Showing 126001 words to 129000 words out of 216282 words

Chapter 43 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

"What are you saying Rauda...? Kin san mayar dake bayan na sake ki a Cairo. Why kike kiran kasancewar mu da zina?."

Ba tare da zato ba yaji ta d'auke shi da zazzafan mari ta ja baya ta nuna shi da yatsa idanun ta sunyi mugun ja baya da idanun ta jajaye tace, "Kar ka sake tab'a ni wallahi na tsane ka, ka matso kusa dani zan iya illata ka zan iya kashe ka Asad bana qaunar ka. Kun cika son kanku da yawa ku masu kud'i da mulki kanku kawai kuka sani bakwa duba lahira balle mu talakawan ku, kana yin abu kamar bakai ba. Allah ya isa tsakanina dakai wallahi bazan tab'a yafe maka ba har Allah ya tashi duniya" ta fad'a tana yin baya zata fad'i shi kam kallonta yake har lokacin saukar yatsun ta yake ji a fuskar sa abu kamar a mafarki.

"Ka sani ko hakkina ne kawai ya rage in na yafe maka zaka shiga aljanna wallahi sai dai a kaita wuta, nayi danasanin sanin ka rayuwata, meyasa ka shigo rayuwata bayan kasan ka shigo ne dan ka tarwatsa ta?. Me nayi maka kayi min wannan hukuncin.....?" Ta fad'a tana dafa bango tana sake fashewa da kuka jiri yana sake d'aukar ta.

Ya kasa koda motsin kirki kallon ta kawai yake rana ta farko da wata ta mare shi bayan marin da Mama tayi masa a kanta, nan take zuciyar sa ta harzuk'a yana jin d'aci a zuciyar sa yana binta da kallon da yake d'auke da ma'anoni kala-kala idanun sa sun juya sunyi jajur sabida b'acin rai.

Kanta a kife a bango tana kuka mai tsuma zuciya kanta yana ciwo ga jirin da yake d'aukar ta tana jan numfashi dak'yar, d'ago kanta tayi ta sunkuya ta d'auki mayafin ta ta yafa bata sake kallon sa ba ta k'arasa wajan k'ofa kamar wasa tana murd'awa ta jita a buWe ta juyo ta kalle shi tace, "Mazinaci bai dace da zama shugaban Al'umma ba, mai son kai bai dace da zama sarkin al'umma ba, banga nagarta da ake fad'a ba a tare dakai, banga ilmin da ake fad'a ba a tare dakai. Tirrr da masu hali irin naka ku kuma jira sakamakon ku tun a duniya Allah sai ya lalata rayuwar ku" ta share hawayen ta tace, "Bani da kud'in da zanyi Shari'a dakai a duniya amma ina da k'arfin guiwar yi dakai a lahira, sai ka fad'awa wanda ya halicce mu dalilin keta min haddi da kayi, wallahi sai Allah yayi mana hisabi nida kai Asad!. Na tsane ka tsana mai muni!" Tana gama fad'a masa hakan ta fita jiri yana d'aukar ta.

A bud'e taga gate d'in ta fita cikin ikon Allah taga mai adaidaita sahu ta fad'a ciki jikin ta na rawa sabida zazzaSin da yake jikinta suka tafi tana bin gidan da kallo tana hawaye tana ji a zuciyar ta har a tashi duniya bazata manta da gidan da ta aikata zina ba.



*Tofa wai Asad ne ko kuwa Aliyu ne?.*>??
[17/12, 10:41 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*064.*

? ? ? ? ? ? Kamar an dasa shi a wajan haka yake a tsaye k'am har ta fita bai motsa ba yana wajan jinin jikin sa yana tafasa kamar an kwashe shi an zuba a wuta ana dafa shi haka yake jin zafin na karad'e ilahirin jikin sa. Mazinaci! shi za'a kallah a kira da wannan sunan mai muni da rashin dad'in ji. Sai a sannan ya zauna ya hard'e hannayen sa yana kallon wani wajan daban zuciyar sa kamar ana gasa a tukubar tsire.

