Showing 201001 words to 204000 words out of 216282 words

Chapter 68 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

k'arasowa ta zauna kusa dashi tare da fad'in, "Cikina Sultan." Hannun ta d'aya ya rik'e ya d'ora daya akan cikin ta yace, "ciwo yake miki? Me kike ji a cikin?. Ki fad'a min na kira Dr" ya fad'a a rud'e yana kallon ta.

Hannun ta ta d'ora akan nasa da yake kan cikin tana kallon sa tace, "ciwon kad'an ne basai yazo ba." K'aramin tsaki yaja ya d'auki waya zai kira Dr, bata hana shi ba ya kira aka d'auka yace, "Yasir kana clinic?." Shiru yayi alamun yana bashi amsa kafin ya kalle ta yace, "Ina da patient."

A speaker ya saka wayar taji Dr yana cewa, "Me yake damun ta?." Ya kalle ta yayi shiru bai magana ba sai zuwa wani lokacin kafin yace, "Ciwon ciki." Dr Yasir yace, "Ranka ya dad'e sosai cikin yake ciwo? Wai dan nasan da wanne irin magani zan tawo mata dashi." Ya kalle ta suka had'a ido sai tace, "Ba sosai bafa Dr, kawai bana jin dad'i ne basai kazo ba yunwa ce ma."

Kallon sa tayi taga ita dai yake kallo bai d'auke ido daga kanta ba sai ya yanke wayar tace, "Bafa ciwo bane ba daka sani baka kira shi ba, babu abinda zai faru tunda wad'acan ranakun suka wuce banyi miscarriage ba bana tunanin akwai abinda zai saka ni yanzu. Yunws ce kawai." ta fad'a tana sunkuyar da kanta k'asa.? Hannun ta ya rik'e yana murza goben da ya bata a Cairo yayi shiru na wani lokaci baice komai ba kafin yace, "Wanne lokaci?."

Ta kalle shi tace, "Lokacin da Baba yayi min duka akan cikin, lokacin da Umma ta dinga min fad'a har tace bata yafe min ba, lokacin da nake confusing akan tsakanin ka da Aliyu waye mamallakin cikin nan. Rana ta k'arshe da Umma ita kanta ta d'auka cikin zai fita shine ranar da Mai martaba ya kira mu. Sultan tunda cikin nan bai fita a cikin wad'annan kwanakin dana lissafa ba bana tunanin zai fita yanzu, ban tab'a shiga tashin hankali a rayuwata ba kamar na wad'annan ranakun."

Idon ta yake kallo tana magana sai yaga hawaye suna taruwa a ciki ya girgiza mata kai alamun kar tayi kuka ya furzar da iska yana sake murza yatsan hannun ta yace, "I'm deeply sorry Muwaddaty!." Batayi magana ba itama sai murmushi da tayi kawai ta d'aga kai tana kallon sama kamaar me neman wani abun.

A kafaWarsa ta kwantar da kansa ya zaga da hannun sa ya rik'e k'ugun ta hannun sa d'aya yana cikin nasa, kuka yaji ta fara a hankali kafin tace, "Na shiga tashin hankali Sultan, nayi dana sanin zuwana duniya gabad'aya." Numfashi ya sauke ya d'ago da kanta yana kallon idanun ta yace, "Ban tab'a al?awari na sab'a ba sai sau d'aya, shima a kanki ne nace wa mama na barki amma Abba ya bani zab'ina tunda yason ina sonki" yayi shiru yana sake kallon ta kafin yace, "Tunda na d'auki al?awarin bazan barki ba Muwaddaty bazan tab'a barin ki ba kawai kafin nazo inda kike ne za'a jima but ina tare dake ko yaushe a kuma ko ina."

Tana kallon idanun sa tace, "Nayi tunanin hakan, tun? can Cairo lokacin da kuka fito kai da Mama ina zaune naga kayi mata magana ta barka kazo inda nake na d'auka zaka yanke igiyoyi guda biyun ne sai naji ka furta ka mayar dani har yanzu ni matar kace, kafin na farga naga ka tafi tun a sannan na saka a raina kamar baza ka karya al?awari ba amma daga baya sai kawai naga kayi min haka ne dan ka wanke min zuciyata amma bawai dan zaka dawo gare ni bane."

