Showing 84001 words to 87000 words out of 216282 words

Chapter 29 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

zuciyar ta kana tace, "Na samu labarin mahaifin wannan shegiyar yarinyar yazo har kuka gana kai dashi, wanne matsayi yake dashi a wajan ka da zaku keb'ance haka?." Asad ya d'ago kai yace, "Babu."
"Meye dalilin aikata hakan to? Bana ce kar ka sake shiga abinda ya shafe ta ba?, kenan ban isa na hana ba ko?."
"Allah ya wuci zuciyar ki."
Taja tsaki kana tace, "wani lokacin kayan haushin ka kamar na shak'e ka haka nake ji Asad. Komai akayi ka bada hak'uri kuma baza ka tsaya ka yiwa mutane bayanin abinda aka tambaye ka ba."

Nan ma shiru yayi bai amsa ba ta girgiza kai tare da yin k'wafa ta mik'e tsaye shima ya daure ya mik'e duk da ciwon da kansa yake yi masa tace, "Tunda abin naka haka ne zanyi maganin su dukkan su." Jin abinda tace ya saka yace, "babu wata alaqa da take tsakanina dasu, yazo taya ni murna ne bayan hakan babu komai."
"To ya tsaya iya hakan! Magana bana so ta sake had'a ka da wani daga cikin y'an gidan su, ka san cewa yanzu kai shugaba ne kowa a k'asan ka yake ba ko wanne talaka zaka dinga yin magana dashi ba."

Kai ya girgiza alamun zai kiyaye har tayi gaba sai ta dawo da baya tace, "naji batun kashe kashen kud'i da ka d'orawa kanka na jama'ar gari, shima ban lamunce ba komai zakayi ka tabbatar ka sanar in ka zartar da hukunci ba tare dana sani ba Asad ranka zai b'aci."
"Zan kiyaye" ya furta a hankali burin sa ya daina magana gashi in tana yi bazai iya shiru ba dolen sa ya bata amsa.

"Na tuna da batun uncle d'inka Mubarak, waye ya baka ikon bashi sarauta mafi kusa dakai Asad? Ban fad'a maka zan baka list d'in wanda zaka yiwa sarauta ba?." Asad ya lumshe idanun sa zuciyar sa cike da mamakin Mama ganin ita take so ta zama sarkin bashi ba yace, "Ina buk'atar sa a kusa dani ne Mama, ban san komai ba shi nake so ya nuna min komai dashi Abbana ya amince nima dashi na amince."

"Munafuki ne, fuska biyu ne dashi ni nasan da hakan. Tunda ka riga ka aikata bani da abin cewa amma ka sani; daga wannan kar ka sake duk wanda kake ganin ya dace ka bashi sarauta kazo ka sanar in yayi min sai ayi."
"In sha Allah."
"Wa zaka bawa sarautar tasa?."
"Wanda kika ce" ya furta kamar zaiyi kuka hakan ya saka ta kalle shi taga yana juya kansa sai ta yanke maganar tace, "Zan duba na gani, amma definitely za'a saka Aliyu da Hydar a ciki."

Hanyar fita yaga ta nufa hakan ya saka yace, "A sauka lafiya." Tana jinsa tayi masa banza ta fita ya sauke ajiyar zuciya ya hau sama ya cire kayan zafin da yake jikin sa ya fad'a band'aki yayi wanka ya fito ya saka kaya k'ananu yasha magani ya kwanta domin Allah kad'ai yasan gajiyar da yayi.

Wayar sace take ta k'ara yayi niyar sharewa amma ganin uncle ne yake wayar ya d'auka ya saka a kunne daga can b'angaren yace, "Allah yaja zamanin mai martaba, ina neman afuwa kira ba tare da neman izini ba." Asad yayi shiru hakan ya saka Uncle yace, "Bak'i ne suka zo daga China sunje wajan babban malamin masallacin cikin gari suna neman ganin mai martaba in hakan zai yu."

