Showing 27001 words to 30000 words out of 216282 words

Chapter 10 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

ranta amma in ta tuna wata k'ila shine yace musu y'ar uwar sace sai taji shi take jin haushi daman tasan ba sonta yake yi ba.

Muhibba tace, "promise me zaki sanar dashi sak'ona zaifi sauraron ki a kaina dan naga yana ji dake, please sister help me before nayi loosing hankalina." Rauda ta k'ak'alo murmushi tayi amma bata ce komai ba ganin hakan ya saka muhibba tace, "Thanks you Sister, ina jiran feedback duk abinda yace ki sanar dani please. I'm coming" ta fad'a tana ficewa Rauda ta bita da kallo bata san lokacin da ta fara jin hawaye na sakko mata ba.

Idanun ta ta goge ta hana kuka a zuciyar ta tace, 'Meye naki na kuka Rauda?, daman kin san ke ba tsarar shi bace ba irin su sune daidai dashi; ta ya zaki had'a kanki da ita...? kalli kyawun ta fa ba dole ma ya so ta ba, ke kuwa kalle ki kowa yasan baku dace ba gwara ki samarwa kanki lafiya kar kiyi asarar hawayen ki.' Bata san ya shigo ba sai ganin sa tayi a kanta a tsaye yana kallon fuskar ta da mamakin meya saka ta kuka lokaci d'aya.

D'ago kai tayi ta kalle shi da hannu yayi mata alama da kukan me take yi, bata iya bashi amsa ba ta sake goge idanun ta tace, "Wacce ta fita yanzu Dr muhibba naji suna ce mata tace na fad'a maka tana son ka." Wara idanu yayi ya zauna a kan kujerar da take kusa da ita yana kallon ta sai kuma ya saki fuska annuri ya bayyana a kai yace, "Shine kike kuka?." Batayi zaton zaiyi magana ba ta d'auka zaiyi banza ne sai taji yayi sai ta kalle shi ta girgiza kai had'i da tab'e baki tace, "A'a wannan daban wancan daban."
"Ohhh!" Ya furta ba tare da yace komai ba yana kallon ta.

Duk sai ta tsargu ta kasa sakewa jin idanun sa a jikin ta sai ta sunkuyar da kanta jikin ta nayi mata wani iri abinda bata tab'a ji ba, hannun ta taji ya rik'e guda d'aya bata kalle shi ba sai abinda take ji a jikin ta taji ya k'aru. Baiyi magana ba itama batayi ba bai kuma ce komai bai kuma saki hannun ba yana rik'e dashi laushin hannun sa yana ratsa ta sosai, wani lokacin har bata so ya rik'e ta dan tasan zaiji hannunta da tauri ba irin nasa ba amma ya riga ya saba yana son rik'e hannun ta. Sun jima a haka kafin ya saki hannun nata ya koma danna wayar sa ba tare da yace komai ba itama kuma batayi karanbanin cewa ba.

*Bayan Kwana biyu.*

Haka suke zaman asibitin shiru babu wanda yake magana daga gaisuwa ya amsa babu abinda yake had'a su kuma kullum a wajan ta yake wuni har dare bata ma sanin lokacin da yake tafiya. Ranar saturday kwana biyar kenan da yi mata aikin k'afa sosai take jin dad'in ta bata jin ciwo ko kad'an a cikin ta har ji take ma zata iya takawa in aka barta, kula sosai take samu a asibitin tun ranar da sukayi magana da Muhibba bata kuma ganin ta ba sai taji dad'i a ranta domin har ga Allah haushi take bata.

Tana kwance da safiyar asabar likita ya shigo tare da Asad bai yi mata magana ba ya k'arasa ya d'ago ta ta zauna sosai yace, "Zaki fara tafiya." Dad'i taji a ranta sosai ta rik'e hannun sa sosai ya mik'e da ita aka zare k'afar daga cikin abinda take ta tsaya da k'afar mara ciwo likitan cikin harshen larabci yake sanar da Asad da ta taka gabad'aya ta tsaya ya gani.


