Showing 135001 words to 138000 words out of 216282 words

Chapter 46 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

bai kamata ki bata ba, yana da dad'in khamshi sosai amma matsayin ta na wacce bata da aure bai cancanci ta shafa shi ta fita ba, yana da k'arfi d'azu ma naji khamshin sa a jikinta ya rik'e fatar ta sosai, ki kiyaye koda nan gaba kema kuma kar ki saka ki fita waje" Umma tana fad'a ta mik'e ta fita daga falon Yaya Ummi ta kalle ta tace,

"Tunda naga kina raba ido nasan baki da gaskiya, ke ina kika sami turaren?." Rauda tayi shiru ta rasa abinda zatace sai Yaya Ummi tace, "tambayar ki nake yi." Rauda tace, "a gidan su k'awata Farida ne na ganshi sai kawai yayi min dad'i na shafa, kin san in na cewa Umma haka fad'a zatayi min shiyasa nace a gidan ki na samu."

Yaya Ummi tace, "Munafuka" ta fad'a tana yar dariya tana ta janta da hira ita dai bata iya bata amsa da ta kulle idonta abinda ya faru take hangowa duk ta koma wani iri lokaci d'aya.

? ? ? Bayan la'asar Anas yazo bata so ma fita ba suka tilasta mata dole taje inda yake kamar ko yaushe yana zaune ta shiga ta zauna da sallama ya amsa ya kalle ta yace, "Amarya ta meya same ki haka kika rame a fuska?" Ya fad'a cikin kalar tausayi yana kallon ta.

Murmushin yak'e tayi tace, "Ina wuni." Jin muryar ta na rawa sai yace, "Taya zan wuni lafiya bayan kina kwance ke baki da lafiya? Ji yadda maganar ki take shaking fa."
"ZazzaSi ne da ciwon kai shima naji sauk'i."
"Anje asibiti?."
"Basai anje bafa naji sauk'i."

Yayi shiru yana kallon ta sai yaga kawai tana kuka hankalin sa ya tashi sosai ya matso kusa da ita yana fad'in, "Haba Rauda ya kike so nayi ne? Kukan na meye kuma?."
"Kayi hak'uri!" ta fad'a murya na rawa sosai tana kuka. Hankalin sa ya tashi babban tashin hankalin sa bai wuce ace za'a raba su ba yace, "hak'urin na meye Rauda bayan ni ya kamata na baki hak'uri nayi miki laifi jiya? Hak'urin me zanyi? Ki sanar dani dan Allah kin saka min tsoro a zuciyata."

Kai take girgizawa tana kuka duk ya rud'e hankalin sa ya tashi yana ta bata baki amma bata daina zubar da hawaye ba, wani yana bin wani haka take kukan hawaye na zuba sosai sun k'i tsayawa, jin bazata iya jurewa ba sai kawai ta mik'e tayi cikin gida a guje ta barshi a tsaye yana binta da kallo gaban sa yana fad'uwa.
[17/12, 10:41 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*067.*

? ? ? ? ? A guje ta shige su a falo zuwa d'aki ta fad'a kan gado tana kuka har suna jiyo gunjin kukan ta daga d'akin. Umma tayi murmushi tace, "Wai ka haifi yaro yace zai maka yawo, tun jiyan nasan akwai wani abun da yake damunta a zuciyar ta tana b'oyewa dan bata so mu sani." Yaya Ummi ta tashi ta bita d'akin lokacin tana fad'in, "Na tsani rayuwata bana son rayuwata, Allah ka aiko da mala'ikan mutuwa ya d'auki raina na mutu na huta da wannan bala'in da nake ciki."

"Ban tab'a dauka ilimin ki ba bashi da amfani ba sai yau Rauda, da bakin ki kike wannan addu'ar bayan kin san yinta babu kyau?." Rauda jin muryar Yaya Ummi ya saka tace, "Yaya ya zanyi? Ji nake zuciyata kamar zata fashe na rasa wanne kalar tunani ma zanyi."? Yaya Ummi ta zauna a kusa da ita tace, "Fad'a min me yake damun ki? Wani abun Anas d'in yayi miki kike yiwa kanki wannan fatan?."

