska ya juya ya hard'e hannayen sa a k'irji ya runtse idanun sa. _Sudai mata duka halin su d'aya basa damuwa da damuwar ka kansu suka sani kawai_. Ya fad'a a zuciyar sa yana sauke numfashi ya zauna akan kujera yana jin zuciyar sa na bugawa.

Baya so kalaman ta suyi tasiri a ransa dan zasu b'ata masa rai ne hakan ya saka bai ma kalli abincin ba ya tashi ya barshi a wajan ya shiga d'aki a zuciyar sa yana aiyana dole ma gobe ya bar garin tunda Mama ta samu lafiya dole ya basu waje ya huta tunda ba son ganin sa zai basu waje tunda babu tausayi a zuciyar ta bata ganin yanayin da yake ciki take sake k'ara masa damuwa.

B'angaren Rauda a fusace ta shiga b'angaren ta ranta duk a b'ace haka take jinta sai girgiza kai take yi ita kad'ai komai ya tsaya mata. "Bashi kad'ai yake ji da kansa ba nima ina ji da kaina, ni mutum ce kamar shi wallahi bazan d'auki wula?ancin dana d'auka a baya ba" ta fad'a a bayyane tana dafe kanta tana zaune a gefen gado.

Sai kuma ta rasa me yake mata dad'i sai kawai ta mik'e ta nufi b'angaren Mama dan ta sake duba jikinta. A zaune ta same ta a falo sanye da hijjabi da carbi a hannunta tana ja ita da Suhaima tana b'are mata ayaba tana bata amma kafin ta cinye guda d'aya ma aiki ne.

Da sallama ta shiga Maman ta amsa ta saki murmushi tana kallon ta Rauda kuma ta sauke kanta k'asa ta zauna tace, "Barka da dare Mama."
"Barka dai Fulanin Asad, ina aka baro mai martaban kuma?." Jin yadda Mama tayi mata magana da barkwanci sai ta d'ago ta kalle ta sai taga tana ta murmushi ta sunkutar dakai k'asa tana murmushin itama.

"Nazo na sake duba jikin Mama ne kafin na kwanta." Mama taji dad'i har zuciyar ta tace, "Jiki Alhamdulillah, daman tarin hakki ne yayi min yawa yanzu kuma duk da kuka yafe sai nake jin ina ta samu lafiya." Rauda bata ce komai ba tayi shiru Suhaima ma batayi magana ba.

Mama tace, "Kije ki huta dare yanayi." Rauda ta mik'e tace, "A kwana lafiya." Daga haka ta juya ta fita tana ji a zuciyar ta badan Umma tace ba wallahi bazata zo ba ta yafe mata amma tana jin haushin ta.

Mama ta kalli Suhaima tace, "Raka ni b'angaren su Sa'adatu" ta fad'a tana mik'ewa Suhaima ma ta mik'e tace, "Mama bakya jin dad'in jikin ki fa." Mama tayi murmushi tace, "zan iya zuwa." Gaba Mama tayi Suhaima na binta a baya da jakadiyar ta har b'angaren Hajiya.

Mama ta manta rabon da ta shiga b'angaren ta hakan ya saka taga ya canja mata amma bata nuna ba hadiman Hajiya suka mik'e ana gaishe ta da Mama ta amsa kafin a sanar da Hajiya zuwan ta su shiga ciki. Tana ganin Mama ta mike tana fad'in, "Rabi'atu da kanki keda baki da lafiya?."

Mama ta zauna itama ta zauna tace, "Jiki Alhamdulillah na samu lafiya." Hajiya tace, "Haka muke fata." Mama ta kalle ta tace, "Nazo neman afuwa akan abubuwan da suka faru a baya wanda nasan na aikata a abubuwa da yawa wanda baau kamata ba, ayi ha?uri dani." Ba k'aramin Mamaki Hajiya tayi ba ta kalli Mama ta girgiza kai kana tace, "Haba babu komai mune mukayi laifi bake ba."

Mama tace, "Nima nayi."
"Amma ba kamar ni ba, nayi abubuwa da yawa a bayan idanun ku wanda baku sani ba, tuun ranar da aka haifi su Asad nake tsaye a kansu dan ganin dukkan su babu wanda za'a mora a cikin su har girman su. Adadin abubuwan da na aikata dan dakushe su bazasu irgu ba dole na nemi afuwar ki nima Rabi Asad ya yafe min saura ke." Mama tayi murmushi tace, "Duk abinda kuka aikata nice na jawo, halina ne ya jawo badan halina ba da duka baku aikata ba, da kun rik'e su tamkar y'ay'an ku amma nine na raba na nuna kuda su akwai banbanci."

Hajiya tace, "Duk da haka ai ke baki nufe mu da sharri ba mu kuwa fa?." Mama tayi murmushi tace, "haka ne, nidai na yafe ko meye ina fatan a yafe min nima." Hajiya tace, "Naji dad'in yafiyar ki nima kuma na yafe miki koma meye, Allah ya bawa Asad ikon cigaba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login