Showing 156001 words to 159000 words out of 216282 words

Chapter 53 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

ta shiga band'aki.

*&&&*

? ? ? ?? Mama tayi sa'a taga Baba malam ta karb'o abinda zata karb'o ta koma gida, ana ajjiye mota aka bud'e mata ta fito taga sarkin mota ya shigo taja ta tsaya har ya ajjiye mota ganin irin kallon da take masa ya saka shi ajjiye motar da gaggawa ya k'araso inda take a guje.

Yana zuwa ya zube yana kai gaisuwa ta kalle shi tace, "Kaine kake fita da Aliyu kwana biyu, ina kake kai shi?." Gaban sa yayi mugun fad'uwa rashin gaskiya ya bayyana akan fuskar sa ya had'd'iye yawu ya fara sosa kai yace, "Ranki ya dad'e" sai kuma yayi shiru.

Mama tace, "Baza ka fad'a ba kenan?." Yace, "Tuba nake ranki ya dad'e, amma ni babu inda muke zuwa tare." Kai ta girgiza tace, "K'arya zaka min kenan ko? Shikenan jeka."
Da sauri yace, "Tuba nake ranki ya dad'e, Allah ya wuci zuciyar ki. Tsakani da Allah gidan sa muke zuwa."
"Mata kake kai masa ko?."
"Ranki ya dad'e wata yarinya ce dai guda d'aya amma bayan ita babu ko wacce mace."

Ran Mama ya kai matuk'ar wajan b'aci ta juya ta wuce ta shiga ciki ya sauke ajiyar zuciya yace, "Na tsallake nata hukuncin sai na jira nasa kuma" ya fad'a kamar zaiyi kuka yana bin Mama da kallo dan da bai fad'a mata ba akwai matsala babba.

Kai tsaye Mama b'angaren Asad ta wuce ta same shi da Hydar kamar yadda ta barsu tana shiga ta k'arasa inda yake kwance ta d'auko ruwan maganin da aka bata ta fara sha masa a fuskar sa da tafin hannu dana k'afa, ta saka Hydar ya d'ago shi ta zuba masa ruwan maganin a baki, kamar wanda aka bawa poison sai ya fara jijjiga idanun sa suna k'afewa suka firfito waje nan take. Hankalin Mama da Hydar yayi bala'in tashi suka rik'e shi dukkan su Mama na kuka tana kiran sunan sa amma har lokacin jikin sa rawa yake bai dawo daidai ba.

Sai da yayi mintina biyu a haka kafin kuma ya lafa sai bacci ya d'auke shi Mama ta sauke ajiyar zuciya tana kuka. Kallon sa take yi ya koma wani iri kamar bashi ba a bayyane tace, "Lokacin da ya nuna min baya son sarautar nan da na k'yale shi da duk hakan bata faru ba, meye amfanin sarautar da babu lafiya a cikin ta? Asad ya koma kamar bashi ba kalli yadda ya koma kamar wanda ya shekara goma yana ciwo. Ka yafe min Asad" ta fad'a tana kuka sosai Hydar yana gefen ta yana goge hawaye.

"Lokaci ya k'ure miki Rabi'atu!" Aka fad'a ana shigowa d'akin ita da Hydar suka kalli k'ofar dan sun san dai babu wanda ya isa ya shigo b'angaren. Mai martaba ne ya shigo da kansa bayan sa Uncle ne ya kalle su ita da Hydar sai yayi murmushi Hydar ya k'arasa inda yake yace, "Abbana." Kallon farin cikin da yake kan fuskar Hydar yayi sai ya girgiza kafad'ar sa yace, "Mazan gaske, sannu da k'ok'ari." Hydar yace, "Ina farin cikin samuwar lafiyar mai martaba, Allah ya k'ara lafiya." Uncle ya amsa da amin.

Mama ta sunkyar da kanta k'asa ya Mai martaba ya kalli Asad da yake kwance a kan gado yace, "Hydar ban amince a fita da Asad wata k'asa ba zaman sa a nan nake so." Hydar ya kalli mahaifin nasa ya kalli Asad d'in da yake kwance amma babu damar musu sai yace, "duk abinda kace daidai ne." Mai martaba ya kalli Mama yace, "Ki daina saukar da kai Rabi'a lokacin saukar da kai d'in ya kusa amma ba yanzu ba. Bama ke kad'ai ba duk wanda ya shuka tsiya a bayan idanuna lokacin girbewar sa yazo."