Rauda ta fara jan numfashi alamun wacce taci kuka ta k'oshi Yaya Ummi tace, "Fad'a min mana meya faru, in baza ki iya sanar da Umma ba ni zaki iya fad'a min." Kallon fuskar Yaya Ummi take yi tana hawaye amma ta kasa cewa komai, taya zata iya fad'a mata ta aikata zina da tsohon mijinta? Taya zata iya ce mata tarbiyyar ta ta shekara ashirin da biyar ta watse a daren jiya? Ta zata ce mata ta aikata babban laifi a cikin mayan laifukan da Allah subahanahu wata'ala yayi hani da kusantar su duniya da lahira?. Ina baza ta iya ba gwara ta cigaba da barin sa a ranta koda zata mutu.

Yaya Ummi ta tab'a ta tace, "Sanar dani ina jinki." Ta sunkuyar da kai tace, "ni tunda naga jiya babar su Farida ta rasu daga shiga d'aki bata sake fitowa ba sai gawar ta shikenan nake jin komai ya yatsa min cak Yaya, hatta auren sai naji bana so wallahi" ta fad'a tana sake fashewa da kuka.

Yaya Ummi tace, "Bayan shi akwai wani abun a ranki, me Anas yayi miki?." Rauda ta girgiza kai tace, "Wallahi bai min komai ba Yaya, abinda na fad'a miki shine a raina kawai."
"Shine kike yiwa kanki wannan fatan?."
"Yaya Ummi ji nake inda Ummana ce ta rasu haka jiya a ina zan saka Raina? Wanne irin hali zan shiga?, tuna hakan shine yake sakawa naji komai ya fita daga raina Yaya."

Yaya Ummi tace, "Dukkan mai rai mamaci ne ai, yadda mahaifiyar ta ta rasu kema taki wata rana zata rasu, bama taki ba sai duniyar ta zama babu kowa a cikinta kaf sai mun mutu. Manzon Allah S.A.W yace muso duniya kamar baza mu mutu ba, sannan muso lahira kamar yanzu zamu mutu. In kika fahimci hadisin yana nuni akan abu biyu, kar tunanin lahira ya hana ki morar abinda Allah ya mallaka miki a duniya, haka kar shagala da abinda kika mallaka ya saka ki manta da lahira. Kiyi amfani da wannan hadisin sai kiyi rayuwar ki cikin sauk'i ba cuta babu cutarwa."

? ?? Kai Rauda ta d'aga alamun gamsuwa da abinda Yaya tace ta kuma cewa, "Haba kamar bake ba, ban sanki da kalamai irin wannan na marasa ilimi ba. Kaf gidan nan babu mai ilimin addinin ki ke Allah ya zab'a ya bawa haddar alkur'ani mai girma, haka duk gidan nan babu wanda Allah ya jarabta da k'addarorin da suke samun ki, ki nutsu ki kwantar da hankalin ki sai kiga komai yazo ya wuce kamar bai faru ba. Maman Farida kuma indai kina son faridan kin kuma ji mutuwar maman nata a jikin ki addu'a zaki dinga mata ba wannan kukan ba."

"To Yaya zanyi in sha Allah." Yaya Ummi tace, "Ina kika baro Anas d'in kika shigo a guje haka?."
"A falo na barshi."
"Haka kawai kin tayar masa da hankali sai ya d'auka ko fasa auren naku ma akayi. d'auki waya ki kira shi ki kwantar masa da hankali." Rauda tace, "Bazan iya ba yanzu."
"Yanzu zakiyi, d'auki nace."

? ? ? ? Ba yadda ta iya haka ta d'auki waya ta kira shi kamar jira yake ya d'auka kafin tayi magana yace, "Dan Allah nayi miki wani laifi ne Rauda?, meya faru kike bani hak'uri? Karki fad'a min abinda zuciyata bazata iya d'auka ba dan Allah." Kallon Yaya Ummi tayi sai Yaya Ummi ta tashi ta bata waje tace, "Kayi hak'uri babu abinda ya faru fa, zuciyata ce babu dad'i shiyasa kaga nayi haka, amma ka yafe min."

Ajiyar zuciya ya sauke jin muryar ta a tausahe alamun ta gama kukan yace, "Alhamdulillah, har naji dad'i farin ciki ya mamaye zuciyata. Me yake damun ki haka?."
"Rasuwa a gidan su k'awata Farida Maman su ce ta rasu bayan mun gama hira da ita shine abin yake tab'a min zuciya nake jin gwara na mutu kar hakan ta faru da Ummana Ina raye."

