Showing 153001 words to 156000 words out of 216282 words

Chapter 52 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

"Lallai Asabe ni kike kallo kike fad'awa ban isa na aurar da Rahma ba, shikenan mu zuba nida ke kiga in ban aurar da ita d'in ba." Inna tace, "Oho dai, ni ba irin ka bace da son kud'i zai rufe min ido nakai y'ata inda zata wahala a dinga yi mata kallon matar cushe, wallahi bazata sab'uba bingida a ruwa." Baba ya mik'e yaja k'wafa ya ware muryar sa yace, "Ke Rahma!." Daga d'akin Rauda ta amsa ta fito jikin ta a sanyaye dan duk taji abinda ake cewa ta fito ta tsuguna tace, "Baba gani."

Baba ya kalle ta yace, "Anas ya nuna yana son ki zai aure ki madadin y'ar uwar ki Rauda kin amince ko a'a?." Shiru Rahma tayi ta kalli Inna ta suka had'a ido ta dawo da kallon ta ga Baba tayi shiru bata amsa ba. Baba yace, "Malama magana nake miki kina kallona, kin amince a d'aura auren ki sati mai zuwa?."

Rahma ta sunkuyar da kai k'asa tace, "Baba a bani lokaci nayi magana da Inna ta."
"Babu lokacin da za'a baki malama, ki fad'i abinda yake ranki bamu da lokacin da za'a baki har kiyi magana." Rahma tayi shiru bata ce komai ba Inna tace, "Matuk'ar bata amince ba wallahi sai dai ka bashi Ummulkhairi amma badai Rahma ba, bazan lamunci auren dole a kanta ba haka kawai nan gaba bazai goranta mata yace ba ita yake so ba bashi ita akayi." Shiru Baba yayi yana kallon Inna yadda take fad'ar magana kamar ba shine yake mata magana ba yaja k'wafa ya fita baice komai ba.

"Jeka, wallahi bazan amince ayi mata abinda aka yiwa Rauda ba gashi ana ta samun matsala har yanzu bamu da tabbacin da gaske akwai auren a kanta ko babu ga ciki kuma. Ina! ni wallahi bazan amince ba, ke Rahma tashi muje" ta fad'a tana kallon Rahma kafin ta fita itama tabi bayan ta. Murmushi Umma kawai tayi dan bata da ta cewa dan ta lura hak'urin ta shine yamr cutar da ita wani lokacin ya zama dole ita ta dage akan sai an tabbatar da auren Asad a kan Rauda in ba haka ba itama bazata koma masa ba.

*&&&*

? ? ? ?? Haka ya kwana babu walwala a tare dashi tunda yayi sallar asuba bai kwanta ba yana zaune yana lazumi har gari yayi haske sannan ya fara karatu bayan ya kammala yayi wanka ya shirya cikin shigar manyan sarakai yayi nad'in malamai akan hular da ya saka shigar ta amshe shi sosai ya sauko zuwa k'asa.

Falon shiru babu kowa yana bin wajan da kallo yana tuna inda Rauda ta zauna jiya kafin ya janye idanun sa daga kallon wajan ya zauna a kan kujera ya d'auko waya yana dannawa, ajjiye wayar yayi a gefe ba jimawa aka danna door bell ta jikin k'ofar cikin maganar sa mai d'auke da isa da k'asaita yace, "Shigo."

Da sallama ya shigo jikin sa har rawa yake yi ya zube a k'asa yana fad'in, "Barka da safiya Sarkin sarakuna, barka da tashi farar atafa, barka da fito taurarin sama sha ado. Allah ya k'arawa Sarki lafiya da tsahon rai, Allah ya k'arawa mai martaba lafiya yayi rik'o da hannun Fulani mai babban d'aki. Ranka ya dad'e" ya fad'a yana yi masa jinjina cikin girmamawa.

Asad ya sauke numfashi a hankali ya amsa da amin kafin yace, "Sarkin mota." Jikin sa har rawa yake yace, "Ranka ya dad'e."
"Kasan meyasa na zab'e ka a zaman gidan nan?."
"Ban sani ba Ranka ya dad'e."
"Sabida kana da amana, tun lokacin Abba na shaida hakan a tare dakai" yayi shiru kafin yace, "Bana son kowa yasan ina garin nan, bana so kowa yasan da abinda yake faruwa a gidan nan kana jina?."