Shiru sukayi babu wanda yayi magana kafin yace, "duka mutanen gidan nan nake so a tattaro min duk wanda ya shafi gidan nan a had'o shi gobe in Allah ya kaimu ina son magana da kowa. Ina matar Asad?" Ya fad'a yana kallon Hydar. Hydar yace, "Tana gidan su wai bata da lafiya."
Mai martaba yayi murmushin takaici yace, "Matar sarkin katagum guda ace tana gida bata da lafiya. An cutar da masarautar nan an b'ata mata suna an lalata garkuwar ta, amma yanzu lokacin gyaruwar tane."

"Ina so aje azo da ita da mahaifiyar ta a goben, hatta tsohuwar matar sa wacce uwar sa ta raba su ina so na ganta a taron gobe ita da nata iyayen. Iya iyalan gidan nan nace a gayyato bance a gayyato min kowa ba, masu tunanin na nakasa bazan sake motsi ba gobe zasu tabbatar da har yanzu da lafiyata. Hydar kaji me nace?" Hydar yayi firgigit ya kalli mai martaba hankalin sa gabad'aya yana ga Asad yace, "Naji ranka ya dad'e, in sha Allah za'a yi abinda aka umarta."

Kai ya d'aga ya k'arasa inda Asad yake ya dafa kansa yaji yadda kan yake harbawa a guje ya kalli Mama da robar maganin a hannunta ya girgiza kansa har zai magana sai ya fasa ya fita Uncle da Hydar suka take masa baya kowa da abinda yake cikin zuciyar sa hatta Mama da take tsaye wannan taro da za'a had'a ya tashi hankalin ta sosai ba kad'an ba.


*Gobe akwai kura kenan*=؃??#?>?#?>?#?
[17/12, 10:42 pm] Nafisat Alwasa: *Arewabooks@nanahaleema11*
*076.*

? ? ? ? ?? Da kallo Mama tabi mai martaba k'irjin ta yana dokawa jin ya ambaci Rauda babban tashin hankalin ta bai wuce ita kuma me zatayi a taron da ya shafi iyalan cikin gidan su?. Bata da bakin magana haka ta juya ta kalli Asad da yake kwance ta zauna a gefen sa ta d'ora hannunta a kansa taji har lokacin yana harbawa.

Numfashi ta sauke haka kawai fuskar Rauda ta fad'o mata a yadda ta tarar da ita sai ta samu kanta da fad'uwar gaba har ta dafe k'irjin ta a bayyane tace, "Fad'uwar gaban me nake ji akan yarinyar nan?." Ta dafe kanta da hannu biyu idanun ta a lumshe sai kuma ta d'ago kai tayi murmushi tace, "Rayuwa kenan." Sake juyawa tayi tana kallon Asad ta rik'e hannun sa tana jin wani irin d'aci a zuciyar ta.

? ? ? ? ?? B'angaren mai martaba yana fita daga b'angaren Asad jama'ar gida da suke so su? tabbatar shine kowa ya zube ana gaishe shi ana mamakin samuwar lafiyar sa lokaci d'aya ba wanda yayi tunanin hakan. Amsawa kawai yayi ya shiga b'angaren da yake bayan ya shiga d'aki Uncle yace, "Amma ranka ya dad'e sai nake ganin kamar anyi kuskuren bayyanar da samuwar lafiyar mai martaba ga iyalan gidan nan, akwai wanda baza su so hakan ba za kuma su so ace mai martaba ya sake kwanciya ciwo."

Mai martaba ya zauna a gefe ya kalle shi yayi murmushi yace, "Mubarak kenan, dukka masu kawowa lafiyata farmaki a yanzu babu wanda ban gano shi ba, duk wanda yake a gidan nan kallon sa nake hatta Asad d'in ya bani mamaki matuk'a ban d'auka haka abin zai kasance ba da banyi gangancin damk'a amanar mutane a hannun sa ba."

