Showing 48001 words to 51000 words out of 216282 words

Chapter 17 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

kai kana yace, "in akwai mai magana ina so ya fad'a mana a wannan mataki da muke kai na lokacin k'arshe a kan karaga." Kowa ya kalle shi duk sai kuma ya basu tausayi zuciyar kowa ta motsa san k'ira ya sake kwalla kirari yace, "Bamu da tacewa sai dai muce? Allah ya k'ara maka lafiya, sai dai muce Allah ya saka maka, sai dai muce Allah ya faranta ranka ya dad'e kamar yadda aka faranta mana. Hakika bamu da bakin godiya domin anyi mana abubuwan alkhairin da baza mu manta dasu ba,? badan an yanke hukunci ba da munce muje a haka bama so muyi rashin adalin shugaba. Ka gama lafiya dan Toron guiwa gaban ka alkhairi bayan ka alkhairi."

Mai martaba ya murmusa kana yace, "Team makers ku shaida Mubarak Wambai kenan shine zai yi rikon kwarya kafin dawowar Asad." A take gaban mutum biyu ya buga Wambai ya kalli Waziri shima ya kalle shi da alamun tashin hankali k'arara a tare dashi. Wambai ya kalli mai martaba yaga bashi yake kallo ba jikin sa duk yayi sanyi domin bai shiryawa hakan ba kwata-kwata.

Mai martaba ya kalli Hydar sai Hydar ya mik'e ya fita jim kad'an ya shigo bayan sa jakadiya ce da babban tray an rufe shi da farin kyalle ta k'araso ta ajjiye bayan tayi gaisuwa mai martaba ya mik'e tsaye kowa ya mik'e tsaye aka bud'e tray d'in mai martaba ya kalli Wambai ganin haka ya saka liman yace, " Allah yaja zamanin Wambai bismillah."

Jikin sa a sake ya tashi ya zauna a kan kujerar akayi kabbara tare da buga bindiga mai martaba sarki mai murabus ya singing akan takardar resignation letter Wambai ya saka hannu aka sake buga bindiga. K'aramar kujera wacce take k'asa da wacce wambai yake kaj Sarki mai murabus ya zauna yana murmushin farin ciki ko babu komai zai bar duniya da yak'inin al'umma zasu samu shugaba na gari.

A wajan aka gabatar da komai na nad'in sarautar kasancewar rok'on k'warya ce a nan aka gama komai sai Asad ya dawo a nan za'ayi gagarumin abubuwa. Kowa ya watse zuciyar su cike da jinjina adalci da tausayin na k'asa irin na Mai martaba Nasir bin Sa'ad sab'anin wasu da suka tashi kamar ana yi musu bindiga a zuciya sabida bak'in ciki da hassada.

? ? ? ?? Cikin lokaci kad'an labari ya shiga cikin gida Mama na zaune tana kallon tv ta hakimce hadimai suna k'asanta a zazaaune jakadiyar ta shigo a guje ta zube a gabanta tana fad'in, "Allah yaja zamanin ki, Allah ya k'ara miki lafiya. Addu'ar mu ta karb'u yau mai martaba yayi murabus ya d'ora Wambai akan karaga kafin dawowar Mai martaba sarki Asad." Mama ta gyara zama ta kalle ta a firgice tace, "Me kike cewa? Kin san bana son wasa da hankali ko?."
"Ni wacece da zan yiwa fulani wasa? Da gaske nake ranki ya dad'e a gaban yallab'ai Hydar akayi komai."

Mama ta daki kujera cikin dunbin takaici zatayi magana sai kuma ta kalle su tace, "Ku tashi ku bani waje." Jiki na rawa suka mik'e suka fita Mama ta dafe kanta tace, "meyasa ba'a jira ya dawo ba za'a yanke wannan hukuncin? Meyasa za'a bada rik'on kwarya?" Ta fad'a tana mik'ewa tsaye hankalin ta duka a tashe yake. Agogo ta kalla taja tsaki domin tasan yanzu yana tare da bak'i da babu abinda zai hana bata bayyana a gare shi ba yanzun nan.