Ya tausasa murya yace, "Duk mai rai mamaci ne My love, yau gare mune gobe ga wanin mu, dole sai an mutu ko muna so ko bama so sai mun mutu kinga gwara muso mu saka ta a ranmu mu kuma tabbatar da zuwan ta nan da wani lokaci kad'an mai zuwa. Allah ya jiqan wacce ta rasu ya bawa y'ay'an ta hak'urin rashin ta."
"Amin" ta amsa tana lumshe idanu dan ita gabad'aya ma bata da wata k'awa Farida a duniya kawai sunan ne yazo zuciyar ta a jiya.

"Kinga mutuwar ta saka kin k'ara imani." Murmushi tayi kad'an tace, "Sosai ma kuwa."
"Shine aka so a jefa ni a wani hali na daban."
"Kayi hak'uri."
"Dolena ai na hak'ura, bakya laifi koda kin kashe dan masu gida."
"Balle ma babu d'an mai gidan da har zan kashe shi" ta bashi amsa hawaye na zuba tana murmushi.

Jin amsar da ta bashi sai yaji dad'i dan yasan ta dawo nutsuwar ta suka fara hira yana d'ebe mata kewa da kalamai masu dad'i har zuciyar ta d'an yi sanyi.

*&&*

? ? ? ? A zaune yake ya hard'e hannayen sa waje d'aya yana kallon k'asa yayi shiru yana saqa da warwara a zuciyar sa, shin me zaiyi? Wanne abu ya kamata yayi ne?. Shi kansa bashi da amsa hakan ya saka dole yayi shiru wai ko zuciyar sa zata sanar dashi abinda ya kamata d'in. Kansa ya kulle ta ko wanne b'angare a cushe yake cikin brain d'insa komai ya tsaya cak, da ya d'auko tunanin baya kai k'arshen sa sai yaji wani a zuciyar sa komai neman canja masa yake yi.

"My king" jidda ta fad'a daga bayan sa ya runtse ido sam baya son jin maganar ta gabad'aya inda yake balle kuma yayi ido hud'u da ita sai yaji zuciyar sa kamar ana hautsina ta sabida takaici.

K'arasowa tayi kusa dashi ta zauna tana kallon sa tace, "My king." Nan ma yayi mata banza bai amsa ba ta kai hannun ta kafad'arsa ta d'ora a kai tace, "My king ni ban san laifin da nayi maka ba kake share ni." Hannu ya saka ya cire hannunta daga kafad'ar sa ya kalle ta yace, "Please and please ki k'yale ni."

"Akan me zan k'yale ka bayan ni matar kace? In banzo wajan ka ba wajan wa zanje?." Ya cize bakin sa yana jin turirin b'acin rai yana taso masa ya kulle idanun sa ta sake cewa, "Ina buk'atar kulawar ka kodan babyn ka da yake jikina." Iska ya furzar ya mik'e zai bar mata wajan ta rik'e hannun sa tace, "In nayi maka laifi ka fad'a min wannan horon da kake yi min bazan iya jurewa ba My king." Hannun sa ya kwace ya shiga d'aki tana nan zaune.

Jim kad'an ya fito ya saka babbar riga ta blue d'in shaddar jikin sa ya saka hula ya d'ora hirami fari a kai taga ya nufi k'asa ta bishi da kallo kawai zuciyar ta na rawa sosai.

? ? ? ? Yana sauka shamaki da zagin sarki da kuma Suhail suka mara masa baya yana gama suna bin sa a baya abin mamakin sai suka ga ya nufi b'angaren Mama kai tsaye, yana zuwa zai shiga ya juyo ya kalle su duk sai suka koma gefe har Suhail suna fadin, "A fito lafiya d'awisu gwanin ado, a fito lafiya sarkin sarakuna, kyau, mulki, kud'i sai sarkin katagum, ga kuma uwa uba ilimi da sanin ya kamata, wane mutum da zai kama kafar mai martaba?. Kaf sarakun arewa a karkashin mai martaba suke, ta tamkar da dubu. A fito lafiya."

