Showing 69001 words to 72000 words out of 216282 words

Chapter 24 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

a ciki." Ta kalle su tace, "to ku bani waje zan shirya." Ba musu duk suka fita tayi dariya ta d'auko riga da zani cikin kayan ta ta saka ta tayar da sallar la'asar da take kanta bayan ta idar Ummulkhairi ta shigo mata da abinci.

Karb'ar abincin tayi taci kad'an bada yawa ba kafin ta ajjiye ta kwanta amma sai ta kasa baccin. Babban tashin hankalin ta abinda zata fad'a musu in suka tambaye ta hakan ya saka ta dinga juyi a haka baccin ya d'auke ta.


Sai magriba ta tashi tunda ta tashi take jin hayaniya ta k'aru bata fita ba sai da tayi sallar magriba sannan ta fito falon sai kuwa akayi ihuu Rahma ta tawo a guje ta rik'e ta tana murnar ganin ta, itama rik'en ta tayi tace, "Nayi kewar ki Rahma."
"Nima haka Anty Rauda, kinyi kyau har fari kinyi ko bleaching kika fara a can?." Murmushi kawai tayi bata ce komai ba Rahma ta kuma cewa, "Kan uba! Kinji fatar hannun ki laushi kamar audiga." Ita dai bata ce komai ba ta tawo cikin falon dan taga Baba a zaune ta k'??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????arasa ta durk'usa har k'asa tace, "Barka da dare Baba."

Baba ya kasa rufe baki sai dashe hak'ora yake yi yace, "lafiya lau yar albarka. K'afa tayi lafiya ko?."
"Eh Baba."
"Ma sha Allah, haka ake so ai. Kinga gidan mu yadda ya koma ko ta dalilin ki?." Gaban Rauda ya yanke ya fad'i tayi murmushi kawai bata ce komai ba kafin Baba ya kuma cewa, "Tare kuka dawo dashi mijin ki?." Gaban ta ya tsananta bugawa tace, "Eh tare muke."

Baba ya sake washe bakin sa farin ciki yake ji kamar ya goya Rauda sabida alkhairin da ta kawo masa kana yace, "Shi ya kawo ki nan?." Rauda had'd'iye yawu tace, "A'a ya saka a kawo ni ya wuce gida zaizo daga baya yace." Baba ya sake sakin murmushi yace, "Allah sarki d'an albarka." Rauda dai bata iya cewa wani abun ba kuma jikinta yayi sanyi har Umma ta lura da hakan Baba yace, "Bara na fita na samo miki gashashiyar kaza kici dan nasan bakin naki ya saba da cin kazar larabawa" ya fad'a yana fita Umma ta bishi da kallon mamaki.

? ? Gabad'aya Rauda ta bar nutsuwar ta had'a idanun da sukayi da Umma sai ta d'an wayance tayi murmushi tana sosa kai k'annen ta suka fara bata labari wannan yace ga abinda ya faru wannan ma ya fad'a haka suka deb'e mata kewa har akayi sallar i'sha tayi sallah ta shiga d'akin da tayi wanka d'azu.

Umma ce ta biyo bayan ta ta ganta a zaune tayi tagumi fuskar ta gabad'aya ta nuna damuwa k'arara ta zauna kusa da ita tace, "Rauda akwai wani abun ne naga kin canja gabad'aya?." Rauda ta kalli Umman cikin alamu na rashin gaskiya tace, "Babu komai Umma. Nayi mamakin gama gidan nan cikin y'an kwanaki haka Umma, ki duba yadda yayi kyau kamar anyi shekara anayi" ta fad'a dan ta kawar da waccan maganar.

? ?? "Banda abin ki Rauda in da kud'i meye baza'a yi ba? Ai aiki akayi bana wasa ba kusan kwana suke ana aikin gidan nan lokaci kad'an aka gama ya bada umarnin zuba komai na gidan nan da kike gani cokali namu bamuyi amfani dashi ba duka sabo aka zuba mana namu bayarwa muyi wasu muka siyar. Kayan abinci kuwa kamar kasuwa dan wallahi zan iya ce miki akwai kayan abinci na shekara a gidan nan, banda kayan miya da nama da kaji da ake kawo mana duk sati. Ai mahaifin ki yaga amfanin haihuwar y'a mace da kullum k'orafin sa bai ga amfanin haihuwar mace tazo a babba a gida ba."

