Showing 165001 words to 168000 words out of 216282 words

Chapter 56 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

akan Asad ne da y'an uwan sa amma banda Mai martaba da mahaifiyar sa" ta fad'a kanta a k'asa idanun ta na cikowa da kwalla.

Ta kuma cewa, "Tunda naji da kunne na yana niyar kashe ni naji komai ya fitar?daga cikin raina, a lokacin da ya saka a daki motar da nake ciki daga nan na sake tabbatar da cewa ramin mugunta kurarrare ne kuma rana d'aya ta b'arawo rana d'aya tak ta mai kaya. Naso ganin bayan Asad sai ban ga bayan sa ba wanda muke k'okarin ganin bayan wani tare dashi ashe nima yana k'ok'arin ganin nawa bayan. Na sanar da mai martaba komai abinda yake faruwa ko wanne hukunci da ya cancanci ayi min a shirye nake dana karb'e shi."

Falon yayi shiru babu wanda yake magana a cikin su sai mai martaba da yayi murmushi yana kallon su kafin yace, "Dukka shirin ku na sani Sa'adatu, keda Yazuha da wacce baku sani ba hatta Suhail d'in na sani. Ko Suhail?" Ya fad'a yana kallon Suhail da yake zaune a gefe ya tankwashe k'afar sa kansa a k'asa.

Murmushi Suhail yayi kawai baice komai ba kafin mai martaba ya kuma cewa, "Yazuha wacece master planer?." Waziri da ya dabarbarce ya fara zare idanun sa gumi yana keto masa kana kallon sa kasan yana cikin tashin hankali sosai ba kad'an ba, ganin ya kasa magana sai ya d'auke kansa ya kalli Asad da yake zaune yace, "Asad akwai magana a bakin ka, ka k'arasa warware abubuwan da suke faruwa dan mu sani."

Asad ya sauke numfashi ya kalli mutanen falon gabad'aya ya lumshe ido ya buWe cikin muryar sa mai taushi da kwantar da hankali yace, "Kamar yadda kuke d'auka Suhail yana cutar dani ba haka abun yake ba, duk wani shiri da kuke dan ganin bayana Suhail yana sanar dani ne yana kuma taimaka min dan ganin na tsira daga dukkan shirin ku shiyasa baku tab'a nasara ba domin kuwa kafin ku aiwatar na sani ni kuma na d'auki mataki. Yana amfani da kune yana jin sirrin ku da abinda kuke k'ullawa a kaina amma bai tab'a cutar dani ba" ya furta cikin muryar sa ta ko yaushe a tausashe yana kallon Waziri da Hajiya.

Hajiya tace, "kar ka amince da dad'in bakin Suhail wallahi dashi ake k'okarin ganin an kashe ka." Asad yayi murmushi yace, "a zahiri kenan, amma a bad'ini baya tare daku yana tare dani. Na amince da Suhail fiye da yadda ba amince da y'an uwana na jini."

Mai martaba yace, "kuna so kusan wacece master d'in da ku kanku baku Santa ba? Kuna so kusan wanda ya jefa ni a cikin rashin lafiya sabida son zuciyar sa?." Kowa ya zuba masa ido masu sunkuyar da kai duk suka sunkuyar da kai ganin hakan sai mai martaba yace, "ban san me zance bane, ban kuma san me zanyi ba. Rabi'atu ta cutar da y'ay'an ta dukkan su sabida son zuciyar ta da kuma burin da ta d'auka ta d'orawa zuciyar ta."

Nan ma falon yayi shiru sai kukan Mama da ya fara tashi tace, "Nasan nayi duk abinda akace nayi dan ganin y'ay'ana sun zama sune gaba a masarautar nan, amma ban tab'a yun?urin kashe wani ba, ban tab'a yun?urin ganin wani ya cutu ta dalilina ba."
"Har matar Asad Rauda?" Ya jefa mata tambayar yana kallon ta.

Kai ta sunkuyar k'asa ta kasa magana ganin hakan sa yace, "ki amsa mana, kince baki tab'a yun?urin kisa ba shine na tambaya har ita?." Nan ma shiru Mama tayi ta kasa amsawa sai hawaye da take tana sauke numfashi a hankali cikin tashin hankali.

