Showing 111001 words to 114000 words out of 216282 words

Chapter 38 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

tace, "Kiyi hak'uri dan Allah."

Rauda ta wayance tace, "Lah babu komai fa Sis, abin ne in na tuna yana saka ni a wani yanayi mara dad'i. Na tab'a aure ban jima da fita daga idda ba Sis." Ramla tace, "kenan lokacin da kina Egypt da auren ki?." Rauda ta girgiza kai tace, "Eh, wanda muke tare dashi shine mijina. Hydar k'anin Asad shine silar samun matsalar k'afa ta shine ya buge ni a mota har k'afata ta samu matsala. Daga nan Asad ya nuna yana sona amma Maman sa ta hana hakan, da yake dai Allah ya rubuta sai na kasance matar sa ban sani ba Mai martaba mahaifin sa ya karb'i aurena wajan Babana akayi auren ba tare da Maman sa ta sani ba, bama iya ita kad'ai ba da yawa mutane basu san anyi auren ba muka tafi nan Egypt aka samar min da lafiyar k'afa ta. At the end dai auren bai wuce sati hud'u ba ya mutu wannan lokacin da Dr ya taimaka min har nazo gidan ki anyi sanki Maman sa tace kuma sai na fita" ta k'arasa fad'a muryar ta na shaking.

Ramla ta kalli Khalifa shima ya kalle ta cike da mamaki da al'ajabi Rauda tayi shiru ta mayar da hawayen idanun ta tace, "Na d'auke ku y'an uwana shiyasa na fad'a muku dan Allah bana so maganar nan ta fita dan bani so mani asan nayi aure, yadda mutane basu san ya aure ni ba d'auke suke aikin k'afa aka yi min muka dawo muje a hakan kawai." Ramla tace, "in sha Allah babu wanda zaiji Rauda. Allah yabi miki hakkin ki domin dukkan su sun cutar dake daga shi har Babar tasa."

Shi dai Dr baice komai ba zuciyar sa cike da mamakin abin har suka je gida suka sauke ta har? gida Ramla ta shiga ta yiwa Umma sallama sannan suka wuce.

Bayan sallar la'asar Umma da Rauda suna zaune suna hira Baba ya shigo yana fad'in, "Rauda har kunje wajan Baba malam d'in?." Rauda tace, "Munje Baba tun d'azu muka dawo." Ya zauna yana fad'in, "To yayi kyau." Ya kalle ta yace, "Binta Anas yazo min da maganar yana neman izinin fara zuwa wajan Rauda mtsayin me neman auren ta a karo na biyu, tun jiya yayi min maganar yanzu kuma yazo yana can k'aramin d'akin can yana jiran ta."

Gaban Rauda ya fad'i ta kalli Umma itama ta kalle ta sai taga Umma tayi murmushi tace, "Alhamdulillah, na jima ina jiran wannan ranar tun bayan kammala iddar ta. Amma Malam kaine ka sanar dashi ta gama idda?." Baba yace, "hira ce tazo har maganar ta shigo ciki ashe ya rik'e bai manta ba." Umma tace, "Allah sarki, wallahi ni daman can shi nake mata sha'awar aure Allah ma ya sani dan ka auri namiji mai sonka shine morewa." Baba yace, "in ya kasance mijin ta sai kiga anyi an gama kamar wancan." Ya kalli Rauda yace, "Saka hijjabin ki kije yana jiran ki zaku tattauna."

Ba musu ta tashi ta shiga d'aki ta d'auki hijjabi ta fita Umma ta bita da kallo shima Baban kallon ta yake yi yana ji kamar komai ya faru da ita shine sila amma babu yadda zaiyi ba'a goge k'addara.