Rauda ta girgiza kai tana kallon gidan fanka tana ta juyawa a d'akin tace, "solar ce wannan ko nepa?." Umma tace, "Solar akayi mana Rauda, awa ashirin da hud'u da wuta a gidan nan sai dai mu gaji mu kashe. Ke y'an unguwar nan fa cewa suke wai mahaifin ku yankan kai ya koma shiyasa yayi arzuk'i lokaci d'aya, wasu kuma suce ya siyar dake ya karb'i kud'in magana dai kala-kala; kaf unguwar nan babu gida mai kyaun wannan fa."

Kafin tayi magana Umma tace, "Duk ranar juma'a kuma da aiken da za'a yo mana kud'in cefane, abinci baya yankewa a gidan nan Rauda madara, milo dasu ake shan shayi a gidan nan, duk baki ga mun canja munyi haske ba?. Sai yanzu na gano Asad ne ya siya miki magani ba Anas ba."

? ? ? Ambatar Anas da Umma tayi sai da gaban Rauda ya yanke ya fad'i tayi shiru bata ce komai ba Umma tace, "Bamu da abinda zamu biya yaron nan ai sai addu'a, yayi mana abinda bamu kawo zai faru ba cikin rayuwar mu ba." Rauda ta girgiza kai hawaye na neman zubo mata tace, "Haka ne Umma."

"Ina Raudan take!" Yaya Ummi ta fad'a tana shigowa ganin Rauda ya saka ta tawo da sauri tana fad'in, "Mutanen Egypt." Umma ta kalle ta tace, "A daren nan kika fito Ummi?."
"Shine ya kawo ni a machine Umma, bazan iya zama har gobe banga Raudan ba" ta fad'a tana rik'e hannun ta cikin kewa.
"Kan bala'i, Umma kinji laushin da hannun Rauda yayi? Ke wai wankan madara kike a can ne naga gabad'aya kamar an sauya miki halittta."

Dariya kawai Rauda tayi amma ta kasa cewa komai Yaya Ummi tace, "Zama dashi ya koya miki rashin magana kema ko sarautar ce ta shiga jikin ki?." Rauda tayi dariya tace, "Haba Yaya sai kace chajin waya?." Sukayi dariya gabad'aya tace, "to gani nayi sai maganar da kika ga dama kike bada amsa. Rauda kalli wayar hannun ki a k'alla ta kusa miliyan; yarinyar nan Allah ya yarda, Baba me cewa waye zai d'auke ki yazo yaga ikon Allah."

Umma tace, "ya sakko ai yanzu, abin mamaki shine ya tafi siyowa Rauda kaza da kud'in sa." Yaya Ummi tayi dariya tace, "To Umma ai dole ki duba kud'in da suke shigowa hannun sa ta dalilin wannan napep d'in yana zaune sai dai a kawo masa balance. Me zamu ce da yaron nan mu in ba godiya ba? Abinci da gagarar ku yake a gidan nan, ga talla da yake d'ora musu ashe ta sanadin tallan Allah zai b'ullo mana da alkhairi."

Rauda tayi dariya tace, "Baba akwai drama ai." Yaya Ummi tace, "k'afa ta warke Rauda."
"Ta warke Yaya."
"Alhamdulillah, bamu da abinda zamuce sai dai mu gode Allah Rauda. Ina tsohuwar wayar taki a bani?." Rauda ta kalli wayar hannun ta kafin tace, "Wallahi tun a lokacin da wayar da tsohon layin ya saka su a shara."

"Shara! Meyasa to bai bar miki ba?." Rauda tace, "ban sani ba wallahi" ta fad'a a tak'aice dan kawai dauriya take. Umma tayi murmushi kawai bata ce komai ba Yaya Rauda tace, "kuma su a can babu wanda zai d'auka nasan bola za'a kai ba kamar mu Nigeria ba. Lallai yana da kishi dan nasan yasan Anas ne ya baki shiyasa ya yar da ita."

