Showing 81001 words to 84000 words out of 216282 words

Chapter 28 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

shine yake da wannan hakkin."

Asad yace, "Uncle nasan definitely Abban Suhail zai ajjiye sarautar nan sabida zai ce bazai yi mulki dani ba kaga sai ayi replacing dinsa dakai." Uncle yayi shiru alamun tunani Asad yace, "Please Uncle kar kace a'a dan Allah badan ni ba dan Allah, ina so mu cikawa Abba burin sa na inganta masarautar nan in ka barni ni kad'ai I can't."

Uncle yace, "Shikenan Allah ya shige mana gaba." Asad yayi murmushi yace, "Amin. Na gode Uncle." Asad ya sake cewa, "Ban san me zance ranar Monday ba Uncle." Yayi murmushi yana kallon sa yace, "Kar ka damu duk abinda yazo zuciyar ka shi zaka aiwatar, kar kayi shayi ko tsoron kowa, kar ka d'auki shawarar kowa, kayi abinda kaga shine daidai a haka mulkin ka zai tafi yadda ya kamata."

Asad yayi shiru Uncle ya kuma cewa, "yana dakyau ka had'a lunch a gayyato mutane da yawa azo a taya ka murna, dan ko iya ranar Monday din Allah kad'ai yasan adadin bak'in da zakayi."
"Not now Uncle, mu fara gamawa da jikin Abba."
"Hakan yana dakyau." Asad yayi shiru baice komai ba Uncle ya kalle shi yace, "kamar akwai abinda kake so ka Fad'a min." Asad ya sosa girar sa guda d'aya ya girgiza kai alamun babu Uncle yace, "Ma sha Allah haka ake so."

Shiru suka kuma yi kafin Uncle yace, "in anyi min izini zan koma." Asad yace, "Thanks you Uncle." Murmushi yayi yace, "koda yaushe ina tare dakai. Ka huta lafiya" ya fad'a yana tashi ya fita.

*&&&*

? ? ? ? ?? "Yanzu Daddy haka zaka yi mubaya'a k'aramin yaro kamar Asad sa'an d'anka ya mulke ka?" Suhail ya fad'a cikin zallar nuna b'acin ransa yana kallon mahaifin sa. Waziri yayi murmushi cikin kunar zuci yace, "Ya zanyi Suhail? In ban bishi ba ya kake so ayi?."
"Ka ajjiye rawanin yafi ka dinga duk'awa masa bazan jure hakan ba ko kad'an." Waziri ya sauke numfashi yace, "Zan ajjiye Suhail daman banyi niyar yin tafiyar nan dashi ba, ba ta yadda za'ayi na kasance a k'ark'ashin baba sa sannan shima na kasance a k'arkashin sa bazai yu ba."

? ? ?? Suhail yace, "Daddy har yanzu babu wani cigaba da ake samu ne akan tafiyar nan?." Yayi murmushi yace, "Lokaci ya kusa Suhail saura kad'an, babban burina shine daman ya hau karagar mulkin kuma ya hau. Ni yanzu Suhail akwai abinda zakayi ka shiga jikin sa sosai? Naga abotar ku taja baya sosai ba kamar da ba."
"Babar sace take hana shi mu'amala dani kasan kuma yana matuk'ar jin maganar ta shiyasa hakan take kasancewa amma shi har gobe ya amince dani, amma zanyi k'ok'ari naga na koma masa dan shi har gobe bai gano ni ba."

? ? ?? "Yauwa haka nake so, komawar ka kusa dashi zai bamu damar yin duk abinda muke so tunda ya amince dakai har abin hannun ka yana ci." Suhail yace, "zan koma Baba, Amma sai anyi maganin babar sa." Waziri yace, "Zamuyi wallahi, ita bata isa ba sai munyi abinda muke so, wannan shine lokacin mu ne."

Suhail yace, "zanyi Daddy, sai nayi iya bakin k'ok'arina wajan ganin mulkin katagum ya dawo hannun ka, bazan bari Asa??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????d ya dinga juya ka yadda yake so ba matsayin sa na d'an cikin ka, lokacin da komai zai dawo hannun ka yayi."
Murmushi waziri yake yi kana yace, "Allah ya yi maka albarka. Tabbas kai d'an dana haifa ne."
Suhail yace, "in kayi min izini zan tafi."
"Jeka duk inda zaka je."
"A tashi lafiya" ya fad'a yana tashi ya fita zuciyar sa cike da saqe-saqen yadda zai b'ullowa lamarin Asad.

