Showing 144001 words to 147000 words out of 216282 words

Chapter 49 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

kuma tace, "Mai martaba." Shiru tayi tace, "ya zama dole a hana bakin sa buWewa in hakan ta kasance I'm in trouble" ta fad'a tana tashi da gaggawa ta saka alkyabbar ta ta nufi b'angaren sa.

Tana shiga ta tarar da Dr da yake kula dashi ya kalle ta yace, "Good day madam." Da yake bature sai tace, "How was your work."
"Fine ma'am."
Kallon sa tayi suka had'a ido sai ta d'aga masa kai shima ya d'aga mata kawai sai ta juya ta fita shi kuma ya d'auko allura a aljihun sa ya balle kanta yaja a sirinji ya zuba Mai martaba a cikin ruwan da yake shiga jikin sa.


*&&&*

? ? ? Washe gari.

Rauda jikinta ta ya samu k'wari kumburin fuskar ya ragu sai dai har lokacin akwai shatin duka a jikin ta idanun ta kuma akwai jini a ciki amma ta samu k'arfi babu laifi. Umma ma taji sauk'i amma jinin yak'i sauka sabida bata cire damuwa a zuciyarta ba.

Rauda kallon Umma kawai take a inda take kwance ita kuma tak'i kallonta gabad'aya hakan ne yake sake tayar mata da hankali taji gabad'aya komai baya yi mata dad'i. Tana shirin sakkowa daga kan gadon taje wajan Umma aka turo k'ofar d'akin aka shigo da sallama. Anas ne ya shigo shida Baba ya k'araso inda Umma take ya duk'a har k'asa yace, "Barka da safiya Umma, ya k'arfin jiki?."

Umma sai taji hawaye yana k'ok'arin taruwa a idanun ta ta daure tace, "Jiki Alhamdulillah Anas." Yace, "ban san abinda yake faruwa ba sai yanzu muka had'u da Baba yake sanar dani duka baku da lafiya, Allah ya k'ara lafiya yasa kaffara ce."
"Amin" Umma ta amsa a tak'aice muryar ta na rawa sosai. Mik'ewa yayi ya k'arasa inda Rauda take yace, "Subahanallah meya same ki haka?." Shiru bata amsa ba sai yace, "ya jikin naki?."
"Da sauk'i" ta amsa idanunta na k'asa murya na rawa sosai.
"Allah ya k'ara lafiya" ya furta yana binta da kallo gabansa hana fad'uwa haka kawai.

Ta amsa da amin kafin ya kalli Baba sai yaga sun had'a ido ya sauke nasa k'asa yace, "Baba zan koma, Allah ya basu lafiya gabad'aya." Baba yace, "Amin Anas, da mun koma gida zan sanar dakai dan ina neman ka." Anas yace, "Baba amma dai lafiya dai ko?."
"Kar ka damu lafiya lau" Baba ya furta ganin ya rud'e lokaci d'aya.

"Shikenan Baba, Allah ya basu lafiya" ya fad'a yana yi musu sallama ya fita Umma ta bishi da kallo kawai sai ta fashe da kuka ita kanta Raudan Kukan take dan karamcin Anas a gare su bai cancani abinda tayi masa ba. Baba yace, "Zaki ci uwarki ai, yanzu kika fara kuka ai; wallahi matuk'ar baki fad'a min wanda kika bawa kanki wallahi sai kin bar min gidana."

Baba kuma cewa, "Da wanne ido kike so na kalli yaron nan?, kawai sai nace masa kina da cikin shege Rauda....?. Kin cuce ni wallahi, kuma bazan yafe ba." Jin abinda yace sai ta k'ara k'aimi wajan kuka hankalin ta ya tashi ta diro daga kan gadon zatayi magana Baba ya fita bai saurare ta ba ta kalli Umma taga ta kulle idanunta alamun bazata ji ba sai kawai ta cure a wajan tana kuka.

Nan da nan zazzaSi ya sake rufeta da ciwon kai Allah ya shigo da nurse akayi gaggawar sake saka mata ruwa da allurai. Sai bayan sallar azahar ta farka taga y'an uwanta wasu suna nan wasu basa nan ana ta rarrashin Umma da alama kuka take tayi har lokacin.

Sauka Rauda tayi daga kan gadon ta shiga band'aki tayi alwala ta fito ta tayar da sallah a zaune dan k'afar ta har lokacin ciwo take bazata iya sallah a tsaye ba. Tana sallah tana kuka bayan ta idar ne take jin sautin muryar Umma tana cewa, "me na yiwa Rauda tayi min wannan sakayyar? Ta rasa abinda zata saka min dashi sai cikin shege..." Sai ta sake fashewa da kuka.