Asad yace, "A basu appointment amma banda yanzu na gaji bazan iya komai ba." Uncle yace, "Zuwa anjima sai mu iso, A huta lafiya." Asad ya yanke wayar ba tare da ya amsa ba. Kallon notification yayi yaga sunan Suhail yayi masa message ya bud'e message d'in yaga yace, _Allah yaja zamanin sarki, ina neman alfarmar ganawa mai martaba anjima._ Asad ya tura masa da Allah ya kaimu.

? ? ?? Message din Dr Khalifa ya gani bai bud'e ba ya ajjiye wayar ya kwanta yana sauke numfashi.? _Mutanen gidan duka sunce a mik'a musu gaisuwa, har ita uwar gidan._ kalaman Baba suka dawo kansa ya sake jin kansa ya sara k'irjin sa na harbawa da sauri maimakon yaji tausayin ta kamar d'azu sai yake jin wani abu mai kama da haushin ta ita da iyalanta gabad'aya. Yaja tsaki ya tashi zaune yace, "Ya zama dole na yanke alaqar mu da ita gabad'aya ko zan huta da abinda nake ji a raina, zanje anjima kamar yadda nace" ya fad'a yana kwanciya ya kulle ido dan so yake yayi bacci.

? ? ? A b'angaren Mama data koma b'angaren ta a nan ta tarar da Mum a zaune tana jiranta ganin shigowar ta ya saka ta mik'e sai da Mama ta zauna itama ta zauna tana cewa, "Ranki ya dad'e barka da dawowa." Mama tace, "Sadiya yaushe kika shigo?." Mum tace, "Ina shigowa aka sanar dani fitar ki."
Mama ta tashi tace, "Muje ciki." Tare suka shiga suka zauna a k'aramin falo Mama tace, "Naje wajan Asad ne yana neman fara tarwatsa min lissafi daga fara zaman fada yana yanke hukunci ba tare dana sani ba."

? ?? Mum tace, "naji a gidan jarida ana ta sanarwa tawowa ta a mota nima sai da nayi mamaki nace daga farawa har anzo nan." Mama tace, "Barni dashi kawai zanyi maganin abun. Ya akayi na ganki kwatsam ba notice?." Mum tace, "batu ne akan yarinyar nan da aka bada aiki za'ayi."
Mama tace, "bayan kun ya kasa komai, yau d'in nan sai da Asad yayi magana da mahaifinta."

Mum tace, "ai a yanzu aka gabatar da aikin a gabana an kuma tabbatar min da ya tsane ta kenan har abada, domin kuwa an bani tabbacin a yau zaiji babu wacce ya tsana kamar ta kuma zaiyi k'okarin yanke alaqa da ita." Mama tace, "Allah yasa hakan. Ni ina so nayi waya ma da Malam Audu a warware aikin da aka yiwa Asad kwanakin baya."

Mum da mamaki tace, "Wanne aiki aka yi masa?."
Mama tace, "Oh baki sani ba ashe, lokacin da suna tare da yarinyar can ne na saka akayi masa aikin da bazai iya kusantar ta ba koda yayi niyar yin hakan bazai iya ba. Aikin ya same shi shiyasa har yanzu tsakanin sa da Jidda ba labari amma zanyi magana dashi yanzu."

? ? ? ? Gaban Mum yayi mumman fad'uwa ta wara idanunta waje tare da dafe k'irji tace, "What! Fulani da kanki kika bada go ahead d'in wannan d'anyen aikin akan sa?." Mama bata amsa ba Mum ta kuma cewa, "Ina laifin tun a baya kisa ace a yiwa yarinyar aikin da bazata burge shi bama kwata-kwata bazai ji wani abun a kanta ba balle ma ya kai ga aikata wani abun, amma sai kisa a yiwa Asad guda?." Mama tace, "lokacin kaina ya kulle neman mafita kawai nake yi, amma yanzu za'a warware komai ai ba wani abu bane mai wahala kar dai ki sanar da Jiddan."

Mum tace, "Wannan ai tsakanin mune." Mama tace, "Good, yanzu zan kira shi da kaina sai muji yadda za'ayi." Mum tayi shiru bata amsa ba amma zuciyar ta a cushe take da tasan da wannan maganar ai da tuni ta saka an warware komai dan ita ko kusa ko alama bata wata tazara a tsakanin su so take komai ayi a gama shi a wannan lokacin kafin uwar ta farga.