"Ina sauraron mai martaba, in sha Allah mai martaba bazai same ni da cin amana ba, zan ri?e amanar mai martaba daga nan har na bar duniya." Kai Asad ya d'aga yayi shiru na wani lokacin kafin yayi masa alama da hannu da ya tashi yayi masa sallama ya fita da sauri.

Numfashi Asad ya fitar ya kalli sama yana kallon adon da aka yiwa rufin d'akin yana tunani, yana so Rauda ta dawo rayuwar sa a wannan tsaka mai wuyar da yake ciki ko zai samu sassaucin abinda yake ji a ransa amma kuma yana so ya bata hutu dan yasan akan gaskiyar ta take shima akan tasa gaskiyar yake. Hannun sa ya d'ora a kan cikin sa yunwa yake ji sosai amma baya tunanin zai iya cin wani abun da bashi da wannan nutsuwar ko kad'an.

Ido ya sauke daga k'asa wayar sa yaga tana k'ara ganin mai kiran sai yaja k'aramin tsaki ya d'auke kansa sunan Jidda ya fad'o masa a zuciyar sa, runtse ido yayi zuciyar sa na bugawa ya mik'e ya fita daga falon zuwa harabar gidan, zaga gidan kawai yake yi shi kad'ai yana takawa har ya gaji ya sake komawa ciki ya zauna ya fara aiki a laptop.

*&&&*

"Sau nawa zan fad'a nace maka Aliyu bazai mana aikin komai ba gabad'aya ya canja dabi'ar sa mu nemi wani ya bawa Asad wannan maganin da yanzu mun wuce wajan" Hajiya ta fad'a tana kallon Waziri da shima ita yake kallo yace, "Kwarai da gaske maganar ki haka take, gashi ya kasa yin komai har kawo yanzu. Wasa da hankali yake mana ya mayar damu tamkar ball ta ko ina buga mu yake yi son ransa, muma zamu buga shi son ranmu kuwa."

"Shawara ya kamata a canja a sakawa Asad layar nan ya haukace kowa ya huta dan lokaci yana tafiya komai sake canjawa yake, matar Asad indai ta haihu komai ya riga da ya lalace dole mu san abinda za'ayi kafin hakan ta faru dan mu ne a ruwa." Waziri ya girgiza kai cikin gamsuwa yace, "Hakan za'ayi, abinda kika ce gaskiya ne a cikin kwanakin nan Asad zai sauka daga mulkin nan, k'arshen wahalar mu tazo lokacin nasara zai fara ina jin hakan a jikina wallahi."

Ta girgiza kai tace, "Ina jin hakan a jikina nima." Kai ya girgiza shima kafin su rabu kowa ya kama gaban sa zuciyar kowa cike da kwarin guiwar samun nasaraa karo na babu adadi.
[17/12, 10:42 pm] Nafisat Alwasa: *Arewabooks@nanahaleema11*
*075*

? ? ? ? ?? A kwance yake a mik'e yana jan numfashi dak'yar hannun sa dafe da kansa yana juya kai da alama ciwon da kan yake yi masa ba d'an kad'an bane. Numfashin sa dak'yar yake sauka sabida ciwo ya rame lokaci d'aya yayi bak'i kansa ya taru da gashi haka fuskar sa kamar bashi ba.

A zaune Mama take a gefen sa rik'e da hannun sa jikin ta yayi sanyi sosai ta kalli Hydar da yake tsaye shima tace, "Yaushe ne tafiyar taku ne? Kullum jikin sa sake gaba yake yi ya koma kamar bashi ba." Hydar yace, "an jima jirgin mu zai tashi zuwa India, amma ni Mama jikin Asad sai nake ganin kamar bana asibiti bane ba." Mama hawaye take ta dafe kanta tace, "Ban san me zance ba Hydar, mahaifin ku yace ciwon sa bana asibiti bane amma yak'i mayar da hankali a nema masa magani, dan Allah laifina sai ya shafi Asad? Duk soyayyar da yake yiwa Asad ace yana kwance a haka Abban ku baiyi komai ba kamar ma bai damu ba. Na shiga uku ni Rabi'a komai sake lalace min yake yi" ta fad'a tana sake dafe kanta da hannayen ta duka biyu.

