Showing 36001 words to 39000 words out of 216282 words

Chapter 13 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

A fusace itama ta koma d'akin da take har k'afar ta nayi mata zafi sabida takun da take yi da k'arfi har ta manta ma tana da ciwo ta zauna a kan gado tana wuci ita kad'ai ita a dole anyi mata laifi.? "An tab'a mutum haka bazai yi magana ba amma ya dinga nuna min iko dan kawai ya d'auko ni da kud'i?. In badan halin Baba na son kud'i ba dashi ya isa azo wannan matsayin? Kud'in sa ko kyau da mulkin sa duka basa gabana kulawa nake buk'ata a gidan aurena ba wannan ba, dan kawai yasan ta yadda ya d'auko ni sai ya dinga min abinda yaga dama, to wallahi bai isa ba daidai nake dashi na; na daina yi masa shiru zan nuna masa asalin wacece Rauda."

Yadda take bayani ita kad'ai sai ka d'auka ita da wani take jawabin sai masifa take ita kad'ai a lallai ba'a kyauta mata ba. Tsaki taja ta jawo wayar ta ta d'auka ta shiga wps ta bud'e novel tana karantawa ko zai d'ebe mata kewa.
Tana ta karatun ta tana yi in ta tuna taja tsaki a haka har akayi sallar asuba bata farga ba sai kira ta gani ta wayar ta ta ajjiye da sauri ta shiga band'aki tayi alwala ta tayar da sallah kafin ayi asuba.
Tana idar da asuba bacci ya d'auke ta mai nauyi.

Bata tashi ba sai azahar tana mik'ewa zaune abinda ya faru jiya ne ya fad'o mata sai kuma jikin ta yayi sanyi tunawa dafa laifin ta d'in ne ba nasa ba tunda a gaban sa wani ya tab'a ta koda baya kishinta baya sonta tunda akwai aure dole zaiji babu dad'i. A haka ta shiga band'aki tayi wanka ta fito ta d'auki riga da wando na Pakistan cikin wanda Yaya Ummi ta siyo mata ta saka ta d'aura d'ankwalin a kanta sukayi mata kyau sosai.

Gyara gadon da ta tashi tayi ta had'e komai waje guda tana niyar fita taji wayar ta tayi k'ara sai kuma ta katse, k'arasawa tayi taga number Yaya Ummi ce tayi mata flashing ta zauna a gefen gadon ta kira ta amma bata d'auka ba sai kawai ta kira Umma. Sun sha hira sosai Umma tana tayi mata fad'a akan zama da mijin ta da yadda yanayin sa yake na rashin magana tayi mata nasiha kamar kullum kafin suyi sallama.

Ajjiye wayar tayi ta tayar da sallar azahar kafin ta idar ta taso ta fito falon gabanta na fad'uwa matuk'a. Baya falon sai dai an gyara shi tsaf sai khamshi air freshener na yake yi ga khamshin turaren sa da ya had'e dana d'akin ga sanyin a.c da ya garwaye da khamshin sai yake bada kalar khamshi mai sanyi daban.? Mamaki take yi wai waye yake gyara d'aki da falon haka ita dai tasan bashi bane ba amma ko yaushe sai taga wajan tsaf kamar ba'a zama a ciki.

? ? ? Kan table ta kalla taga abincin ta gashi nan sai ta kalli d'akin da yake taga k'ofar a kulle ta zauna ta fara cin abincin da yake a wajan. Taci sosai tana rufe bowl d'in ya shigo falon hannun sa zube a aljihu cikin riga da wando y'an kanti da suka yi masa bala'in kyau kansa da hular sanyi kalar rigar ta lura baya son sanyi sosai. Gaban ta ya fad'i ta d'auke ido daga kansa ya k'araso inda take baiyi magana ba taga ya d'auki wata leda ya ballo magani ya mik'a mata, hannu ta mik'a ta karb'a ya kalli ruwan da tasha ta rage sai itama ta kalla ta d'auka ya juya zai bar wajan amma bata sha ba.