Kai ya girgiza ya goge mata hawaye cikin muryar sa mai sanyi yace, "Bana al?awari na sab'a Muwadda, in na barki a wannan lokacin da kika fara qaunata na cutar dake har abada Allah bazai yafe min ba kema kuma haka." Cize bakin sa yayi ya kulle ido ya buWe yana kallon ta idanun sa sun koma jajaye itama kallon sa take. Matse hannun ta yayi a cikin nasa tana kuka tace, "Shiyasa na kasa fad'a a gida, zuciyata tana rawa ne wani b'angaren yace na sanar dasu ka sake ni wani b'angaren yace kar na fad'a tunda ka mayar dani duk da nasan mayarwar bata da wani amfani sabida Mama. Umma ta lura da bani da walwala ta tambaye ni nak'i fad'a mata har na b'ata mata rai tace bazata kuma tambayata ba."

Ta sake kwanciya a kafaWarsa tace, "A lokacin da abin ya faru badan Dr Khalifa ba ban san inda zanje ba ga security sunce saina fita ance musu ni mai laifi ce ga kaina yana min ciwo" ta fad'a da kuka tana cusa fuskar ta a kafad'arsa.?

Shiru baiyi magana ba yana bubbuga bayanta a hankali shud'ewar wasu mintina kafin yace, "Haushin ki na farko dana fara ji kenan Muwaddaty, meyasa kika bi Khalifa bayan kin san bazan tab'a tafiya na barki ba? Meyasa kika bari Khalifa ya rik'e ki a lokacin da zaku bar wajan?. Kin san zafin da naji a raina kuwa?."

"Bani da zab'i ne sai na binsa Sultan, in ban bishi ba ina zanje? Ban san kowa ba ban kuma san ko ina ba sai kai kawai gashi an raba ka dani ina zani?. Dole ce ta saka na bishi gidan sa kuma rik'e ni da yayi ban sani ba Sultan sabida bani da lafiya a lokacin."

Shiru ya sake yi na wani lokaci yana sauke numfashin sa kafin yace, "Muwadda baki sanshi ba sai da kika je Cairo, meyasa kika amince har ya kaiki gidan sa? Da yayi miki wani abun fa?" Ya furta a kausashe yana d'ago da ita daga jikin sa yana kallon ta tare da rik'e hannayenta duka biyun. Idon sa take kallo ta saukar da nata k'asa tace, "Ni kaina hankalina bai kwanta ba sai da matar shi ta dawo, Sultan in ban bishi ba wa zanbi a wannan lokacin? Bani da kowa fa sai kai kad'ai ina zanje?."

Kai yake girgiza mata yana rik'e da hannunta tana kallon sa ya cize bakin sa ya sauke ajiyar zuciya idanun sa sun tara ruwa kamar zaiyi kuka amma baice komai ba. Shiru ya sake ratsa su kafin yace, "Naji wannan. Meyasa kin san da aurena a kanki kike kula wancan banzan mijin k'anwar taki? Kina da aure fa kike sauraron sa hards maganar aure tsakanin ku, meyasa Muwaddaty?."

Tace, "Sabida ban san da aure a kaina ba a lokacin na kammala iddar ka ta saki ukun da kayi min, kar ka manta a lokacin na d'auka kaine kazo ka bani takardar saki biyu ban san Aliyu bane ba. Ummana tana so taga nayi aure sabida abinda ya faru dani wata d'aya da yin aurena ya mutu na dawo gida da zama ana ta wayo dani a dangi da unguwa daman kwad'ayi ne da son abin duniya in ba haka ba ina kai ina ni?, harda wanda suke tarar Ummana face to face suna cewa Allah ya k'ara dalilin da ya saka na amince zan aure shi kenan."