"Ranka ya dad'e amma sai nake ganin Asad kamar sharrin sihiri ne a tare dashi." Mai martaba ya sake yin murmushi yace, "Akwai sharrin sirihi sannan kuma akwai....." Sai kuma yayi shiru sai yace, "Allah dai ya nuna mana goben akwai abubuwan da dama da zaku sani wanda zuciyar ku sai ta motsa da junsu, in ba'ayi sa'a ba wasu zasu suma na wucin gadi." Sai ya sake yin murmushi yace, "Akwai kuma wanda baza su so na kai goben da rai ba."

Uncle yayi shiru kana yace, "Allah ya nuna mana goben da rai da lafiya." Ya amsa da amin kafin yace, "Da zarar Aliyu ya shigo a sanar dashi ina neman sa, sannan ko waye yazo zai shigo b'angaren nan kar a bashi dama ko wace shima Aliyun sai dare nake neman sa." Uncle yace, "In sha Allah, a huta lafiya" ya fad'a yana fita yaja k'ofar ya bar mai martaba a zaune yana juya abubuwa da yawa a kansa.

? ? ? B'angaren Fulani Hajiya tunda aka kawo mata labarin anga mai martaba da k'afar sa ya shiga b'angaren hankalin ta kai mak'ura wajan tashi ta kasa zaune ta kasa tsaye, gabad'aya hankalin ta yakai makura wajan tashi ta shiga d'akin ta hannu na rawa take kiran number abokin shirin ta amma bai d'auka ba.

Tsaki tayi ta kalli gefen gadon ta taga maganin da aka bata wanda take so ta bayar a masu dafa abincin b'angaren Mama su saka mata ta d'auke kai daga kansa dan yanzu ba shine a kanta ba so take ta same shi a waya su tattauna. Suhail ta kira yana d'auka tace, "Suhail mahaifin ka yana gida?." Daga can b'angaren ya bata amsa tace, "Zanje na same shi a can k'yale shi" tana fad'a ta yanke wayar ta sauke numfashi tana kallon agogo ganin la'asar ta kusa taja tsaki ta zauna.

Sai yamma sosai sannan ta fita kai tsaye gidan da suke had'uwa dashi ta wuce jikin ta har rawa yake ta shiga falon kai tsaye sai kuma taja ta tsaya jin abinda take jiyowa daga ciki ana fad'a. Sak tayi jikin ta yayi sanyi ta wara idanun ta waje k'irjin ta yana bugawa sabida tashin hankalin abinda take jiyowa daga ciki.

Muryar waziri taji yana fad'in, "Nasara munyi ta a akan Asad, munyi akan Aliyu sannan munyi a akan mahaifiyar sa. Asad lokacin haukacewar sa ne yayi domin an tabbatar min da tunda aka saka masa wannan layar da cikin kujerar zaman sa kuma ya zauna zance ya k'are ni hankalina baya tashi akan sa. Babban tashin hankalina yanzu Yayana Nasir da lafiyar sa ta dawo da kuma uwar gidan sa Sa'adatu."

Muryar matar sa taji tana fad'in, "Ai tun farko sai da na fad'a maka bai kamata ka had'a kai da ita ba amma kace min tana da amfani yanzu gashi k'arshen abun yazo itama zata bamu tata matsalar, domin kasan baza'a yi maganin ta cikin sauk'i ba." Waziri yace, "tana da amfani ta taka rawar gani a cikin tafiyar nan, kinga master planer ta jaddada min tafiya da ita domin amfanin ta a cikin tsagin mu, tayi aiki yadda ya kamata amfanin ta ya k'are itama maganin ta zanyi."

Matar tasa tace, "Me zaka yi mata?." Ya kalli matar tasa yace, "Zan saka a kulle mata baki ne yadda baza ta tab'a iya furta ko wacce irin kalma a kaina ba ko kuma na saka a kulle bakin nata har abada ya zama bazata kuma magana ba." Matar tasa tace, "Gaskiya dai ya kamata a d'auki mataki a kanta in ba haka ba zata zamar mana babbar barazana nan gaba."
"Ko itama ayi mata irin ta Asad d'in ta koma ita ba mai hankali ba ita ba mara hankali ba, kinga kenan duk abinda zata ce babu wanda zai amince da ita."
"Ko a ga bayan ta ba" matar ta fad'a tana kallon sa.

