Showing 207001 words to 210000 words out of 216282 words

Chapter 70 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

yake yi ta k'arasa inda yake ta wara hannayen sa ta shiga ciki ta mayar ta rufe ta kwanta a jikin sa.

Baice mata kanzil ba ya cigaba da danna wayar sa dan yasan ba yunwa take ji ba taci abincin da Suhail ya kuma kawo musu, "Sultan!" Ta furta a hankali tana kallon sa. Bai kalle ta ba ta kuma cewa, "Sultan nayi maka laifi?."
Nan ma baice komai ba ta sauke numfashi tace, "Kayi ha?uri."

"Kar kiyi min kuka" ya fad'a bai kalle ta ba jin muryar ta fara rawa ta mayar da hawayen ya cigaba da abinda yake yi. Sun jima a haka kafin yace, "Nasan kin san Khalifa har kina da number sa meye naki da zaki tambaye ni? Tare kika ganmu ko?." Ta d'ago ta kalle shi tace, "Kayi ha?uri ban fad'a da wata manufa ba, Khalifa ya taimake ni kuma muna zumunci da matar sa. In baka son hakan zan daina."

K'aramin tsaki yayi baice komai ba ganin hakan duk sai jikin ta yayi sanyi tace, "Kayi ha?uri dan Allah bazan sake yin maganar sa ba." Nan ma bai kulata ba tayi shiru bata ce komai ba shima kuma baice ba.

Sun jima a haka babu wanda yake magana sai danna waya da yake yi ita kuma tana kwance a jikin sa. Wayar tace tayi k'ara ta d'auka ba tare da ta bar jikin sa ba ganin Rahma ce take waya tace, "Hajiya Rahma." Rahma tace, "Anty Rauda nida wallahi fushi nake dake har yanzu baki zo ba gashi su Umma sunyi tafiya sai ni kad'ai."

Rauda tayi dariya tace, "Kiyi hak'uri ki daina fushi in sha Allah zanzo gidan, bazata zan miki sai dai kawai ki ganni." Rahma tace, "Allah ya kawo ki. Shima jiya yake cewa kink'i kizo mana ko sau d'aya nace nasan kina hanya yace shi ai yayi fushi." Ta sake yin murmushi? tace, "Ki basa ha?uri zaku ganni in sha Allah in nazo sai kun kore ni."
"To Anty Allah ya kawo ki. An yiwa su Umma da Inna abin alkhairi fa Allah ya biya mai martaba ya saka masa da gidan aljanna. Kinga yadda y'an uwa suke murna da wannan abun da ya faru kuwa? Ai Anty Rauda addu'ar da kika sha dake dashi ba y'ar kad'an bace."

Rauda tace, "Amin Rahma. Ban ma sani bafa ni sai yanzu da Yaya Ummi take sanar dani, ashe har sun kwanaa d'aya."
"Wallahi kuwa Anty, abu ai yayi mugun dad'i. Harda Baba malam fa." Rauda tace, "Au harda shi? Ni da yake ban ma gama jin labarin ba na kashe."

"Wallahi harda shi." Rauda tayi murmushi tace, "sun tafi sun bar mu daga ni sai ke." Rahma tace, "Lahh nima passport dina ne bai fito ba da ya fito zamu tafi nida shi." Rauda tace, "Ma sha Allah. Ina taya ki murna."
"Na gode Antyna." Daga nan sukayi sallama ta yanke wayar tana fad'in, "Nidai naga ranar da zanje gidan ki Rahma, in sha Allah zanje ko zan huta da gorin nan da ake min."

Gaban ta ya fad'i ganin kallon da yake mata ta had'd'iye yawu tana kallon sa yace, "D'aga ni." Jin yadda yayi maganar ya saka ta mik'ewa ya tashi ya shiga d'aki ta bishi da kallon mamaki ganin ya sake birkicewa. Sai da ta bari ya d'an jima da shiga sannan ta tashi tabi bayan sa ta ganshi a zaune yayi shiru ba tare da? yana wani abun ba.