Hydar yace, "Za'a tafi India tunda kina so aje can sai muje in sha Allah zai samu lafiya." Hydar ya kalli Asad da yake kwance sai yaga kamar magana yake yi ya sunkuya da kunnen sa yana sauraron abinda Asad d'in yake cewa yaji yana fad'in, "Aliyu, Mama Aliyu."

Hudar ya dago yace, "Mama Aliyu yake kira fa." Mama tace, "Wai ina yake tafiya ne? D'an uwan sa yana kwance babu lafiya amma shi yana can yawon duniya da y'an matan sa." Hydar yace, "Kiyi hak'uri Mama. Ina Jidda matar sa?." Mama ta dafe kanta bata bashi amsa ba dan bata san me zata ce ba.

Kamar wacce ta tuna wani abu? sai ta mik'e tace, "Kafin ku tafi India akwai wajan wani malami da nake so naje na karb'o masa magani, maganin sa yayi tasiri sosai a kwanakin baya ka jira ni" ta fad'a tana fita ta sauka ta nufi b'angaren ta. Bata jira Suhaima ba ta nemi driver ya d'auke ta bai wuce ko ina da ita ba kai tsaye gidan su Rauda ta nufa.

Dawowar Rauda kenan daga Bauchi tana zaune kamar ko yaushe jikinta a sanyaye ta rame sosai sai hasken ciki da tayi dan a lokacin cikin ta yayi wata d'aya harda kwanaki. Kasancewar bata laulayi baza ka fahimci ma ciki ne da ita ba sai ka sani. Umma na zaune kusa da ita gidan babu kowa duk an watse daga su sai su kamar ba shine akayi taro ba.

Sallama sukaji anyi an shigo falon Umma ta kalli wacce ta shigo tare da amsawa, Rauda bata juya ba tana zaune hannun ta rik'e da ruwa wanda tasha ta rage ta rik'e a hannu bata kalli wacce ta shigo ba. Mama da take tsaye Umma ta kalle ta tace, "Bismillah ki zauna mana." Jikin Mama a sanyaye ta zauna ta kalli Umma tace, "barka da gida." Umma tace, "Yauwa sannu da zuwa" Umma ta fad'a da mamaki ganin yadda tayi magana kamar ba ita ba harda murmushi.

Kallon Rauda tayi har lokacin bata san wanda ta shigo ba ta kalli Umma sai taji mugun nauyi ya danne mata k'irji ta sunkuyar da kanta k'asa a karo na farko da tayi hakan ga wank kafin ta d'ago ta sake kallon Umma tace, "Bata da lafiya ne?" Ta fad'a tana nuna mata Rauda. Umma tayi mata wani irin kallo kafin ta tab'e baki tace, "Eh bata jin dad'i." Mama tace, "Allah ya k'ara lafiya."

"Amin" Umma ta amsa a tak'aice tayi shiru bata sake magana ba dan so take taji da me tazo kuma. Mama ta had'd'iye yawu dak'yar tace, "Alfar......" Sai ta kasa furta alfarma tayi shiru dan kalmar bata zauna a bakinta ba dan ba fadar ta take yi ba ta sake bud'e baki dak'yar, "Nazo neman alfarmar sake ganin Malam a karo na uku." Umma ta numfasa tace, "To ai ba'a gidan nan yake ba ko kin manta ne?." Mama ta girgiza kai tace, "Ban manta ba, iso nake so ayi min kamar wancan lokacin, ina son ganin sa da gaggawa ne."

Umma tace, "Ai tunda kun gana wancan lokacin in kikayi masa bayani zai gane ki zai baki lokacin da zaki same shi." Mama a tausahe tace, "emergency nake son ganin sa, wanda zaiyi amfani da maganin India zai wuce anjima kad'an." Umma ta girgiza kai ta sauke numfashi tace, "To ga gidan namu shiru babu kowa balle a raka ki, sai dai in a neme shi a waya in ya bada dama sai kije ki ganshi." Mama ta girgiza kai tace, "Na gode."