Tunda ta doshi d'akin sai take jin fad'uwar gaba ta sauke numfashi ta shiga da sallama yana zaune cikin farar shadda anyi mata aikin bak'in zare sai khamshi yake yi ya amsa yana kallon ta, a gefe ta zauna tace, "Ina wuni." Yayi murmushi yace, "lafiya lau Rauda ta, ya naga kina jin kunya kamar bamu zama y'an uwa nida ke ba?." Murmushi tayi shima shi yayi ya gyara zama yace, "Nasan Baba ya sanar dake qudirina a kanki a karo na biyu Rauda, a karo na biyu na dawo gare ki ina neman auren ki Allah yasa zaki amince.:

Ta d'ago ta kalle shi tayi murmushi tace, "Yanzu ba dah bane ba, kar ka manta na tab'a yin aure." Yayi murmushi yace, "Na sani ai, k'addarar auren kice ta zama silar raba mu har iyayena suka min zab'i da Allah yayi nufin dawowar ki sai ya d'auki ran wacce aka bani tun ban aure ta ba kema ya raba ki da naki mijin. In kika duba zaki ga Allah ya tsara mana faruwar hakan tun farko K'addara ki kalar tawa ce." Kai ta girgiza cikin gamsuwa da abinda yace iya tsara kalaman sa da nutsuwar sa yana daga cikin abinda yake burge ta a tare dashi tace, "Baka ganin a wannan karon ma zasu iya yi maka zab'in?."

Yayi murmushi yace, "A wannan karon sun bani ikon zab'ar wacce nake so na riga na sanar dasu kece wacce nake so sun amince min yanzu taki amincewar kawai nake so. Bana so a d'auki lokaci nan da wata biyu nake so ayi bikin a gama bana so wata k'addarar ba fata nake ba ta sake kawo mana barazana tsakanin mu. Dan Allah Rauda ki fad'a min gaskiyar abinda yake ranki, kin amince na zama mijin ki? Kina sona a kafo na biyu ko A'a....?.Kar ki b'oye min abinda yake ranki." Shiru tayi ta sauke ajiyar zuciya ta lumshe idanun ta ta d'ago ta kalle shi tace,..........
[17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*060.*

? ? ? ? ? ? Shiru tayi kanta na k'asa sai kuma ta d'ago kai ta kalle shi ta fitar da sigh kafin tace, "zanyi tunani a kai a bani lokaci." Ya d'an wara ido yace, "Yanzu ashe ina da wani hali da sai anyi tunani a kaina?." Ta girgiza kai tana murmushi tace, "A'a ba haka nake nufi ba, kawai ina so nayi tunani ne a bani wannan damar."
"An baki ranki ya dad'e, ina fatan dai baza'a d'auki lokaci ba." Tace, "Babu lokaci in sha Allah."

"Godiya nake gimbiya." Sai tayi murmushi kad'an shima yayi murmushin tayi shiru bata ce komai ba kafin yace, "Ina sonki wallahi Rauda, duk abinda ya faru a baya ban tab'a jin sonki ya ragu a zuciyata ba. Har fa addu'a na dinga yi Allah ya cire min ke a zuciyata nasan kina da aure amma kuma na kasa daina sonki, ashe kina nan dawowa gare ni." Lumshe ido tayi ta bud'e ta kalle shi kamar zatayi magana sai kuma ta fasa tayi murmushi kawai shima sai yayi murmushin.

"Naga alama yau sarautar kike ji da ita, shikenan to zan koma yamma tayi sosai." Ta kalle shi tace, "a gaida mutanen gidan." Yace, "Zasu ji in sha Allah. Zan fad'awa Mamana sirikar ta Rauda tana gaishe ta." Murmushi ta kuma yi kafin ya fita ita kuma ta ta shiga cikin gida fuskar ta har lokacin d'auke da murmushi. D'aki ta wuce ta zame hijjabin ta har lokacin bata daina murmushi ba Umma da ta shigo d'akin tace, "Rauda."

? ?? Juyowa tayi ta kalle ta tace, "Na'am." Umma ta kalle ta tace, "ya kike ji a zuciyar ki akan Anas?." Ta sunkuyar da kanta Umma tayi murmushi tace, "Allah yasa kin amince dashi dan ni wallahi ina miki sha'awar auren sa sabida yana sonki so na hak'ika sosai." Rauda tayi d'ago tace, "Umma indai kina son na aure zan aure shi." Umma ta wara ido tare da rik'e hab'a tace, "Ni zan zauna miki dashi da zan so ki aure shi Rauda? Kawai ina fad'a miki ra'ayina ne amma yankewa ai yana wajan ki."