Kallon ta yake yi hakan ya saka tace, "Ban san ba kai bane ba, duk wani abu da zai tabbatar min kaine na ganshi a tare da Aliyu Sultan, hatta wannan zanen daka nuna min na hannun ka na ganshi a hannun sa. Ya kira ni Muwadda cikin voice d'in da kake fad'ar sunan, na fad'a maka komai dana san nida kai kawai muka san dashi ya fad'a taya zan d'auka ba kai bane ba? Hatta yadda kake hugging d'ina yayi" ta fad'a murya na rawa.

"Subahanallah!" Ya furta yana cize bakin sa jin kalaman ta na k'arshe ya sauke numfashi mai k'arfi ya matse mata hannu sosai yana jin kamar ya goge kalmar da ta fad'a cikin tarihin rayuwar su amma bazai yu ba.

Rauda ta kuma cewa, "Ba nice na haife ku ba dole na d'auka kaine yadda yayi min magana da rauni sai na sake tabbatarwa kaine Sultan domin ta ko wacce fuska a yanayin ka yazo. Dalilin dawowar sa rayuwata kenan da niyar aurena a karo na biyu bani da zab'in da ya wuce amince masa dan ni da farko ban so ba makaranta naso na koma Umma ta nuna min auren take so nayi shiyasa na amince."

Ya sauke numfashi yana kallon sama yayi shiru itama tayi shiru tana goge hawayen idanun ta.
"A ranar kika tsane ni ko?." Jin yadda yayi maganar sai ta kalle shi ya juyo shima ya kalle ta ta d'aga masa kai tace, "Tabbas a ranar naji ina ma ban tab'a sanin mai iri Sunan ka a duniya ba, nayi dana sanin sanin ka na kuma yi dana sanin mallaka maka kaina da nayi a wannan lokacin, na tsinewa zuciyata da ta fara son naji kamar na cire zuciyata na cillar sabida abinda nake ji a cikinta. Na ha?ura na mik'awa Allah komai abinda ya sake b'ata min rai rushe gidan mu daka aiko ayi, na fusata sosai tsanar ka ta ninku a raina nake ji da ina da iko dana zo har cikin fadar da kake na tsinke ka da mari na fita. Hydar shine ya daidaita komai a lokacin amma duk da hakan ban daina jin haushin ka ba."

Yayi murmushi kad'an yana kallon bango tare da lumshe idanun sa amma baice komai ba sai dai yana sauraren dukkan abinda take cewa. Shiru itama tayi ta goge idanunta ta mayar dasu ta kulle yana ajiyar zuciya.

"Duka kinyi min hukunci ba'a kan laifina ba, bazan iya rabuwa dake ba Muwaddaty, bazan iya sakawa a yiwa kowa abinda Hydar ya saka ayi akan gidan ku ba balle ke, ko babu ke Umma da Baba ina musu kallon iyayena bazan iya ganin an yiwa wanda ya shafe su ba balle ke Muwadda" yayi shiru yana ajiyar zuciya idanun sa a kulle sannan yace, "Kika tsane ni kina jin haushina duka kuma bani nayi miki laifin ba, in na tuna kin tab'a tsana ta a duniya ina jin duniyar tayi min zafi" ya fad'a yana rik'e jijiyoyin kansa da suke harbawa da sauri sabida halin da yake ciki.

Rauda tace, "Ban san ba kai d'in bane ba Sultan a ganina kabi umarnin Mama ne ka yanke duka alaqar dake tsakanin mu dalilin sakin da sake yi min kenan." Ya sake kallon ta na wani lokaci ko kifta idanun sa bayayi kafin ya janye idon sa ya sake sauke numfashi yace, "Tunda kika baro Cairo duk motsin ki na sani Muwadda, ko fita kikayi kikaje wani waje sai an sanar dani. Ko lokacin da na bar Nigeria na koma Bahrain da zama ina bibiyar ki, abinda akayi min ya karye da tasirin addu'a da kuma tasirin aure da naji ance zakiyi, hankalina ya tashi sosai har sai da na dawo Nigeria shine na saka aka d'auko min ke Muwaddaty."

