Showing 105001 words to 108000 words out of 216282 words

Chapter 36 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

har lokacin a wajan ya kalle ta yace, "ki dinga nutsuwa mana Rauda ko yaushe zuciyar ki a sama ki dinga sassautawa mana, nasan anyi miki ba daidai ba amma shi wannan meye laifin sa? Naga taimaka mana yayi ko?." Rauda tace, "Wallahi Baba gabad'ayan su na tsane su bana son su ko kad'an, mu da gidan mu ace sai alfarma akayi mana aka k'yale mu dan mu zauna? Wanne irin wula?anci ne wannan?."
"Ya dai isa komai ya wuce yanzu ai."
"To Baba" ta furta a sanyaye.

Ya kalle ta yace, "Maman ki ta sanar dani lokacin Iddar ki ya k'are ko?." Gabanta ya fad'i ta d'aga kai ba tare da ta d'ago ba yace, "To Allah ya kawo miki miji na gari da gaggawa." Bata amsa ba ta canja maganar tace, "Baba indai zaka amince min a wannan lokacin ina so zan koma makaranta na cika burina na zama y'ar jarida." Baba yace, "me zai hana Rauda? Sai ki koma ai ba wani abun bane ba, da zaman gidan ai gwara ki koma. K'anwar ki Rahma ma in tana so duk sai ku koma d'in."

Rauda taji dad'i sosai cikin mamakin Baba jin fad'a d'aya har ya amince kafin tayi magana yace, "Ba kuna da takardun sakandiri ba?." Tace, "muna dashi Baba, Jamb kawai zamuyi wannan shekarar in mun ci sai mu nemi makarantar." Baba yace, "Ba laifi, Allah ya taimaka" ya fad'a yana fita Rauda ta amsa da amin ta buga tsalle ta nufi d'akin Umman ta.

"Ummana!, Baba ya barni na cigaba da karatu" ta fad'a cikin farin ciki tana kallon ta. Umma ta tab'e baki tace, "Na taya ki murna."
"Umma wai me ya canja Baba ne lokaci guda haka? Ya daina yi min fad'a sosai, zancen makarantar nan fa ina fad'a masa baiyi musu ba ya amince."
"Jeki ki tambaye shi ya baki amsa. Ni ba karatu nake so kiyi ba Rauda aure nake so kiyi Allah ya sani."

Jikin Rauda sai yayi sanyi ta kalli Umman tace, "Umma meyasa bakya son karatun?." Umma tace, "Haka kawai, nafi so kiyi auren ki in yaso kyayi karatun a gidan mijin ki. Lokacin karatu a yanzu ya wuce tun a baya da ya amince kunyi da yanzu ba wannan zancen ake yi ba amma ya hana. Gobe in Allah ya kaimu gidan Baba Malam zan koma na karb'o maganin farin jinin da yake baki Allah ya fito miki da miji kiyi aure ko zaki wuce takaicin abinda aka yi miki. Zaman gida ba naki bane yanzu Rauda."

Rauda jikin ta sai ya mutu murnar da take yi ta koma ciki ta kalle ta tace, "Ummana ai aure lokaci ne, ki duba wancan lokacin da yazo bamu shirya ba gabad'ayan mu sai da akayi haka wannan ma ko bamu shirya ba sai anyi. In na fara karantun in Allah ya kawo mijin ba shikenan ba?." Umma ta rausayar da kai tace, "To Allah ya bada sa'a."
"Amin Umma, na gode."

Fitowa tayi daga d'akin ta shiga d'akin ta taji wayar ta tana ihu tana dubawa taga sabuwar number da bata sani ba ta d'auka da sallama daga can b'angaren tace, "Sis Rauda kin manta dani gabad'aya ko?." Rauda tayi y'ar dariya da ta gane muryar tace, "Ni na isa? Wallahi kina raina Allah ne bai bani ikon kiran naki ba Anty Ramla. Ya na ganki da number Nigeria kuma?."
"Ai mun shigo gari yanzu ma kiran ki nayi in kina gida mu shigo mu gaisa."
"Dan girman Allah da gaske kike zaku zo?."
"Wallahi da gaske nake, Dear yasan address d'in ki ai yanzu zaki ganmu yau in sha Allah zamu sauke al?awarin da muka d'auka."

