Showing 183001 words to 186000 words out of 216282 words

Chapter 62 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

Tabbaci nake baka akan cikin jikin matar ka sai ya zama babu shi dan in zan k'yale komai bazan k'yale cikin ba, ka shammace ni ban san za'ayi ciki da sauri haka ba dan ban bari an zo wajan ba. Duk d'auka nake har yanzu abin sautin ya daina d'aukar sauti ashe ya gyaru har amo yake fitarwa ba iya sauti ba" ya fad'a yana kallon sa shima shi yake kallo.

Hydar yace, "Ashe sitiyarin motar ya dawo da aiki yadda ya kamata na d'auka tunda Mama ta lalata shi bai dawo daidai ba ashe nine nake haukan banza tunda gashi harda ciki."

Asad ya sau ke numfashi yace, "Ko a mafarki kar ka d'auka wannan abinda kake fad'a zai kasance." Hydar ya hard'e hannu a k'irji yace, "to muyi deal mana, in na zubar da cikin ta me zaka bani? Ni kuma indai ban zubar da cikin ba ka saka a kashe ni."? Asad yace, "bani da lokacin da zan tsaya yin deal dakai Hydar, bana da lokacin da zan saurari shirmen ka mai kama da tatsuniya. In kayi nasara a kaina a kwanakin baya tabbas yanzu ni zanyi nasara a kanka."

Hydar ya murmusa yace, "Kana nan yadda na sanka confidence d'inka yana nan, to in ban tabbatar da shirina a kanka ba ai ba sunana AliyuHydar ba." Asad yace, "fitar min a mota." Hydar yace, "Daga na ambaci Rauda sai a kore ni daga mota? Ayi ha?uri tuba nake ranka ya dad'e ba wani abun nace zanyi da ita ba ai" ya fad'a yana yi masa jinjina kafin ya sake kyalkyalewa da dariya yace, "Zan fita Asad koda baka ce ba, amma ina so kasan zan dawo gare ka bazaka tab'a zama lafiya ba matuk'ar ina raye sai na raba ka da komai da ka mallaka ni na mallake shi ciki kuma harda matar ka da kake so. Zamu had'e nan bada jimawa ba, ina nan zuwa gare ka" yana gama fad'ar hakan ya fita daga motar ya shiga tasa motar yaja a guje.

A lokacin escorts d'in sa da Suhail suka dawo Suhail ya shiga motar uana fad'in, "Ranka ya dad'e fatan komai lafiya? Naga bindinga a hannun sa." Asad ya masa alama da su tafi kawai driver yaja motar kai tsaye gida suka wuce.

Shiru Asad yayi suna tafiya tunani yake yi ta ko ina Hydar ya gama gano lagon sa, ta ko wanne b'angare ya karance shi sosai shiyasa cutar dashi bazai yi wahala ba. Tambayar da yake yiwa kansa itace anya Hydar zai iya kashe shi? Yasan har yanzu Hydar yana sonsa anya zai iya kashe shi?. Bai gama nemo amsar tambayar ba suka iso cikin gidan kai tsaye b'angaren sa ya wuce.
Suhail yana bayan sa bayan sun shiga falon yace, "Suhail a tabbatar an sake k'ara tsaro a kaf gidan nan, inda babu camera ina so a saka" ya fad'a yana dafe kansa.

Suhail yace, "An gama ranka ya dad'e. Allah yaja zamanin ka Fulani Hajiya ce take neman izinin ganin ka." Asad ya sauke numfashi a wahale yace, "Suhail bana jin zan iya ganin kowa. Suhail na gaji sosai."
"To ranka ya dad'e sai a sanar da ita" ya fad'a yana juyawa zai koma.

"Tazo" ya fad'a a hankali Suhail ya amsa ya fita. Zama yayi a kan kujerar da take mallakin sa ba jimawa Hajiya ta shigo da kaf y'ay'anta mata da namiji ganin hakan sai ya mik'e tsaye suka k'araso yace, "Hajiya da an sanar dani da nazo da kaina."