? ? ?? Shigar sa falo na farko duk hadimai suka zube jiki na rasa suna kwasar gaisuwa ya amsa yayi ciki su kuma suka fita. A zaune ya tarar da Mama da Hydar da kuma Aliyu da Suhaima a zaune a k'asan carpet Mama na kan kujara Suhima tana matsa mata k'afar ta.

Sallamar sa ya saka Hydar da Suhaima mik'ewa tsaye Mama da Aliyu kam ko gezau basuyi ba suna zaune, a ka'idar gidan sarauta rashin kunya Aliyu yayi ga shugaba k'arara dan bai bashi girma ba rashin mik'ewa tsaye da baiyi ba.

? ? ?? Yadda sauke a zube a k'asa shima haka ya zube duk suka zauna shima yana kallon Maman sa itama shi take kallo ta mik'e zaune sosai tana kallon sa tace, "Asad!." Kai ya saukar k'asa cikin taushin murya da rauni yace, "Allah ya k'ara miki lafiya da tsahon rai." Kallon Aliyu tayi ya kalle ta shima ta sake kallon Asad tace, "yau kaine a gabana kodai mafarki nake yi?."

K'afar ta ya dafa yace, "Ba mafarki mahaifita ta take ba da gaske ni d'in ne a gabanta a zaune." Mama farin ciki ya mamaye mata zuciya har ta kasa b'oyewa? tace, "Alhamdulillah, Allah shine maji rok'on bawa a koda yaushe. Asad da gaske kaine?."

Yayi murmushi cikin sanyi muryar sa ta ko yaushe yace, "Kwarai da gaske." Ya girgiza kai ta koma ta jingina da kujera tace, "Na jima ina mafarkin wannan ranar ashe zata tabbata ina da rai."
"Akwai wacce zata zo nan gaba wacce tafi na baya muni" Aliyu ya fad'a a bayyane yana kallon k'asa.

"Aliyu me kace?" Ta fad'a tana kallon sa sai a sannan ya tabbatar da maganar zuciya ta fito fili yace, "Afuwan ranki ya dad'e, wani tunanin ne a zuciyata." Mama ta sake kallon Asad ta mik'a masa hannu tace, "Zo ka rik'e hannuna Asad." Ba musu ya k'arasa inda take ya rik'e hannun ta ta sauke ajiyar zuciya tace, "Allah ya yiwa rayuwar ku albarka." Duk suka amsa da amin tace, "Meyasa kayi sakaci da rok'on Allah Asad?."

Shiru yayi yana kallon k'asa baice komai ba tace, "Koma meye ka dawo kamar wanda na sani a da, karka bari shaidan ya sake jinyar zuciyar ka." Ya girgiza kai yace, "Ki yafe min Mama, nasan na sab'awa mahaifiyata sau babu adadi amma ina neman afuwar ki akan komai. Bana sanin nayi sai bayan abin ya faru in naso na baki hak'uri sai na kasa, mahaifiyata kuma tasan bazan tab'a iya juya mata baya in ina cikin hankalina ba, ki yafe ni Mama."

Mama tayi murmushin farin ciki tace, "Babu komai Asad, ni nasan duka abubuwan da suka faru ba laifin ka bane aikin sirihi ne amma yanzu tunda ka dawo daidai Alhamdulillah."
"Godiya nake Mamana, Allah ya k'ara miki lafiya." Suka amsa da amin dukkan su kafin ta kalle shi tace, "Ya akayi kake iya doguwar magana haka ba tare da ka huta ba Asad?."

Yayi murmushi yace, "Ina k'okarin furtawa ne dan na ro?e ki afuwa akan abubuwan da suka faru a baya,na kuma tabbatarwa da Mamana Asad d'in da ta sani a baya ya dawo da izinin Allah amma sai Maamna tana taya ni da addu'a, ina ganin abubuwa sosai a rayuwata wanda k'iris ya rage su h????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? aukata ni."

"Na sani Asad, rik'e ragamar masarauta ba abu bane mai sauk'i. Addu'a yanzu aka fara yi maka ita in sha Allah duk wani mai son ganin bayan ka sai dai kai kaga bayan sa. Baga shi nan yanzu kana iya magana ba babu laifi, ai duk cikin addu'ata ne da wacce mahaifin ka yake maka."