"Ya zamar maka dole Asad ka dawo a cikin kwanakin nan, ko ya bada dama ko bai bayar ba zan dawo da Asad ya dawo ya karb'i mulkin sa. Bazan lamunci wannan zaman rik'on ba komai zai iya faruwa" ta fad'a da sauri tana shiga d'aki jikin ta na rawa sosai.

Cikin gida gabad'aya ya d'auka aka ta bushe-bushe da kid'a domin kowa yaji dad'in zab'in mai martaba dukka su biyun ba abin yarwa bane koda Wambai d'in ne zai d'ore da mulkin abin murna ne ga talakawan sa.

Fulani Hajiya kuwa hankalin ta yafi na kowa tashi har rama tayi a lokaci guda cikin ta ya juya ta shiga band'aki har sau hud'u ta sha magani tana sauke numfashi zuciyar ta na bugawa kamar zata fito daga k'irjin ta. Kiran Waziri take jira amma shiru hankalin ta ya tashi ta rasa inda zata saka ranta taji dad'i domin ba haka suka so ba sun so a bawa Waziri rik'on kwaryar ba Wambai ba.
Baza ta iya jurewa zaman ba zuciyar ta zata iya bugawa ta fita ta d'auki driver ita kad'ai ya kai ta inda suka saba had'uwa da Waziri da Aliyu.

Kamar yadda ta saba ta shiga ta same su a zaune Waziri hankali tashe jikin sa na tsuma ta kalli Aliyu da yake tsaye tace, "Meyasa ba'a sanar dani akwai meeting ba badan nazo na da anyi babu ni kenan?." Waziri yaja tsaki a harzuk'e yace, "Amma dai kin san dole a had'u duba da abinda ya faru ko?." Sai kuma yayi shiru yana tari yana dukan zuciyar sa da take masa ciwo.

Aliyu bin sa yake da kallo kafin yace, "Nayi mamakin yadda ka tayar da hankalin ka na d'auka baza ka damu ba ai." Waziri ya kalle shi a harzuk'e yace, "a bawa Wambai kujerar karaga kace bazan damu ba?, kasan burina a akan wannan kujerar?, kasan adadin kwanakin dana d'auka ina jiran wannan ranar?." Aliyu ya bishi da kallo sai yayi murmushi yace, "Ohh kenan duk abinda kake fad'amin ba gaskiya bane kanka kake yiwa yak'i bani ba?."

Sai a sannan ya dawo hankalin sa ya dafe kai yana jin yaji a idanun sa kuka ma yake so yayi amma ya kasa ya cize bakin sa Aliyu ya murmusa bai maimaita maganar ba dan baya so ya gano ya fahimce shi ba tun yau ba yace, "Bai kamata ku d'aga hankalin ku ba mu jira dawowar Asad d'in, kun manta da cewa daman shi muke so yau karagar? Ko kun manta plan d'in ne?."

? ? ? Waziri ya rausayar da kai yace, "Sai yanzu na tuna, amma kana ganin Mubarak zai bari Asad ya dawo k'asar nan?." Aliyu yace, "Akwai Mama fa, duk wahala duk runtsi sai ta dawo da Asad cikin kwanakin nan. Kar kayi mamaki nan da kwana biyu zaka iya ganin sa domin in akace Mama akan burin ta an gama magana." Fulani Hajiya tace, "Kana ganin kuma zaiyi saurin amincewa shi Asad d'in?."
"Ai zance ya k'are tunda har an riga anyi komai."
Waziri yace, "na k'agu, na matsu, na damu, na tsanantu naga wannan lokacin Aliyu." Ya murmusa ya mik'e tsaye ya zuba hannu a aljihu yace, "Kar ka damu lokacin yazo" ya fad'a yana fita daga d'akin zuciyar sa fess domin burin sa ya kusa cika.

Yana fita Hajiya taja tsaki tace, "nemo mana master planer muna buk'atar ta yanzu domin komai yana neman lalacewa." Waya Waziri ya d'auka take sai ga kira ya shigo yace, "Y'ar hakal" ya fad'a yana d'aukar wayar daga can b'angaren tace,

"Na rasa dame zan fara jaje zan muku ko kuma farin ciki zan taya kanmu, abinda muke so ya kusa faruwa amma ba haka muka so ba." Waziri yace, "Mafuta muke nema Master in har Asad ya karb'i mulkin nan na shiga tara bama uku ba, ga wannan zararren da kika saka muka kawo cikin mu yana da wayo sosai bana tunanin zai bar wata gab'a da zan kwace mulki a hannun sa."