Umma ta d'auki wayar ta a gabanta ta kira Baba malam a waya ta katse bai d'auka ba ta sake kira a nan ya d'auka bayan sun gaisa ta sanar dashi dalilin kiran ya bata amsa sukayi sallama ta kashe ta kalli Mama tace, "Yace ganin sa yau bazai yu ba gaskiya, sai dai ki bari zuwa gobe in Allah ya nuna mana." Mama kamar zata zubar da hawaye ta kalli Umma muryar ta har rawa take yi tace, "Ina so na ganshi a yau d'in matsalar da take tare dani a yanzu har tafi ta baya." Umma tace, "To ga abinda yace ban san me zan miki bayan wannan ba."

Mama tace, "a nema min alfarma a wajan sa dan Allah. Maganin sa yayi min tasiri matuk'a a kwanakin baya yanzu matsalar da Asad yake ciki har tafi wancan, dan Allah ki sake masa magana" Mama ta fad'a kamar da alama ta manta da talaka kamar Umma take magana jin yadda take karyar da murya baza ka d'auka ita bace ba, kana jin maganar ta kasan tabbas akwai damuwa sosai a tare da ita.

Ambatar Asad da Mama tayi sai gaban Umma ya yanke ya fad'i amma sai ta jure bata nuna ba tace, "To ya kike so nayi miki? Nayi iya abinda zan iya tunda yace haka babu damar ganin naki ne a yau." Mama ta sauke numfashi jikin ta duk yayi sanyi ta kasa furta komai domin bata san me zata ce ba, duka burin ta akan maganin sane gashi bazata samu ba.

K'arar wayar Umma ya saka Umma ta kalli wayar ganin mai kiran sai ta d'auka ta saka a kunne tayi magana kafin ta kashe ta kalli Mama tace, "Yace kije nan da mintina ashirin, kika wuce haka baza ki same shi ba." Nan take fuskar Mama ta washe farin ciki ya bayyana tace, "Yanzu kuwa zanje. Na gode sosai" ta mik'e tsaye ta kalli Rauda nan take sai gaban ta ya fad'i sosai amma bata nuna hakan ba tace, "Allah ya baki lafiya."

Har lokacin bata kalle ta ba Mama ta fita zuciyar ta cikin farin ciki amma wani b'angaren na zuciyar ta mamakin kanta take yau itace ya nemi alfarma wajan k'ananun mutane kamar su Umma har tana had'a su da Allah. Tana fita Umma ta kalli Rauda tace, "Ke Rauda sai naji tace Asad ne babu lafiya, kenan wanda yake tare dake waye?." Nan take gaban Rauda ya buga ta d'ago ta kalli Umma itama ita take kallo ido cikin ido ta had'd'iye yawu tana kallon Umma.

Umma tace, "Naji tace shine babu lafiya da alama jikin yayi zafi kuma ciwon duk yadda akayi bana asibiti bane ba duba da yadda ta tashi hankalin ta har take had'ani da Allah, kenan bayan ya daina zuwa wajan ki ya fara rashin lafiya ko kuma daman ba shi bane yake tare dake? Nifa jikina ya bani k'anin sane a tare dake bashi ba Rauda" Umma ta fad'a cikin tashin hankali tana kallon Rauda.

Dumm gaban Rauda ya buga ta zaro idanu waje ta kasa magana ta rasa me zata ce tana kallon Umma itama cikin tsananin tsoro, Umma tace, "Bara baban ki yazo yana dakyau a bincika dakyau zuwan babar sa gidan nan ya saka ni a rud'ani, tunanina yana bani bashi ne a tare dake ba Aliyu ne." Rauda tayi shiru tana sauke numfashi hankalin ta har yafi na Umma tashi bata da kuzarin da zata nuna ne.

Umma ta kuma cewa, "in kuma Asad din ne kenan bashi da lafiya? Babar sa bata san har yanzu da auren sa a tare dake ba kenan kome?. Tabd'ijam gaskiya akwai sauran rina a kaba." Ita dai Rauda shiru tayi amma yadda gaban ta yake fad'uwa Allah kad'ai yasan abinda take ji a zuciyar ta.