? ? ? ? ? *&&5:00pm&&&*

B'angaren saukar bak'i ya cika da manya manyan bak'i fararen fata da bak'aken fata suna ganawa da sabon sarki suna ta hotuna cikin burgewa. Yana jin larabci da turanci shiyasa ganawa dasu baya yi masa wahala ko wanne yare ka juya masa zai baka amsa, abokan sa larabawa sun iso taya shi murna sosai yaji dad'i a ransa sosai.

Asad yayi kyau cikin kaya light blue komai blue hatta takalmin k'afar sa blue ne ga alkyabbar tayi bala'in amsar jikin sa yayi kyau matuk'a hakan ya saka sai hotuna ake masa kana kallo kasan ya saka dukiya a jikin sa. Sun jima kafin bak'in su tashi tafiya su bada kyaututtuka su tafi.

Daga nan ya fara ganawa da mutanen cikin gida duk wani wanda ya shafe shi a wannan lokacin sun tattauna. A wannan shigowar Suhail yazo Asad yana zaune a kan karaga Suhail ya zauna a k'asa yana kai gaisuwa hadiman da suke k'asa suna fad'in, "An gaishe ka Suhail, mai martaba ya karb'i gaisuwar ka."

? ? Suhail ya zauna a gefen sa yace, "Allah yaja zamanin mai martaba sarki." A tare suka amsa da amin Asad ya kalle shi yace, "Suhail." Suhail ya gyara zama yace, "Ranka ya dad'e." Asad ya murmusa kawai baice komai ba Suhail yace, "Allah yaja da ranka zuwa nayi na gaida mai martaba, ina fatan an karb'i gaisuwata."
"Mai martaba yana godiya" suka had'a baki gabad'aya suka fad'a kafin ya sake yin gaisuwa ya tafi.

Bayan kammala zaman fada Asad yana zaune shine da Uncle Asad yace, "Uncle ina so zanje Germany wajan Abban cikin week d'in nan." Uncle yace, "Allah ya k'ara maka lafiya sai a shirya komai nima daman ina so naje." Asad yace, "Uncle ya kake gani zamuyi da Suhail?."
"Ban fahimta ba kamar ya kenan?."
"Sai nake ganin a bashi sarauta mafi kusa dani."
"Eh kuma a'a, abin ne a cikin duhu in ka duba waye mahaifin sa."
"Na amince da Suhail tun ba yau ba."
"In mai martaba yana ganin hakan babu matsala Allah ya shige mana gaba."

Asad yayi shiru yana kallon wani wajan daban kafin suyi sallama ya hau saman sa ya samu Jidda a zaune a falon sama. Yana shiga ta taso ta k'araso kusa dashi ta zaga ta bayan sa ta zame allyabbar jikin sa tana fad'in, "welcome back my king."
"Thanks" ya furta a tak'aice yana zare hannun sa daga alkyabbar, ta duk'a ta zare masa takalimin k'afar sa ya taka zuwa tsakiyar falon ya zauna.

Ajjiye su tayi ta koma inda yake ta cire rawanin kansa shi kuma ya zare k'atuwar rigar da take saman shaddar jikin sa yana sauke numfashi dan ji yake iska na shigar sa ba kamar d'azu ba da zafi ya dame shi. Wajan fridge ta d'auko ruwa mai sanyi da glass cup ta k'araso kusa dashi ta zuba masa ta mik'a masa, kamar bazai karb'a ba sai kuma ya karb'a yasha farin ciki ya mamaye mata zuciyar ta ganin yasha ya ajjiye glass cup d'in ba tare da ya kalleta ba.

? ? ? Tashi tayi ta shiga d'akin sa ya bita da kallo shi bai san me zai yiwa yarinyar nan gabad'aya bata burge shi ko kad'an bata cikin zuciyar sa ga tausayin ta yana ji ta wani b'angaren in ya tuna halin da yake ciki bazai iya sauke hakkinta da yake kansa ba dalilin da ya saka yake d'aga mata k'afa. Jim kad'an ta fito ta k'araso kusa dashi tace, "wanka fa." Bai amsa mata ba hakan ya saka tace, "na ajjiye maka ruwan wanka."