Hajiya tace, "Mune ya kamata muzo da kan mu ranka ya dad'e." Zama yayi ya nuna musu waje su zauna duk suka zauna Hajiya tace, "Ranka ya dad'e nazo da kaina ne neman afuwa akan abubuwwan da suka faru a baya, shiyasa na tawo da duka iyalana dan su taya ni baka ha?uri da kuma neman yafiyar ka."
Asad yayi murmushi yace, "Dan Allah Hajiya a bar maganar nan ta riga ta wuce."
"A'a Asad bata wuce ba, an cutar dakai da yawa ko nace mun cutar dakai Asad. Nayi abubuwa a kan ganin bayan ka ni kaina ban san adadin su ba tun ba'a je ko ina ba na fara ganin sakayyar da Allah yayi maka akan Yahuza. Wallhi tun ranar da kazo duniya nake son ganin bayan ka Allah bai tab'a bani nasara ba. Ina had'a ka da kyawawan sunayen Allah kayi hak'uri ka yafe min abubuwan dukka da suka wuce" ta kalli y'ay'an ta tace, "Ku taya ni rok'on sa."

Babbar yayar su tace, "A madadin iyalan Hajiya muna neman afuwa abinda ya faru a baya ranka ya dad'e, abinda aka aikata wanda aka fad'a da wanda aka aikata ba a fad'a ba muna rok'on mai girma sarki da ya yafe mana mun yi alqwari in sha Allah hakan bazai sake faruwa ba."

Asad yayi murmushi yace, "Dan Allah ku daina wannan maganar bana son ji, komai ya wuce ban rik'e kowa a raina ba." Hajiya tace, "Da gaske mai martaba sarkin mu ya yafe min?."
"Na yafe duk da daman ban rik'e ki ba Hajiya. Ina miki kallon mahaifiyata." Zata fara godiya yace, "Dan Allah kar kice komai, uwa kike a gare ni bazan jure ganin kina zubar da hawaye ba. Komai ya wuce dan Allah a daina kuka."

Ba musu ta goge idanun ta tana murmushi ya kalli y'an uwan nasa gabad'aya dukkan su fuskar su a sake yace, "Ina rok'on ku dukkan ku in akwai abinda ya faru a baya wanda ba'a ji dad'in saba a yafe. Sannan ina so duk inda akaga wani abu ba daidai ba a ciki da wajen masarautar nan ayi hanzarin sanar dani."

Dukkan su da farin ciki suka amsa kafin suyi sallama duk su tafi shi kuma ya tashi ya wuce saman sa Suhail yana bayan sa. A falon Suhail ya tsaya shima yana tsaye yace, "Ranka ya dad'e Hydar fa barazana ne ga rayuwar mai martaba bai kamata a sake dashi ba."

Asad ya sauke numfashi yace, "kar ka damu babu abinda zai faru."
"Haka muke fata, a kwana lafiya" ya fad'a yana juyawa ya sauka shi kuma ya wuce bedroom d'in sa. D'aki ya shiga sai ya tsaya a jikin mudubi yana kallon kansa kafin ya runtse idanun sa yana jin d'aci a zuciyar sa.

_ni kuma in ban zubar da cikin jikinta ba na amince ka kashe ni._ kalaman Hydar suka fad'o masa ya cire rawanin kansa ya kalli wayar sa ya d'auka da niyar kiran ta sai kuma ya ajjiye yaja k'aramin tsaki ta ko wanne b'angare haushin ta yake ji a zuciyar sa shiyasa yayi banza da ita bai sake waiwayon ta ba har yau. _Yana dakyau ka neme ta kodan abinda Hydar yace._ Zuciyar sa ta fad'a masa ya runtse idanun sa a bayyane yace, "In sha Allah babu abinda zai faru da ita, ina tare da ita a ko yaushe."

Fuskar Mama ta fad'o masa sai ya d'auki wayar sa ya kira Suhaima tana d'auka yace, "Mama."
Suhaima tace, "Har yanzu bacci take." Datse kiran yayi ya kama k'ugun sa sosai kansa yake masa ciwo har jiri yake ji yana d'aukar sa. "Hasbunallahu wani'imal wakil" ya furta a bayyane yana zama a gefen gadon ya dafe kansa lokacin da Jidda ta saka a kashe shi har ya kamata tana waya ya fad'o masa.