_Kayi gangancin bari ta raina ka, in ba raini ba ita har ta isa ta kalle ka ta fad'a maka wad'annan maganganun harda marin ka..? Mama ce kawai ta tab'a marin ka shima sau d'aya ne tak kuma a kan son tane sai ita. Wacece ita me take dashi da zatayi maka wannan cin fuskar? Dan kawai kana sonta ko me?._ Zuciyar sa tace take bashi wannan labarin ya furzar da iska ya jingina da kujera yana kallon fitilun da suke saman d'akin.

_Ba'a tab'a ci min fuska kamar yau ba, ban tab'a danasanin aikata abu kamar yau ba, ban tab'a jin haushin kaina kamar yau ba, ban tab'a jin haushin wata halitta kamar yadda nake jin haushin ta yau ba. Mari fa...ta kuma kira ni da mazinaci, zina abinda na tsana a rayuwata dashi zata danganta ni?. Duk matsayin da nake dashi a garin nan dama duniya baki d'aya na sauke shi na nemi yafiyar ta akan abinda ya faru duk da ba laifina bane ta sani amma shine zata yi min wannan rashin hankalin?. Allah ya sani banyi niyar mata komai ba magana kawai naso muyi but lokaci d'aya nayi losing control ya kamata ta fahimce ni tunda tasan ina sonta, Ni Asad wata mace ta mara ta kuma kirani da mazinaci....!_ A zuciyar sa yake wannan maganar yana girgiza kai alamun abun ya tab'a shi sosai ba d'an kad'an ba.

_Ni ba matar ka bace, har abada bazan zama matar ka ba, babu komai a tsakaninmu._ kalaman ta suka fad'o masa a zuciyar sa ya runste ido ya dafe kansa da duka hannayen sa yana mamakin dalilin ta na furta hakan bayan tasan lokacin da ya sake ta a Cairo ya mayar da ita.

Suya ransa yake masa sosai amma yasan shine ya jawo da bai d'auko tama da duk hakan bai faru ba gashi a banza a wofi tayi masa abinda har duniya ta tashi bazai manta ba, kai yake girgizawa kansa na sarawa yace, "Is okay!" Ya furta sai kuma ya kwab'e fuska kamar zaiyi kuka ya daki kujerar da yake kai yana cize baki alamun kalaman nayi masa ciwo sosai.

? ? ? ? Bai san adadin lokacin da ya kwashe yana haka ba sai agogo ya kalla yaga dare yayi ya tashi ya shiga d'akin ba jimawa ya fito ya rufe ko ina na fuskar sa ko waye kai baza ka gane fuskar sa ba ya fita daga falon gidan ya hau mota ya bar gidan gabad'aya.

? ? ? ? Rauda kuwa kuka take a cikin adaidaita sahun kamar wacce dangin ta kaf suka mutu a lokaci d'aya, mai napep din ma ya d'auka mutuwa akayi mata sai ta bashi tausayi yace, "Kiyi hak'uri baiwar Allah." Bata saurare ba kuka take yi suna tafiya taji yace, "Mun zo unguwar baiwar Allah." Kallon wajan tayi tace, "ga layin.....can" ta fad'a muryar ta na rawa sosai ya k'arasa da ita ta sauka yace, "ki bar kud'in, Allah ya jikan wanda ya mutu" ya fad'a yana jan napep d'in sa ya barta ita kuma ta nufi gida gaban ta yana mugun fad'uwa ko ta kan mai napep d'in ma bata bi ba.

Haka take takawa kamar wacce kwai ya fashewa a jikinta ta shiga cikin gidan ta same su a tsaye sun zubawa k'ofa idanu da alama ita suke jira, ganin hakan sai gabanta ya tsananta bugawa duk suka zubo mata ido harrrr sai taji ta sare ta tsaya cak a tunanin ta in ta k'arasa kusa dasu zasu ji wata alama da zata nuna ta aikata zina a wannan daren.