? ? ?? *&& 8:00pm &&.*

? ? ?? Tun bayan magriba matar sarki Asad ta hallara a apartment d'insa tayi kwalliya cikin rigar bacci fara mai kyau wacce tafi ta jiya nuna jiki kanta babu d'ankwali gashin kanta ya kwanta luf bak'i sud'ik sai tashin khamshi jikinta yake yi tana zaune tana danna waya a falon saman.

K'arar k'ofa taji hakan ya saka ta kalle shi ya fito daga d'akin karatu sanye jikin jallabiya maroon mai gajeren hannun hannun sa rik'e da wayar sa.?
Cak ya tsaya ya d'auke numfashin sa sabida barazanar da turaren ta ya kawo masa ba tsammani ya jita kwance a k'irjin sa ta zagaya da hannun ta bayan sa ta rik'e shi gam idannun ta a kulle.

Shiru yayi ko motsin kirki baiyi ba sai numfashi da ya sauke a hankali ya lumshe idanunsa ya bud'e ya saka hannun sa ya janye ta daga jikin sa ya kalle ta na sakan 1,2,3, ya d'auke idanun sa daga kanta ya rab'a ta zai wuce tayi saurin sake rik'e shi tana fad'in, "my king wai laifi nayi maka baka kulani?."

Kulle ido ya sake yi ya bud'e kana ya sake janye ta daga jikin sa ya kalle ta suka had'a ido yaga ta kwab'e fuska tana kallon sa bakin ta a gaba alamun shagwab'a.
Wucewa Asad yayi ba tare da ya ce komai ba ya shiga d'aki ya ajjiye wayar sa ya cire agogon hannun sa ya shiga band'aki. Wanka yayi ya fito d'aure da towel a k'ugun sa da k'arami a hannun sa yana goge kansa da k'irjin sa. Without permission ta turo k'ofar ta shigo bai juya ba balle ya kalle ta ya cigaba da abinda yake yi.

? ?? "Subahanallah" ya furta a can k'asan makoshi lokacin da ya sake jin jikinta a jikin sa tana goga fuskar ta a fatar k'irjin sa muryar ta can k'asa tace, "My king......" hannu biyu ya saka ya d'ago ta daga jikin sa ya kalli face d'in ta yace, "leave me pls."
"I can't, ina so na kasance dakai a ko yaushe" ta fad'a kamar zatayi masa kuka ya zagaye ta ya wuce ya bud'e inda kayan sa suke ya d'auko dogayen kaya milk colour ya juyo ya kalle ta suka had'a ido ya d'auke kansa domin shi kam bazai iya saka kaya a gabanta ba.

? ? ?? Kamar tasan tunanin da yake yi sai ta fita ya girgiza kansa zuciyar sa wani iri babu dad'i domin bai san ya zai mata ba baiga kuma laifin ta dan tana neman hakkinta a wajan sa ba dalilin da ya saka yake jin sa wani iri kenan kamar ya tauye mata hakki. Yana tsaka da shiryawa unexpected yaji an kashe hasken d'akin an fad'a jikin sa a guje an fashe da kuka mai tsuma zuciya.
"Oh my god!" Ya furta a hankali yana jin yadda take shafa k'irjin sa sam hakan baya masa dad'i.

Jin abin nata yana neman wuce gona da iri ya fincike ta daga jikin sa yace, "I said leave! Baza ki samu abinda kika so ba so please ki barni" ya fad'a yana kallonta yana k'ok'arin gifta ta ta rik'e hannun sa tace, "Why zan k'yale ka? Bayan kasan ina neman hakkina a wajan ka."
"Nace baza ki samu ba, sorry please" yana fad'a ya fita ya k'yale ta ta zube a akan gadon tana girgiza kanta a zuciyar ta tayi aniyar bazata bari yau d'in nan ta wuce ta ba.