Yaya Ummi tace, "Dan Allah ki daina Kuka Umma kinga ance jinin ki yak'i sauka sabida damuwar da take ranki dan Allah kiyi hak'uri."
"Nayi hak'uri fa kika ce, yanzu fasa aurenta za'a yi fa saboda cikin jikinta wanda bamu san waye uban sa kuma kice nayi hak'uri?. Fasa auren bashi ne matsala ba babbar matsalar shine cikin jikin ta." Shiru Yaya Ummi tayi ta kalli Rauda da take kuka itama tace, "Rauda ki sanar damu cikin waye a jikin ki dan Allah ko hankalin Umma zai kwanta."

"Meye amfanin fad'ar Ummi? An riga anyi fa da ace ba'a yi bane sai a san wane dan a d'auki mataki sabida kar ayin to an riga da an aikata, ta rik'e a ranta koma waye karta fad'a kanta ta cuta" Umma ta fad'a tana goge idanunta. Yaya Ummi cikin tsawa tace, "Baza ki fad'i wanda yayi miki ba?."
"Shineee!" Ta fad'a da k'arfi tana fashewa da kuka.

"Shine wa?" Yaya Ummi ta tambaya da k'arfi tana kallonta rai a b'ace.? Rauda ta sake fashewa da kuka tace, "Shine!."
"Akace miki shine wa? Anas?."
Ta girgiza kai alamun a'a tace, "to shine wa?."
Umma ta fusata rai a b'ace tace, "bazata fad'a bata so take taga na mutu an fitar da gawata kinga shikenan ai ta huta."

Rauda ta runtse ido jin abinda Umma ta fad'a tana kuka sosai tace, "Asad.......!" Sai ta sake fashewa da kukan da yafi na d'azu fitar da sauti.[17/12, 10:42 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks @nanahaleema11
*072.*

? ? ? ?? Numfashi yake saukewa a hankali yana kallon fuskarta da ta jiqe da hawaye ko kad'an baya k'aunar ganin kukan ta gabad'aya yana tayar masa da hankali sosai shiyasa kawai ya zuba mata ido yana kallo cikin rashin sanin abinda zai ce mata wanda zata amince dashi nan gaba. Sarawa kansa yake yi ya runtse ido ya kalli wayar sa da yaji tana vibrating yaga sunan Hydar yana yawo a kai ya d'auke kansa ya dawo da kallon sa a gare ta a daidai wannan lokacin tace,

"ka daina bibiyata ka k'yale ni nayi rayuwata kamar yadda ka barni, kaje kaji da matar ka nima zanji da wanda zai aura kowa ya rik'e abinda ya mallaka bayan rabuwar mu, cewa matar kace ni da kake yi kai kasan ba gaskiya bane gwara ka daina dan k'arya ma haram ce" Sai kuma ta dafe kanta tace, "ka gama cucata, da wanne ido zan kalli Anas nace masa ina da cikin ka? Wanne kallo zai yi min?, fasiqa, mayaudariya ko kuma mazinaciya? Wanne zai d'auka a ciki?. Meyasa kayi min haka wanne laifi nayi maka ka yanke min wannan hukuncin mai d'aci?" Ta k'arasa fad'a murya na rawa ta zube a wajan tana kuka sosai.

Kunnuwan sa babu abinda suke jiyo masa sai kalmar wanda zata aura Anas yafi komai d'aga masa hankali da tafarfasa masa zuciya, dukkan kalaman data fad'a akan sa baiji zafi ba sai sunan Anas data ambata nan take yaji kamar ana tafasa jinin sa idanun sa suka canja kala haka fuskar sa tayi ja sosai cikin muryar sa da bata da hayaniya yace, "Kar na sake jin kin ambace shi matsayin wanda zaki aura."

A fusace ta mik'e tsaye tace, "Sai na ambata d'in ina ruwan ka dani! Duk cutar da kayi min har kana? bakin kallona kace kar na sake kiran Anas matsayin wanda zai aure ni? Ka manta wula?anci da kayi min a Egypt? Ka manta wanda kayi min a cikin gidan mu? Ka manta wanda kayi min a cikin gidan ka...?. Ka saka na aikata abinda ban tab'a yi ba, na sab'awa Allah da laifi mafi muni" ta fad'a muryar ta na rawa sosai.

Shi mamakin tsiwar ta yake yi bai d'auka tsiwarta ta kai haka ba duk da bata iya kallon idon sa tayi magana amma tana k'okarin fad'a masa duk abinda yazo bakin ta shi kuma ko kusa baya jin haushin ta dan yasan akan gaskiya take shima akan tasa gaskiyar yake.