Jin yayi shiru sai sake matse ta da yayi a jikin sa ya sakata sauke ajiyar zuciya itama kusan minti biyu suna a haka kafin yace, "Amma da kika zo sai naga kin canja kina ta min fad'a da rashin kunya na rasa gane me kike nufi Muwaddaty, a wannan lokacin banyi niyar maki komai ba wani dalili ne ya gifta har hakan ta kasance." Ta kalle shi tace, "wanne dalili ne?." Ya sauke numfashi ya kalle ta? ya rik'e fuskar ta yana kallo yayi shiru kamar bazai kuma magana ba.

Har ta fitar da rai bazai ce komai ba sabida d'aukar lokacin da yayi baice komai ba kafin ya kai bakin sa idanunta yayi musu kiss kafin ya sake rik'e hannunta yace, "Ranar da na sake sanin ki a karo na biyu a Cairo Muwaddaty wani ciwo ya same ni wanda bazan sake iya sanin wata mace ba shine dalilin wannan ciwon da kika ga nayi." Rauda ta mik'e daga jikin sa tace, "Amma wannan ciwon da aljanu yayi kama fa, yadda nake maka addu'a kana firgita aljanu ne."

Yayi murmushin takaici yana girgiza kansa ya kalle gefe guda d'aya ya sake yin shiru kamar bazai ce komai ba kafin ya sake kallon ta yace, "Aikin aljanun ne Muwadda, duk dan a raba ni dake." Rauda tace, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Amma mutane basu da tausayi da imani, ina ruwana a wannan lamarin da za'a cutar dakai? In ba'a so ka zauna dani basai ka rabu dani ba lallai sai an cutar dakai?. Ni na rasa abinda mutane suke nema a duniya suka mayar da cutar da d'an uwan su musulmi ba koman komai ba."

Jin kalmar da ta fad'a mutane basu da tausayi da imani sai ya sake yin murmushi yana sauke numfashi yana kallon hannunta kamar me ganin wani abun a hannun nata dan ya kula lokacin da Abba ya fad'i wasu maganganun a taron da akayi duk bata ji ba da alama bata hankalin ta a lokacin kafin yace, "Mama ce!" Ya fad'a yana kallon ta sai yaga ta sauke idonta k'asa bata ce komai ba.

Murmushi yayi yana jin kansa na mugun ciwo amma baya so yayi shiru yace, "Inda tasan akwai idda a kanki a wannan lokacin saki uku zata saka ayi ba saki d'aya ba, dogoranta akwai aikin shine ta amince da saki d'aya" ya fad'a yana murmushi kana kallo kasan murmushin takaici ne da bakin ciki.

Shiru ya sake yi itama tayi shiru aka rasa mai magana a cikin sa yayi baya ya kwanta ya dafe kansa da guda hannayen sa yana ji kansa yana juyawa amma yafi so ya bayyana mata komai ko hankalinta zai kwanta ta daina jin haushin sa shiyasa ya zab'i ya cutar da kansa ta hanyar yin magana mai tsaho badan yana so ba.

"Naso na sanar dake a can ban samu dama ba Mama tazo, daga nan ban sake samun lafiya ba sai da naje Madina daga Bahrain nayi addu'a a Rauda nasha maganin karya asiri da dama a can, manyan malamai suka bani magani da addu'ar tsari a wannan lokacin na fara jin sauk'i a jikina ina jin son dawowa gida yana shiga raina a hankali."

Shiru ya sakeyi ta kafa masa ido tana kuka sosai yana jinta amma bazai hanata ba shima kukan yake so yayi hakan ya saka shi yin shiru kawai baice komai ba. Ya sake d'aukar dogon lokaci kafin yace, "Ranar da abin ya faru shine ranar da aikin ya karye a kaina gabad'aya, a sannan na tabbatar na samu lafiya amma sai kika d'auki abin ba daidai ba, kika kirani mazinaci Muwaddaty, har kika d'auki hannu kika mare ni."