Ta zauna kusa dashi tana kallon sa tace, "Sultan kayi ha?uri naga ranka ya b'aci." A fusace ya kalle ta yace, "Waye shi d'inki da zaki je gidan shi? Waye a wajan ki da zaiyi fushi dan baki je gidan sa ba?. Har abada baza kije ba!" Ya fad'a yana tashi tsaye ya juya mata baya ba tare da yace komai ba.

Yanzu ta gano laifin ta wato maganar gidan Anas da maganar Khalifa itace laifin da tayi masa sai ta tashi ya isa inda yake ta rugume shi ta baya ta kwanta akan bayan sa tace, "I'm sorry Sultan bazan sake ba in sha Allah. Rahma k'anwata ce dan naje gidan ta a ganina ba wani abun bane dan ita naje badan mijin ta ba amma tunda baka so bazan je ba, kayi ha?uri dan Allah."

Shiru yayi bai amsa ba yana jin zafin kishi yana taso masa daga cikin zuciyar sa yana sauke numfashi ta dawo ta gaban sa tace, "Dan Allah kayi ha?uri Sultan, bana so kana fushi dani hankalina yana tashi. In baka so zan daina kula Khalifa ko gaisawa zamu daina." Ya sauke numfashi yana kallon ta in ya tuna yadda ya rik'e ta a Cairo sai yaji haushin sa yake ji gabad'aya shiyasa wani lokacin ko wayar sa baya d'auka sabida haushin hakan.

Amma kuma ya taimake ta haka kuma Rahma k'anwar tace bazai raba su ba amma baya so yaga ta rab'i Anas balle taje gidan sa dan yasan tabbas zasu had'u shi kuma baya son hakan ko kusa. Jin ta fara yi masa kuka ya saka ya kalle ta tana jikin sa yace, "Shikenan ki bar kuka."

"Ka yafe min?." Kallon sa tayi shima ya kalle ta ya rik'e hannun ta ya d'ora a saitin zuciyar sa yace, "Bana son naji kina maganar wani Muwaddaty, ina ji kamar zuciyata zata fashe."
"Bazan sake ba in sha Allah, kayi ha?uri ka yafe min dan Allah bazan kuma ba." Rarrashin ta yake yana bubbuga bayanta ba tare da yayi magana ba.

"Ina sonki Muwaddaty! Sonki a jinina yake, na fara sonki tun a mafarki" ya furta yana sauke numfashi ya rik'e ta sosai a jikin sa. D'agowa tayi tace, "Mafarki?." Ya d'aga mata kai alamun eh tace, "Ka bani labari." Murmushi yayi ya girgiza kai alamun a'a ya jata kan gado suka zauna ya kashe hasken d'akin ya jata suka kwanta zata sake magana ya fara kissing d'inta dole taja bakin ta tayi shiru ta fara taya shi a karo na farko.


Bayan kwana biyu.
[17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*092.*

? ? ? ? ?? A kan stool d'in dake tsakiyar make makeken kitchen d'in ya ajjiye ta da yatsan sa yayi mata alama da ta zauna ta gani, binsa take da kallo taga ya dafe kai kad'an ya runtse idon sa zatayi magana ya karkad'a mata tsayan sa dole tayi shiru tana binsa da kallo. Sai da ya daidaita kansa sannan ya tsaya yana kallon kitchen da tunanin abinda zai dafa mata taci.

Kettle ya kunna bayan ya zuba ruwa a ciki ya d'auko cup ya d'auraye shi da ruwa ya buWe drawer ya d'auko coffee ya had'o da madara da sugar ya ajjiye a gefe. Kallon sa take yi yana sanye da rigar wanka wacce da kad'an ta wuce guiwar sa farar k'afar sa a bayyane a cikin takalmi yawo a cikin gida sai d'aukar ido k'afar tasa take hatta farren k'afar sa abin so ka kalla ne.

"Yawan kallo yana saka mutum ya fad'i." Abinda taji yace kenan tayi murmushi ta sunkuyar da kanta k'asa ya kalle ta shima sai yayi murmushin shima ya kashe switch d'in ruwan ya zuba coffee d'in da sugar ya zuba ruwa kad'an ya d'auko coffee maker ya jona ta itama ya saka a cup d'in yayi making coffee yayi kumfa sosai ya cire ya ajjiye, madarar ya zubawa ruwan zafi a wani kofin daban sannan ya zuba akan coffee d'in nan take yayi sama kamar zai zube sai ya dakata da zubawar ya d'auko ya kalle ta yana nuna mata cup d'in.