? ? ?? D'akin kusa da wanda ya fito ya shiga ya jingina da bango yana sauke numfashi haka kawai ana neman yi masa fyad'e, sai da ya daidaita kansa ya dafe kansa da yake masa ciwo duk abin nan da ya faru ko kaWan baiji wani da zai tabbatar da yana cikin wani yanayi ba kawai haushin yarinyar yake ji shiyasa baya so ta rab'e amma bawai dan yana cikin yanayi da baya son hakan ba, ya furzar da iska yana kallon kansa a mudubi yana tuna lokacin da lalaurar ta same shi rana tsaka ba tare ya shiryawa haka ba. Zama yayi a kan stool na mudubi rigar sa da take hannun sa ya saka ya sunkuyar da kansa ya rasa tunanin ma me zaiyi.

_Ko wanne yanayi take ciki yanzu?_ya furta a zuciyar sa sai yaja k'aramin tsaki ya dafe kansa da hannayen sa duka biyun, duk da baya sonta ko kad'an amma matar sace tana da hakki a kansa ko wanne yanayi ta shiga shine ya jawo gashi bashi da damar sauke mata wannan hakkin.? Bai san adadin lokacin da ya d'auka yana tunanin ba ya tashi yana so ya fita amma baya so su had'u dan bai san me zaice mata, fasa fitar yayi ya kwanta a kan gadon badan yana jin bacci ba.

? ? ? ? *Monday.*

? ?? Babbar fadar mai martaba sarki Asad ta cika maqil da hakimai wajan fadar bak'i ne manya da yara an cika kowa yana neman hanyar da zai bi yaga sarki. Asad yana zaune a kan kujerar da babu wanda yake zama sai ka kasance sarki a wannan gari an cika gefen sa dogarai biyu ne suna yi masa fifita, k'asan sa shamakin sane d'aya b'angaren kuma babu kowa wajan zaman Waziri ne kuma ba'a ganshi a wajan ba.

Camera ce a kansa ta ko ina yayi gyaran murya kowa yana sauraron abinda zaice yace, "Alhamdulillah, muna godewa Allah ya nuna mana wannan rana cikin k'oshin lafiya da kwanciyar hankali. Ina rok'on Allah yadda ya nuna mana wannan rana lafiya ya had'a mu da alkhairin da yake cikin ta."

Aka amsa da Amin yayi shiru kafin yace, "A matsayina na sarkin wannan gari nayi alqawarin?d'aukar nauyin duk wani wanda yake k'arkashin garin nan. Mace, namiji, yaro da babba mai kud'i da talaka, bazan yi cuta ba bazan amince ayi cuta ba da izinin Allah."

Shiru yayi jin yadda kansa yake bala'in harbawa ya lumshe idanu ya bud'e ga rawanin da yake kansa ya k'ara masa ciwon kai ga kayan zafi a jikin sa dan riga ma guda uku ce a jikin sa kuma manya hakan ya sake rud'a shi ba kad'an ba, "Allah yaja zamanin Sabon sarki, Allah ya karya mak'iyan ka ya datar dakai ga duka abinda ka saka a gaba!" Aka furta da k'arfin gaske daga can k'arshen fadar.

? ? ? ? "Duba da yanayin da ake ciki na rashin abinci munyi alqawari da aljihun mu bada aljihun gwamnati ba zamu bunk'asa sadakar da ake yi kullum domin wanda basa samu su amfana, zamu rarrbawa mutane maza da mata jari?dan su dogara da kansu, za'a bud'e makarantu na koyan sana'a ga mata da maza in sha Allah."

"Allah ya amince maka amintattacen sarki mai zuciyar alkhairi, Allah ya dafa mata zab'ebben sarki mai zab'in alkhairi, Allah ya baka ikon ganin bayan mak'iyan ka!" Dogarai suka sake fad'a aka amsa da amin.