Kasawa tayi sai a lokacin take jin zugi a k'afar wanda bata jishi sa ba farkon aikin Dr Khalifa da ya shigo yace, "Gwada tsayawa mu gani zaki iya." Ba musu take k'okarin mayar da nauyin jikin ta kan waccan amma ta kasa sabida zafi take mata.

"Kina jin ciwo?" Dr Khalifa ya tambaye ta. Kai ta d'aga alamun eh Dr Khalifa yace, "sake gwadawa zaki iya." A hankali ta tsayar da ita ta tsaya sai kuma tayi saurin d'agawa ta jingina da jikin Asad ya rik'e ta yana kallon su, wani iri take ji in ta had'a jikinta da nasa duk sai ta rud'e daurewa kawai take.

"K'afar tayi kyau amma zata dinga amfani da sanda before ta warware gabad'aya" babban likitan ya fad'a da larabci yana kallon Asad. Sandar aka kawo guda d'aya mai kyau a lokacin aka bata akace tayi tafiya da ita Asad ya koma gefe cikin ikon Allah sai gashi tana takawa da duka k'afar tata a hankali.

Asad yaji dad'in hakan ganin anyi nasara k'afar ta ta dawo akace ta zauna amma ta dinga yawan tashi tana takawa, ita kanta murna take na dawowar k'afar dan bata d'auka zata dawo d'in ba sai murmushi take tana jin dad'i Asad yana lura da ita ganin nata farin cikin sai nasa yaji ya k'aru.

*Nigeria.*

Mama an sauka a katagum ita da Suhaima tun daren juma'a ta wayi gari asabar a gidan aka dinga zuwa ana mata gaisuwa wanda basu samu damar binta can ba. Hydar ya shigo Aliyu ya shigo amma mamaki take da bata ga Asad ba bata tambaya ba amma ta baza idanu tana jiran ganin ta inda zai shigo.
Hydar ne ya kuma shigowa ta kalle shi tace, "Tun safe nake zaman jiran ganin Asad ban ganshi ba har azahar tayi, na kira shi bana samun sa yana ina?."

Hydar yace, "baya nan Takawa ya aike shi."
"Ina ya aike shi?."
"Ban sani ba" ya bata amsa a tak'aice yana fita da mamaki ta bishi da kallo kafin ta mik'e ta kimtsa ta nufi b'angaren mai martaba dan bata amince da wannan batun ba.? Tasan daman weekend ne shi kad'ai yake zaune yana karatu kamar koda yaushe ta zauna bata ce komai ba har sai da kai inda zai tsaya ya kalle ta yace, "Ya akayi? Naga kamar akwai magana a bakin ki."

"Allah ya k'ara maka lafiya wani abu ne ya d'aure min kai, Naga kowa ne banga Asad ba na tambayi Hydar yace min mai martaba ya aike shi amma bai san inda ya tafi ba shine nazo na tambaya naji in babu damuwa." Mai martaba yayi murmushi yace, "Kina son Asad sosai, bakya so ya matsa daga kusa dake amma kuma bakya son abinda yake so." Shiru tayi bata amsa ba yace, "K'warai Asad baya nan baya Nigeria gabad'aya na aike shi Egypt."
Gaban ta ya fad'i jin ya ambaci Egypt ta kalli mai martaba tace, "Takawa me yaje yi Egypt?."
"Aiki na."
Tayi shiru tana jin abinda yace tunani ta rasa abinda zatace a haka ta taso ta fito haka kawai zuciyar ta bata amince da abinda yace mata ba.

Da yamma tana zaune Suhaima ta shigo ta zauna a k'asan carpet tana kallon ta tace, "Mama wani abu nake ji a gidan nan ana fad'a but ban sani ba ko Mama ta sani." Mama tace, "meye shi?."
"Ji nayi ana cewa Asad yayi auren sirri ya tafi Egypt shida matar tasa, haka ne?." Gaban Mama ya fad'i ta kalli Suhaima da sauri tace, "wa kika ji yana maganar nan?."