Jinjina tayi masa yayi murmushi ya fita ya kai coffee d'in falo ya dawo tana inda take ya d'auke ta kamar yarinya har inda ya ajjiye coffee d'in ya zaunar da ita akan kujera ya jawo coffee d'in ya kai bakin ta ta buWe tasha ta yamutsa fuska ya kalle ta ya d'aga gira tace, "Babu laifi." Murmushi yayi ya d'auki cake a leda cikin wand Suhail ya kwaso masa ya b'are mata ya mik'a mata ta karb'a taci ta kalle shi tace, "kaima kaci."

Wara ido yayi ya girgiza kai baice komai ba tace, "Allah sai kasha." Ya kalle ta na wani lokaci ya lumshe ido ya furzar da iska amma baiyi magana ba tace, "in fa baka karb'a ba nima na fasa." Ya sake kallon ta yace, "In nasha coffee bazan iya bacci ba."
"Ka karb'a kasha a hakan." Ya kalli agogo ya nuna mata itama ta kalla tace, "Nidai kasha kawai."

Sha d'in yayi kamar yadda tace ya d'aga girar sa sama ya kalle ta ya kalli coffee d'in alamun yayi dad'i, ta tab'e baki tace, "Ba laifi dai, na tabbatar shi kad'ai ka iya shima dan kayi zaman garin larabawa ne." Murmushi yayi yana bata tana sha shima yana sha a haka suka shanye cup d'in.

Ta jingina da kujera shima haka ya rik'e hannun ta suna kallon tv ba dan tana kunne ba tace, "Na fara jin bacci." Ya kalle ta yace, "Na fad'a miki bana iya bacci ko?." Tace, "Aini zanyi baccin ba kai ba."
Ya zuba mata ido har sai da ta kawar da fuskar ta tace, "in kana kallona wani iri nake ji a jikina, idanun ka bana iya kallon su sosai" ta fad'a tana buWe ido taga fuskar sa daidai tata yace, "me kike ji?."

Yadda yayi maganar ya sakata yin shiru tana kallon sa ya d'aga mata gira alamun ta bashi amsa sai tak'i magana ta sauke ido k'asa, "kince nasha abinda bazan bacci ba nasha, so dole kema bazaki ba." Ta kalle shi ya girgiza mata kai alamun abinda yace kenan tace, "To in na zauna me zanyi ga dare yayi?."

Kafin tayi magana taji saukar bakin sa a wuyan ta ta kulle idanun ta tace, "Sultannnn!."
"Sultanaaaa!" Shima ya furta ba tare da ya d'ago daga jikinta ta ba.
"Na gaji fa Sultan."

Rigar ta yake tattarewa ta k'asa tayi saurin rik'e hannun sa tunawa fa da babu komai a jikinta sai rigar kawai tace, "Sultan dan Allah." Bai bari ba ya kwace hannun sa ya kai hannun sa kan fatar cikin ta yana shafawa a hankali.

Shiru tayi dan ya kashe mata baki gabad'aya, daga shafa cikinta taji yana kai hannun sa sama ta sauke numfashi tace, "Sultannnn!." Yadda tayi maganar ya saka shi juyo da fuskar ta ya hanata sake magana ta hanyar saka bakin sa cikin ta dole tayi shiru badan taso ba.

Bata san ya akayi ba sai akwai ganin ta tayi a kan gado zata kuma magana ya sake hana ta dole tayi shiru tana jin sabon yanayi yana sake yin nink'aya a cikin jikin ta, "Say something Sultanaaaa! Ina so naji kinyi magana" ya fad'a a kunne ta amma babu damar yin maganar a wannan lokacin idanun ta a kulle suke gabad'aya ta kasa cewa komai.