? ? ? Yace, "Mata da za'a aurar dasu babu kayan d'aki k'ofa wannan masarauta a bud'e take wajan ganin an tallafawa wanda suka samu, baza mu ce duka zamu taimaka ba amma zamuyi iya bakin k'ok'arin mu wajan ganin mun taimakawa kaso saba'in bisa d'ari. Ga maza manoma wanda basu da gonar noma kuma suna son yi akwai bbar gonar masarauta wacce a qalla mutane sama da dubu zasu iya noma a cikin ta, zata bayar kyuata ga duk wanda yake da ra'ayin yi ya noma ya girbe ya kuma kai gidan sa ba tare da ya bamu koda kwaya d'aya na abinda ya noma ba. Muna fatan wannan mulki ya zama silar shigar mu aljanna" ya k'arasa fad'a a hankali muryar sa na shaking alamun yanayin sa yana gab da canjawa maganar tasa tayi yawa dak'yar ya iya k'arasawa dan ma abin yana ransa ne ya saka shi ya fad'a.

Kirari ake masa ta ko ina ya kalli Uncle alamun ya k'arasa abinda zai fad'a Uncle ya k'arasa bayanin kamar yadda yace sannan ya sanar da matsayin Uncle ya koma Wazirin sa aka bawa wani sarautar Uncle a nan take akayi sabon nad'i don kowa ya shaida. A haka zaman fada ya tashi cikin farin ciki da walwala musamman mutane da suka ji dad'in kalaman Asad domin kuwa kowa ya burge shi musamman yadda yake magana cikin izza da k'asaita da kuma ilimi.

Hotuna aka dinga yi dashi y'an jarida suna cigaba da d'auka ana watsa labaran a duniya kafin a gama Mai martaba ya nufi komawa gida a k'asa? ba tare da mota ba, shamaki ne a gefen sa na haggu waziri a gefen sa na dama sai mai rik'e da lema da masu fifita yana takawa a hankali ana cigaba da zubewa ana gaishe shi cikin girmamawa shi kam kai kawai yake d'agawa domin ya gaji matuk'ar gajiya.

? ? ?? "Allah yaja zamanin sabon sarki, Allah ya taimake ka ya bada ikon gudanar da mulki lafiya." Cak Asad yaja ya tsaya jin muryar wanda bai yi zato ba ya had'd'iye yawu mai d'aci ya juya yana kallon Baba suka had'a idanu Baba yayi murmushi shima Asad d'in murmushin yak'e yayi domin bai kai zuciya ba. Da hannu ya yiwa Baba magana da ya tashi daga durk'uson da yake yi sannan ya bada umarnin ya biyo shi ciki.

Kan Baba ya fasu ya washe baki yana take masa baya har k'aramar fada ta cikin gida aka raka shi ya zauna yana sauke numfashi ya rad'awa shamaki wata magana nan take kowa ya fita har Uncle aka barshi shida Baba kawai.

Asad ya kalli Baba yayi murmushi yace, "Baba barka da Rana."
"Allah yaja zamanin ka" ya fad'a yana yi masa jinjina. Asad ya nuna masa kujera yace, "Bismillah." Ba musu Baba ya tashi ya zauna Baba yace, "Ina neman Afuwa anyi shagali babu ni babu dangina, ina fatan an yafe mana."

Gaban Asad yayi mugun fad'uwa jin abinda yace zai zuciyar sa ta fara rawa ya daure yace, "Babu komai." Baba yace, "Allah ya bada ikon gunadar da mulki lafiya ya bada lafiya da tsahon rai, ya kare ka ya kuma tabbatar maka da duk abinda ka saka a gaba" ya amsa da amin Baba yace, "Mutanen gidan duka sunce a mik'a musu gaisuwa har ita uwar gidan."
Dammm gaban Asad ya buga ya runtse ido domin zargin sa ya tabbata bata fad'a musu abinda ya faru ba nan take tausayin ta ya sake mamaye masa zuciyar sa har yana jin ruwa na taruwa a idanun sa yace, "Ina neman afuwa Baba, Amma in sha Allah yau zan shigo gidan da kaina."

? ?? Baba da farin ciki yace, "Mai martaba da kansa zai ziyarce mu..? Alhamdulillah wannan abin farin ciki ne babba da ya same mu muna dakon zuwan mai martaba, Allah ya bada ikon zuwa muna maraba da bak'untar mai martaba har inda muke."

