Showing 6001 words to 9000 words out of 216282 words

Chapter 3 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

Saudia yace yana so. Banda abinda akaje har gida aka yi muku?." Umma tace, "to ina dalili auren sa da gafara zai saka ayi mana ba? Ko gafarar ubangiji zaka samu ta hanyar auren sai kayi addu'a Allah ya kawo maka wata hanyar a bar wannan, yaje ya nemi daidai shi amma banda Rauda baza mu zuba ido a kashe ta a banza ba."

Yayar mu tace, "wallahi fa, ina dalili daga zancen ana so sai a fara maganar kisa? Me yayi zafi shi ba wuta ba. Sannu Rauda Allah ya saka miki." Suka amsa da amin kafin Rahma tace, "Kuma abin haushi ma ko Yayar mu har yanzu babu wata maganar kirki da ta shiga tsakanin sa da ita, k'asaita da sarauta yake ji da ita ya kasa bata lokacin sa balle su fahimci juna." Umma ta sake cewa, "Wallahi shiyasa ban amince da soyayyar da yace yana yi mata ba ko kad'an, ni zuciyata fad'a min t??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ake akwai manufar da yasa yake sonta amma ba dan Allah ba."

Yaya Shamsiyya tace, "Babu lallai kuma Umma shi had'uwar jini haka yake wanda baka d'auka zai saurare ka ba in Allah ya had'a jinin ku babu wanda zai ji yana so sai kai. Ita duniya ai haka take daidan wani karkataccen wani." Umma ta kawar da kai tace, "Kayya dai Shamsiyya." Yaya Ummi tace, "To me Baba yace?."
"Me zai ce kuwa? Shi har yanzu bai saduda ba yana kan bakar sa ta aura masa Rauda sabida wani abun ya rufe masa ido baya ganin aibun hakan. Nidai na fad'a masa Rauda bazata aure shi ba." Shiru suka yi kowa yana juya abin a ransa daga baya aka cigaba da tattaunawa a kan maganar.

Da misalin k'arfe sha biyu na safe Walida da Habiba suka kawowa Rauda ziyara lokacin ta d'an ware ba laifi ana hira da ita, ita kad'ai ce a d'akin suka shiga Habiba tana yi mata jinjina irin na sarakai tace, "Allah ya ja zamanin uwar gida kuma amaryar yarima Asad." D'an k'aramin tsaki taja suka zauna kusa da ita Habiba tace, "Ai na rantse da Allah babu amana, ace wannan abin alkhairin ya same ki sai dai naji na gari amma ko a waya baki kira kin sanar damu ba?." Walida tace, "Ai wallahi Rauda baki kyauta mana ba duk yadda muke dake."

Rauda tace, "Sai abu ya dame ka ko yana maka dad'i sannan kake tunanin fad'awa wasu, ba auren sa zanyi ba kinga babu amfanin fad'ar" ta Fad'a a hankali tana kallon su. Habiba tace, "Akan me baza ki aure shi ba?, arzuk'i yazo miki har gida kisa k'afa ki ture shi."
"Ba irin wannan arzuk'i ake nema ba Habiba."
Walida tace, "irin wanne ake nema? Kamar a gaban ki aka fad'a mana halayyar wanda yace yana sonki d'in meye abin kin amincewa?."

Rauda tace, "gidan sarauta bai dace dani ba Walida. A tak'aice ma ya akayi kuka san da maganar nan?." Habiba tayi dariya tace, "Ke kina wasa da lamarin gidan sarauta kina kuma wasa da lamarin y'an unguwa, maganar babu inda bata zaga ba wallahi." Rauda ta girgiza kai cikin mamaki kafin Habiba tace, "meyasa bai dace dake ba? Ke ba mace bace ba?."
"Macece amma ba irin wacce ta dace taje can bace."
Habiba tace, "kawai dai bakya ra'ayi amma ni banga aibun hakan ba." Rauda tace, "Daga furta zai aure ni abubuwa marasa kyau sai faruwa suke dani da iyalan gidan nan, har gida suka je aka dake ni da Ummana har aka ji mata ciwo a hannun ta har yanzu bai warke ba; suka d'aye kwanikan gidan mu kawai dan a wulak'anta mu.? Allah ya kawo shi Asad d'in da wanda ya buge ni aka kaimu asibiti daga nan suka kawo mu nan da sunan za'a gyara wancan ashe rushe su sukayi. Mahaifiyar sa tazo har gidan nan tana yi min gargad'i akan in na aure shi sai taga bayana, akan me zan kai kaina halaka?."