? ? ? ? ? *&*? Tana cikin bargo a jikin sa gabad'aya tana kukan shagwab'a tana fad'in, "Sultan ka b'alla min bayana, wayyo k'afana, cikina zai cire Sultan." Duk ta rud'a shi hankalin sa ya tashi yace, "to ki daina kuka, I'm sorry Sultana." Ta sake shigewa jikin sa tana fad'in, "nidai na gaji bayana ciwo yake min."

"Shiiiii!" Ya furta a kunnen ta ta sauke numfashi jin yana mata tausa a bayan dan da gaske ciwo yake mata sai tayi shiru ta lumshe idanunta bacci yana k'ok'arin d'auke ta. Sai da yaji ta fara bacci sannan ya k'yale ta ya zame ta daga jikin sa yana kallon fuskar ta ynaa murmushi. Allah ya sani yana son wannan baiwar Allah, yana Qaunar ta fiye da tunanin mai tunani, baya so yaga tayi nisa dashi hakan yana sakawa yaji kamar shi kad'ai ya rage a duniya sabida kewa. Kiss ya mata a goshi ya tashi ya shiga band'aki.

Alwala yayi ya fito ya saka doguwar riga ya shinfid'a sallaya, "Sultan ina so nayi sallah nima amma bazan iya ba." Yaji ta fad'a ya juya ya kalle ta sai ya k'arasa kusa da ita ya zauna yana shafa kanta yace, "Zan miki duk addu'ar da kike so, kiyi bacci." Kulle ido tayi baccin ya sake d'auke ta ya gyara mata abinda ya rufe ta ya tashi ya koma kan sallayar ya tayar da sallah.

Har akayi asuba yana sallah sai da ya idar da sallar asuba ya k'arasa inda take ya zauna ya yaye abinda ta furta yana matse mata hancin ta, bata buWe ido ba dan bacci take sosai ya sake matse hancin ta nan ma bata buWe idanun ta ba. Sunkuyawa yayi ya cizi kunnen ta yana jan sa da hak"oran sa.

BuWe ido tayi idanun ta sunyi nauyi sabida bacci ta kalle shi yace, "Sallah Muwaddaty" ya fad'a yana yaye bargon gabad'aya ya d'auke ta bai sauke a ko ina ba sai a band'aki. A gefen bathtub ya ajjiye ta yace, "lokaci yana tafiya." Idanun ta har lokacin akwai bacci sosai ga kanta yayi nauyi hakan ya saka shi zuba ruwa a hannun sa ya shafa a fuskarta, ta yatsine fuska tana shafa fuskar ta ta d'ago ta kalle shi ya d'aga mata kai.

Fita yayi ya barta bata jima sosai ba ta fito tayi alwala cikin kayan sa riga da wando marasa tsaho masu kama jiki sai sukayi mata kamar nata, tana fitowa ya bata abayar ta ta jiya ta saka ta yafa mayafin ta tayar da raka'atanul fijir, bayan ta idar tayi sallar asuba dak'yar ta iya karanta ayatul kursi bayan ta idar ta mik'e ta zauna a kan gadon tana kallon sa yana karatu.

"Barka da safiya Sultan" ta fad'a tana kwanciya ta sake lullub'e jikin ta yayi murmushi dan yasan dole taji bacci badan baya so ta rasa sallah bama da bazai tashe ta ba yace, "Barka da safiya Sultana." Bata sake magana ba bacci ya d'auke ta. Sai da gari yayi haske sannan ya kashe hasken d'akin shima ya kwanta a bayan ta ya dawo da ita jikin sa gabad'aya a haka shima bacci ya d'auke shi.

*&&&*
? ?
? ? ? ? ?? Yadda take kuka sosai sai ta baka tausayi jaririn d'anta da bai gama zama cikakken mutum ba har lokacin take kallo tana zubar da hawaye tana fad'in, "Ina son shi a haka, dan Allah ya tashi kar ya mutu ya barni."