Mama ta kalli Suhaima tace, "Suhaima kinga yana da kyau mu koma wajan Malamin nan baban yarinyar nan muyi masa godiya, maganin sa da addu'ar da ya bani tayi tasiri sosai akan duk abinda na saka a gaba."

Suhaima tace, "tsohuwar matar mai martaba kike nufi?." Dummm gaban mutane hud'u ya buga a wajan, Asad, Aliyu, Mama, da kuma Hydar. Babu wanda gaban sa bai fad'i ba har ita Maman nan take annurin fuskar ta ya canja ta kalle ta tace, "Lallai sai kin danganta ta dashi kenan? Ko kin fini sanin tsohuwar matar sace?."
Suhaima tace, "Allah ya wuci zuciyar ki. Gani nayi ta taimake mu badan ita ba da Mamana ta kwana biyu da rasuwa ta sadaukar da tata rayuwar sabida ta Mamana."

Mama ta kalli Suhaima tace, "tashi ki bani waje tunda kin gama basu labarin abinda ya faru." Suhaima da take mamakin Maman nata tace, "Allah ya wuci zuciyar ki, ki tashi lafiya" ta fad'a tana shiga d'akin ta ta barsu a zaune kowa yayi shiru a wajan.

? ? ?? Mama ta kawar da zancen tace, "Asad akwai abubuwan da nake so a aiwatar a cikin kwanakin nan." Asad yace, "Umarnin ki nake jira."
"Batun canja min wajan zama da muka fara mgana tun lokacin baya aka fara ginin wajan aka tsaya ina so a cigaba nan da sati zan koma can. Sannan duk ma'aikatan gidan nan a tabbatar an biya su albashin su domin bana tunanin ana biya a watannin baya, abu na gaba kuma matar ka Jidda."

Zirrrrr zirrrr zirrrr wayar Asad ta fara vibration ya kalli kiran yaga gwamna ne ya d'ago ya kalle ta sai tace, "Pick it."
"Godiya nake" ya fad'a yana d'aukar wayar ya saka a kunne. Ya jima yana amsa wayar kafin ya sauke ya kalle ta yace, "Taro na gaggawa na majalisar d'inkin duniya ya taso a England yanzu zan bar k'asar nan."

Mama tace, "Kai da wa zaku tafi?." Yace, "Nida shamaki da zagi sai Uncle."
"Jeka" ta fad'a jin babu Jidda a lissafinta yayi godiya yace, "Mama a dinga taya ni addu'a ina manta wasu abubuwan dana aikataa baya, koda an fad'a min bana sani nayi." Kai ta girgiza ya tashi ya fita yana fita zuciyar sa cike da jin dad'in maganar Jidda da ta katse aka rufa masa baya da kirari zuwa b'angaren sa.

Yana fita bai jima ba Aliyu ma ya fita Mama ta kalli Hydar tace, "halin Aliyu ya canja kamar bashi ba ka lura da hakan?." Hydar ya murmusa yace, "Na lura mama, abin farin ciki ne ganin hakan ko babu komai an daina mana gori da halayyar sa." Ta girgiza kai alamun gamsuwa kafin tace, "Allah yasa ba wani shirin yake yi mana ba." Hydar ya amsa da amin daga nan shima yy mata sallama ya fita.

*Bayan wasu kwanaki.*

? ? ?? Sati d'aya Asad yayi a London ya dawo aka cigaba da gudanar da mulki a satin ya ziyarci wata saukar alkur'ani ya yiwa daliban kyautar kud'i da kuma na alkur'ani mai girma. Yana k'ok'arin canjawa sosai amma bai canja d'in ba sai ya d'auko hanya sai ya karkace dan tuni jidda ta sake kamo lagon sa tsawa ko hantara ya daina ya koma mata kamar da sai abinda tace ake yi amma yana zuwa wajan Mama duk d ba sosai ba.

? ? ? ?? Aliyu kuwa kowa yasan ya canja bama kasafai yake zaman gidan ba wata rana bama a nan yake kwana ba yayi shiru har lokacin babu abinda ya aiwatar bincike yake a sirrance yana kama duk wani wanda yasan hana da hannu abinda aka masa, su Waziri tun suna jiran sakamakon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login