Tayi murmushi bata ce komai ba Umma ta sake cewa, "Allah ya zab'a abinda yafi alkhairi, ki cigaba da addu'a" tana fad'a ta fita Rauda ta zauna a gefen gado tana murmushi ita kad'ai wanda bata san dalilin sa ba.

Tunawa da kalmar Anas da yace sarauta take ji da ita sai fuskar Asad ta fad'o mata a zuciyar ta tayi saurin kawar da ita tare da runtse ido ta cize baki tare da dukan goshin ta a lallai sai ta kawar da tunanin da ya kawo mata ziyara ta tashi ta fita daga d'akin gabad'aya gudun ma kar tayi tunanin sa.

Washe gari da yantsi Rauda ta shirya ta tafi gidan Baba Malam dan karb'o sak'on Ramla da kuma nata, kamar ko yaushe layi kamar babu gobe ta wuce zuwa cikin gidan mutane sai kallon ta suke wanda suka ganta jiya sun gane ta wasu kuma a ranar suka zo bata jima sosai ba aka sake ganin ta fito da leda a hannun ta alamun ta karb'i sak'on ta.

Kusa da wata mota tazo wucewa sai ta wayar ta tayi k'ara ta d'auka ta tsaya a jikin tagar motar ta baya ta ????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? saka a kunne tare da fadin, "Kin kira a daidai Sis yanzun nan kinga sak'on a hannuna na karb'o miki." Shiru tayi alamun ana bata amsa kafin tayi dariya tace, "Har na ganshi tuni ma, layi kam akwai shi har yafi na jiya ma wallahi."

"Eh to mu had'u a gida sai ki karb'a" tana fad'a ta kashe wayar ta cigaba da tafiya. Mama da take zaune a mota ita da Suhaima ta kalli Suhaima tace, "Ita wacece yarinyar nan da naga jiya tazo bata jima ba ta tafi yanzu ma haka?." Suhaima ta kalli bayan Rauda tace, "Wata?ila ta san shine shiyasa." Mama ta kalle ta daidai lokacin da ta samu keke napep tace, "bita Suhaima muje ko wani abun ne a biyata ta kawo mu na gaji da dogon layin nan" ta fad'a tana dafe kanta domin ita kam bata saba bin layi ba.

Suhaima tace, "Amma da an tura ance masa kece da kanki gani nake bazai ki sauraren ki ba." Mama tace, "Jiya an sanar dashi ashe shi baya alfarma. Banda dole me zai kawo ni wajan nan?, Sadiya ta cuce ni." Suhaima bata ce komai ba tabi bayan napep d'in da Rauda ta hau har k'ofar gidan su ta sauka ta biya shi sannan ta shiga.

Suhaima jira take Mama tayi magana ita kuma ta rasa me zata ce ne, a zahiri tana son ganin Baba malam kodan bakin da yayi yawa akan aikin sa amma kuma bata tunanin zata iya neman alfarma a wajan wasu mutanen duba da matsayin da take dashi.

Dan k'aramin tsaki taja kana tace, "Juya mu koma gida." Ba musu ta juya suka d'auki hanyar komawa gida. Bayan sun sauka direct b'angaren mai martaba Mama ta wuce kamar ko yaushe Hydar yana zaune a gefen sa idanun mai martaba a kulle alamun yana bacci. Zama tayi a inda Hydar ya tashi ya bata tana kallon mijin nata kawai sai ta fashe da kuka.

Kuka take yi sosai Hydar yana tsaye yana ji kamar shima yayi mata kukan dan yasan an mata rauni a zuciyar ta ga rashin lafiyar da take fama da ita, ga Asad ga kuma Abba. Ta jima tana kukan kafin yazo ya dafa ta yace, "Dan Allah Mama kiyi hak'uri, Allah ya wuci zuciyar ki." Sassauta kukan nata tayi ta kalle shi ta goge idanunta sai kuma ta mik'e tana kallon sa tace, "Hydar me ya same ka? Badai ciwon kane zai tashi ba? Kayi min rai kar ciwon ka ya tashi in hakan ta faru ban san ya zanyi ba, ba Asad ba kai ba Aliyu."