Juyowa yayi ya kalle ta sai ta saka maganungunan a baki ta kora da ruwa sai taga ya juya ya fita daga d'akin gabad'aya ba tare da yace mata k'ala ba. K'irjita dafe domin ba k'aramin bugu yake mata ba ta kalli inda yabi taga baya nan tayi ajiyar zuciya tace, "Allah sarki ni na manta ma da maganin ashe shi bai manta ba jira yake na tashi." Sai kuma ta tab'e baki tace, "To ba dole yaso na warke ba tunda d'an uwan sane silar komai" ta fad'a tana bud'e na shafawar tana shafawa.

Bayan ta gama ta mayar dasu leda ta tashi kenan taji ana buga k'ofar sai tayi jimmm gudun kar ta bud'e a samu matsala jin ana ta bugu ya saka ta nufar wajan ta bud'e k'ofar. Balarabe ta gani sanye da riga fara wando bak'i da broom machine a hannun sa cikin harshen larabci yake mata magana amma bata gane me yake nufi ba. Asad ta gani a bayan sa sai ya juya suna magana da larabci kafin ya kalle ta, irin kallon da yayi mata basai yace mata komai ba ta fahimta tayi baya shi kuma balaraben ya wuce zuwa d'akin ta daman nan ne bai gyara ba.

Asad d'akin sa yayi niyar shiga sai ya kalle ta da hannu yayi mata alama da ta shiga yayi baya ta fara shiga sannan shima ya shiga ya k'arasa inda kayan sa suke yana dube-dube. Rauda sai yanzu ta fahimci wanda suke yin shara tana ta girgiza kai tana jinjina aikin kud'i wato in akan da kud'i komai ma yi maka za'ayi. Asad kuwa yana d'aukar abinda yake nema ya fita dan ta sake bashi haushi bama d'an kad'an ba.

Sai da ta tabbatar ya fita sannan ta fito ta shiga d'akin ta ganshi tass kamar kar ka daina kallon sa komai yayi kyau ta shiga band'aki nan ka kamar ka zauna kaci abinci sabida yadda yayi kyau. Falon ta fito ta zauna ta rasa me zatayi sai kawai ta fara karatun alkur'ani a fili.
Ta jima tana yi sauk'in karatu ya d'auke tayi da yawa sosai sai da akayi la'asar ta tashi tayi sallah ta dawo ta cigaba da karatun dan bata san abinda zatayi ba.

? ? ?? Tana cikin karatun ya shigo bata ji shigowar sa bama tana ta karatu ya zauna kusa da ita yana saurarar abinda take fad'a yana kallon ta jin yadda take karatun da k'warewa kana ji kasan ba y'ar koyo bace ta iya sosai haddar ta zauna sosai a kanta. Lumshe ido yayi yana jinta tana k'aruwa a zuciyar sa fushin da yake da ita yana raguwa a hankali ya samu kansa da yin murmushi yana kallon ta har lokacin bata san yana nan ba. Sai da taje k'arshen aya sannan ta tsaya ta kalli falon ta ganshi a zaune amma ba ita yake kallo ba.

Tana so tayi masa magana amma tana jin tsoron hakan gudun kar yayi mata banza dan ba son hakan take yi ba sai taja bakin ta tayi shiru amma nasihar da Umma tayi mata ce take mata yawo a kanta. Wayar sace tayi k'ara ya duba ganin sunan mai kiran sai ya share bai d'auka ba ya cigaba da kallo waje d'aya kamar me neman wani abu a bangon da yake kallo. Tashi yayi ya shiga d'aki ba jimawa ya dawo da laptop a hannun sa? ya zauna yana dannawa a hankali.