Cikin farin cikin Rauda tace, "Lallai kam, ko yaushe ace min za'a zo sai yau Allah yayi. Ina gida sai kunzo." Dariya Ramla tayi ta kashe wayar Rauda ta ajjiye wayar ta fita da sauri zuwa d'akin Umma tace, "Umma!." Ta kalle ta tace, "Ke lafiya kuwa?."
"Ina wanda na baki labarin sun taimaka min a Egypt lokacin da abin nan ya faru...? Ita tayi min waya gasu nan zasu zo mu gaisa."

Umma tayi murmushi tace, "Lallai manyan bak'i ne, to ki samu ki dafa musu wani abun kafin su k'araso." Rauda tace, "Wallahi ban san me zan dafa bane ba Umma." Umma tayi hanyar fita tare tana fad'in, "ki musu abu mai sauki na hausawa tunda daga k'asar waje suke zasu fi sha'awar abincin mu." Da Baba suka had'u yace, "Su wa za'a yiwa abincin hausawa?."

Umma tace, "Bak'i ne Rauda zatayi kuma a can k'asar da aka yi mata aiki suke zaune sai yanzu suka zo nan shine tace zata zo su gaisa." Baba ya kalli Rauda yace, "Ke a ina kika santa?." Rauda tayi shiru tana kallon Umma itama ita take kallo kafin tace, "Itace wacce nake fad'a maka mijin ta ya taimaki Rauda a lokacin akayi sakin nan a can misira, kaga ai manyan bak'i ne ayi musu abinci ko?."

Baba ya girgiza kai yace, "Inda abinda yafi abinci ma ai a basu, tsayuwar me kike yi to kije ki samar musu abinda zasu ci. In sun zo kuma ki shigo da mijin nata har nan sai kiyi min magana mu gaisa" ya fad'a yana ficewa Umma ta shiga wajan Inna ita kuma ta nufi kitchen.

Ba jimawa tayi musu lafiyayyen d'anwake kasancewar suna da kayan sa a hannu umma bata rasa yaji dakakke nan da nan ta gama ta zuba musu a flake sabo cikin wanda aka fara siya mata na tafiya gidan miji ta koma d'aki tayi wanka tana cikin saka kaya taji ana kiran ta alamun sun zo.

Da sauri ta gama shiryawa ta fito taga Ramla a zaune da murmushi a fuskar ta ta k'arasa kusa da ita ta rugume ta tace, "Oyoyo Anty Ramla sannu da zuwa."
Itama murmushin take yi tace, "Tunda kika gudu Nigeria sai aka daina jin ki sosai." Rauda tayi dariya tace, "Ina Dr yake?."

"Yana k'ofar gida bai shigo ba." Rauda tace, "meyasa ya tsaya a waje?, Khalil!" Ta fad'a da d'an k'arfi Khalil yazo a kuje tace, "maza jeka kace wanda yake waje ya shigo." Ya kuwa fita a guje Rauda ta zauna suna cigaba da gaisawa da Ramla cikin fara'a. Ba jimawa ya suka shigo Rauda tace, "Yanzu dan Allah Dr sai ka zauna a waje?." Murmushi yayi ya zauna tace, "Ina wuni."

"Lafiya lau Rauda, ya mutanen gidan kowa lafiya?." Rauda tace, "Suna nan lafiya. Khalil yiwa Baba magana yace in kunzo a sanar dashi zuwan ku bara na kira Umma" ta fad'a tana tashi ta shiga d'aki jim kad'an suka fito tare da Umma.

Cikin girmamawa suka gaisa da Umma Baba ma ya shigo har da Inna suka gaisa cikin girmama juna kamar sun san su Baba yace, "Ta sanar damu duka taimakon da kukayi mata angode Allah yasa da alkhairi ya bar zumunci." Dr Khalifa yace, "babu komai ai yiwa kaine." Umma tace, "Ko ruwa baki kawo musu ba Rauda." Da sauri ta mik'e tama fad'in, "Murnar ganin Anty Ramla ce." ta kawo ruwa tare da abinda ta dafa musu lokacin da ta dawo su Umma basa nan.