"Malam! Malam!! Gata ta dawo" Inna ta fad'a cikin d'aga murya sai ga Baba ya sakko daga sama, Umma binta kawai take da kallo kamar mai son gano wani abun a tare da ita sai sake ware idanunta take akan Raudan kafin tace, "Ina kika shiga Rauda? Tun bayan la'asar Ummi tace min kin tawo ina kika tsaya haka har takwas na dare?." Hawaye sharrr ta durk'usa a wajan kawai ta fashe da kuka, dukkan su sai hankalin su ya tashi Rahma tayo wajan ta a guje tana fad'in, "Anty Rauda meya same ki?."

Baba ya kalle ta yace, "Ana tambayar ki inda kika tsaya kina yiwa mutane kuka..? Ina kika je har dare yayi baki dawo ba sai yanzu?." Rauda bakin ta rawa yake yi ta rasa abinda zata ce dan Allah ya sani baza ta iya fad'a musu abinda ta aikata ba koda zata mutu. Kukan ya sake tsamari Umma taja tsaki tace, "ba magana ake miki bane zaki saka mu gaba kina yiwa mutane kuka? Gidan ubanwa kika je har dare yayi haka?."

"Naje...gidan.....Farida y'ar ajin mu ta islamiyya na duba Maman su, da naje sai na samu Mamanta ta rasu a lokacin da muke hira da faridan kuma mun gaisa da Maman, shine na tsaya akayi jana'iza dani sai na tawo. Umma mun gaisa fa da Maman nasu amma tana shiga d'aki sai gawar ta aka fito da ita......." ta sake rushewa da kuka kamar gaske duk sai jikin su yayi sanyi Baba ya tausasa harshe yace, "Amma meye amfanin wayar ki da bazaki kira ki sanar damu ba? Kafin nan yaushe kika fara zuwa gidan su k'awa baki fad'awa Umman ki ba?."

? ? ? "Kuyi hak'uri hanya ce ta bi dani sai na shiga" ta furta tana goge idanunta. Baba ya sauke numfashi yace, "to jeki ciki Allah ya jiqan rai, amma ko dan gaba kar ki sake aikata abinda kika yi kinji ko?." Ta d'aga kai alamun to ta mik'e tana jan k'afar ta ta shiga ciki ta kulle kanta a d'aki ta cillar da mayafin jikinta ta cillar da wayar ta cire doguwar rigar ta watsar tayi zaman dirshan a k'asa ta fashe da sabon kuka mai tsuma zuciya.

Had'a kai tayi fa guiwa ta cure waje d'aya tana furta, "Ka cuce ni, ka gama da rayuwata, ban tab'a aikata sabon Allah ba sai yau, me nayi maka kayi min wannan hukuncin? Me na aikata maka ka zab'i ka lalata min rayuwa...?" Ta sake fashewa da kuka tana jin yadda zazzaSi ya rufe jikinta gabad'aya.

Tunawa da tayi bata da tsarki sannan kuma batayi sallah ba sai ta mik'e dak'yar dan gabad'aya jikinta ciwo yake mata sosai ta shiga band'aki, ruwan band'akin yayi sanyi da yawa amma bazata iya fitowa tace zata dafa ba kar su zargi wani abun haka tayi amfani dana sanyin duk da zazzaSin da da yake jikinta.

Doguwar rigar da skin tried d'in da komai da ta cire ta cure su ta saka a leda bayan ta fito ta cusa can k'arshen wardrobe dan har abada bazata sake amfani dasu ba ta tsane su, _Meye na tsanar kaya Rauda bayan fatar jikin ki da ita aka aikata zinar?._ kalaman da suka zo ranta kenan ta buga kanta a jikin kwabar tana jin zafi a zuciyar ta sanyi yana ratsa jikinta.

A haka ta daure ta saka kaya ta kalli gabas da niyar tayar da sallah sai take jin kunyar mahaliccin ta zuciyar ta na rawa a haka tayi sallar magriba tayi i'sha ta tayar da shafa'i da wutri ta kwanta a kan sallayar ta cure a cikin hijjabi tana jan numfashi. Buga k'ofar ake yi ta d'ago ta kalli k'ofar ta mik'e dakyar ta k'arasa ta buWe k'ofar Ummulkhairi tace, "Anty Umma tace kizo kici abinci." Rauda tace, "na k'oshi, ki karb'o min maganin ciwon kai" ta fad'a tana komawa ta zauna a gefen gado.