Tasowa tayi cikin dauriya ta dawo kusa dashi kan kujerar da yake ta zauna ta kalle shi taga ba ita yake kallo ba tace, "kayi hak'uri in nayi maka laifi." Cak ya tsaya da danna laptop d'in da yake yi ya juyo ya kalle ta ya d'auke kansa ya cigaba da aikin sa ba tare da yace komai ba, Rauda tace, "Bana so nayi magana ayi min banza Allah ya sani" ta furta cikin nuna rashin jin daWin ta ga hakan kamar zatayi masa kuka.

Nan ma yayi mata banza bai kula ta ba ta yunk'ura zata tashi ya rik'o hannunta ta tsaya ba tare da ta juyo ba ya dawo da ita ta zauna kusa dashi har lokacin bai cika hannun ta ba, baice komai ba ya cigaba da aikin sa wayar sa ta sake yin k'ara ya kalla yaga number Egypt yaja k'aramin tsaki ya d'auka ya danna a speaker ba tare da yayi magana ba. Daga can b'angaren Muhibba ta sauke ajiyar zuciya tace, "finally u pick my call. Ni ko baza kayi min magana ba indai nasan kana jina hakan yayi min, ina Sister na?."

Gaban Rauda ya fad'i jin abinda take cewa bata san lokacin da ta kashe wayar ba ya kalle ta itama ta kalle shi tace, "Haushin ta nake ji." Sai ya murmusa kad'an baice mata komai ba itama tayi shiru bata ce komai ba. Suna nan zaune hannun ta yana cikin nasa ya rik'e yana murza tafin hannun ta a hankali ba tare da yace mata komai ba. Rauda wani iri take ji a jikin ta taja hannun ta zata kwace ya kuma ri?ewa yak'i bata damar hakan sai ta kalle shi tace, "Meyasa baka ce mata ni matar ka bace?."

Bai daina abinda yake yi ba kusan sacan goma da yin maganar tata kana yace, "Meyasa baki ce ba ke?." Mamakin abinda yace tayi ta kalle shi tace, "fad'ar a kanka yake ai bani ba sabida ban santa ba." Murmushi ya kumayi bai ce komai ba itama bata kuma magana ba amma taji dad'i da taga yayi murmushi.
Sallar magariba ce ta tashe shi yaje masallacin hotel d'in yayi sallah bayan ya idar ya dawo yayi wanka ya saka doguwar riga fara sai kyalli take ya d'auko key na mota da wayar sa ya fito falon.

? ?? A zaune ya ganta da alama tayi wanka dan yaga ba kayan d'azu ne a jikin ta ba doguwar riga ce mai mayafi a jikin ta ya kalle ta yace, "Let go" abinda yace kenan ya fita ta bishi da kallo tace, "ko ina zamu je oho, bama ku fita d'in ba ya kasa yi maka magana" ta fad'a tana yafa mayafin tabi bayan sa ya kulle k'ofar suka shiga elevator suka sauka.

Basu wuce ko ina ba sai The Egyptian museum Cairo, inda komai na tarihi yake tun daga kan gawar fir'auna har zuwa kayan tarihin da ya faru ka k'asar misra akwai shi a wajan.

Sun sha wayo kasancewar sa babba d'an masu mulki kuma wanda yayi karatu a k'asar labarawa shugaban mai kula da wajan ya san shi har inda gawar fir'auna take ta asali sai da suka je, ba'a nunawa mutane ta asalin sai wacce sukayi creating suka ajjiye manyan mutane ake nunawa ta asalin Asad da Rauda sun shiga cikin su.

Ana ta nuna musu Rauda sai d'aukar hoto take hannun ta yana cikin nasa ya lura da tayi farin cikin zuwa wajan shiy???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?asa shima yaji dad'in zuwan. Rauda mamakin yadda aka sanshi kawai take yi wani b'angaren na zuciyar taji farin cikin hakan wani b'angaren akasin sa.