Mai martaba ya kuma cewa, "Nasan baza ki amsa ba daman dan kin san kin aikata ba sau d'aya ba ba kuma sau biyu ba, ita kuma yarinyar tayi miki alkhairi ba sau d'aya ko biyu ba, domin ina so kowa yasan ta silar ta na samu lafiya har nake tafiya yau kuka ganni a zaune a gaban ku."

Asad ne ya kalle shi alamun mamaki yace, "Eh Asad, nasan kaima baka sani ba dan babu wanda ya sani daga ita sai Mubarak sai kuma Yayan mahaifiyar ta Baba Malam, ta silar sa da tata silar na samu lafiya. Ina so kusan duk dare sai anzo an kaini wajan sa yana min magani wanda nake jin dad'in sa sosai ba kad'an ba, duk cikin maganin da ake bani ban tab'a jin dad'in ko wanne ba sai nasa. akwai ranar na same ta a can gidan an kaini ita kuma Kawun nata ya kirata ta kawo ruwan da za'a bani magani a lokacin akwai allurar da ake min a hannu Mubarak ta nuna ta san allurar lokacin da suka je can Cairo nema mata lafiya ta nemi k'arin bayani a kanta an kuma tabbatar mata ana yiwa mutumnin da ba'a so ya motsa ne, kamar wanda za'a yiwa aiki ko kuma wanda ake som cutar dashi ta hanyar allurar" ya dakata da magana yana kallon yanayin fuskar kowa da yake wajan.

Mai martaba ya kuma cewa, "Nan take duk da dare ne ta kira likitan da ya sanar da ita a can ta d'auki hoton allurar ta tura masa ya tabbatar itace ya kuma turo mana maganin ta a lokacin ya kuma ce kar a sake yiwa wanda ake yiwa ita domin nan gaba zata kashe masa gab'obi ne dan bata sanar dashi nine ba, daga wannan lokacin aka daina yi min wannan allurar aka koma yi min wacce ta kasance maganin da take karya ta. Ta silar ta na samu lafiya ita da dangin ta domin badan ita ba da yanzu wata?ila ina kwance har yanzu."

Kowa yayi shiru babu wanda yake magana sai Suhaima tace, "Muma munje wajan sa ta silar ta Abba, domin munje ba sau biyu bama samun ganin sa sai da muka je har gidan su Mamata ta saka ta raka mu ya bamu magani lokacin da muke d'auka Aliyu Asad ne, mun karb'o masa magani mun kuma karb'o maka mun karb'owa Yaya Hydar ma. A hanyar mu ta dawowa akaso kashe Mama? badan tayi hanzarin janye Mama ba da yanzu Mama ta jima da rasa ranta. Itace ta cece Mama a wannan lokacin ta silar ta Mama take zaune yanzu badan haka ba da yanzu mota ta markade ta tuni.'

Mai martaba yace, "Ta yaya ta iya zuwa gidan su neman alfarma bayan tarin abubuwan da tayi musu a baya? Ta yaya ta iya had'a ido da y'ay'an gidan har ta iya shiga ciki?. Koda yake jiya ma taje cikin gidan nasu ta silar Mahaifiyar ta ta sake karb'owa Aliyu magani gashi har zaune ana magana dashi, ko ina izza da raina na k'asa da ita d'in suka tafi oho" ya fad'a yana kallon ta Mama ta runtse idanun ta.

Falon ya sake yin shiru babu wanda ya kuma magana a cikin su Asad ya kalli Rauda suka had'a ido sai tayi saurin d'auke idonta daga kallon sa gabanta yana fad'uwa sosai ita har yanzu bata tabbatar da cikin wanda yake jikinta ba.