Ba jimawa Ummulkhairi ta dawo da p.c.m ta bata had'e da ruwan pure water ta bata tasha ta koma kan gadon tayi lamooo hawaye na sauka ta gefen idanun ta. "Rauda!." Jin muryar Umma a kanta sai ta firgita abinka da mara gaskiya ta kalle ta tace, "Na'am." Umma tace, "meya same ki?." Rauda murya na rawa tace, "ZazzaSi ne Umma shima kuma kukan da nayi a gidan su Farida ne." Umma ta k'arewa fuskar ta kallo sannan tace, "Kin tabbata?." Rauda ta d'aga kai alamun eh.

Hannu Umma takai ta tab'a wuyan ta taji zafi sosai tace, "Jikin ki akwai zafi sosai kin sha maganin?." Ta d'aga kai alamun eh Umma tace, "dukkan mai rai mamaci ne ai nima wata rana haka za'a fitar da gawata dole kuma kiyi hak'uri." Rauda ta sunkuyar da kanta k'asa? tana jan numfashi.

Umma ta sake kallon ta tace, "Amma d'azu da kika gifta ni naji sabon khamshin turare a jikin ki wanda ban sanki dashi ba, yana da khamshi luma yana da k'arfi har yanzu ina jin tashin sa a jikin ki a ina kika same shi? Ko duk a gidan mutuwar kika shafa?."

? ? ? Rauda ta rud'e ta gigice ta ta mik'e zaune tana waige-waige bakin ta yana rawa gashi Umman ta zuba mata ido alamun tuhuma ita kuma alamum rashin gaskiya ya bayyana a tare da ita, Umma tace, "Ya naga kin rud'e kamar mara gaskiya ne?, ko wani ne ya baki turaren?." Sai Umma ta kai fuskar ta wuyan Rauda ta d'ago tace, "Akwai khamshin sa sosai a wuyan ki, waye ya baki kika saka bayan fitar ki?."

Rauda ta sosa kanta idanu na zubar da kwallah murya na rawa tace, "gidan....Yaya Ummi."
"Ita ya baki ki shafa?." Rauda ta d'aga kai alamun eh, Umma tace, "To yayi kyau, kwanta Allah ya k'ara lafiya. Amma ki daina kukan in kina so kanki ya daina ciwo" tana fad'a ta fice Rauda ta koma da baya ta kwanta ta sake fashewa da kuka.

Bata tab'a yiwa iyayen ta k'arya gashi a akan Asad ta fara, taya baza ta tsane shi tsana ta har abada ba? Ai ya gama cutar ta sai dai Allah yayi mata sakayya ranar alqiyama. Da wannan tunanin ta kwanta lamoo tana share hawaye ciwon kan yana raguwa a hankali, smun sassaucin ciwon kan sai bacci ya kwashe ta.

? ? ? ? *&&&.*

? ? ? Jidda ce zaune cikin d'akin ta waya rik'e a hannun ta fuskar ta da gwada alamun damuwa k'arara a kai tace, "Mum wallahi yau gabad'aya fa tsoro ya bani, ya canja daga daren jiya zuwa yau d'in nan, zancen da nake miki ko tun d'azu ya fita har yanzu bai dawo ba gashi dare yayi, kuma shi kad'ai ya fita dan baza ma ka gane shi ba in ka ganshi." Mum tace, "Uwar sa ta dage ai lallai sai ta dawo dashi yadda yake a baya, amma kin san me za'ayi?."

Jidda tace, "A'a Mum."
"Za'a sake sabunta aikin da akayi ne da alama ya fara lalacewa sai mun kuma yin sabo."
"Mum kika ce za'a kasheta, ai gwara a kashe d'in kawai a huta kinga da duk ba haka ba da bata raye."
"Na gwada hakan yafi sau biyar amma babu nasara, amma za'a sake gwadawa a karo na shida."
"Mum nidai ayi abinda za'ayi kar a raba ni dashi."