Habiba tace, "bata da imani wannan babar tasa tsaf zata aikata, bana son talaka bata son talaka ya rab'e ta, amma in sha Allah sai kin shiga gidan nan matsayin matar sa in yaso ta mutu." Walida tace, "Ai na rantse da Allah zan so naji ace ta aure sa domin a nuna mata in Allah ya k'addara abu babu wanda ya isa ya canja."

Rauda tace, "Nidai ku cigaba da yi min addu'a kawai amma ina cikin tsaka mai wuya. Kalli wuya na ku gani" ta fad'a tana d'aga kanta suka kalla ga shatin igiya a wajan tace, "jiya aka shigo har d'akin nan aka shak'e ni da igiya za'a kashe ni ashe sune suka aiko a kashe ni." Habiba ta dafe k'irji tace, "Mun shiga uku, daman ana irin haka a gaske?."
"Nima dai abinda na gani kenan Habiba, kisa fa." Rauda tace, "To kunga meye amfanin shiga ta gidan nan matsayin matar sa?." Walida tace, "Babu wallahi." Rauda tace, "Kuma nida shi bawan Allah nan bai tab'a cewa yana sona ba, maganar sacan biyar bata had'a mu balle na tabbatar da yana sona ko akasin haka."

Habiba tace, "Na fad'a miki dalilin sa baya iya doguwar magana haka Allah ya halicce shi ko ita babar tasa baya yi mata doguwar magana." Walida tace, "Amma matsayin wacce yake sonta yaci ace ya d'an yi mata magana kodan ya kafa gwamnatin sa a zuciyar ta. Itafa soyayya babu ruwan ta da wani mulki ko sarauta ko rashin maganar sa." Rauda tace, "gane min hanya Walida, babu maganar da ta tab'a had'a mu sai sau d'aya a haka zan aure shi shima?."

Habiba tace, "haka ne amma dai kun san halitta mutum baya canja kansa. Mudai muna addu'a Allah ya tabbatar da lamarin nan." Rauda bata ce komai ba tayi murmushi suka cigaba da hira sama-sama.

*&&*

Hankalin Mama baya jikin ta jin labarin jikin mahaifin ta yayi tsanani wajan ciwo ba b'ata lokaci ta d'auki hanyar Kano ita da jakadiyar ta da Suhaima. Da taje nan taga duk yadda ake fad'a mata yanayin jikin nasa yafi haka duka y'an uwan ta suna nan na nesa dana kusa kowa ka kalla kasan yana cikin yanayi mara dad'i.

Bayan sun baro inda yake suka ware kansu iya y'ay'an d'akin su kamar yadda suka saba tunda mahaifiyar su ta rasu basa shiga cikin y'an uwan su ware suke waje guda kamar ba jinin su ba. Suna tare su hud'u mata mazan guda uku suna nasu waje suke tattaunawa akan abubuwan da ya shafe su. Babbar cikin su itace mai hali d'aya da Mama ta kalle ta tace, "ya batun Asad kuwa?." Mama tace, "Hmm baki ga yadda na rame ba? Tashin hankali ya sako ni gaba akan auren nan nasa." Wacce take bin Mama tace, "Asad d'in aure zaiyi?." Mama tace, "Allah ya sawwake ai batun wannan aure an soke shi bai isa ya jawo min abinda fad'a a dangi ba." Y'ar autar su tace, "Abin fad'a a dangi? Auren shine zai zama abin fad'a?."