"Aliyu yayi mulkin katagum na watannin da suka wuce, Asad ya kasance baya tare damu a yanayin da muke d'auka shine a tare damu Aliyu ne baya nan, Aliyu ya goge duk wata alamar da ake gane su da tsakanin sa da Asad hatta k'aramin yankan allurar da yake hannun Asad wanda babu wanda ya san dashi daga shi sai matar sa Aliyu yayi irin sa dashi ya yiwa matar sa barazana har ya sake ta a madadin Asad ita kuma ta amince. Ta hanyar azurfar hannun Asad tana nan yaji lokacin da yake fad'a akwai alamar shi kuma yayi amfani da wannan damar da ya dawo yaga a hannun da yake shima yayi irin sa. Asad ya dawo shi kuma sai ya koma muku Aliyu duk dan sabida ya aiwatar da komai cikin sauk'i duk da Aliyu yasan shine haka Jidda ma amma basu nuna ba duk tunanin su hankalin sa ya bar jikin sa, babu wanda yasan ba Aliyu bane daga shi sai Aliyun sai matar sa Jidda sai kuma y'an bayan fage."

Ya kalli su waziri yace, "Dashi kuke meeting d'in kashe shi, badan shi ba da yanzu mahaifiyar jidda ta kai ga kashe Rabi shine yayi maganin abun dan ya gani da jakadiyar ta Ladidi suke yin komai. Shi Jidda taso a kashe bata san yasan shirin ta ba dan Asad d'in yanzu bana da ba bane ba."

Ganin kowa ya kasa motsi sabida abinda suke ji kamar almara ya saka yace, "Lokaci yayi da ya kamata kusan wacece master sannan kuma su waye wad'anda nake kira y'an bayan fage."?

Ya kalli k'ofa yace, "A shigo min dashi." Nan take aka shigo da Hafiz duk an d'aure shi jikin sa duk ya b'aci haka fuskar sa tayi bak'i matuk'a sabida wahala. Umarni ya bawa wanda suka kawo shi da su koma suka koma suna godiya ya kalli kowa yaga kowa kallon Hafiz yake yi.

Mai martaba yace, "Nasan kowa yana mamakin ganin Hafiz, kowa yasan Hafiz da Asad abokai ne shine manager director a company sa, shine yake k'okarin kare shi daga masu son ganin bayan sa a zahiri kenan. Tsakanin sa da Suhail ba'a shiri a zahirance Hafiz yana nunawa Asad Suhail yana so ya cutar dashi ne shiyasa baya so ya ganshi a kusa dashi, amma a bad'ini shine yake k'okarin cutar da Asad shiyasa baya so yaga Suhail a kusa dashi. Suhail yayi kwantan b'auna dan cimma nasara a b'angaren kare lafiyar abokin sa na yarinta Asad. A yayin da Hafiz yayi kwantan b'auna ya cimma cutar da abokin sa na yarinta Asad."

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!" Aka fad'a baki aka fad'a gabad'aya ana kallon Hafiz. Mama da take kuka tace, "Hafiz! Hafiz kai da kanka?." Ya d'ago ya kalli Mama cikin muryar sa da ta d'an yi k'asa yace, "kar kayi mamaki mama, jin wad'anda zan ambata yanzu sai yafi jefa zuciyar ki cikin mamaki."

"Kenan yasan master planer?" Fulani Hajiya ta fad'a tana kallon sa. Yace, "Kwarai na Santa domin ita nake yiwa aiki, ku bakwa ganin ta ni kuma kai tsaye nake magana da ita, bama iya ita kad'ai ba hatta wanda suka bayan ta na sansu."
"Fad'a mana muji wacece" ta fad'a tana kallon sa. Yayi murmushi yace, "kun shirya jin wacece master planer?."

Mai martaba yace, "Fad'i abinda yake bakin ka kai tsaye." Ya kalle su dukkan su ya saukar da ido k'asa yace, "Duk wad'annan abubuwan da suke faruwa ba kowa ne yake shirya su ba face...........!"


Guess who? @&?>??=??
[17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*080*

? ? ? ? ? K'irjin kowa motsawa yake a cikin su burin su suji abinda Hafiz zai fad'a dukkan su sun zuba masa ido suna kallo hankali a tashe tsoro da al'ajabi ya bayyana k'arara akan fuskar su.? Hafiz ya sake yin shiru ya kalle su dukkan su yace, "Kuna tunanin wacece master planer..? Hmm abinda ya dace kuyi tunani shine waye master planer dai domin ba mace bace namiji ne."