Bayan sun gama da nan suka wuce shogun Japanese Restaurant baban gidan abinci a k'asar Egypt cikin garin Cairo, suka zauna a teburan da aka tanada har lokacin murmushi take yi ya kalle ta suka had'a ido sai yayi murmushi shima sai ta kulle fuskar ta. Yanayin garin larabawan yana burge Rauda ganin dare yayi amma kamar ba dare ba mutane sai zirga-zirga suke abin su.

? ? ? Abinda suka yi order aka kawo musu suka fara ci juyawar da Rauda zatayi taga Muhibba a bayan su sai murmushi take musu, k'aramin tsaki taja ta dawo da kallon ta gare shi ya kalle ta alamun meya faru tace, "bakuwar kace."

Muhibba ya gani ta k'araso ta zauna kusa dashi tana kallon sa tace, "banyi niyar zuwa joint d'in nan ba ashe rabon zan ganka ya fito dani." Baice komai ba ta kalli Rauda tace,? "Sister ya kike?." A dakike Rauda ta amsa mata ta sake dawo da kallon ta ga Asad tace, "Handsome kayi min magana please." Nan ma baice komai ba hannun sa guda d'aya da yake kan table d'in ta d'ora nata a kai yana kallon ta shi kuma ya tsaya cak da cin abincin.

Kallon hannun nasa yayi ya kalle ta bata d'auke hannun ta sai murmushi da take masa tace, "please talk." Asad ya kalli Rauda yaga itama shi take kallo ya kalli Muhibba ya janye hannun sa kana yace, "Depriving me abeg."
"I can't Handsome, I love you so much, I want to be your wife forever. Please allow me to show u how much I love you abeg."

Yatsun sa ya murza ya nuna Rauda da yatsa yana kallon Muhibba yace, "She's my wife, so respect yourself and stay away from me." A tare k'irjin mata biyu ya buga Muhibba ta kalli Rauda itama Raudan kallon ta take yi kafin Muhibba tayi murmushi tace, "Nooo Handsome you must be joking, nasan baka da aure don kana sona rabu dakai kar kayi min k'arya." Banza yayi mata ya girgiza kansa? ta kuka cewa, "ba wasa nake ba ina sonka, ka kalle ni ina da kyau da ilimi zan dace da rayuwar ka. Please and please ka taimake ni."

"Ina girmama mace that's why ban dakatar dake ba tun farko. Rauda is my lovely wife not my sister, so ko k'yaleni bana son takura" ya fad'a da alama ya fusata yana kallonta dan ya gaji da bibiyar sa da take yi shiyasa yayi maganin abun. Kallon Rauda take yi da mamaki ganin abincin ta take ci duk da yanayin ta ya canja daka kalle ta zaka ga haka ta nuna ta da yatsa tace, "Wannan abar ce matar ka? Ka daina irin wannan wasan Handsome baka dace da yin k'arya ba."

Ba wanda yayi mata magana ta sake kallon Rauda tace, "take a look at her how com wannan abin zata zama matar ka for god sake?." Ta sake kallon Rauda sai tayi dariya tace, "nasan kana min wasa ne amma wannan sai dai tazo a housemate d'inka amma ba matar kaba. See her face abeg; she look like mon....." dukan table d'in da yayi k'arfi ya hana ta k'arasawa sabida yadda ta tsorata ya kalle ta yana cize baki yana nuna ta da yatsa cikin fushi da b'acin rai amma baiyi magana ba. Rauda ce ta mik'e tsaye shima ya mik'e bai kalle ta ba yayi gaba Rauda ta kalle bayan ya wuce tace, "Ni da kike rainawa na fiki sau dubu a wajan sa, da a bashi ke gwara a bashi matattaciyar dabba mara motsi, ki duba yadda yanayin sa ya canja da kika fad'a min magana ko a nan zaki tabbatar da matsayin da nake dashi a wajan sa, ki nemi wani wannan kam nawa ne ni kad'ai" ta fad'a tana wucewa ta barta a zaune tana kallon su. Muhibba ta mik'e tsaye tace, "Noo that can't be possible! babu ta yadda za'ayi wannan abar ta zama matar handsome kamar prince. I'll surely find out the truth ko meye zan gane."