Umma tace, "Da kika ce Anas sai kika tuna min, bayan tafiyar ki baifi da sati ba yazo neman ki yake shaida mana matar da zai aura Allah yayi mata rasuwa ya dawo wajan ki a karo na biyu muke shaida masa auren ki. Baki ga yadda ya gigice ba Rauda har kuka sai da yayi ya bani tausayi sosai a nan take kuma yayi tawakali yayi miki addu'ar samun zaman lafiya tun daga ranar kuma bai yanke zumunci damu ba Rauda yana yawan zuwa mu gaisa har ya zama ma da yazo zai shigo gidan nan kai tsaye."

Rauda jikin ta duk yayi sanyi sun kasa gane bata son maganar sabida abinda take ji a zuciyar ta tace, "Allah Sarki, Allah ya gafarta mata." Suka amsa da amin. Yaya Ummi tace, "Ina shi mijin naki wai?." Rauda tace, "ya wuce gida bai zo nan ba."
"Ai gobe dole na dawo ko dan na ganshi dan nasan dak'yar in ba goben zai zo ba." Murmushin yak'e Rauda kawai tayi bata ce komai ba domin tasan bazai zo ba har abada.

Umma tace, "Ummi tashi ki tafi dare yana kuma yi." Yaya Ummi tace, "ya zan tafi ba tsaraba? Ke Rauda yanzu baki tawo min da komai ba?." Umma ta rik'e baki tace, "Amma anyi yayar banza, ita da taje jinya ina ita ina yo tsaraba?." Rauda tace, "bara muga akwai dogayen riguna Allah yasa suyi miki naga kin zama k'atuwa" ta fad'a tana tashi ta janyo akwatin ta ta bud'e tana fito da kayan.

Cikin ikon Allah duk wad'anda ta siyo musu matsayin tsaraba duka sune a ciki har dana Baba nata ne babu sosai sai guda biyu; ta d'auko ta Umma ta bata ta bawa Yaya Ummin ta sauran tace, "Gata Baba, gata Inna, gata Rahma. Wannan takalmin na Ummulkhairi ne dana na Khalil da Sammani, wannan doguwar rigar kuma ta Yaya Shamsiyya da Yayar mu da Yaya Nafisa da Yaya fariha." Umma tace, "Kice kud'i kika saka ya kashe haka." Rauda tace, "A'a Umma ni bance zan yi tsaraba bama shine ya saka ni."

Yaya Ummi tayi dariya tace, "wannan doguwar rigar gobe da ita zan fito na yiwa talauci barazana ko babu komai na saka rigar Egypt. Allah ya barku tare Rauda ya k'ara muku zaman lafiya me d'orewa; shiyasa kake murna in k'anwa mace ta samu jin dad'i domin gabad'aya iyalan gidan kune suka samu." Umma tace, "Gaskiya kam. Allah ya k'ara muku zaman lafiya ya saka mutuwa ce zata raba ku."

Sharrrr hawaye suke fara zubowa daga idanun Rauda tayi sauri ta goge Yaya Ummi da ta kula tace, "Dole kiyi kuka Rauda jin dad'in duniya kin same shi ke kam sai dai fatan ki samu na lahira." Murmushi kawai tayi zuciyar ta nayi mata ciwo tana sake goge idanun ta.

Umma tace, "Ummi ki tashi ki tafi itama a barta ta huta dare yayi." Rauda tace, "Ai a can Umma ba'a bacci da daddare sai da safe dare shine lokacin zuwa kasuwa da yawo." Umma tace, "haka akace su can daman dare shine rana." Yaya Ummi ta mik'e tace, "Rauda na wuce gobe zan dawo da wuri na sha labari" ta fad'a tana ficewa Rauda tayi dariya kad'an. Umma ta kalle ta tace, "ki kai musu tsarabar sai kizo ki huta kin dawo Nigeria nan ba can bane."

Tashi tayi ta kwashi kayan ta fita dasu ta kai musu suka dinga ihu ana murna, Baba ma a lokacin da ya shigo ta bashi tasa ya bata kaza yana ta saka mata albarka kamar bashi bane yake kiran ta da mujiya ba.