Fulani Hajiya tace, "kar ka raina mana hankali mana, ta yaya zai kasance namiji bayan ni nasan macece." Hafiz yace, "murya kike ji amma kin tab'a ganin ta a zahiri?." Shiru tayi ta kalli waziri suka had'a ido ta dawo da kallon ta ga Hafiz tace, "Ban tab'a ba." Hafiz yace, "ta tab'a amincewa kunyi video call?."

Ta girgiza kai alamun a'a ya sauke numfashi yace, "Shiyasa nace miki namiji ne ba mace ba."
"To waye ka fad'a mana ka tsaya kana rainawa mutane hankali, ka fad'a way......."
"Hydar ne!" Ya katse Mama da ihuu yana kallon ta idanun sa a waje.

Dummmmm zuciyar kowa ta buga a wajan nan duk suka juya suka kalli Hydar da yake zaune kansa a k'asa tunda aka fara wannan abin baiyi magana ba kuma bai d'ago kansa ba har lokacin, mamaki kwance a fuskar su dukkan su Mama ta kalli Hydar ta kalli Hafiz tace, "Wanne Hydar d'in kake nufi?."

"Hydar da kika sani Mama, Hydar da yake tare dake a ko yaushe, hydar da yake kwanciya rashin lafiya, Hydar d'in Asad, Hydardai naki shi nake nufi" ya fad'a yana kallon ta itama kuma shi take kallo idanun ta a waje gabad'aya.

Suhaima ta kalli mahaifin su dan tana so tayi magana amma tana jin tsoro shima ya kalle ta yace, "kowa yana da ikon yin magana a wannan lokacin." Jin hakan ya saka Suhaima tace, "K'arya kake! Kwatankwacin wannan abinda aka lissafa Yaya Hydar bazai aikata shi ba. Kowa ya shaida son da Yaya Hydar yake yiwa Yaya Asad bazai cutar dashi ba, ko yaushe ciki bashi kariya yake taya zaka ce shine master planer?."

"Da kariyar yake amfani yake cutar dashi a ko yaushe, Hydar ya wuce tunanin ki yadda kuke kallon Aliyu mai wayo da makirci Hydar ya dame shi ya shanye" ya sake fad'a yana kallon Suhaima da itama shi take kallo fuskar ta ta jiqe da hawaye.? Fusata Mama tayi ta zabura ta mik'e ta tsinke Hafiz da mari ta nuna shi da yatsa tace, "In ka sake furta magana makamanciyar wannan a kan Hydar sai na saka anyi maka hukuncin da har ka mutu baza ka manta ba."

Hafiz yace, "Mama sai dai kiyi min duk abinda zakiyi amma bazan fasa fad'ar abinda yake gaskiya ba, duk wani tuggu da ake k'ullawa a gidan nan Hydar ne sila shine yake shirya komai duk su Waziri, Aliyu, Jidda da duk wani mai son ganin bayan Asad umarnin sa suke jira." Mama ta sake tsinke shi da mari ta juyo ta kalli mai martaba tace, "Taya mai martaba yana ji yana fad'ar kalamai mara sa dad'i akan Hydar zaiyi shiru" ta dawo da kallon ta ga Asad tace, "Baka ji me yake cewa bane ba Asad? Hydar d'inka fa yake jifa da wannan kalamai masara dad'in ji."

Asad ya d'ago ido ya kalle ta sai yayi murmushi yace, "Mama duk abinda yace ba K'arya yayi ba gaskiya ce. Duk wani abu da ya faru a gidan nan Hydar ne sila, shine ya shirya komai yake kuma bada umarni."