"Jakadiyar Hajiya." Mama ta dafe kai tashin hankali ya bayyana a tare da ita tace, "Zai iya kasancewa tunda kika ji maganar daga bakin ta, kira min Hydar da gaggawa." Suhaima ta d'auki waya ta kira Hydar ba jimawa ya shigo yana kallon Mama yace, "Lafiya?."
"Hydar da gaske ne abinda nake ji a masarautar nan?."
Hydar da mamaki yace, "me ya faru?." Mama tace, "Da gaske ne Asad yayi auren sirri ya tafi da matar tasa Egypt?."

Gaban Hydar yayi mugun fad'uwa har rud'ani yaso bayyana a fuskar sa yayi k'okarin dannewa gudun kar ta fahimta tayi saurin ganowa ganin yayi shiru bai amsa ba cikin tsawa tace, "Ka amsa min da gaske ne......?!."
[17/12, 10:39 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*035.*

Shiru Hydar yayi ya kasa furta ko wacce kalma domin bai san me zaice mata ba duk tsoro ya dabaibaye masa zuciya har hakan ya bayyana akan fuskar sa. Ganin ya kasa magana ya saka ta girgiza kai tace, "abinda aka fad'a haka ne kenan ko?."

Sai a sannan Hydar ya dawo hankalin sa ya kalle ta yace, "Mama ban sani ba, ni ban ma ji maganar ba in ba yanzu da Mama take fad'a ba; abinda na sani Abba ne ya aike shi."
"K'arya kake Hydar! K'arya kake, bakin ku d'aya kai da Asad baya yin komai sai ka sani, ka fad'a min gaskiya kafin na gano da kaina ranka ya b'aci" ta fad'a tana nuna Hydar da yatsa.
"Allah ya wuci zuciyar Mama, amma ban sani ba, Mama zata iya tambayar Abba wata?ila haka ne amma ni ban san da hakan ba in ba yanzu ba."

Mama tayi k'wafa ta kalli Suhaima tace, "kira min number Asad." Suhaima ta d'auki wayar Mama tana kiran number Asad amma bata shiga ta sake gwadawa bata shiga ba ta kalli Mama tace, "bata shiga Mama." Mama ta kalli Hydar tace, "ka fad'a min inda kuka tura Asad, wanne aure ake zance yayi ban sani ba?." Hydar ya rausayar da kai yace, "Ban sani ba Mama, ban sani ba." Girgiza kai tayi ta wuce ciki a fusace Hydar ya fita da sauri ya d'auki waya yana turawa Asad message.

Hankalin Mama ya tashi matuk'a ta kasa zaune ta kasa tsaye zagaye kawai take yi a d'akin ta a haka akayi sallar magariba, jikin Mama har rawa yake buri kawai take yi sallar i'sha ta nufi b'angaren Mai martaba taji abinda yake faruwa wanda yake k'okarin tarwatsa mata tunani.
Ana idar da sallar i'sha Mama ta fito zuwa b'angaren mai martaba tana takawa a cikin taqama kamar koda yaushe.

"Allah yaja da ran Fulani, Allah ya biya miki buqatun ki, Allah ya jiqan mai martaba sarki, ya jiqan Hajiya babba ya raya mana Asad, Aliyu, da Hydar da k'aramar su Suhaima" wani dogari ya fad'a bayan ya zube a gaban ta yana jinjina. Kallon sa tayi a hankali tace, "Amin."
"Munji labari ashe yarima mai jiran gado ya angwance, Allah ya sanya alk....." cikin tsawa Mama ta dakatar dashi tace, "Kaii! K'arya ne wannan labarin k'anzon kurege ne kar na sake jin sa a bakin ka."

Ya rud'e yace, "Allah ya wuci zuciyar ki." Tsaki taja tayi gaba da sauri tana zuwa b'angaren mai martaba ta shiga bata same shi a babban falon ganin bak'in cikin gida ba sai a turakar sa wanda babu wanda yake shiga sai matan sa sai kuma Asad da ya amince dashi. A k'aramin madaidaicin falo yake a zaune yana cin tufa ya ganta kamar an cillo ta ta zauna a gefe tana wuci bata yi magana ba.