Ya sauke numfashi yace, "nata duk daga baya ne, babban tashin hankalina yanzu dawowar mai martaba yafi komai d'aga min hankali ta wacce hanya zan daqile wannan kira na gaggawar da yayi?." Matar sa tace, "Ya dai kamata, a jikina nake jin wannan kiran bana alkhairi bane ba kira ne na tarwatsa dukkan plan d'in mu."

"Allah ya tona asirin ka Yahuza!" Fulani Hajiya ta fad'a tana banko k'ofar falon ta shigo tana wuci tana kallon su. Dukkan su mik'ewa tsaye sukayi suna kallon ta da mamaki Waziri ya kalli matar sa itama ta kalle shi suka dawo da kallon su a gare ta babu alamun tsoro ko tashin hankali a tare dasu.

"Nayi dana sanin had'a kai dakai akan komai, Yahuza ni kake k'ok'arin kashewa? Duk fad'i tashin da mukayi ko nace muke kan yi ashe daman hak'ar ka kake so ta cimma ruwa ka cillar dani a gefe?" Ta fad'a cikin d'aga murya tana kallon sa da mamaki da kuma tsoro. Waziri ya sassauta murya yace, "baki fahimci abinda nake nufi ba, amma zauna nayi miki bayanin komai."

"Babu wani bayani da zakayi min naji komai da kunnena. Naji duk abinda kuke kitsawa kaida munafukar matar ka, ni kake shirin haukatarwa ko kashe ni dan ka rufe bakin tsanya babu wanda yasan abinda ka aikata ko?. Meyasa ma na amince dakai ne ni?" Ta fad'a tana dafe kanta da hannu d'aya tana cizon tsaya.

Matar tasa zatayi magana tace, "Dalla rufe min baki, munafuka algunguma. Duk taimakon da na yiwa mijin ki ke kike bada shawarar kashe ni ya kamata ayi sabida kuyi mulki son ranku babu mai kawo muku barazana a cikin sa. D'ana ba mulki zaiyi a cikin shekarun nan ba amma na gwammace na had'a kai da mijin ki akan y'ay'an mijina. Nayi dana sanin bashi goya baya a rayuwata, ban tab'a aikata abinda naji na tsani kaina lokaci d'aya ba kamar wannan ba, kun bani mamaki matuk'a kun kuma koya min hankali kodan sabida gaba."

Waziri yace, "Baki fahimci abinda nake nufi bane Sa'adatu ki zauna nayi miki bayani." Ta sake fusata ta nuna shi da yatsa tace, "Bazan kuma tab'a fahimta ba har a tashi duniya. Ka bani mamaki na kuma gano kuskuren dana aikata sabida kai, sabida kai na juyawa mijina baya kawai dan ka samu abinda kake so amma yau kaine kake tunanin hanyar da zaka ga bayana sabida kar nan gaba na tona maka asirin abinda ka aikata. Ka kyauta na kuma gano kuskurena ne tun farko dana had'a kai da mugu mai bak'ar zuciya irin ka. Inda na bar Asad d'in yana mulki lafiya lau ai da hakan bata faru ba amma na zab'e ka na barshi bayan bai tab'a aikata min wani abun mara kyau ba tun yana yaro."

Waziri ya canja fuska yace, "kar ki yi k'ok'arin kawo min maganar banza dan kinga nayi miki shiru, bawai tsoron ki nake ji ba ya kamata kisan da hakan."
"Nima kuma ba tsoron ka nake ji ba! Kai kasan nida kai kar ta san kar ne babu wani sirrin ka da baya tafin hannuna kuma lokacin da zan bayyana shi yazo, dan wallahi tunda niyar ka ta kashe ni ce sai na tabbatar ka rasa mulkin nan koda zan rasa raina ta dalilin hakan domin bazan barka kaci riba ba, sai na tabbatar da shiga gidan sarauta ya gagare ka kamar yadda ka saka ya gagari wasu daga cikin gidan. Duk wani shirin mu zanje na samu mai martaba na zayyana masa komai sai dai ya saka a kulle mu nida kai dan wallahil azim sai dai ayi tab'are!" Ta fad'a tana dukan kujera tana nuna shi da tsaya.