Murmushin yak'e yayi yace, "in sha Allah." Shiru fadar tayi kafin Baba yace, "Ina neman izinin tafiya domin naje na sanar da mutanen gidan baban bak'on da zai ziyarce mu yau."
Asad yace, "A sauka lafiya, muna godiya." Daga nan sukayi sallama Baba ya tafi Asad ya tashi ya shiga cikin gida ta k'ofar da take fadar a nan ya tarar da hadiman sa suka rakaya suka bi bayan sa zuwa ciki yana jin zuciyar sa kamar ana tafasata saboda tashin hankali ga kansa yana ciwo.


*Asad is coming*=؃?>?#?
[17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*051.*

? ? ? ? ?? Shigar sa babban falon sa na k'asa ya tarar da Mama a zaune a kan kujera ta hakimce fuskar nan tata a d'aure ganin wannan yanayin ta sai da gabansa ya fad'i ya k'arasa inda take ya zauna a k'asa kusa da k'afafun ta hadiman sa suka ja da baya falon ya rage daga ita sai shi. Ta kalle shi taga fuskar sa tayi y'ar k'arama jijiyoyin kasa sun tashi alamun kansa na ciwo sosai har bak'i yayi.

D'auke kai tayi daga kallon sa hakan ya saka yace, "Allah yaja da ran mahaifiyata, da an sanar dani da nayi tattaki na amsa kira." Mama tace, "ba dole nazo da kaina ba kana neman kashe ni Asad." Da sauri ya d'ago kai ya kalle ta tace, "eh, kana neman kashe ni, daga fara gudanar da mulki kwana biyu yau har ka fara yanke hukunci ba tare da izinina ba?." Asad ya sunkuyar da kansa tace, "waye yace kace zaka bada babar gona ga duk namomin da bashi da wajan yin noma? Kasan burin da nake dashi a akan wannan gonar?."

? ? ? ? Asad yace, "Mai martaba ya sanar dani nayi dukkan abinda talakawa zasu amfana shiyasa na yanke wannan hukuncin."
"To a soke shi! Mallakina nake so wannan gonar ta zama dan haka bata aro bace. Gidan gona zan mayar da ita shine burina a kanta ba tun yau ba. Girman ta ya wuce tunanin ka k'afa bata iya zagata sai dai da helicopter."
"Allah ya wuci zuciyar ki."
"Wucewar zuciyata shine a soke abinda ka fad'a, kuma daga rana irin ta yau kar ka sake yanke hukunci ba tare da izinina ba."

Asad yace, "Za'a yi Mama. Amma dan Allah ina neman alfarma badan ni ba badan kuma na isa ba, ki bari su amfana da wannan shekarar in lokacin ya wuce sai komai ya dawo hannun ki...." ya dafe kansa da yake masa mugun ciwo kana yace, "na riga na furta Mama, in aka canja maganar zasuyi tunanin wani abun za kuma su fara d'aukata mara cika al?awari daga farawa. Kiyi min alfarman nan dan Allah."

Numfashi ta sauke tayi shiru ganin hakan ya saka yace, "Godiya nake, Allah yaja da rai ya jiqan Abie da Ummi." Ta juyo ta Harare shi kana tace, "Meyasa ka kasa sauke hakkin yarinya da yake kanka yau kwana uku da auren ku?." Ya sunkuyar da kansa k'asa baice komai ba yana jin maganar tayi masa mugun nauyi dan bata tab'a fad'a masa ita gata gashi ba sai dai ta fad'a a waya dalilin da ya saka kunya ta lullub'e shi ya kasa motsin kirki amma yaga ita ko a jikinta.

"Magana nake maka." Ya sauke k'aramin numfashi ya d'ago idanu ya kalle ta yace, "Kiyi hak'uri."
"Ba laifi nace kayi min ba tambayar ka nayi ka bani amsa." Nan ma yayi shiru ya kasa furta komai ta sake cewa, "Akwai matsala ne?." Ya girgiza kai alamun A'a ta bishi da kallon tuhuma sai kuma taji gabanta ya fad'i tunawa da abinda ta aikata a baya ta girgiza kai zuciyar ta na bata tabbacin wannan shine dalilin da ya saka komai ya tsaya.

Kawar da zancen tayi a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login