? ? ? A mota ta same shi ta shiga motar ta zauna yaja motar suka bar wajan kana kallon sa kaga ransa a b'ace yake sosai har suka koma baiyi magana ba, suna shiga d'akin sa ya shiga itama ta wuce nata jikin ta duk yayi sanyi a haka tayi wanka tayi sallar i'sha da take kanta ta shirya cikin kayan bacci riga da wando masu tsantsi ta fito falon.
Agogo ta kalla taga k'arfe d'aya na dare ta nufi d'akin sa jikin ta duk a sanyaye ba tare da tasan abinda zai kaita can d'in ba ta tura k'ofar ta hango shi a inda ta same shi jiya.

A hankali take takawa ciki har tazo daf dashi cikin murya mai sanyi tace, "Prince!." Runtse ido yayi jin sunan yayi har cikin bargon sa bai juyo ba bai kuma motsa ba ya dai yi ajiyar zuciya. Rauda tace, "ka fad'a min gaskiya, meyasa ka aure ni....?." A hankali ya juyo ya kalle ta ta d'ago masa kai tace, "ban dace dakai ba abinda likitan can ta fad'a gaskiya ne ban dace dakai ba da y'ar aikin ka na dace ba mata ba. Ina so nasan gaskiyar lamarin ko zan samu peace of mind sabida a zahiri ban dace da kai matsayin mata ba.? Meyasa ka aure ni?."

Takowa yake a hankali yana kallon idanun ta itama kallon sa take duk da abinda take fani a idanun sa amma bata janye ido ba har yazo gab da ita yana kallon ta ya saka hannun sa duka biyun ya jawo ta jikin sa ya rungume ta tsam-tsam for the first time.
[17/12, 10:39 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*038.*

? ?
? ? ? ?? Yadda ya rik'e tsam a jikin sa a karona farko dukkan su sun tsinci kansu cikin bak'on yanayi mai wahalar fasarawa musamman zuciyoyin su da ta k'ara kaimi wajan gudu da bugu wanda basu tab'a riskar kansu a cikin yanayi irin sa ba. Gangar jikin su tayi sanyi ko wanne a cikin su ya kasa kwatar kansa daga wajan d'an uwan sa tafiyar wani abu suke ji a cikin fatar su yana zagaya har cikin gashin kansu. Ruwan soyayya suke ji ana kwararo musu daga sama tun daga kansu har Farcen k'afar su.

Sun kwashi tsahon mintina biyar a haka ya manta k'afar Rauda har lokacin ba lafiya ne da ita ba tsayuwa mai tsaho tana sakawa ta sagewa ta fara yi mata ciwo, a daidai wannan lokacin k'afar ta rik'e ta d'aga ta sama ta furta, "k'afa ta." Yadda ta furta maganar a hankali har lokacin tana jikin sa ba k'aramin sabon yanayi ya sake jefa shi ba bai sake ba a haka yake tafiya da ita har kan gado ya zaunar da ita ya zauna gefen ta yana kallon ta idanun ta a rufe. Rana ta farko kenan da ya fara jin abinda yake ji akan wata mace shiyasa ya rud'e tsintar kansa da yayi a wani yanayi wanda ya kasance bak'o a wajan sa. Umarnin da zuciyar take bashi shi kawai yake bi hakan ya saka shi kafa mata idanu tare da rik'o hannun ta yana sake k'arewa fuskar ta kallo.

A hankali ta bud'e idanun ta suka had'a ido ya saukar da nasa k'asa yana kallon hannun ta kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa sabon tunani ya d'arsu a ransa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login