"Kiyi hak'uri Mama" ya fad'a a tausahe ta kalle shi tace, "Ina Asad?." Ya sauke numfashi yace, "Mai martaba ya tafi England shida matar sa." Runtse ido tayi bakin ta yana rawa tace, "ya tafi ban sani ba, meyasa yake min haka Hydar?" Ta fad'a hawaye na sake zubo mata Hydar ya rik'e ta sosai duk da ciwon da yake ji a zuciyar sa da kansa.

"Ranki ya dad'e dan Allah ki daina kuka mutane suna shigowa ba girman ki bane" ya fad'a a tausahe ta goge idanun ta ta sauke numfashi ta juya ta fita daga d'akin. Numfashi ya sauke domin shima dauriya kawai yake yi mugun ciwo kansa yake masa zai iya cewa ciwon sa yana gab da tashi baya so ya nuna mata ne dan kar hankalin ta ya tashi.

D'aki ta koma ta kwanta ta fashe da kuka mai tab'a zuciya kanta yana sarawa zuciyar ta na tsagaita bugawa, ta jima tana kuka kafin ta sassauta ta mik'e zaune kanta yana mugun sarawa ta dafe kai da hannu biyu sabida ji take kamar zai fashe. Wayar ta take ji tana ihu bata iya dauka ba sai da taji kiran yayi yawa ta mik'a hannu ta d'auka ba tare da ta duba ba taji ance, "Yaya Rabi'atu." Jin muryar k'anwar ta ya saka ta bud'e baki tace, "Uhumm." Daga can b'angaren tace, "Subahanallah Yaya meya same ki haka naji muyar ki kamar mai kuka?."

Jin bata amsa ba ya saka yace, "Ko akan maganar da Yaya Babba ta fad'a mana ne? Nasan ma itace ta mayar dake haka Yaya daman maganar gaskiya kin sake da wannan Sadiyan da yawa, ko wanne sirrin ki ta sani bakya b'oye mata komai ba dole ta samu lagon ki da sauri haka ba. Yanzu ba wannan ba ya riga ya faru ki daure a bazama nema masa magani muma nan muna tayi ko za'a dace."

Mama ta cize bakin ta tace, "Na rasa abinda zanyi."
"Ki tuna, sai kin tuna sannan zaki aiwatar da komai wannan zaman naki bazai haifar da komai ba sai dai ma ya saka ki sake nisanta dashi. Mahaifin sa bashi da lafiya balle ya taimake ki dole ki dage." Bata amsa ba ta yanke wayar ta kwanta tana sauke numfashi zuciyar ta cike da tunane-tunane kafin kuma bacci ya d'auke ta.

Data farka taji dad'in baccin sosai tayi wanka ta fito babban falon ta hadimai suna ta hidama ta zauna ta kalli Jakadiyar ta tayi mata alama da tazo, jiki na rawa ta k'araso ta zube a gabanta Mama tayi banza da ita kamar bata san wata wajan ba sai daga baya tace, "Kin san wani Baba Malam?." Jakadiya ta duk'ar da kai tace, "Allah yaja da ran fulani na san shi, kwanaki akwai matsalar sammu da aka yiwa dan wajena dana je na same shi cikin ikon Allah an samu waraka."

Mama ta sake yin shiru kamar bata ji ba kafin tace, "Taya kika samu ganin sa?." Jakadiya tace, "Ranki ya dad'e ta hanyar Gwaggo da take b'angaren k'aramar Fulani na ganshi." Mama ta sauke numfashi tace, "Jeki ki kira min ita."
"An gama ranki ya dad'e" tana fad'a ta mik'e ta fita da sauri Mama ta kwantar da kai a jikin kujera tana jiran dawowar su.