Mum da take jingine a gado ta rame gabad'aya ta koma kamar ba ita ba saboda rama ta firgice lokaci d'aya, maza ne a tsaye a kanta sai Eman da take kuka ta saka hannu ta karb'i yaron ta mik'awa mazan tace, "Ki daina kuka Allah ne ya baki kuma ya karb'i abin sa, ki bari a kaishi makwancin sa." Mazan suka fita da yaron a hannun sa Jidda ta sake fashewa da kuka ta rik'e hannun Eman tace, "Eman na cuci kaina na cuci rayuwata, Mum ta lalata min rayuwata gabad'aya ta gurb'ata min tarbiyya da addini na. Wallahi badan Mum ba da zuciya d'aya naso zama da Asad ita take zuga ni akan sai na mallake shi Eman."

Eman kuka take itama tace, "Kiyi ha?uri k'addarar ki kenan." Jidda tace, "Ba k'addara bace Eman nice na jawowa kaina, nice na biyewa son zuciya da son mulkin da Mum ta dasa min a zuciyta na biyewa Aliyu muka aikata sabon Allah da auren k'anin sa a kaina. Wallahi Asad ko hannuna bana tunanin ya tab'a ri?ewa sai dai ni na rik'e shi amma Aliyu tamkar shine Asad haka ya koma wajan mu'amalar aure dani bana jin tsoron Allah haka nake biye masa dan kawai na kai kaina matsayin da Mum take fad'a min."

"Na raba Aliyu da babar shi duk a tunanin su Asad ne nida shi ne kawai muka san ba Asad bane Aliyu ne...... Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, na shiga uku Eman a ina zanga Asad ya yafe kin?" Ta fad'a yana sake fashewa da kuka sosai.

Eman ta rik'e ta tana kukan itama bata ce komai ba Jidda ta kuma cewa, "Sabida Mum ta mayar da kisan rai ba komai ba nima na koya na dinga k'okarin kashe Asad kawai dan kar asirina ya tonu Eman, Mum ta cuce ni wallahi itace ta koyar dani hanyar da za'a kashe mutum domin mun sha yun?urin kashe Babar Asad d'in kawai dan kar ta bamu matsala akan kudurin Mum. Dole ma hakkin Mama dana Asad ya dinga bibiyar mu gashi nan Daddy ya barmu kema ya raba ki damu babu wanda yake zuwa wajan mu dan abinda muka aikata ba k'aramin sabon Allah bane."

Eman ta girgiza kai tace, "Daddy fushi yayi amma In ya wuce zai dawo Jidda."
"Gwara karya dawo Eman domin mu ba irin wanda za'a rab'a bane nan gaba kad'an shi d'in ma Mum zata iya kashe shi. Eman ina so na kai kaina kotu a yanke min hukuncin da musulunci ya tanadarwa Irina na karb'i hukuncina tun a duniya kafin naje wajan mahalicci na."

Eman tace, "Jidda za'a jefe kine fa har sai kin mutu shine hukuncin wanda ya aikata Zina da aure a kansa." Jidda tace, "Meye amfanin rayuwata Eman? Gwara ace na mutu d'in kowa ya huta dan rayuwata bata da amfani Kwata-kwata. Mum ta gama cutata sai Allah ya tsayar dani da ita yayi mana hisabi."

Kuka take Mum d'in ma haka, sun cika d'akin da kuka babu mai rarrashin wani kafin Jidda tace, "Ina so naga Asad ya yafe min wallahi na tuba, na kuma taya shi murna da bai zauna da mace Irina ba Allah ya kawo masa mafita da yake ya kasance mai bautar Allah. Mu kuwa da babar mu ta d'ora mu akan turba mara kyau ga inda k'arshen mu ya kasance a wula?ance a lalace. Eman koda an jefe ni na mutu kar ki biyewa son zuciyar Mum ki bi Allah da abinda ya umarta wanda yace a bari ki bari Eman in ba haka ba zakiyi k'arshe irin nawa mara kyaun gani da kyaun ji."

Rungume ta Eman tayi tana kuka sosai itama tana kuka Mum ma tana kuka sosai, Jidda tace, "Tun Mama da Mum suna makarantar secondry school a Kano aminan juna ne har sukayi aure a waje d'aya suka cigaba da aminci, Mama ta amince da Mum amma ita kuma cutar da ita take yi. Ina ma kafin ta haife ni cikina ya zube na huta da wannan bak'ar rayuwar da ta saka ni a ciki."

"Eman ki cewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login