? ? ? Lokacin da ta koma Umma bata d'akin ta zauna ta bud'e kazar da Baba ya bata amma sai taji ta kasa ci gabad'aya ta rufe Ummulkhairi ta shigo ta bayar ta bawa Umma. Kwanciya tayi a kan gadon tayi lamoo kamar marainiya hawayen da take ri?ewa suka sakko mata ta fara kuka mai sauti ko zata samu sassaucin da take ji a zuciyar ta.

"Me zance musu ni Rauda? Nace musu ya sake ni sabida Maman sa bata sona?. Suna ta fad'ar hidimar da akayi dasu sabida ni, suna tayi min addu'ar cigaba da zama dashi ya zasu ji in nace musu ya sake ni? Ya zasu ji in nace musu na zama bazawara a cikin sati hud'u kacal?, ya zasu ji in na fad'a musu irin wula?ancin da akayi min?. wa'inna ilaihir raji'un, ya zanyi ni Rauda nayi shiru ko na fad'a musu?. Daman can nasan sai hakan ta faru dole ya rabu dani daman akwai dalilin yin auren" Ta kuma fashewa da kuka mai tsuma zuciya.
"Anty Rauda kukan me kike yi?" Ummulkhairi ta fad'a tana shigowa tana kallon ta.

Goge idanun ta tayi da sauri ta kalle ta tace, "kaina ne yake min ciwo kad'an, karb'o min magani wajan Umma in akwai." Da to ta amsa ta juya Rauda ta tashi ta goge idanun ta sosai Khairi ta dawo da magani ta bata tasha ta haWa da ruwa, Ummulkhairi tace, "Ki kwanta to Anty zaki ji dad'in ciwon kan Umma tace gajiya ce." Ta amsa da to ta tashi ta canja kaya ta saka na bacci ta kwanta zuciyar ta cike da saqe-saqe.

*&&&*
? ? ? ? ? _Love you girl no get holiday, I do am all day everyday uhmmmm I need no one like oh no no, love you girl i get pom pom shey if u go know how I want pom pom shey ooo? I need no one like i need you oh no no? mmmmm, shower body down and come my lover mmmmm make i dirty you well with my love la la la, and I say hop on my bed let's sin, baby coman good sin good sin, no be bad sin good sin good sin._ wakar da take tashi kenan tun daga farkon estate ake jin sautin ta da muryar y'an mata da suka had'a baki suna yi kamar karatu.

Cikin harabar gidan y'an mata ne y'ay'an masu kud'i kai da ka gansu da wayoyin hannun su kasan ba y'ay'an talakawa bane. K'atuwar banner ce a manne a bango anyi mata ado da balloons a jikin banner d'in an rubuta _welcome to Jidda's bridal shower_ an had'a da k'aton hoton ta da yayi kyau sosai kanta babu d'ankwali kamar ba y'ar musulmai ba.

An yiwa gidan ado an zuba kujeru ana kid'a ga kayan ciye-ciye da shaye-shaye kamar kamar an dad'e ana tsara abin. Rawa suke matan cikin pink d'in dogayen riguna amaryar kuma ta saka blue mai haske kanta babu d'ankwali ta nad'e gashin ta tayi bala'in kyau kamar ba ita ba sai chasar rawa suke ana hotuna da video.

Tun k'arfe takwas suke rawa ana kid'a har k'arshe sha d'aya a lokacin suka fara watsewa da nufin sai gobe za'a kuma had'uwa masu decoration suka cire kayan su kowa ya kama gaban sa. Jidda da Eman? bayan sun cire kwalliya an kwanta a gefe ana ta sauke numfashi gajiya Mum ta shigo tana fad'in, "kun sha rawa ai dole ku gaji ai." Eman tace, "Sai ma gobe ai Mum, daman ma abin yazo mana a haka da wlh event biyar zamuyi."