Dr Khalifa yace, "Su Umma suna da kirki sosai har sun fiki." Tayi dariya tana fad'in, "Musamman na dafa musu abincin nan Allah yasa kuna ci" ta fad'a tana bud'ewa Ramla tace, "kaii ai ko a k'oshe nake sai naci, favorite food d'ina ne fa" ta fad'a tana gyara zama Rauda taji dad'i ta fara serving d'in su ta basu ta zauna suna hira suna ci da alama kuma sunji dad'in sa.

Bayan sun gama Dr yace, "Gaskiya kin samu lada Rauda, na jima banci d'anwake ba sai yau gashi yayi dad'i sosai da alama Umma ce tayi." Dariya ta kuma tace, "Nima naji dad'i da kuka ci wallah?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? i." Ya kalli Ramla yace, "ya kamata muje magriba tayi" ya fad'a yana duba agogon hannun sa. Ramla ta kalli Rauda tace, "Yauwa Rauda, kin sani Baba Malam wani babban malami ance ya tsufa a garin nan yake amma bamu san wacce unguwa ba."

Rauda da mamaki tace, "Baba Malam dai tsohon malamin nan?da ake masa layi?." Ramla tace, "Shifa."
"To ai Yayan Ummana ne, shine babba a d'akin su gobe ma naji tana cewa zata je wajan sa." Ramla ta kalli Khalifa da farin ciki a akan fuskarta tace, "Alhamdulillah, kice ta kwana gidan sauk'i ma kenan." Rauda tace, "ta kwana kam, ganin sa zakuyi?."
"Eh Rauda."
"Tabd'ijam ai kafin ku samu ku ganshi wallahi a kwana goma layi baizo kanku ba, amma yanzu tunda da Umma zai iya cewa goben ma kuzo tare da kunje kuma cikin gida zaku shiga zaizo da kansa inda kuke."

Ramla ta rik'e hannun Rauda cikin farin ciki tace, "Na dad'e banji labari mai dad'i ba kamar yau Rauda, yanzu yaushe zamu ganshi?." Rauda tace, "Umma zata yi masa waya ta fad'a masa zai baku rana sai aje nasan in akace masa ba'a nan kuke ba zai bada ranar kusa."
"Na gode Rauda Allah ya bar zumunci, kinga dad'in zumunci ko? Ta dalilin ziyarar da nazo miki ga abinda ya faru."

Rauda tace, "Lah babu komai Anty Ramla kun wuce haka wallahi." Dr yace, "mun gode sosai Rauda, naji dad'i sosai wallahi." Rauda tace, "babu komai, yadda mukayi da ita anjima zan fad'a miki ko a chart." Daga nan sukayi sallama da Umma da Baba Rauda ta raka su k'ofar gida a nan Khalifa yake cewa, "Rauda ina Asad kuwa?."

Gabanta ya fad'i matuk'a amma bata nuna ba tace, "Yana gidan su." Yace, "kwanaki munyi waya dashi, yanzu samun sa a waya sai kayi da gaske abubuwa sun masa yawa, ya zama shugaban katagum baki d'aya jan aji ya k'aru. " Shiru tayi bata bashi amsa ba ya d'an kalle ta sai yayi murmushi Ramla tace, "Sai munyi waya Sis. Ga wannan tsaraba tace" ta fad'a tana d'auko leda a mota, Rauda tayi musu godiya daga nan suka ja suka tafi itama ta koma gida.

? ? ?? Rauda tana shiga gida ta tarar da Umma da Ummulkhairi da Rahma a zaune su Rahma suna cinye ragowar d'anwaken ta kalle su tace, "Ku kam kuna da abin haushi, yanzu da zanci fa kuka cinye?." Umma tace, "Sai dai kiyi hak'uri ai." Ta k'arasa ta nunawa Umma k'aramar ledar tace, "Umma kinga abinda suka bani wai tsarabar Egypt."

Umma tace, "kin gode, suna da kirki sosai kamar mun saba." Rauda tace, "mun saba sosai a waya Umma tunda na dawo ai ban yarda dasu ba muna zmuncin sosai. Kuma kin san wa suke son gani?." Umma ta girgiza kai alamun A'a Rauda tace, "Baba Malam suke nema an musu kwatancen sa basu san inda zasu ganshi ba." Umma tace, "Baba malam dai Yayana?."
"Shifa Umma."
"Allah sarki, sai nayi masa magana sai ya basu lokacin da zasu ganshi, sun huta bin dogon layi."
"Haka nace musu, sai godiya suke yi."
Umma tace, "Babu komai ai."