Mama tayi baya zata fad'i Suhaima tayi saurin tare ta suka zauna jikin ta yayi sanyi kamar wacce aka zarewa rai kanta yana sarawa kamar zai rabe gida biyu. Hafiz yace, "Duk wani abu da ake tunanin Suhail ne ya saka na cutar da Asad nine nayi ba Suhail ba, in Mama ta tuna lokacin da na same ta nace an zubawa Asad abu ya tsallaka yana ciwo ba wani ne yayi ba nine ina sane nake saka Suhail a ciki dan a ture shi gefe ni a amince dani dan tabbas Asad ya yarda da Suhail. Yadda ya amince dashi bai amince dani ba shiyasa nake jin zafi da d'acin hakan. Da ina aiki da Aliyu ne amma da na gano Hydar shine babbar giwar sai na koma tsagin sa badan komai ba sai dai abin duniya."

Hafiz ya sake cewa, "Duk son mulkin da Aliyu yake dashi Hydar ya fishi; iya taku shine ya saka yake nuna ko a jikin sa amma yafi kowa d'aga hankalin sa a kai. Ko Mama tasan da cewa gab da Asad zai dawo Hydar ya kwanta ciwo wannan ciwon bana gaskiya bane na shiri ne...? Yayi amfani da cutar da take damun sa ya kwanta ciwo ya aiwatar da dukkan abinda yake so hankalin kwance babu wanda ya kawo komai a ransa. Hydar yasan Aliyu ne yake mulki ba Asad ba sai kuma abinda yace masa yakeyi. Na fad'a muku abinda zai fi haka gigita ku..?" Ya fad'a yana kallon su dukkan su.

Ya cize baki yace, "Hydar shine silar kwanciya Abba ciwo, shine silar da dukkan gab'obin Abba suka daina motsawa. Yana sane tsarin sane yayi hakan da Mama ta dawo da Asad shi kuma ya aiwatar da duk abinda yake so, ya kuma tabbatar matuk'ar mai martaba yana da lafiya wani abun bazai kasance ba shiyasa na aikata abinda ya aikata ko nace yake kan aikatawa. Lokacin da Asad yana Cairo yana sane yak'i sanar dashi rashin lafiyar Abba ya tafi dashi Germany ya hana ko wanne likita ganin sa in ma sun duba shi da zarar sun fita zai masa allurar da ita Rauda ta bada maganin ta."

Ya kalli Aliyu yace, "A tunanin ka maganin da suka baka ka shafawa Asad a fatar hannun lokacin da ya dawo daga Cairo don yayi swapping layin sa a tunanin ka shine silar da ya saka ya manta da Mama? Hmm ba shine bane domin a abincin da yaci ni da kaina na karb'o maganin da aka zuba masa a ciki a wajan matsafan k'asar turkey. Nasa ne yayi aiki ba naka ba yana sane yayi hakan duk dan ya sake tunzura Mama da take ta dawo dashi. Waye ya fad'awa Mama inda Asad yake a Cairo? shine yayi hakan yana sane a wannan lokacin burin sa ya dawo."

"Aliyu kaima kana naka aikin a wannan lokacin amma aikin Hydar yafi naka k'arfi, kaine kaje gidan su Rauda ka sake ta amma kuma turawa a rushe musu gida ba kai ka yishi ba shine yayi badan komai ba dan ya sake tunzura tsanar Asad a zuciyar ta dan kar tayi marmarin sake waiwayar sa har abada; duk inda muka je ana fad'a mana akwai yuwar dawowar ta kuma barazana ce a gare mu, gashi kuwa daga dawowar tata komai yana bayyana." Hafiz ya kalli Hajiya yace, "kina ta kokwanton waye ya zuba guda a zogalen da kika bawa Asad ko? Ba kowa bane yayi Hydar ne, yana sane dan a jefa zargi a kanki a kawar da hankali daga shirin sa ya kuma jefa kin."

Ya sake kallon kowa na falon yace, "Zuwan Asad Germany ya takura sai an dawo da Abba a wannan tafiyar ya shirya canja Asad inda ya yiwa Aliyu zazzafar message ya tsara masa komai shi kuma ba tare da tunanin komai ba ya hau kan plan d'in ya zauna daman neman mafita yake yi. Duk wani likita da zaku gani a gidan nan indai Hydar ne ya kawo shi yana karya garkuwar jikin Abba ne ba lafiya yake samar masa ba, ya shirya komai nasa tsaf amfani yake da Aliyu so yake da zarar an haukatar dashi sai shi ya maye

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login