Showing 42001 words to 45000 words out of 216282 words

Chapter 15 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

jin zafi tana daurewa ne kawai. K'arewa d'akin kallo sai kuma taja tsaki hawayen da take rik'ewa suka sakko mata towel d'in na jikin ta take takawa har taje bakin k'ofa ta bud'e ta fito falon.

Babu kowa a falon ta wuce zuwa d'akin ta ta shiga yana nan yadda ta barshi ta saka kaya har lokacin kuka take bayan ta gama ta tayar da sallah har ta idar hawaye bai daina zuba daga idanun ta ba ta kwanta a kan sallayar tana cigaba da kuka. Taji motsin bud'e k'ofar amma bata motsa ba sabida haushin sa take ji bata so ta ganshi ko kad'an hakan ya saka tayi kamar bata ji shi ba.?


A hankali ya k'araso inda take kwance yana jiyo sautin kukan ta ta cikin hijjabin da yake jikin ta wanda ta b'oye kanta a ciki ya durk'usa ya saka hannayen sa duka biyun ya d'ago ta zaune tayi luuuu zata koma ya rik'o ta yayi mata garkuwa da jikin sa ya zauna shima kamar yadda ta zauna gabad'aya tana kwance a jikin sa.

? ? ?? Shiru ya sake ratsa tsakanin su bata daina kuka ba shima kuma baice komai ba ya zubawa waje d'aya ido yana kallo amma ya rasa ta inda zai fara fad'a mata abinda yake zuciyar sa game da ita, ya rasa ta hanyar da zai bi ya fayyace mata sirrin zuciyar sa da yadda yake jinta a jikin sa ko zata fahimta ta daina wannan kukan. Ya kalle ta sai ya d'ago da kanta yaga kukan take har lokacin bakin ta har rawa yake yi ya matsa da fuskar sa kusa da tata yana kallon ta, tana jin hakan a zuciyar ta tasan kallon ta yake amma duk da hakan bai hana ta daina zubar da hawaye ba.

A hankali ya had'e bakin sa da nata yana kissing a hankali a nutse babu tashin hankali, hawayen bai daina zuba ba hakan ya saka shi rik'e kanta da hannun sa guda biyu yana kissing yana kallon fuskar ta yana so yaga hawayen sun daina sakkowa. Bai d'auki lokaci mai tsaho ba cak kukan nata ya tsaya sai hawayen da suke kan fuskar ta tayi shiru tana fuskantar yanayin da ya kawo mata ziyara a karo na biyu, wani abu take ji a jikinta wanda baza ta iya jure masa ba hakan ya saka taja baya duk da ya rik'e kanta amma hakan bai tana ta zare bakin ta daga cikin nasa ba.

Bai hana ta ba daman abinda yake so ta daina ta daina d'in ta kifa kanta a guiwar ta haka kawaj take jin wani abu mai kama da kunya yana zaga jikinta lokaci d'aya, tashi yayi ya fita jim kad'an ya dawo ya same ta a yadda take ya ajjiye abinda ya shigo dashi ya a inda ya tashi zauna yace, "kici abinci then Kisha magani."


K'in d'ago kanta tayi ya saka hannu da niyar d'ago ta ta sake cusa kanta ciki sai ya k'yaleta ya jingina da gadon kamar yadda take yi ya zaro hannun ta d'aya daga cikin jikin ta ya rik'e yace, "I'm sorry!." Yadda ya furta kalmar sorry d'in ji tayi kamar an soka mata wani abu a zuciyar ta taja numfashi amma bata d'ago ba ya kuma cewa, "Amsar tambayar ki ta jiya ita na baki a jiyan, in baki amince u can cheek your phone, but kici abinci" ya fad'a a sanyaye yana jawo abincin ya d'auki tea d'in da ya had'a mata yana jiran ta d'ago kanta.

Bata d'ago ba har lokacin ya zuba mata ido yana kallo jin shiru babu motsin sa sai ta d'auka baya wajan ta d'ago a hankali sai suka had'a ido ta firgita zata mayar da kanta yayi saurin rik'e kan nata yace, "Please" ya furta yana kai cup d'in bakin ta.

Ido ta lumshe tak'i bud'e bakin shi kuma yak'i janye cup d'in, a hankali ta bud'e bakinta ya bata tea d'in ciki sai tayi saurin dawo dashi jin zafi hankalin sa ya tashi ya ajjiye na hannun sa yace, "I'm sorry ban yasan miki zafi ba, I hope bb damuwa?" Ya fad'a yana rik'o kanta ganin bakin ta a buWe har lokacin sai ya sake mayar da bakin sa cikin nata duk dan kar taji zafin shayin.

Mintina biyu ya sake kashewa kafin ya zame bakin sa ita kuma har lokacin idon ta yana kulle ya sake d'aukar tea d'in ya kai bakin ta ya bata tasha dan ya wuci. Sai da ta shanye tasss sannan ya ajjiye glass cup d'in ya mik'e tsaye.