Rauda ta kalli Falon ganin duk sun fita sai su biyu tace, "Kin san basu da yara kusan shekara bakwai da auren su bata tab'a samun ciki ba, har cewa tayi nayi mata addu'a ina jin matsalar ce zata kai su wajan sa." Umma tace, "Allah Akbar! Kice gwara da Allah ya hane ni d'azu k'iris nace musu ina yaran."
"Wallahi fa Umma."
"To in ma itace matsalar da zata kaisu Allah ya basu na gari in suna da rabon haihuwar."

"Amin Umma" Rauda ta amsa Umma ta kuma cewa, "zan masa waya gobe in Allah ya kaimu yadda mukayi dashi sai na fad'a miki ki sanar dasu." Rauda tace, "To Umma." Rauda ta tashi ta shiga d'aki.

*&&&*

? ? ? ? ? K'arfe sha d'aya na safe a garin Kano ta yiwa Mama ko gidan sarki ma bata je ba gidan yayar ta ta wuce kai tsaye tana zuwa bata zauna zaman hutu ba suka d'auki mota suka d'auki hanyar k'auyen kura. Isarsu kura ba wuya suka tsaya a k'ofar wani gidan k'asa da motoci manya a k'ofar gidan mata da maza suna ta shiga da fita suma suka fito suka shiga ciki.

Basu jima da zama sosai ba aka kira su suka shiga wajan malamin yana ganin su yayi murmushi yana fad'in, "Barkan ku da zuwa." Zama sukayi kafin Babbar Yaya tace, "mun same ka lafiya malam?."
"Lafiya lau ranki ya dad'e."
Ta nuna masa Mama tace, "itace wacce na sanar dakai zuwan ta jiya, mahaifiyar sarkin katagum sarki Asad Nasir Sa'ad."

Ya sake yi mata jinjina yace, "An gaida y'ar sarki mahaifiya ga shugaban Katagum." Babbar Yaya ta kuma cewa, "Zancen mai martaba Asad d'in ne d'anta gabad'aya an mallake mata shi yanzu ko inda take baya zuwa bayan da yana da tsananin biyayya a gare ta." Malamin ya fara istihara yana duba lamarin kafin ya kalle su yace, "Tsakani da Allah na jima banga bak'in aiki kamar wanda aka yi masa ba, wannan sai dai a kira shi da tsafi ma ba sihiri ba."

Mama suka kalli juna hankalin ta ya tashi jin abinda akace mata a can an kuma maimaita mata Mama tace, "Karya shi nake so ayi da gaggawa." Ya sake yin shiru yana istihara kafin yace, "Karya shi ba abu bane mai sauk'i dole sai anyi da gasken gaske sannan za'a iya karya shi kuma dole sai an raba shi da matar sa sannan za'a samu abin yayi nasara, Matuk'ar suna tare bazata barshi shan duk wani magani da aka bashi ba." Mama ta gyara zama tace, "Wannan ba matsala bane zan saka shi ya sake ta koda baya so, duk da shugaba ne Bai kamata ace yayi saki ba amma dole yayi." Babar yaya ta kalle ta tace, "Kina ganin zai amince ya sake ta cikin sauk'i?." Mama ta kalle ta tace, "Zai yu."

Malam yace, "Indai zai yu zan bada maganin da za'a bashi ya dinga wanka dashi, sannan akwai rubutun da zan bayar ya zama kamar ruwan shan sa koda yaushe ya dinga sha. Sannan akwai wani babban malami a can garin naku Allah ya bashi ilimin maganin gargajiya sannan yasan ayoyin alkur'ani yana karya tsafi komai munin sa indai Allah ya bashi iko." Mama tace, "waye shi? A ina yake?." Malamin yace, "A nan katagum d'in yake ana ce masa Baba Malam ya tsufa amma kuma akwai ilimi ba kad'an ba."

Mama tace, "Wacce unguwa yake?." Malamin yace, "a nan gaban katsalle yake ni kaina in abu ya shige min duhu ina zuwa wajan sai kiga an samu nasara." Mama tace, "Zanje wajan sa da zarar na koma, yanzu bamu naka taimakon."