Mum tace, "Allah ya kaimu goben, tunda ba'a nan zakuyi ba kuje ku k'arata." Eman tace, "Mum muna so fa gobe Asad yaje dinner d'in kinga ba'a yi dinner babu ango ba." Jidda tace, "abinda yake raina kenan kika riga ni fad'a, in bai je dinner d'in nan gobe ba an gama wula?anta ni a idanun k'awayena." Mum ta rik'e k'ugu tace, "Amma dai kin san Asad bazai je wajan dinner ba ko? Kamar kin san halin sa basai an fad'a miki ba."

"Amma Mum wannan ai bikin sane yana da kyau ya ajjiye duk wata halayyar sa ya bari ayi shagali, in fa ranar ta wuce baza ta sake dawowa ba har abada." Mum ta kalli Jidda da take maganar tace, "Kar ki sakawa zuciyar ki domin ba zuwa zaiyu ba na tabbatar, kar abin yazo ya dame ki gwara kar ki saka rai." Eman tace, "Sai mu had'a shi da Mama dan baza mu bari a dinga munafurcin bikin mu kamar yadda muke na wasu ba."

Mum tace, "ku kuka sani dai nidai na fad'a muku" tana fad'a ta fita ta barsu. Jidda tace, "Eman bafa zan bari hakan ya faru ba gaskiya." Eman tace, "Ina bayan ki dole mu san abinda zamuyi." Daga haka suka cigaba da tsara yadda abu zai tafi kafin goben.

? ? ? Kamar yadda suka tsara washe gari Thursday tun safe k'awaye ta suka cika gidan aka sake k'aramin event mai taken henna party aka yi musu henna zuwa azahar aka fara make up bayan la'asar sun shirya dukkan su magriba ake jira a tafi wajan event. Duk wata hanya da Jidda tasan zata bi Mama ta saka Asad yazo tayi amma hakan babu nasara domin ta sanar da ita bazai zo ba tayi taron ta ita kad'ai kawai gabad'aya hankalin ta ya tashi.

Magariba tayi k'awaye aka fara tambayar zuwan ango duk taron ya fita a kanta ta fara k'ok'arin kuka sabida a ganin ta ba k'aramin wula?anci bane rashin zuwan sa. An firfito harabar gidan Jidda tayi kyau cikin gown ash colour an yi mata mayafi mai adon kalar fabric d'in? a jiki yana jan k'asa sosai, tayi kyau ba kad'an ba henna hannun ta red and black ya haska fatar ta in ka kalle ta sai ka kuma sabida kyaun da tayi, fuskar ta a cushe babu walwala kana gani kasan ranta a b'ace yake daurewa kawai take yi. Babbar k'awar ta Farha tace, "Jidda kince yana hanya yana ina? Ana can fa an cika jiran mu kawai ake yi?." Idanun ta suka ciko da kwalla zatayi magana kenan ash d'in mota kirar benz ta danno hancin ta cikin gidan ta haske su da fitar motar.

Kowa sai da ya kalli motar sabida kyaun ta da yadda aka d'auki hankalin su aka k'i bud'e koda tagar motar Eman ta kalli Jidda itama ta kalle ta Eman ta fara takawa zuwa gaban motar ta kwankwasa glass d'in tana jira a sauke taga waye. Zuuuu aka sauke glass d'in motar ba Eman kad'ai ba hatta Jidda da take tsaye a baya sai da gabanta yayi mugun fad'uwa suka zaro idanun su waje cikin d'inbun mamakin wanda suka gani zaune a cikin motar..........
[17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*048.*

? ? ? ? Eman baya tayi farin ciki ya cika zuciyar ta da fuskar ta lokaci d'aya hakan ya bayyana a gare ta domin basu tab'a tunanin ganin sa a wannan lokacin ba ta kalli Jidda cikin iyayi da yanga da nuna sun isa tace, "Sis your groom is here." Jidda tayi b'oyayyiyar zuciyar nan take fara'a ta bayyana a tare da ita ta fara takawa a hankali da niyar nufar motar.

K'awar ta d'aya ce ta rik'e mata hannu tace, "Eman kice masa ya fito muyi pics before muje can please." Eman ta kalle shi a lokacin glass d'in motar yake kallo tace, "prince can u come out please?." Agogon Rolex d'in hannun sa kalar golden ya kalla ya kalli Eman ya sake d'auke kansa alamun bazai fito ba.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login