Bai kula ta ba ya cigaba da abinda yake yi dan yasan tatsuniyar gizo bata wuce da kok'i daman yasan labari baya tab'a b'uya a masarauta indai anyi sai ya fita wannan al'ada ce ta ko wanne gidan sarauta haka yake. Ganin bai saurare ta ba sai tace, "Ranka ya dad'e wani labari nake ji a masarautar nan wanda yake neman tarwatsa min lissafi da tunani na gabad'aya." Sai da ya kwashe sakanni baiyi magana ba kafin yace, "Ina jin ki."
"Magana nake ji tana wayo wai Asad yayi auren sirri ya tafi Egypt haka ne?."

Mai martaba ya kalle ta yace, "yanzu tutsiye ni kika zo kiyi?." Ta girgiza kai tace, "A'a ranka ya dad'e ba haka bane ina so na sani ne dan na samu peace of mind." Mai martaba yace, "babu lallai abinda zan fad'a miki yasa ki samu kwanciyar hankalin." Gaban ta ya fad'i ta kalle shi tace, "Kenan da gaske ne?" Ta fad'a tana dafe k'irjin ta da yake bugawa.
Mai martaba yace, "Abinda kika ji gaskiya ne, d'an ki Asad nayi masa aure da wacce yake so a karon farko na tura shi wata k'asar yaje can ya huta."

A firgice Mama ta mik'e ta dafe k'irji idanun ta a waje jikinnta har rawa yake yi tana so tayi magana ta kasa yi ta koma ta zauna ta dafe kanta tana ji yana juya mata sabida barazanar tarwatsewa da taji yana niyar yi. Ta jima a haka kafin ta sake kallon mai martaba dan dai tasan bazai mata k'arya ba amma tace, "dan Allah in wasa kake min ka daina zuciya ta zata iya bugawa wallahi."
Mai martaba yayi murmushi yace, "Ba wasa nake miki ba Rabi'atu abinda kika ji shi na fad'a, Asad d'an ki yayi aure yana kuma tare da matar sa wacce yake so."

Mama ta kalle shi a firgice tace, "Wacece wacce yake so d'in? Badai wannan gurguwar kake magana a kai ba?" Ta fad'a tana waro idanun ta waje jikin ta na tsuma sabida firgicin da take ciki. Mai martaba ya bita da kallo ganin yadda ta rud'e kamar wacce akace ya auri wata dabba ba mutum ba yace, "ita nake nufi, ba ita yake so ba?."

Mik'ewa tsaye ta kuma tana girgiza kai tana ja da baya tana kallon sa hawaye na k'okarin sakko mata daga idanun ta tace, "A'a kar kayi min haka dan Allah, bana son yarinyar; na tsane ta bana son ganin ta kusa da Asad, ba tsarin sa bace na ajin sa bace, shi da ita sai dai taimako dan Allah ka daina fad'a. Yace min ya barta tunda bana so meyasa za'ayi min haka!" Ta k'arasa fad'a da ihu tare da durk'ushewa a wajan ta fashe da kuka zuciyar ta na bugawa da sauri.

Mai martaba mamakin ta yake yi ganin yadda ta fita daga hankalin ta akan abinda bai kai ya kawo ba take wannan jan numfashi kamar wacce numfashin ta zai bar jikin ta ko mai ciwon zuciya. Kuka Mama take yi sosai guiwoyin ta a zube a k'asa tana jin zuciyar ta na tafasa gangar jikin ta kuwa kamar ana kwaro mata ruwan zafi tafasashshe.

"Ta yaya za'a ce d'an dana haifa shine ya auri talaka, gurguwa, mummuna mai tallan abinci?. Anyi min adalci kenan yanzu matsayina na wacce ta kawo shi duniya?, meyasa ba'a yi shawara dani ba aka yanke hukunci babu sanina?, shin bani da hakkin zab'a masa mata ne?, bani da hakkin da za'a fad'a min abinda aka yanke?!." Yadda take maganar da d'aga murya da alama ta manta da wanda take magana shiyasa ya zuba mata ido kawai yana kallon ta ganin yadda ta rud'e gabad'aya ga fita daga hankalin ta kalaman ma da take yi bata san tana yi ba.