Mum tace, "karfa ki damu tunda ina raye ai zance ya k'are, zan turo Eman yanzu ta kawo miki wani magani ki tabbatar ya kwanta dake yau bayan kin sha wannan maganin zai mana amfani sosai." Jidda tace, "toh Mum zanyi." Tana fad'ar hakan ta yanke wayar Jidda ta sauke numfashi tana kallon wayar zuciyar ta a cushe, burin ta kar a raba ta da Asad gashi an d'auko hanya shiyasa duk sai ta tsorata a iya yau kawai.

Suhaima da take tsaye a k'ofar d'akin Jidda taji komai hannunta toshe da bakin ta take girgiza kai ta koma da baya a guje zuwa b'angaren Mama, da bak'i ta tarar da Mama hakan ya saka ta wuce d'aki tana ta zagaye burin ta bak'in su tafi duk minti biyu sai ta lekoo falon amma suna nan.

Bak'in suna tafiya Mama Jamila k'anwar Mama ta shigo Mama ta kalle ta tace, "Jamy kina son tafiyar dare ke kam." Tayi dariya ta zauna tana fad'in, "tun d'azu fa muka zo mun sauka a guest house ne mun huta sai yanzu na fito. Barka da dare Mama."

Mama tace, "Barkan ki, ya hanya?."
"Alhamdulillah."
"Ya kika baro mutanen Kano?."
"Suna lafiya Mama, ina Suhaima?." Suhaima da dama jira take ta fito a gigice tana fad'in, "Mama!." Mama ta kalle ta tace, "lafiya?."

Suhaima tace, "Naje apartment d'in Jidda naji tana waya tana cewa za'a sake sabunta aiki wanda aka yiwa Yaya Asad ya fara barin jikin sa, kuma wai gwara kawai a kashe ki in ba haka ba zaki sake lalata komai. Mama ina jin muryar Mum tana cewa ta saka a kashe ki har sau biyar babu nasara."

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!" Suka furta a tare suna mik'ewa tsaye Mama Jamila tace, "Suhaima kin tabbatar da abinda kike fad'a gaskiya ne?." Suhaima tace, "wallahi da gaske nake small Mama, abinda naji tana cewa kenan." Mama Jamila tace, "kinji ko? Na jima da sanin Sadiya da y'arta amanar ki suke ci gashi yunk'urin kashe ki ma suke yi. Yanzu mr gari ya waya Maman Suhaima?."

Mama kuwa tayi cak ta kasa cewa komai jikinta yayi sanyi ta sulale ta zauna akan kujera tayi tagumi da hannun ta duka biyun ta kulle idanun ta fuskar Mum tana gilma mata. Small Mama tace, "Bafa shiru zakiyi ba mataki za'a d'auka tunda Allah ya tona mata asiri dole tayi prison."

Mama dai bata iya cewa komai ba tayi shiru da alama ta rasa ma abinda zata ce small Mama ta durk'usa a kusa da ita tace, "Maman Suhaima kallona zakiyi wannan tagumin babu abinda zai haifar miki sai zallar damuwa, ki bari muje muci ubanta sannan mu saka a kulle ta bata fimu da komai ba."

"Jamy komai ya faru nice na jawo, nice na jawo komai Jamy, Da ban bata k'ofa ba da duk hakan bata kasance ba. Na fifita sama ta da kowa ko ku bana d'aukar shawarar ku kamar yadda nake d'aukar tata. Duk da karfafa zumuncin mu na had'a d'ana da y'arta na tsallake duka y'ay'an ku na raba shi da wacce yake so na bashi wacce nake so. Hasbunallahu wani'imal wakil" Mama ta furta tana tashi tsaye.

Small Mama tace, "Wacce yake so kika saka ya sake ta ita kuma wacce kike so yace bazai yi ba." Mama ta girgiza kai tace, "Jamy ku k'yale ta in sha Allah bazata ga fad'uwa ta ba" tana fad'a ta shiga d'aki Jamila ta bita rai a b'ace domin bata ga dalilin da zai saka a k'yale wacce take son kashe ta.

Tana shiga d'aki ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login