Ba jimawa suka shigo su biyu suka zube a a gabanta Gwaggo tace, "Allah yaja zamanin Fulani, yaja da ranki ya k'ara miki lafiya." Mama tace, "Wa kika sani ya kai ki wajan wani malami Baba Malam?." Tayi mata jinjina kana tace, "Allah yaja zamanin ki akwai wata mahaifiyar k'awar y'ata Binta ita kuma k'anwar sace ta dalilin ta na ganshi har na yiwa Jakadiya iso wajan sa." Mama ta furzar da iska tace, "Abinda nake kuje gidan su kuzo min da k'anwar tasa nan." A tare suka amsa da fad'in, "An gama ranki ya dad'e" suka mik'e suka fita.

? ? ? ? ? Suna fita mota suka hau zuwa gidan su Rauda suka same su kamar ko yaushe suna tare a zaune harda Inna ana ta hira suka shiga da sallama, bayan sun gaisa ne Gwaggo tace, "Rauda shugabar muce ta taso mu yanzu ta aiko mu." Umma tace, "Wacce kenan?."
Gwaggo tace, "Fulani Rabi'atu mana mahaifiyar Asad.." Umma da mamaki tace, "To lafiya dai?."

Gwaggo tace, "lafiya lau, cewa tayi nazo na tawo mata dake wajan ta."? Rauda tace, "Wacce shugabar taku kenan Gwaggo wai?."
"Yanzu fa na fad'a Rauda, Shugabar mu gimbiya mana, matar sarki kuma babar sarki. Fulani Rabi'atu babar sarki Asad."

Gaban Rauda ya yanke ya fad'i ta daure tace, "to me Umma zatayi mata zata ce a kai mata ita?." Jakadiya tace, "Kwantar da hankalin ki yarinya, tana son ganin Baba malam ne akan matsalar mai martaba duk da bata fad'a mana matsalar ba amma nasan akan sane zata je, to kunfi kowa sanin halin sa baya danne lokacin talakawa sabida masu mulki taje amma bata samu ganin sa ba shine take tambaya ta na sani nake sanar da ita na tab'a zuwa na ganshi ta dalilin Gwaggo itama kuma ta dalilin ku, shine tace muzo aje da Umman ki."

Inna tace, "Kenan alfarma take so ayi mata?." Jakadiya tace, "Eh to kusan hakan zamu ce." Rauda tace, "Wallahil azim Ummana bazata je ba, in ita bazata tako k'afar ta tazo nan ta nemi alfarmar ba tasha zaman ta ita take nema ba mu ba."

Jakadiya tace, "Hattara y'an mata magana ake ta Fulani Rabi'atu" ta fad'a tana murmushi tana kallon Rauda. Rauda tace, "in ma Asad d'in ne da kansa ba babar saba wallahi bazata je ba. Dan ma ta raina mana hankali tana neman alfarma kuma ace Umman ce ma zata je wajanta kamar itace take nema?. Itafa take nema bami ba in bazata zo ba tasha zaman ta Umma ce dai bazata ba." Gwaggo tace, "Haba Rauda sai magana kike baki bari munji ta bakin Umman taki ba."

Umma tace, "Abinda Rauda tace shine daidai ai Gwaggon Habiba, zan iya yi mata alfarmar ganin Baba malam wannan ba komai bane amma sai dai tazo inda nake badai ni naje ba. Itace take nema bani nake nema ba dan haka bazan je inda take ba."

Gwaggo ta kalli Jakadiya tace, "to kinji." Jakadiya tace, "ta yaya zamu sanar da ita wannan sak'on mai tsauri? Kinfi kowa sanin halin ta fa." Gwaggo tace, "koma meye haka zamu jure, tashi muje." Suka tashi suka yi sallama dasu suka koma.

Da suka koma basu ganinta ba sai da yamma suka zauna a gabanta dukkan su tace, "Ina jin ku." Gwaggo tayi k'arfin halin cewa, "Ina neman afuwar fulani akan abinda zai fito daga bakina. Munje gidan amma sun tabbatar mana da sai dai Fulani da kanta taje ta nemi alfarma a wajan su amma su baza su zo ba, Tuba nake ranki ya dad'e" ta fad'a da girmamawa tana kallon Mama.

Mama tayi k'aramin tsaki tace, "kun fad'a musu wacece ni?." Jakadiya tace, "kwarai ranki ya dad'e."
Ta daki kujera tace, "Me ake yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login