Tace, "Zaman Aliyu cikin ku kariya ce domin shine next target d'in mu tunda abinda yazo da haka. Ta dole zamu kwace mulkin ai ba ta laluma ba kudai yanzu kuyi addu'ar dawowar Asad da wuri da zarar ya shigo Nigeria komai ya k'are."
"Amma kin manta aikin da mukayi dan mu tura shi wata k'asar? Yanzu kuma muce ya dawo bayan kin san k'arfin aikin" Hajiya Fulani ta fad'a.

Master tayi dariya tace, "Asad zai dawo yana nan tafe zai dawo, komai ma zai karye kuma Rabi'a zatayi nasarar raba shi da matar sa zai kuma dawo ya auri wacce take so ya kuma karb'i mulkin, mu kuma wannan itace last chances d'in mu."

Waziri yace, "Ina jin tsoron hakan fa." Tace, "ka k'arfafawa kanka guiwa a taswirar k'addarar ka akwai mulki kuma yana nan tafe."
"Allah ya tabbatar Master, in hakan ta faru zanfi kowa murna." Murmushi tayi tace, "Shine lokacin bayyana ta a gare ku. Ku koma kuyi mubaya'a kar ku nuna akasin haka kuyi farin ciki ni kuma ina gefe ina taimaka muku" tana fad'a ta yanke wayar.

Waziri ya kalli Hajiya yace, "naji dad'in bayanan ta domin kuwa na tsorota da yanayin wannan makakken Aliyun, kansa akwai daud'ar kwaya da giya zai iya aikata komai." Hajiya tace, "Shiyasa ban so ya shigo team d'in kwantan b'auna ba gabad'aya."
"Ki barmu dashi mun fishi iya tsara film aiki zamu dashi kafin shima mu ture shi gefe."

Aliyu da yake tsaye yana sauraron su ya murmusa tare da cize bakin sa ya kad'a kai ya tab'e baki ya bar wajan domin kuwa ko aljani bai isa ya gano shirin sa akan su ba sai shi kad'ai yasan abinda yake tsarawa kuma k'iris ya rage komai ya bayyana......



Tofa masarauta ta rikice. Yanzu aka fara wasan?&
@&??&
@&??&
@&?
[17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*041.*

? ? ?? A gaban Dr Asif suke a zaune yana duba k'afar Rauda a cikin wani inji da yake nuna ko wanne k'ashi na jiki. Bayan ya kammala ta sakko ta zauna a kujerar da take kallon ta Asad Dr ya dawo shima ya zauna ya kalli Asad cikin harshen larabci yace, "Asad komai ya dawo daidai k'afar ta babu sauran matsala ta warke gabad'aya." Asad ya girgiza kai alamun gamsuwa Dr ya kalli Rauda yace, "Congratulations Madam."

Murmushi tayi tace, "Thanks." Had'a ido sukayi da Asad sai ya d'auke kai kafin ya tashi suyi sallama da Dr Asif su fito daga office d'in. Suna fitowa suka hango Muhibba tana nufo su Rauda ta d'aure fuska hannun ta da yake cikin nasa ta rik'e nasa sosai har ya kalle ta sai yaga abinda take kallo shima ya d'auke kansa yayi kamar bai gani ba.


K'arewa musu kallo Muhibba take yi kafin ta tab'e baki ta k'araso tace, "Ban tab'a karo da couples wanda basu dace da juna ba sai wannan, koda yake maybe akwai manufar da ya saka ya auri wannan abar amma ba so ba" tana fad'a ta wuce su babu wanda ya tanka mata jiran elevator sukeyi suna tsaye.

Elevator ya danna suka shiga suka sauka k'asa suka fita daga asibitin suka shiga mota, yayi niyar su d'an yi yawo but baya jin dad'in jikin sa suka koma hotel suna shiga ya cika hannun ta ya shiga d'aki itama bata damu ba ta wuce inda take. Yana shiga wayar sa tayi k'ara ya duba ganin sunan mahaifinsa ya saka shi zama ya nutsu sosai kana ya d'auka da sallama.