Babbar cikin su tace, "To abin fad'a mana in kuka ji yarinyar da ya d'auko zai aura sai abin ya baku mamaki; kamar Asad ace ya d'auko y'ar talakawa yace ita yake so?." Mama tace, "Ai baki K'arasa ba, gata bak'a ga muni gata gurguwa gata mai tallan abinci a kan titi." Wacce take bin Mama mai suna Maimuna tace, "Shi kuma a ina ya gano ta?." Mama tace, "Bari kedai kawai, Hydar ne ya buge ta a mota kafin ya kwanta ciwo shi kuma ya nemo ta da niyar yi mata magani shikenan fa sai ga magana wai sonta yake yi, kina jin maganar nan kin san akwai asiri a lamarin."

Y'ar autar su tace, "Ba wani asiri soyayya ce fa daga Allah ni banga aibu dan ya aure ta ba. Nidai nasan Asad bazai d'auko mara asali da ilimi ba, an fa daina wannan abun ace wai d'an sarauta sai y'ar sarauta indai Allah ya kulla kawai ayi." Maimuna tace, "Nima dai haka tunda har yana sonta ai zance ya k'are." Babbar cikin su tace, "Daman ku ai ba'a tab'a abin kirki daku. Yanzu namiji kamar Asad zaku goyawa baya ya auri yarinya mai kammin da aka lissafa?."
"To meye a ciki da ya auri Jiddan da take so ba gwara ita ba, Jiddan nan bata da tarbiya ko kad'an ga shegiyar rawar kai a cikin ta. Meye abin so a Jidda? Kyaunta ne kawai yake rud'ar Mama amma me take dashi?."

Babbar cikin su tace, "Ke malama bama son rashin kunya." Tab'e baki tayi suka tashi suka basu wajen yadda zasu fi jin dad'in tattaunawa.
Ta kalli Mama tace, "Kar fa ki amince da auren nan amincewar ki daidai yake da fad'uwar darajar ki a idanun kishiyoyin ki wallahi, ki dage kai da fata wajan ganin auren nan bai yu ba in kuwa ba haka ba kina ji kina gani wata y'ar talakawa zata kwance miki d'an ki domin nan gaba in zaki ganshi sai kin neme ta sabida ta fiki kusanci dashi." Mama ta sake zuwa wuya tace, "Bari kawai Yaya zan san abinda zanyi."
"Ya dai kamata" ta fad'a daga na suka cigaba da tattaunawa a kan lamarin jikin mahaifin su.

A Katagum kuma da yamma mai martaba ya nemi ganin Baba kamar yadda aka tsara su biyu ne kacal a d'akin ganin bak'i na musamman mai martaba yana kan kujara shi kuma yana k'asa a zaune mai martaba yace, "Dalilin da ya saka nace a kira min kai akan batun auren y'arka da Asad, wanne mataki ake kai a yanzu ta amince ita yarinyar?."
Baba ya gyara zaman sa yace, "Ranka ya dad'e ta amince; sai dai tana jin tsoron Fulani duba da abubuwan da suka faru bayan furta zai aure ta d'in da yayi."

Mai martaba ya murmusa har cikin zuciyar sa yaji dad'in hakan domin kuwa shi kad'ai yasan alkhairin da ya gani a auren Asad da Rauda yace, "Ba abar tsoro bace; kamar yadda ta isa dashi muma mun isa da ita kar taji tsoro indai ta amince shine abinda nake so naji." Ba tare da tunanin komai ba Baba yace, "ta amince ranka ya dad'e, naso ma ta biyo ni sai ta nuna min baza ta iya zuwan ba shiyasa nazo ni kad'ai."

Mai martaba yace, "Alhamdulillah. D'aurin auren nan kusa nake so ayi shi in yaso sai su tafi k'asar da za'a ayi mata aikin k'afar tare in sun dawo sai ayi biki a tare. Bana so ma yasan an d'aura auren sai bayan an d'aura in ba haka ba mahaifiyar sa zata iya canja masa ra'ayi lokaci guda. In Allah ya kai mu asabar jibi kenan ina so a d'aura musu aure da ita in da hali."