Tashi tayi ta shiga d'aki kafin ta zauna wayar ta ta fara ihu ta kalli wayar taga Anty Ramla a kai sai ta samu kanta da yin murmushi har cikin zuciyarta ta samu waje ta zauna ta d'auki wayar ta saka a kunne, daga can b'angaren tace, "Amarsu ta ango, amarya kin sha khamshi." Y'ar dariya Rauda tayi kad'an kafin tace, "Ina kwana Anty."

"Kin tashi lafiya Amarya? Ya kwanan amarci?." Rauda bata amsa ba sai tace, "Ina Dr fatan yana lafiya?."
"Lafiya lau Rauda. Munyi miki laifi bamu shigo Nigeria bikin ki ba ko?. Wallahi Dr ne aiki ya masa yawa a asibiti ni kuma exams muke shiyasa baki ganmu ba amma dan Allah kiyi hak'uri, ki bawa Umma hak'uri zamu zo takanas dan ke."

Rauda tayi murmushi tace, "Babu komai Anty meye na bada hak'uri dan Allah?." Ramla tace, "Ai dole na baki hak'uri duk yadda muke dake ace ban zo bikin ki ba ai babu dad'i." Rauda tayi murmushi tace, "Wallahi babu komai." Ramla tace, "To na gode da kika karb'i uzurina amarya" ta fad'a da niyar zolaya.

Rauda murmushi ta sake yi kamar tana gabanta daga nan suka cigaba da hira kafin suyi sallama ta kashe wayar ta ajjiye a kan gado nan take kuma sai annurin fuskar tata ya d'auke ta lumshe idanun ta tana jin duniyar gabad'aya tana juya Mata komai yayi mata zafi kanta ya cushe. K'arar wayar tata ta sake ji ta d'ago taga sunan Rahma yana yawo akai nan take gaban ta yayi mugun fad'uwa kamar ta share sai kuma ta fasa ta d'auki wayar ta saka a kunne tace, "Asslamu alaikum."

Daga can b'angaren Rahma tace, "Anty Rauda ashe kin dawo shine baki zo ba." Rauda tace, "Rahma kin san yanayin jikina ba lafiya ce dani ba." Rahma tace, "Haka ne, amma dai ya kamata ace kinzo." Ta sauke numfashi tace, "To zanzo in sha Allah. Amma ban ce ga rana ba zaki ganni dai kawai."
"To ina nan ina jiran ki. Ya jikin?."
"Alhamdulillah."
"Kiyi hak'uri Anty Rauda."
"Hak'uri name Rahma?."
"Na komai ma."

Rauda tayi murmushi tace, "to nayi akan komai d'in, bacci nake ji Rahma sai anjima mayi magana ko a whatsapp." Rahma tace, "shikenan sai anjima." ta fad'a tana yanke wayar ta ajjiye tana sauke numfashi k'irjin ta yana bugawa. Wai jinin ta Rahma ce matar Anas saurayin ta wanda suka jima tare suke burin yin aure ashe Allah bai rubuta ita zata aure shi ba ita ba duk wannan tsahon lokacin mijin Rahma ne ba mijin ta ba.

Hawayen da take rik'ewa suka fara zuba a bayyane tace, "Meye makomar rayuwata? Cikin da ban san uban sa ba.....;eh ban san baban saba Asad ne ko Aliyu ban sani ba" ta fashe da kuka mai sauti harda shashsheqa. Umma da take tsaye tana kallon ta sai zuciyar ta ta karye itama hawaye ya ciko idanun ta dan ita kanta yanzu zuciyar ta tafi bata tabbacin Aliyu ne a tare da ita ba Asad ba.

Da baya ta koma dan baza ta hanata kuka ba ta shiga nata d'akin ta goge hawayen idanun ta tace, "Meye amfanin mutum irin Malam? Meye ribar aure ????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
irin wannan, sabida kud'i kayi abinda ya saka jinin ka cikin wani yanayi wanda a shekaru ta yanayin ya girmi tunanin ta. Allah ka kawo mata mafita da sassauci" ta fad'a hawaye na sake sakko mata ta saka hannu ta share

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login