? ? ? ? Tashi yayi ya d'auko wayar ya ajjiye mata kusa da ita ya fita, tana jin rufe k'ofar sa tayi tsaki ta buWe ido tace, "Iya abinda zai iya cemin kenan matsayina na wacce yayi disvirgin, ina so da k'auna a nan?. Allah ka bimin hakkina ba laifina bane laifin Baba ne badan shi ba da hakan bata faru ba" ta sake fad'a tana kuka sosai sai kuma taja wayar tata ta kunna nan tayi karo da notification ta danna taga godon message ta fara karantawa kamar haka.

? ? ? ? _Heey Muwaddaty!. nayo miki wannan sak'on ne ba dan komai sai dan na bayyana miki the kind of love i have for you, and the reason why i have gotten married to you is because i love you muwaddaty believe me or not wannan shine gaskiyar abin dake cikin zuciyata,na aure ki ne dan ina sonki badan na wulak'anta ki ba, ban tab'a son wata y'a duniya kamar yadda nake sonki ba, ina sonki tsakanin da Allah ba dan wani abu ba . It's my nature rashin yin magana Rauda bake kad'ai nake yiwa hakan ba, ina so na koya kodan na fad'a miki sirrin da yake raina game dake but a duk lokacin dana shirya wa hakan sai naji na kasa, ina so ki sani d'an adam baya iya canja halittar Allah ne yaso ya ganni a haka nima bawai yin kaina bane. Kince you don't deserve to be my wife which i don't no what makes you think of that, that's why na nuna miki ke kad'ai na amince da ita ta zama matata kuma ta san sirrina, ke ce mace ta farko dana tab'a having sex da ita. Nasan wannan kad'a ya isa tabbatar miki dake nake so na zauna bada wata ba, inda ace bana sonki bazan taba bari hakan ta kasance a tsakanin mu ba Raudaaa. I'll never forget what happened between us Muwaddaty kin bani abu mafi qima da daraja wanda ni Asad bazan taba mantawa dashi ba a rayuwata ta duniya, kece mace ta farko dana fara sani kamar yadda yake a wajan ki Nina mutum na farko da kika fara sani, you mean everything to me Muwaddaty zan iya yin komai because of you. Please muwaddaty i want you to stop thinking that i don't love, because it hurt me a lot. You're the first and last da zan so a rayuwata ina so ki sanya wannan acikin zuciyar ki._


? ? ? ? Wani irin yammm take ji a jikin ta hawayen idanun ta sun tsaya cak hannun ta na rawa ta sake yin scrolling ta sake ganin another one ta cigaba da karantawa,

_Ko wacce mace at her first night tana samun kalamai masu dad'i da kwantar da hankali but ta bangare na ba wannan because of my nature. A jiya Muwaddaty na zubar da hawaye najin haushin yanayina for the first time a rayuwata, ina sona nuna miki how much i care and how much i love you . I'm really sorry; na rashin Nuna kulawar da banyi ba akan, i promise to always be by your side duk runtse duk wuya, Sabida son da nake miki Muwaddaty I'm ready to face anythings for the sake of your love. You're my world wanda kaf duniyar nan ban tab'a jin wata a raina kamar ki ba, bazan barki ba in sha Allah muna tare ._

Bata san ta mik'e tsaye ba sabida zafafan kalaman da suke cikin rubutun sa sun saka ta mik'e bata sani ba, ba'a tab'a fad'a mata kalamai irin su ba tunda Allah ya kawo ta duniya hakan ya saka jikinta yake tsuma tana jin wani irin abu a jikin ta, sake scrolling tayi ta sake ganin cigaba,

? ? ?? _Yeah ni d'an sarki ne ta ko ina but kema matar d'an sarki ce ki daina tuna komai ni na ganki nace ina sonki. Muwaddaty da ban same ki ba ban san iya adadin abinda zai same ni ba ina jurewa ne kawai like i don't care about you amma deep inside my heart a ko yaushe kice maqale acikin ta. Finally na fad'a miki abinda yake raina i hope zaki goge duk wani tunani da kike a ranki ki zauna dani da zuciya d'aya, ina ji a jikina i can't live without u so please ki amince dani kar wani abun ya raba mu dake in hakan ya kasance ban san ya zanyi ba Muwaddaty. Thanks you for gave me the most important thing in your life, I really appreciate. And nayi alqwarin babu abinda zai faru ina tare dake bazan rabu dake ba ina fatan zaki amince. Kici abinci Kisha magani badan ni ba saboda Allah. I love u so much._

? ? ? Hawaye taji suna is sakkowa daga idanun ta wanda ta rasa dalilin zuwan su a lokacin da taje k'arshe message d'in nata, tana d'ago ido ta ganshi a tsaye yana kallon ta da murmushi a fuskar sa itama kallon sa take yi ta motsa sai yaga ta runtse ido ya k'araso da sauri ya bata hut hug ya rik'e ta very tight yana sauke sigh idanun sa a kulle. Kunnen ta ya kai bakin sa in low voice yace, "I love you Muwaddaty!." Sai da ta zabura yayi saurin sake rik'e ta kam a jikin sa itama ta rik'e shi tana jin wani abu na shiga jikin ta game dashi ya sake shiga jikin sa tana sauke numfashi.