"Allah yaja da ran mai martaba ai babu komai umarni kawai zaka yanke mu namu aikin mu bi." Mai martaba yaji dad'in kalaman Baba ya d'auko wata leda a kusa dashi ya mik'awa Baba yace, "kud'in na gani ina so, kud'in lefe da duk wani abu dake yiwa mace. Bana so a d'auki lokacin da za'ace sai an had'o kaya shiyasa na bada wannan kud'in ayi amfani dasu." Baba ya karb'a ya koma ya zauna kana yace, "Allah ya taimake ka, muna godiya Allah yaja da rai Allah yasa ayi damu."

"Amin. Nine da godiya ai duk da abubuwan da suka faru aka amince aka bamu y'a kamar ta mai ilimin addini da tarbiyya." Baba dad'i yake ji har cikin b'argon sa yace, "Ranka ya dad'e dad'i mune ya kamata muji shi baku ba, Allah ya k'arawa mai martaba lafiya da imani muda aka had'a jini damu ai mune zamu gode."

Murmushi yayi kana yace, "Aje ayi komai yadda ya kamata in Allah ya kaimu jibin koma gobe juma'a za'a d'aura musu aure da ita dan bana so wani abu ya jifta da za'a fasa." Baba yace, "Goben ma yayi ranka ya dad'e Allah ya nuna mana." Daga haka sukayi sallama da Baba ya yi godiya sosai ya tashi ya tafi zuwa gida zuciyar sa fari kallllll kamar an wanke masa ita haka yake ji.


*sai Baba*=؃?>?#?
[17/12, 10:39 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*029.*

Cikin tsantsar farin ciki Baba ya koma gida koda yaje bai sanar dasu komai ba ya adana kud'in a waje mai kyau ya cigaba da sabgar sa hankali kwance domin ya lashi takobin babu abinda zai hana auren Asad da Rauda koda bata so, daman Anas ya saka yake d'aga k'afa yanzu tunda babu batun sa ko ana muzuru ana shawo sai ya zama sirikin sarki mai jiran gado.

Lokacin da ya shiga gidan da magariba suna zazaaune a waje d'aya har su Inna suna kallon tv ya samu waje ya zauna ya kalli Rauda yace, "ya jikin naki?." Rauda tace, "Da sauk'i."
"Haka ake so. Wacce irin shawara kika yanke?." Rauda ta kalli Baba tace, "Akan me Baba?."
"Auren ki" ya bata amsa yana kallon ta. Kai ta saukar k'asa kana tace, "Bana ra'ayin auren sa gaskiya." Baba ya d'aure fuska yana kallon ta yace, "Kamar ya bakya ra'ayi?."

Rauda ta d'ago ido tace, "Eh Baba, bana son na aure shi." Baba yace, "To akan me bakya son auren sa? Wani abun kika fishi da bakya sonsa?." Umma ta bud'e baki da niyar bashi amsa ya d'aga mata hannu kana yace, "Kar naji bakin kowa a nan indai ba Rauda ba, da ita nake magana bada ku ba kar a saka min baki"ya fad'a a kausashe yana kallon ta. Dole tayi shiru ya mayar da kallon sa ga Rauda yace, "Ina jin ki." Rauda tace, "Ya fini komai Baba, kawai ni bana son auren sa ne sabida bana son sa." Baba ya gyara zama yana kallon ta yace, "ya kamata ki fara son sa kuwa domin auren ki dashi babu fashi."

Rauda ta wara idanu tace, "Baba auren sa daidai yake da rasa rayuwa ta."
"Nasan daman tsoron da kike ji kenan ai shiyasa kika ce bakya son sa, ki kwantar da hankalin ki a ko ina Allah yana tare da mai gaskiya, Allah bazai bari ya cutar dake ba tunda baki hakkin komai." Rauda tace, "Duk da haka Baba ni bai min ba."
"Daman ai basai yayi miki ba tunda shi kinyi masa ai zance ya k'are. Zancen yayi miki ai bai tashi ba tunda shi har ya ganki yace yana so shikenan." Umma da take sauraren su ta kasa jurewa tace, "Auren dole kenan zakayi mata?."