Bayan sun gaisa daga can b'angaren yace, "Zaki nasan zaka samu labari abinda ya faru a nan Katagum, yau dai Allah ya nufa na sauka daga kan karaga na kuma tamk'ata a hannun kawun ka Mubarak shi kuma da zarar ka dawo Nigeria zai baka domin rik'on kwarya aka bashi kaine shugaba ba?shi ba." Gaban Asad ya fad'i har sai da ya runtse idon sa ya sauke numfashi a hankali jin hakan mai martaba yace, "ka zauna har matar ka ta samu lafiya Asad, in ka gama komai da ya kaika sai ka dawo kayi abinda nace."

Cikin murya mai sanyi da rawar murya yace, "Amma Abba....." ya dakatar dashi ta hanyar fad'in, "Kayi min alqawari zaka dawo ka karb'i karagar mulkin katagum, kayi min alqawari zakayi k'okarin sassauta wannan dabi'ar taka ta rashin son magana babu ta yadda za'ayi shugaba ya kasance a haka shiyasa nake makaa addu'a a ko wanne lokaci, nasan halittar kace amma zaka iya k'okarin ganin ka d'an gyara wani abun kana shugaba kamata yayi ka zama mai magana akan komai in ka kasance haka na k'asa dakai ya kenan?. Kayi alqawari min zaka canja; kayi min alqawari kome zai biyo baya baza ka hak'ura da karb'ar mulkin nan ba. Zaki kayi min alqawari zaka tafiyar da shugabancin katagum fiye da yadda nake tafiyar dashi, bana jin ka ta b'angaren abubuwa da yawa nasan talakawan ka zasu ji dad'in mulkin ka ko mutuwa nayi nasan na bar su a hannu wanda zai kula dasu ya taimaka musu ya kuma jiqan su. Abu biyu nake ji daman a tare dakai mahaifiyar ka da kuma wannan dabi'ar nan taka ta rashin magana. Babar ka zatayi k'ok'arin ganin ta takwara ka kayi abinda bashi kake son yi ba shima kayi min alqawarin kome zata zo maka dashi indai ya sab'a tsarin ka kar ka amince mata."

Mai martaba yayi shiru kafin ya cigaba da cewa, "kana saurarona Zaki?." Asad muryar sa tayi sanyi yace, "ina sauraron Mai martaba." Mai martaba ya cigaba da fad'in, "komai zaka dawo ka tarar a katagum kayi hak'uri ka jure masa ka fuskanci abinda yake gaban ka. Asad duk runtsi duk wahala karka bari mulkin katagum ya sub'uce maka duk hannun wanda ya fad'a ba kai ba masarautar da wanda suke k'arkashin ta gabad'aya ta lalace, za'a shiga hali mara dad'i a duk sanda mulkin ya bar hannun ka, kayi min alqawarin duk dana roka a wajan ka?." Asad yayi shiru yana tunani ta Ina zai fara gudanar da abin baya so?, ta Ina zai fara mulkar al'umma?, wanne irin sarki za'ayi?, kurma ko bebe?.

"Na Amince Takawa, nayi yiwa mahaifina alqawari in sha Allah zanyi iya bakin k'ok'arina nayi abinda akace, ina rok'on mai martaba daya taya ni addu'a Allah ya bani ikon gudanar da komai cikin ilimi da nutsuwa" ya furta a hankali.


Takawa yayi murmushi yace, "Allah ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?yayi maka albarka Zaki, Allah ya kare ka daga sharrin duk mai nufin ka da sharri, ya baka ikon bawa mak'iyan ka mamaki wanda suke ganin baza ka iya gudanar da sarauta ba ka basu kunya. Ka cigaba da addu'a Asad akwai wanda suna nan suna yi maka mummanan aikin da baza ka kuma dawowa Nigeria ba, amma mu da Allah muka dogara ka cigaba da rok'on sa zai baka kariya a ko ina."