Saurin kawar da tunanin yayi ya tashi ya shiga wanka. Wankan ma da ruwan magani ya yishi bayan ya fito ya shafa mai da magani ya fesa turare mai magani ya saka kaya wanda aka turara su da magani. Hannun sa ya d'ora a cikin sa baya jin yunwa ko kad'an gashi shidan yasan tun daren jiya bai sake cin komai ba.

_Wallahi na tsane ka bana qaunar ganin mazinaci._ kalaman Rauda suka fad'o masa abinda yaji a zuciyar sa sai da ya datse labban sa da hakorin sa ya runtse ido yana sauke numfashi zuciyar sa na rawa. Bai san adadin lokacin da ya d'auka a haka ba sai da dare yayi sosai ya sauko kai tsaye b'angaren mai martaba ya shiga.

Kamar yadda yayi tunani yana zaune akan sallaya ganin hakan sai ya koma ya shiga d'akin da Aliyu yake kwance. A zaune ya same shi shima a kan gado idanun sa a waje ya yaga rigar jikin sa yayi tagumi ya zubawa waje d'aya ido kamar mai kallon wani abun.

Ganin Asad ya shigo ya saka Aliyu zabura yana kallon sa har ya k'araso inda yake ya zauna ya dafa kafad'arsa yace, "Allah ya baka lafiya Aliyu." Kai Aliyu ya fara girgizawa yana fad'in,? "Ba sunana Aliyu ba sunana Asad, ni sarki ne ina hawa doki ana zagawa dani, ina zuwa na bawa yara y'an islamiyya allo a lokacin bikin sauka. Ka daina cemin Aliyu zan iyawa yin komai akan hakan."

Asad ya runtse idanun sa ya buWe yana kallon Aliyu cikin tausayin halin da yake ciki ya zuba masa ido kawai baiyi magana ba. K'arar buWe k'ofa yaji hakan ya saka shi ya juya ganin mahaifinsa sai ya mik'e tsaye har ya k'arasa ya dafa kafaWarsa sa yace, "me ya fito da kai a daren nan?." Asad ya nuna Aliyu yace, "hankalina yak'i kwanciya."

Mai martaba ya kalli Aliyu yace, "zai samu lafiya da iznin Allah shiyasa na zab'i a barshi a nan yana karb'ar magani." Asad ya girgiza kansa yace, "Abba jikin Mama ma babu dad'i." Numfashi ya sauke yace, "dole ta samu gigita da rud'ani a wannan yanayin da ake ciki amma itama zata samu lafiya."

Mai martaba ya kalle shi yace, "Zuciyar ka a wanke take Asad kyakykyawar zuciyar da kake da ita Allah bazai bawa kowa damar cutar da kai ba." Asad yyi shiru ya sunkuyar da kansa mai martaba yace, "Ka koma kaje ka huta gobe akwai zaman da zaka gabatar domin gyara mulkin ka. Bana son a sake samun matsala a wancan karon ma kaine ka bada dama ka dinga karb'ar duk abinda babar ka tazo dashi. A wannan karon bazai faru ba." Kai ya girgiza kai kafin yayi masa sallama ya wuce ya koma yana ji kamar ana tura shi in yana tafiya sabida jiri.

*&&&*

? ? ?? "Duk abinda kuka aikata yazo kunnena Sadiya, duk yadda kuke da Rabi'a ta d'auki aminci ta baki tun kuna makarantar secondary a Kano kuke tare amma ki rasa abinda zaki saka mata sai da cuta, cutar ma kuma wai kisa Sadiya? Yaushe kika zama y'ar ta'adda ban sani ba?" Daddy ya fad'a da alamun bacin rai a tare dashi yana kallon Mum.

Mum tana kuka sosai tace, "Ambassador ka tsaya nayi maka bayanin abinda ya faru, banyi hakan da....." dakatar da ita yayi ta hanyar fad'in, "Rufe min baki domin baki da wani kalami da zaki fad'a min na amince. Sabida tsabar son zuciyar ki aminiyar ki kike k'ok'arin kashewa bayan kin rabata da d'an da ta haifa sabida wani banza burin ki na iska. Kin d'ora y'arki a tafarkin zina da aure a kanta take zmaan fasiqanci da Yayan mijinta kuma duk kina sane kikayi shiru sabida cikar burin ki."