Baba ya kalli jama'ar falon yaga har su Khalil suna wajan sai ya fasa fad'ar abinda yayi niya ya tashi yana kallon su yace, "Kowa ya tashi yaje yayi sallah" yana fad'a ya fita daga falon bai kuma cewa komai ba.

Babu wanda ya kuma magana aka tashi aka tafi sallah bayan sun idar da sallar i'sha a d'aki Rauda ta kalli Umma da take kan sallaya tace, "Umma kenan Baba auren dole zaiyi min?" Ta fad'a idanun ta na kawo ruwa zatayi kuka.
"Babu batun auren dole tunda kince bakya so auren nan baza'a yi sa ba, abu mai sauk'i ne naje har fada na nemi ganin martaban na fad'a masa halin da ake ciki ai ina da k'afar zuwa, dan san abin duniyan mahaifin ki tsaf zai aurar musu dake."

Rauda tayi shiru tana tunani tace, "Ina jin yawan fad'uwar gaba tsakanin kwanakin nan Umma." Umma tace, "Ai dole kiji fad'uwar gaba, har gida fa akazo za'a kashe ki in baki ji fad'uwar gaba ba ai baza kiji dad'i a zuciyar ki ba."

Shiru Raudan tayi ganin kamar ta shiga damuwa ya saka Umma tace, "Ki kwantar da hankalin ki kome kika ga ya faru Allah ya rubuta faruwar sa tun farko, ki nutsu ki ta addu'a Allah zai kawo miki mafita." Kai kawai ta d'aga jikin ta a sanyaye Umma ta fita daga d'akin ita kuma ta samu ta lallab'a tayi sallah raka'a biyu ta karanta addu'ar da manzon Allah S.A.W ya bayar ta istikhara kana ta tashi ta kwanta badan tana jin bacci ba.

Da safe jiki a sanyaye ta tashi sabida mafarkin da tayi wai ana bikin su da Asad shi da ita sai kuka suke amma da an gansu anga yanayin amarya da ango, gamsuwa take ji a zuciyar ta da gangar jikin ta na Asad shine mijin ta amma ta k'i barin hakan yayi tasiri a jikin ta sai kawar da tunanin take yi a dole baza ta bari yayi tasiri ba sai hakan ya haifar mata da sanyin jiki. Ko abinci bata iya ci ba tana zaune a d'akin tayi uban tagumi dana sanin ma yin istikhara take yi da tasan abinda zata gani kenan ko abinda zata ji a jikin ta kenan da bata yi ba.


Tana nan zaune Umma ta shigo ganin yanayin ta ya saka tace, "Ke kuma lafiya kike ko lek'owa bakiyi ba?." Numfashi ta sauke kana tace, "Umma mafarki nayi." Umma ta zauna kusa da ita tace, "Mafarki kikayi kin auri Asad ko?."

Rauda ta kalli Umma da mamaki kafin tace, "Umma ya akayi kika sani?." Umma ta dafa ta tace, "Nima nayi Rauda. A daren jiya ban kwanta ba sai da nayi ta addu'a akan nema miki zab'in Allah, na kuma rok'i Allah da ya nuna min zab'in da yayi miki ko a mafarki ne. cikin ikon Allah sai Allah y nuna min Asad shine mijin ki duk da mafarki ba gaskiya bane amma yana kasancewa wani lokacin Rauda. bazan ja da ikon Allah ba addu'ar kuma da nayi Annabin mune ya koyar damu ita sai nake ji a jikina yanzu na gamsu da auren ki dashi."
Rauda ta rausayar da kai kana tace, "Umma akwai tarin abubuwa a gaba wanda shekaru na sunyi kad'an na fuskance su, ki duba ikirarin mahaifiyar sa a kaina, bana son auren nan ko kad'an Umma."

"To Rauda nidai ban san me zance ba amma mu barwa Allah zab'i kawai, in ya zab'a miki shi ki saka a ranki shine alkhairin, in kuma akasin haka ya faru ki saka a ranki ba alkhairi bane ba. Ki tashi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login