Jin farin ciki a muryar mahaifin sa sai yaji sanyi a zuciyar sa shima yace, "Amin Takawa. Allah ya k'ara lafiya da nisan kwana."
"Amin Zaki, ina jiran dawowar ka nan da wasu kwanaki." Daga haka sukayi sallama ya yanke wayar Asad yayi tagumi yana tunanin ta inda zai fara.

? ? ?? Bud'e k'ofar da akayi bai saka ya kalle ta ba ta k'araso tana kallon sa ganin gabad'aya ya canja kamar bashi ba tace, "Prince Lafiya?." Sai sannan ya kalle ta ya rik'o hannun ta guda d'aya ya dawo da ita kusa dashi ya zaunar da? ita a akan cinyar sa ya d'ora kansa a wuyan ta d'umin wuyanta yana shiga jikin sa idanun sa kulle yana jan numfashi yana saukewa. Gabanta ya fad'i domin tun ranar da wani abun ya shiga tsakanin su bai sake koda rungume ta da wata niya ba ganin abinda ya faru a yanzu sai taji fad'uwar gaba bashi yadda yake sauke mata numfashi a wuyan ta jikinta sai yayi sanyi.

"Baba ne yace kwana biyu baku gaisa ba" ta furta a hankali ba tare da ta kalle shi ba dan kar ma ya d'auka wani abun ne ya kawota. Sarai ya jita amma bazai amsa bane ya zaga da hannun sa cikin ta ya rik'e ya sake had'a ta da jikin sa zuciyar sa na gudu sosai yana buk'atar rarrashi a halin da yake ciki. Lup dup, lup dup, lup dup, haka take jin bugun zuciyar sa a jikin ta ta kalle shi taga idanun sa a kulle suke har lokacin fuskar sa ta canja alamun akwai abinda yake damun sa.

Kam taji ya rungume ta a jikin sa kamar zai b'alla mata k'ashin baya kafin jikin sa ya fara rawa a hankali zazzab'i ya mamaye fatar jikin sa, zafin taji yana shiga har cikin jikin ta kalle shi gashi ya matse ta sosai ta kasa motsin kirki a jikin sa. A hankali taji ya sassuta mata rik'on ta tab'a wuyan sa tace, "Jikin ka da zafi prince" ta fad'a da kulawa tana kallon sa.

Ya sake ta ita kuma bata tashi ba ta saka hannu ta tallafi hab'ar sa tana kallon idanun sa da suke a lumshe tace, "Me yake damun ka?." Bai magana ba bai kuma bud'e ido ba ta saka hannu ta shafi gashin fuskar sa sai ya bud'e idanun sa da suka koma jajaye ta wara ido waje tace, "me yake damun ka dan Allah?." A hankali ya ya dawo da fuskar sa kusa da tata ya had'a goshin sa da nata ya furta, "Bana so! bana so!."? Yadda bakin sa yake motsawa ya saka tace, "meye baka so?."

A wuyan ta ya sake kifa kansa yana juya fuskar sa kafin ya tsotsar fatar wuyan ta da zafi-zafi, lumshe idanun ta tayi duk da tana jin zafi kad'an-kad'an a fatar ta tana jin sa bata da abinda zatayi ta hana shi sai daga baya ya d'ago kansa ya kalli idanun ta yace, "Bana so, bana so su raba mu dake, kiyi wani abun kar su rabu. Ina sonki Muwadda." ya fad'a a sanyaye tare da lumshe idanun sa yana ji kamar yayi kuka. Nan take taji gabanta ya fad'i jin abinda yace baya so a raba su tace, "Waye zai rabu mu? Meye baka so?, kayi min bayani pls."

Bai amsa mata ba yayi shiru ta sake cewa, "jikinka da zafi sosai kana buk'atar san magani." Kamar zaiyi magana sai yayi shiru ta kasa gane shi ba magani yake so ba kwantar masa da hankali yake buk'atar ayi ba magana ba, da baya ya kwanta ya zama daga k'ugun sa zuwa kansa na kwance guiwyoyin sa suna yadda suke a tsaye har lokacin tana zaune a jikin sa. Ganin yak'i magana sai tayi niyar tashi ba zato taji ya jawo ta ta fad'a jikin sa gabad'aya ya saka hannun sa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login