Mum tace, "Wallahi ban san ba Asad bane, bata fad'a min ba, ban san zaman fasiqanci sukeyi da Aliyu ba ka yarda dani."
"Babu abinda zaki fad'a na yarda dashi, kin cutar dani kin kuma cutar da kanki da rayuwar yarki. Baxan lamunta ba wallahi bazan iya cigaba da zama da mata irin ki ba, daga asibitin nan kar ki sake ki koma min gidana kije can ku k'arata dake da y'ar taki da kuma d'an shegen da ta haifar miki da aure a kanta, wannan bak'in zunubin bazai zauna a gidana ba domin wata rana kar fushin Allah ya shafe ni."

Hankalin Mum ya sake tashi ta zube a k'asa tace, "Kar kayi min haka Daddy wallahi duk abinda ya faru bada son raina ba ka tsaya nayi maka bayani."
"Ni na tsaya na saurare ki? Har abada bazan tsaya ba domin ban san me kika k'unso kike so ki kashe ba nima dan tunda kikayi yun?urin kashe Rabi baki duba alaqar ku babu wanda zaki bari a duniya. Ga takardar sakin y'arki nan an bani sai kije da ita ku k'arata ko babu komai tahiri ya kafu a kanta wanda baza'a manta dashi ba a duniya. Mace ta farko da tayi zina da yayan mijinta y'ar kice, mace ta farko da taso kashe mijin ta sabida karta rabu da yayan mijin nata y'ar kice, mace ta farko da sarki guda shugaban al'amma ya fara sakin ta. Kar ki sake ki dawo min gida bazan iya zama da dake da kuma y'arki ba" ya fad'a yana cilla mata takardar hannun sa.

Har ya juya zai tafi yaga Eman na kuka sosai ya damk'o hannunta yace, "muje kar kema ta lalata min ke da bak'ar zuciyar ta!" Ya fad'a yana jan Hannun Eman suka bar wajan tana kuka sosai Mum tana kuka.

#FitattuBiyar
#Nanahaleema
[17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*086*

? ? ? ? ?? Gabanta yayi mugun fad'uwa ganin da wanda suka had'a ido ta sauke ido k'asa bata motsa ba shi kuma bai daina kallon ta ba da alamun b'acin rai a tare dashi. Suhail ne ya fito daga motar ya bud'e mata baya da hannu ya mata alamar ta shiga kafin yace, "Ranki ya dad'e bismillah." Ba musu ta shiga ya kulle musu k'ofar ya tsaya a bakin motar ba tare da ya koma ba.

Shiru babu wanda yayi magana cikin su ita shi yake kallo cikin tsantsar b'acin rai da takaicin abinda ya gani, d'ago kai tayi ta kalle shi suka had'a ido ta sunkuyar dakai k'asa ta sosa kanta kad'an kana tace, "Barka da dare." Banza yayi mata yana kallon ta ba tare da ya bata amsa ba sai tamke fuska da yayi yana hararar ta.

Kusan mintina biyu suna haka kafin yace, "Daga ina kike?." Ta d'ago ta kalle shi ta shagwab'e fuska tace, "na rako Yaya Ummi titi."
"Da izinin wa?." A sama taji maganar ta d'ago ta kalle shi taga tamkar bai tab'a yin dariya ba a duniya sai taji tsoro ya mamaye mata zuciya tace, "Ba kowa."

Ya sauke numfashi ya jingina da kujerar yana kallon ta ji yake tamkar ya tsinka mata mari sabida yawan haushin ta da yake a cikin zuciyar sa, ya d'auki sacannin baice komai ba kafin yace, "Zaman kanki kike kenan?." Gajiya tayi da bashi amsa cikin k'osawa tayi tace, "A'a." Kai ya girgiza ya kalli titi kafin yace, "Shine kika tsaya bakin titi kina siyayyar banza da wofi?."