"Bazan lamunci wannan abun ba zuciya ta zata iya tarwatsewa gwara na raba su koda nima za'a raba ni da duniya, babu ta yadda wuta da ruwa su had'u waje d'aya, babu ta yadda za'ayi zafi da sanyi su had'u waje d'aya, babu ta yarda za'ayi fari da bak'i su had'u waje d'aya haka babu ta yadda za'ayi Asad da ita su zauna waje d'aya. Sai na raba koda nima za'a raba ni da duk abinda na mallaka!" Ta fad'a da k'arfi tana dafe kanta da ya sara mata tana komawa da baya ta zauna tana cigaba da zubar da hawaye.

Mai martaba ya cigaba da kallon ta yayi murmushi kana yace, "Koda kin raba su Rabi'a anci riba domin Asad ya samu abinda yake so a karo na farko a rayuwarsa, dole in aka kalle ta ace tsohuwar matar Asad ce kinga kenan koda kin raba su baki ci riba ba itace taci riba. Balle ma yau auren nasu ya wuce sati in ma rabo ne yanzu za'a iya samu kad'an daga cikin ikon Allah, kinga ta ko ina tayi miki fintinkau tasan sirrin d'anki wanda har duniya ta tashi ke baza ki san dashi ba. Raba su kuma baki isa kiyi ba Rabi'atu auren su ya zama mutu ka raba takalmin kaza."

Dummm Mama taji a zuciyar ta ambatar ciki da mai martaba yayi ta d'ago da sauri ta kalle shi sai kuma ta dafe kai tana jijjiga kanta alamun sai yanzu tunanin ta yaje wajan, zabura tayi kamar mai tab'in hankali ta mik'e zata fita taji an rik'o hannun ta ya zaunar da a kan kujera zatayi magana yace, "Kar kice min komai, ke ba mai ja da ikon Allah ba? Har gidan su yarinyar kika je kika ciwa iyayen ta mutunci, kika tura a kashe ta, kika tura aka jiwa mahaifiyar ta ciwo; duka kinyi wad'annan abubuwan sabida ki raba su sai gasu tare shi da ita a inda babu ke a wajan, sai ki had'd'iye zuciya ki mutu domin indai ina da rai da lafiya babu abinda zai raba auren Asad da Rauda."

"A'aaaaaaaa! Bazai yu ba!" Ta fad'a da k'arfi tana sake fashewa da sabon kuka mai shashshek'a kamar k'aramar yarinya. Mai martaba ya kalle ta yace, "ki kuma zauna a nan ban baki umarnin fita daga nan ba sai da safe." Hannayen ta ta had'e alamun rok'o ta zube a k'asa tana kuka sosai amma ta kasa magana. Tsaki yayi yana jijjiga kansa sam halayyar ta haushi take bashi a komai nata kanta kawai ta sani bata hangen kowa sai kanta, tauye kowa take indai ita zata b'ulle to kowa ma ya dawwama a wajan bata san komai ba sai son kai shiyasa ya nuna mata shima yana da iko da Asad kamar ita.

"Asad d'ana ne meyasa za'ayi min haka?" Ta fad'a cikin kuka tana kallon sa. Baice mata komai ba ta had'a kai da guiwa tana kuka tana hasashen irin matakin da zata d'auka domin babu abinda zai hana ta raba auren koda nata auren zai mutu sai dai ya mutu bata damu, babu abinda zai hana d'aukar mataki koda za'a d'auki mataki a kanta itama, koda zai zama silar mutuwar kowa sai ta raba Asad da Rauda domin ruwa ba sa'an kwando bane ba.

*&&&*

? ? ? ? ? ? _Asad Mama tasan komai a yanzu, kasan abinda zakayi kafin ta raba ku, ka cigaba da addu'a dan tabbas Mama bazata barku lafiya ba. Matsayina na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login