Juyawa tayi zata fita Matar sa tayi saurin tsayawa a gaban ta tace, "Hajiya duk wannan tashin hankalin fa bai tashi ba dan Allah ki tsaya ki fahimci juna abin bai kai haka ba." Rai a b'ace Hajiya tace, "Zaki matsa min daga hanya ko sai na tsinke ki da mari? Ba kece munafukar da kike cewa gwara aga bayana ba..? To ni zan fara ganin naku bayan kafin ku kuga nawa, kud'irin ku akan mai martaba ne yanzu ai ko...? Ina tabbatar miki da zai ji komai tun kafin ku aiwatar da nufin ku a kansa dana y'ay'an sa" tana fad'a ta rab'a ta gefen ta fita a fusace.

Matar ta dawo kusa daahi tace, "Ranka ya dad'e kayi wani abun kafin ta tarwatsa mana shirin da mukayi shekara da shekaru muna shiryawa, fitar ta ba k'aramar illa bace a gare mu kasan abinda zakayi." Ya kalli inda Hajiya ta fita yace, "Kyale ta zanyi maganin ta, ba burin ta taje ta sanar dashi shirin mu ba...? Ina tabbatar miki da baza taje inda take so taje ba."

Matar sa cikin tashin hankali tace, "Ta yaya kenan?."
"Ki yarda na fad'a miki, bazata isa gida lafiya ba kota mutu ko tayi mumman hatsari" yana fad'a shima ya fita tabi bayan sa da sauri suka shiga mota suka bar gidan.

Bayan sallar magariba a cikin gidan Sarki aka sanar da mummanan hatsarin motar da Hajiya ta samu a kan hanyar ta ta dawowa gida, hankalin iyalan ta ya tashi sosai suka d'auki mota zuwa asibitin da akace tana can.

? ? ? ? *&&&*

? ? ? ? ?? Umma ce ta shiga d'akin da Rauda da take ta ganta kamar ko yaushe tana zaune tana aikin tunani bayan ta idar da sallah. Umma ta k'arasa ta shiga ta zauna a gefen gado tace, "Rauda." Rauda ta d'ago ta kalli Umma tace, "Na'am Umma."

Umma tace, "tsohon sarki Katagum mahaifin Asad kenan shine ya aiko da sak'on yana son ganin ki bama ke kad'ai ba harda mu gobe." Rauda da take kallon Umma tana jin me take ji tace, "Neman na meye?." Umma tace, "Wallahi ban sani ba Rauda. Tunda y'ay'an sarkin nan suka shigo rayuwar mu suke buga mu kamar kwallo, wannan ya buga mu nan wancan ya tare, wannan ya sake buga mu can wannan ya tare. Rauda lamarin nan gab yake da saka min ciwon zuciya."

Rauda tayi shiru kanta na k'asa tace, "To Umma basai muk'i zuwa ba." Umma tace, "bamu san abinda zai faru a can ba yana da kyau muje dan duk abinda zai faru nasan akan rayuwar kine. Rauda in cikin jikin ki ya tabbata na d'an uwan Asad ne ba nashi bane ya zanyi da raina? In ta kasance da gaske kuma Asad ya sake ki fa?. Wannan kwamachalar bata d'aukar hankali da tunani; zata iya barazana a gare mu."

Rauda tace, "Kiyi hak'uri Umma."
"Ba laifi kikayi min ba Rauda, nasan duk abinda ya faru k'addara ce daga Allah amma duk mahaifin ki shine sila." Rauda tayi shiru har Umma ta kai k'arshe sai ta rik'e hannun Umma ta d'ora a kan k'irjin ta tace, "Umma kullum ji nake zuciyata kamar zata fashe, Umma a kullum bana tunanin in na kwanta zan tashi da raina sabida a yanayin da nake kwanciya bana tunanin zan iya tashi. Umma in na tuna Allah ya isar ki a kaina sai nayi dama na mutu na huta" ta fad'a tana fashewa da kuka ta d'ora kanta a cinyar Umma.

Umma ta sauke numfashi tace, "Ki cigaba da hak'uri komai yana gab da zuwa k'arshe in sha Allah. Rayuwar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login