Kai ta kawar domin bazata bashi amsa ba itama sai dai yayi duk abinda zaiyi yadda yake jin haushin ta itama nasa haushin take ji sosai bai kuma isa ya juya ta ba, ganin ta juyar da kai bata bashi amsa ba itama ta d'aure fuskar ta sai ya share ta ransa ya sake b'aci bai kuma kallon ta ba ya kira number Suhail yana ganin kiran ya shigo motar kai tsaye gidan su Rauda aka nufa.

Babu wanda yake magana a lokacin da yake babu tafiya sosai lokaci d'aya akazo gidan su Rauda ya tsaya ya bud'e motar ya fita ya sake barin su. BuWe motar zatayi taji an saka lock ta koma ta zauna tana kallon gidan nasu da yake tarr da haske tamkar ba dare ba.

Mota ce ta tsaya a k'ofar gidan Rahma ta fito daga gaban motar Anas ya fito shima yana yi mata magana kafin Rahma ta shiga ciki ta barshi a wajan a tsaye. A tare Rauda da Asad suka kalli juna ta sake kallon Anas da yake taaye ta sauke numfashi kafin tace, "Ka BuWe min motar zan shiga gida."

In motar da suke ciki ta amsa tabbas shima ya amsa yayi mata bama ita yake kallo ba wani wajan yake kallo zuciyar sa kamar ana bulbula mata kalanzir ganin Anas a tsaye a k'ofar gidan su. Kamar tayi kuka sabida takaici tace, "Ka buWe min." Nan ma yyi mata banza ta kalle shi idanun ta ya taru da hawaye amma bama ita yake kallo gabad'aya.

Itama banza tayi ta juya hawaye ya sakko mata ta girgiza kai tana cize bakin ta dan tasan babu abinda zata iya, kusan minti biyu suna a haka kafin ta juyo ta kalle shi tace, "Ka bud'e zan shiga gida bacci nake ji" ta fad'a cikin muryar kuka tana kallon sa. Juyowa yayi ya kalle ta ya d'aga gira sama ya tab'e bakin sa ya sake mayar da kallon sa ga wajen gidan.

Ganin kiran mai martaba yana shigowa ya saka shi kallon ta yace, "In kika sake kika kula wancan sai ranki ya b'aci" ya fad'a yana danna lock d'in ya buWe ta fita daga motar bayan ta d'auki ledar kayan ta. Yana kallon ta har taje kusa da Anas d'in sai yaga tayi saurin shiga gida bata tsaya ba sai a sannan ya d'auke ido daga kan gidan Suhail ya shigo suka tafi bai san itama bata son had'a ido dashi dan kunyar sa take ji.

Akan hanyar su ta tafiya Suhail yace, "Ranka ya dad'e zan iya magana?."
"Uhum" ya furta yana danna wayar sa. Suhail yace, "ayi ha?uri zan shiga abinda bai shafe ni ba, amma ranka ya dad'e bai kamata a dinga barin fulani tana fita ita kad'ai ba, akwai tarin mak'iyan da suke nufin kawo mata hari ko a mutanen gari y'an unguwa akwai wanda baya qaunar ta yake neman hanyar cutar da ita, barin ta tana fita ita kad'ai akwai matsala. Allah ya taimake ka bawai zan koyawa mai martaba abinda zaiyi bane amma yana dakyau ace tana da personal driver wanda aka amince dashi before ta dawo gidan sarauta."

Asad yana jinsa yasan kuma gaskiya ya fad'a ya girgiza kansa alamun gamsuwa amma baiyi magana ba daga nan bai sake mgana ba shima ba suka cigaba da tafiya.

? ? ? ? A b'angaren Rauda rai a b'ace ta shiga falon Umma ta samu Rahma a zaune suna gaisawa da Umma ganin ta sai ta d'an saki rai Rahma ta mik'e ta rungume ta tana dariya tace, "Yanzu nake tambayar ki, duk da fushi nake dake Anty Rauda har yanzu baki je inda nake ba." Rauda tayi murmushi tace, "Banda son wayo Rahma ina ke ina fitowa yanzu?."

Umma tace, "Nima haka nace Rauda, amma dai baki kyauta ba da baki je ba." Rauda ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login