Kai ya d'aga kawai kafin ya d'auki wayar sa yana dannawa suna charting da Hydar akan rashin lafiyar Abba sai kuma ya shiga Ig ya dinga karo da maganganun sa na d'azu da video da hotuna ana ta yabon abinda ya furta ya kashe data ya tashi ya shiga d'akin.

? Tsalle ta buga bayan taga shigar sa tana murna tace, "ka fara zuwa hannu wallahi, wuuuu Allah yaja da ranki Mummyna dole na kira ki na baki labari" ta fad'a tana sauka da sauri.

*&&&*


? ? ? ? ? Tunda Baba ya koma jikin sa yake rawa ya sanar Umma yadda sukayi da Asad ya tashi hankalin kowa na gidan akan a tashi a shirya masa abin motsa baki gabad'aya ya rud'a su. Rauda jikin ta duka a sanyaye take komai dan bata amince da zuwan wani Asad ba dan bata da yadda zatayi ne baza ta yiwa Baba musu ba shiyasa taja bakin ta tayi shiru kawai.

A zaune ya shigo ya samu Rauda tana duba waya yace, "baza ki tashi kiyi abinda yake gaban ki ba sai yazo?." Umma ta kalle shi tace, "Dan Allah malam ka kwantar da hankalin ka basai an had'a masa komai ba dan ko an bashi ba ci zaiyi ba, ka manta matsayin da yake dashi ne a yanzu? Ba komai suke ci ko suke sha ba in aka basu."

Baba ya zauna a akan kujera kana yace, "Eh kuma fa gaskiyar kine, amma ai nan gidan sirikan sane ba wani abun zamu bashi da zai cutar dashi ba." Umma tace, "Kaine kake ganin hakan."
"Amma yanzu haka zai zo babu abinda zamu bashi?."
"Sai a d'ora ai Malam" ta fad'a tana kawar da kanta gefe ba tare da tace komai ba.

? ? ? ?? "To ki tashi kije ki shirya sai wani sanyin jiki kike yi kamar ba mijin ki ne zai zo ba" Ya fad'a yana kallon Rauda bata musa ba ta tashi ta shiga d'aki shima ya fita Umma ta bishi da kallon mamaki, wato shidai duk inda akace kud'i a nan jikin sa yake rawa.

? ? ?? Rauda koda ta shiga d'akin bata iya aikata komai ba tsayawa tayi tana tunani kafin ta samu waje ta zauna ta rafka uban tagumi zuciyar ta na harbawa dan bata san me zai kawo Asad d'in gidan su ba. Sallah ce kawai take tashin ta a nan take zaune har akayi magariba babu Asad babu labarin sa har lokacin Baba bai sare da zuwan Asad ba ita kam daman tasan bazai zo ba.

Wanka tayi lokacin ana kiran sallar i'sha ta fito ta saka doguwar riga ta bacci mai gajeren hannu jikinta yana rawa sosai kalar ja da bak'a ta saka hula ta d'ora hijjabi ta tayar da sallah. Bayan ta idar tayi shafa'i da wutri ta mik'e ta zare hijjabin kenan Baba ya shigo jikin sa har rawa yake yana cewa, "Ke Rauda yi maza-maza kije ga Asad d'in can yazo yana?sitirum d'ina na waje." Gabanta yayi mugun fad'uwa ta dafe k'irji sabida yadda zuciyar ta ta buga fattt ji tayi kamar zata fito.

? ? ? "Ba magana nake miki bane kin tsaya kina kallona? Dallah malama kiyi da jiki kije yana jiran ki an gaisa dashi ke kad'ai ake jira" Baba ya fad'a cikin fad'a hakan ya dawo da ita hankalin ta ta d'auki hijjabin data cire ta saka tana kallon Baba ta fita. A falo ta tarar da Umma ta wuce ta jikinta duk a mace gabanta yana cigaba da tsantanta bugawa haka ta wuce ta fita daga falon ta fito tsakar gida ta fita harabar gidan a nan ne set room d'in Baba yake.