Sun jima a haka kafin ya sassauta rikon da yayi mata ya d'ago da ita ya kalli face d'in ta su had'a ido tayi saurin kai idanun ta k'asa yace, "do u love me? And kin amince zaki zauna dani a haka?, I can't talk too much" ya fad'a yana fesa mata numfashi a fuskar ta ta lumshe ido ta sake mayar da kanta k'irjin sa ya kuma rungume ta tsam. Jikin ta yaji da zafi sosai ya d'ago ta ya k'arasar da ita kan gado ya zaunar da ita ya d'auki abincin a cikin bowl ya fara bata tana ci a hankali, kawar da kai tayi tak'i cin abinci ya kalle ta alamun lafiya tace, "bakina babu dad'i." "Sorry" ya furta yana cigaba da bata har taci rabin chips d'in ya ajjiye ya bata magani tasha ya sakko k'afar ta ya bud'e cream d'in maganin ta yana shafa mata a hankali yadda zata ji dad'in hakan.


Kallon sa kawai take yi zuciyar ta tana fad'a mata wai daman haka ya iya kalamai masu dad'i? Daman haka yake sonta ko kuwa dai duka dad'in baki ne? Daman haka ya iya kula da mace ko kuma duk salon yaudara ne?. Ina mulkin yake yake bata abinci da kansa har yana shafa mata magani?.

Bayan ya gama ya dawo kusa da ita ya zauna ta kalle shi sai ta d'auke kanta domin ita bawai ta gama amincewa dashi bane amma dai zata zuba ido taga iya gudun ruwan sa tunda babu mai bata amsar tambayoyin ta, yace, "Baki amsa ba."

Ta sunkuyar da kanta k'asa tayi murmushi kad'an tace, "Kunyar ka nake ji." Murmushi taki yayi mai sauti ko tace dariya ma yana girgiza kai ya d'ago da kanta yace, "Meye kunya?." Kwace kanta tayi ta sake kawar da idon ta wani wajan daban ta lura shi kam baya jin abinda take ji.

Ba tare da ta kalle shi ba tace, "in nace ina son ka zakayi da Maman ka? Kasan bata sona." Gaban sa yayi mugun fad'uwa kamar ta tsira masa allura ya d'auki wayar sa zai kirata amma sai ya kasa ya rasa me ma ya saka shi d'aukar wayar, ya dafe kansa ya d'ago ya kalli Rauda da take kallon sa yace, "wa nace zan kira ma?."
"Mama" ta bashi amsa tana kallon sa yayi saurin mayar da hankalin sa kan wayar amma ya kuma mantawa.

"Oh god!" Ya furta yana dafe kansa yayi shiru na wani lokaci kafin ya mik'a mata wayar yace, "kira min ita da sauri." Rauda mamaki ya kamata ta karb'i wayar tana dubawa taga sunan Mamana a jiki ta danna ta kira ta saka a speaker, kira d'aya biyu a??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ka d'auka daga can b'angaren tace, "Asad d'ina yau kaine ka kira ni? Ashe zaka iya mantawa dani ka tafi ka barni ka zab'i wata mace a kaina Asad?. Meyasa zakayi min haka bayan kace min ka barta tunda bana so?, kenan kafi sonta dani Asad?" A jere take maganar burin ta ta isar b masa da sak'on dake ranta.

? ? ? "Katse kiran Muwadda,disconnect it please!" Ya fad'a yana dafe kansa da duka hannayen sa Rauda ta bishi da kallo ganin ya gigice kamar ba shine yace a kira ba tace, "Prince Maman ce take magana fa." Cikin tsawa wacce bai tab'a yi mata ba yace, "I said disconnect!." Hannu na rawa Rauda ta katse kiran ta bishi da kallo hannun sa na rik'e da jijiyoyin kansa yana runtse ido yana bud'ewa.

Me yake faruwa? Ta tambayi kanta tana kallon sa cikin mamakin canjawar sa lokaci guda sai kuma taga yana sauke numfashi a hankali yana komawa normal kamar bashi ba.