Ta kalle shi yana kwancen idanun ta suka cigaba da zubar da ruwa zatayi magana ya d'aga mata hannu ya sake tashi zaune ya hard'e hannayen sa waje d'aya yana kallon k'asa kafin yace, "Naji zafin kalmar Muwaddaty ba'a tab'a kirana da makanmanciyar ta ba tunda nake a duniya sai a kanki, banji ciwo da zafin marina da kika yi ba amma naji zafin kalmar ki, naji b'acin rai sosai a ganina kina sane baki da wata hujja kin fad'a ne dan ranki yana b'ace akan abinda nayi miki. Daga ranar nace bazan sake neman ki ba tunda kika ce min haka......" yayi shiru ya furzar da iska daga bakin sa ya kulle idanun sa na wani lokaci.

Shiru ya sake ratsa su sai jan numfashin Rauda ake ji ya juyo ya kalle ta ya d'auke kansa ya sake yin shiru kamar bazai yi magana ba kafin yace, "Ina sonki dalilin sonki ya saka na kasa daina neman ki, na shirya ba tare da kowa ya sani ba na tawo gidan ku amma sai na kasa zuwa sbd kunyar su Baba, a nan naga kannen ki k'aramin Khalil shine yake fad'a min abinda ya faru."

Ta kalle shi shima ya kalle ta sai yayi murmushi ya d'ora hannun sa kan cikinta ya matso sosai kusa da ita har tana jin numfashin sa mai zafi da yake fita ya dafe kai da hannu d'aya, hannun sa ta cire ta d'ora akan fatar goshin sa taji zafi sosai jijiyar kan tana ta harbawa ta kalle shi taga ya had'd'iye yawu yace, "hankalina ya tashi da naji yace Baba yana dukan ki dalilin zuwana kenan dan nasan nine silar komai."

Kai ta sunkuyar hawayen ta na zuba akan hannun sa ya shafi hannun sa yana murza ruwan hawayen nata yayi shiru baice komai ba tana kuka tace, "Ban d'auka akwai auren ka kaina ba a wannan lokacin Allah ya sani, banyi dana ci maka fuska ko naci mutuncin ka ba; wallahil azim da gaske na d'auka na aikata Zina ne shiyasa hankalina ya tashi na rasa me yake min dad'i. Ban tab'a sanin kowa ba sai kai ka rabu dani kuma na ake sanin ka sai nake jin k'yamar kaina na gwammace ma wai daban ne ba kai ba. Kayi ha?uri!" ta fad'a tana kuka sosai ta kifa kanta akan hannun sa.

Murmushi yayi yace, "Na zama silar abubuwa da yawa a rayuwar ki Muwaddaty, tun farkon shigowata rayuwar ki abubuwa suke faruwa dake marasa dad'i, sau da dama ina jin ina ma ban shigo rayuwar ki ba na barki ki huta kamar kowa amma k'addara ta riga fata. Abinda ya sake k'ona min rai na rantse da Allah akan ban sake ki ba amma kika shafawa idanun ki toka kina ganin kamar zan rantse akan k'arya ne sabida wani burina."

"Kayi ha?uri, dan Allah ka yafe min wallahi banyi ina sane ba duka nayi ne dan kare mutuncin kaina amma bawai dan na wula?anta ka ba. Kayi ha?uri ka yafe min dan Allah!."

Yayi murmushi kad'an jin yadda take kuka ya cize baki yace,? "Akan gaskiyar ki kike Muwaddaty banga laifin ki ba ina fad'a miki abubuwan da banji dad'in su bane amma badan ina jin haushin ki ba."
"Kaima akan gaskiyar ka kake Sultan nice na kasa fahimtar ka duk da dole kaina ya kulle sabida abubuwan da suka faru bazan yi saurin fahimta da wuri ba. Kayi ha?uri ka yafe min dan Allah. Ka kuma yi min duk abinda kasan zaka wuce akan marin da nayi maka wallahi nayi dana sani."

Fatar cikin ta ya murza yana murmushi kad'an amma bai ce komai ba tace, "Kanka akwai zafi sosai fa, ka daina maganar ka huta dan Allah kar ya jawo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login