Tare da Baba suka fita ya tsaya a bakin k'ofa yace, "Shiga." Yawu ta had'd'iye ta saka kanta cikin falon nan take khamshin turaren sa ya bata tabbacin shid'in ne da gaske ba wasa bane. Kanta a k'asa take takawa jikinta yana rawa ta zauna a kan carpet har lokacin bata kalli inda yake ba gabad'aya tsoro ya gama mamaye mata zuciya.

Tunda ta shigo yake kallonta k'irjin sa yana bugawa da sauri-sauri ya runtse idanun sa ya bud'e yana jin wani iri a zuciyar sa, shiru falon yayi babu mai magana tsabar bugawar da k'irjin ta yake yi ta kasa magana sai raba idanu da take a k'asa tana kallon k'afar sa da take sanye da takalmi ta mayar da kanta k'asa ba tare da tayi magana ba.
Yadda tayi shiru haka yayi shiru baice komai ba kallonta kawai yake yi ta k'asan idanun sa domin tasan dai bazai mata magana ba sai dai in a kwana a haka.

Gajiya tayi da zaman ga bugun da zuciyarta take yi ta yunk'ura ta tashi zata fita taji an rik'o hannun ta zuciyar ta ta cigaba da gudu ta runtse idanunta hawaye na ciko mata idanun ta, kwace hannun ta tayi daga rik'on da yayi mata sai a sannan tace, "Meya kawo ka gidan mu?."

Hannayen sa duka biyun ya saka ya juyo da kafad'ar ta kanta na k'asa hawaye suna sauka daga idanunta ya d'ago fuskar ta suka had'a ido sa a sannan ta kalli fuskar sa ta ganshi sanye da face mask da kuma bak'in glass da alama yayi b'adda kama ya saka hannu ya zare glass d'in ya cire face mask d'in fuskar sa ta bayyana sosai ya lumshe idanun sa ya bud'e yana kallon fuskar ta da idanun ta suke zubar da hawaye har lokacin.

? ? ? ? "Na mayar dake d'akin ki Muwaddaty! You're still my wife!" Ya fad'a a sanyaye yana bin fuskar ta da kallo yana so ya fahimci reaction d'inta. Wara idanun ta waje tayi cikin tsananin bugun zuciya tana k'arewa fuskar sa kallo ya d'aga mata kai alamun tabbacin abinda yace ya jawota ya had'a ta da jikinsa hannun sa na zagaye da k'ugun ta yace, "Yeah, you're still my wife!."


*Tofa anya Asad yana cikin hankalin sa kuwa?*=?1? @&?
[17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*052.*

? ? ? ?? Yanayin yadda yaga ta gigice ta zuba masa ido fuskar ta ta nuna tsantsar tashin hankali da mamaki had'i da al'ajabi a kai k'arara sai zare idanu take tana binsa da kallon da alama mamaki ya hana ta magana. Shima baiyi magana ba yana rik'e da ita har lokacin ganin kamar bata hankalin ta ya saka shi ya rik'e hannunta guda d'aya ya murza yatsun hannunta ta kalli yatsun nata ta sake kallon sa tana bin hannun nasa da kallo nan tayi karo da abinda take nema a hannun nasa ta sake kallon fuskar sa dan ta tabbatar shi d'in ne.

"Nine a gaban ki kar kiyi tunanin wani abun daban" ya fad'a cikin maganar sa mai d'aukar hankali yana cigaba da kallonta. Sakin ta yayi ya kalle ta yace, "where is your phone?." Bata iya magana ba sai bin sa take da ido gani take kamar baya cikin hankalin sa in ta tuna yadda aka rabu bata d'auka zai dawo har yace ya mayar da ita ba.

"Kin san yanayina bazan iya magana da yawa ba, amma I'm sorry." Wani irin abu take ji yana tasowa daga jikinta ta lumshe ido dan ji take yana tafiya kamar kiyashi yana zaga ko wanne b'angare na jikinta har cikin gashin kanta take jin maganar sa.

Sake rik'e hannunta yayi duka biyun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login