Malamin ya juya yana had'o mata maganin kafkn yace, "Amma fa ganin sa yana da wahala sosai sai ka jera kwana goma layi bai zo kanka ba sai an jure. Baya duba mulki ko kud'i gaskiya in layi bai zo kanka ba bazai ganka ba." Mama taja k'aramin tsaki domin ita kam a ganinta babu wani wanda bai mata wahalar gani tana da kud'i da mulki kome take so zatayi.

Maganin ya basu suka zube masa kud'i suka koma gidan Baban Yaya sai a sannan Mama ta samu ta huta ga zazzaSin da yake cin jikinta sai da tasha magani sannan tayi bacci.

Washe gari ta sauke d'aukar hanyar Katagum da sassafe, kafin rana tayi ta isa katagum tana takawa a hankali tana shiga cikin gidan tazo giftawa ta wani d'an lungu da ake aikin abinci a wajan taji hadimai mata d'aya tana cewa, "Bikin yarinyata yazo amma ban san da wacce fuska zan tunkari Mai martaba da maganar nan ba, ya canja gabad'aya ni tsoro ma yake bani shiyasa na yanke shawarar samun Fulani mai babban d'aki da maganar."

D'ayar tace, "Me ta isa tayi a yanzu? Hmmm ai dama matar tasa kika samu Zakanyar Sarki in ta saka baki sai kiga yayi miki." D'ayar ta kuma cewa, "Allah mai iko, yanzu wai mai martaba ne baya zuwa inda Fulani take? Lallai duniya juyi-juyi. Amma fa maganin ta kenan kodan wula?anta mu d'in da take yi alhaki sai ya kamata." Da sassarfa Mama ta wuce wajan zuciyar ta na suya zazzaSi na sake rufe ta ruf haka ta isa b'angaren ta.

? ? ? ? Tana shiga falon ta hadimai suka zube ta kalle su tace, "Asad ya zauna a fada?." Hadima d'aya tace, "Eh ranki ya dad'e, amma ya shiga ciki yanzu." Bata ce komai ba ta shige ciki tana shiga d'aki tayi wanka ta shirya cikin shigar alfarma duk da bata jin dad'i sosai amma hakan bai hanata yin kwaliyya ba.

Tana zama a k'aramin falon ta Hydar da Suhaima suka falon suka zauna kusa da ita Hydar yace, "Barka da dawowa Mama, da fatan an sauka lafiya?." Numfashi ta sauke kana tace, "Alhamdulillah. Ku taya d'an uwan ku addu'a." Hydar yace, "Muna yi masa Mama" ya fad'a yana dafe kansa ta kalle shi cikin tsoro tace, "Ya dai? Ko ciwon ne?." Girgiza kai yayi kawai ta koma ta zauna tace, "yana ina yanzu?."
"Yana ganawa da bak'in da suka zo daga Cairo." Shiru Maman tayi bata ce komai ba.

"Ina so na ganshi nasan bazai zo nan ba." Jin yadda tayi maganar cikin sanyi duk sai ta basu tausayi Hydar yace, "Allah wuci zuciyar mahaifiyar mu. Kiyi ha?uri komai tsanani yana tare da sauk'i." Tayi murmushin takaici kana tace, "Zanje da kaina" ta fad'a tana mik'ewa dole suma suka mik'e suka rufa mata baya zuwa b'angaren sa zuciyar su cike da tunanin abinda zai biyo baya a can.

? ? ? ?? Lokacin da suka je ya gama ganawa da bak'in ba hadimai gabad'aya yana niyar hawa saman sa kenan Mama suka shigo ya juyo yana kallon su, ya bada umarnin kar wanda ya shigo masa b'angaren amma babu wanda ya isa ya hana Mama shigowa yasan shiyasa aka barta ta shigo ya lumshe ido ya bud'e ya dawo da baya ya k'araso inda take ya duk'a har k'asa kamar ko yaushe yace, "Barka da Rana."

Ajiyar zuciya tayi tana jin ruwa yana taruwa a idanunta ta dafa kansa da yake cikin rawani yellow wanda ya amshi fuskar sa tace, "Asad" ta fad'a tana d'ago k'afadun sa ya mik'e tsaye tana kallon fuskar sa sai taga ya sunkuyar da kai kamar yadda ya saba a wancan lokacin tace, "Asad kana lafiya?."

Zaiyi magana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login