Had'a ido sukayi da Rauda bayan ya dawo daidai ya sake kulle idanun sa ya sake kallon ta kana yace, "kina buk'atar hutu Muwaddaty, ki kwanta" ya fad'a yana kallon ta ta kalli agogo tace, "lokacin sallah yayi." Baice komai ba ya tashi har zai fita sai ya dawo ya tsuguna a gabanta ya tab'a wuyan ta yaji babu zafin sosai ya tab'a jijiyoyin kanta yaji suna harbawa alamun ciwon kai ya kalli cikin idon ta yace,"kanki yana ciwo."

Rauda ta sauke ido k'asa tace, "Na sha magani zai daina." Shiru yayi ya d'an kulle ido na wani lokaci ya bud'e kafin yace, "Bb abinda yake damun ki?." Kai ta d'aga alamun eh ya mik'e ya rik'e goshin ta yayi mata kiss ya juya ya fita.

Ta bishi da kallo tace, "ikon Allah! me yake faruwa dashi haka?." Babu mai bata amsa ta girgiza kai ta lallab'a ta tashi tayi alwala ta fito ta tayar da sallar la'asar. Tana idarwa kwanciya tayi bacci ya d'auke ta domin daman baccin take ji.

*&&&*

? ? ? ? Lokacin da Asad ya datse kiran Mama duk taji abinda ya faru ba komai ya d'aga mata hankali ba sai jin muryar Rauda tana magana, zagaye take a d'aki hankalin a tashe jikin ta har rawa yake sabida tashin hankali da tsoro da ya mamaye mata zuciyar ta. _katse kiran Muwadda_ abinda taji ya fad'a ya fad'o mata gaban ta ya fad'i ta maimaita kalmar, "Muwadda! da hausa yana nufin Qauna" a bayyane tana jin zuciyar ta na buguwa kamar zata fito daga k'irjin ta.

"Me hakan yake nufi kenan? Har sun samu kusancin da zai dinga kiran ta da wannan sunan ko me ake nufi?." Bazai yu ba wallail azim bazai yu ba!" Ta fad'a da d'aga murya tana d'aukar wayar hannun ta na rasa tana jin idanun ta yana kawo ruwa ganin kirikiri an raba ta da d'anta wanda take mutuwar so sama da komai. Malam ta dannawa waya ya d'auka kafin ma yyi magana tace, "Wai yarinyar nan wacece ita da baza'a kiya kashe ta ba?."

Tana fad'ar hakan ya gano bakin zaren yace, "Ranki ya dad'e bawai baza'a iya ba za'a iya; kawai dai abin ne yana da wahala sabida tunda bata gari aiki kuma za'ayi mai kyau sai an samo wani abu nata kamar riga ko d'ankwali ko gashin kanta, kinga samun su zaiyi wahala shiyasa."
Mama tace, "in aka samo ka tabbatar za'a kashe ta?."
"Tabbas zamu zama silar barin ta duniya."
"Za'a kawo maka zuwa dare a gobe nake so a aikata komai."
"An gama ranki ya dad'e" tana fad'a ta yanke kiran ta kira layin Mum.

Mum na d'auka kafin tayi magana tace, "Ta wacce hanya za'a bi a samo mana d'ankwalin kucakar can data asirce min d'ana?." Mum tayi shiru kafin tace, "abu ne mai wahala duk da baza'a rasa sauran kayan ta a gidan su ba amma shiga gidan a d'auko shine aiki."
"Zai yu ko bazai yu ba?" Mama ta fad'a a fusace. Mum tace, "Zai yu, ki bani daga nan zuwa dare" tana fad'ar hakan Mama ta yanke kiran ta koma gefe tana wuci.

? ? ? ?? B'angaren Mum tana katse kiran key ta d'auka na mota da hijjabi ta sauka k'asa har zata gota kitchen d'in ta sai taga y'ar aikinta ta juya tana aikin nama ta k'are mata kallo tace, "Safiya." Ta juyo tace, "Na'am Hajiya."
"Baki saka pad bane naga kayan ki sun b'aci da jini?." Gaban Safiyan ya fad'i tasan Mum bata san k'azanta tace, "Wallahi ban sani bane Hajiya." Mum tayi tsaki tace, "dallah wuce ki bawa mutane waje, abincin in baki dafa ba kar ki dafa in kuma kin dafa ku cinye iya ku kije ki sake wanka ki shirya kanki then kiyi mana wani abincin."

Safiya tace, "To Hajiya." Mum har ta wuce sai wani tunani ya fad'o mata ta dawo da baya tace, "Jeki ki saka ki canja rigar jikin kizo." Da sauri ta wuce Mum ta shiga kitchen d'in ta bud'e fridge ta d'auko kwalbar flavor ta k'arasa wajan naman ds take wanke ta d'aga naman taga jini ta tsiyaya a kwalbar tana rik'e dashi ta fito har Safiya ta fito ta kalle ta tace, "kifa shirya kar ki b'ata min mota."
"Na shirya" ta furta a sanyaye Mum tayi gaba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login