"Matata ce ke, na haramta miki ambatar sunan wani a gaban idona ko a bayan idona." Yadda yayi maganar cikin bada umarni da izza a cikin ta sai da ta d'aga ido ta kalle shi suka had'a ido tayi saurin d'auke nata idon tace, "Ni ba matar ka bace, a da na zama matar ka ta y'an kwanaki qalilan yanzu ni ba matar ka bace, ina so na shaida maka wannan tsinanen cikin wallahi sai na zubar dashi hankalina zai kwanta, bazan tab'a amincewa a fasa aurena da yake gabatowa ba."

Cize bakin sa yayi ya lumshe ido ya lura bata jin magana ko kad'an ta kasa fahimtar dauriyar maganar yake amma shi kad'ai yasan irin ciwon da kansa yake yi masa, inda ya kasance mai saurin hannu da babu abinda zaj hana bai mare ta ba, idanun sa ya wara waje ya fiddo su dukka suka fito sun koma jajaye yace, "ki nutsu ki dawo hankalin ki ki san da wanda kike magana kar ki sake kuskuren yi min shouting."

Banza tayi masa ta kawar da kanta gefe tana kuka ta zauna a akan kujera tayi tagumi ta rasa wanne ma irin tunani zatayi, "Tun farko Baba ne ya amince da aure na dakai ba nice na amince ba, ta silar ka abubuwan da basu tab'a faruwa dani ba sun faru. Ta silar ka na zama bazawara ban tab'a hango kaina a wannan matakin ba sai da ka shigo rayuwata, ta silar ka Ummana tayi min Allah ya isa..." Sai kuka yaci k'arfin ta ta kifa kanta akan cinyar ta tana kuka sosai mai tab'a zuciya.

"Ya salam!" Ya furta a bayyane ya rasa meyasa take son yin kuka har haka, k'arasawa yayi inda take ya zauna a gabanta akan carpet yana kallon yace, "D'ago ki kalle ni." Kai take girgizawa tace, "Bana son ganin fuskar ka, na tsane ka bana sonka." Shiru yayi na wani lokaci yana jin d'aci da rad'ad'in kalmar bana sonka da tace ya sauke numfashi yayi tagumi kawai yana kallon ta.

Muryar sa a sanyaye yace, "Dan Allah ki daina kuka kina k'ara min ciwon kai, bana so naga kina kuka please ki bari." Ta d'ago ta kalle shi tace, "kasan da hakan kasa na sab'awa Allah?." Kawar da fuskar ta take so tayi yayi saurin rik'e fuskar ta ta kulle ido yace, "Dan Allah ki bud'e idon ki." Bata bud'e ba ya jijjiga mata fuska ta buWe idon a hankali suka had'a ido yace, "Kice bakya sona." Idonta ta saukar k'asa taji kamar an kulle mata bakin ta ta kasa magana ko kad'an kwarjinin sa ya mamaye duka ilahirin jikin ta nan take jikin ta yayi mugun sanyi.

Ganin hakan ya saka ya saki fuskar ta ya rik'e hannun ta yace, "Na koyi doguwar magana tunda aka shiga wannan situation d'in Rauda." Hannun ta kwace tace, "ka daina rik'e ni, ka fad'a min abinda zaka ce ina so na koma gida."
"Rauda ban sake ki ba."
"Ka sake ni." Ya sauke numfashi ya dafe kansa da dukkan hannayen sa zuwa wani lokaci.

Shiru sukayi dukkan su hannun sa na rik'e da kansa kusan mintina goma haka kafin yace, "A Cairo dana sake ki na mayar dake ko a'a?." Ido ta goge a fusace tace, "ka mayar dani. Amma ka kuma zuwa har gida ka sake ni kai da kanka kaga takardar da ka rubuta meyasa kake son yin wasa da hankalin mu ne dan kaga kai wani abu ne a duniya?."
Kamar zaiyi kuka yace, "Rauda bani bane, ki yarda dani banzo gidan ku ba. Aliyu ne!" Ya fad'a muryar sa raunane yana kallon ta.

Damm gaban ta ya buga jin abinda yace ta kalle shi da sauri sai kuma ta d'auke kai ta tsaya cak kwakwalwar ta tana tuno mata abinda ya faru a ranar da yazo da kamannin sa da maganar sa da komai nasa na Asad ne bana Aliyu ba.

Murmushi tana girgiza kai tace, "Kai ka nuna min zanen hannun ka kace min dashi kad'ai ake banbance ku da Aliyu koshi bai san da wannan zanen ba a ranar da kazo naga wannan zanen a hannun ka. Kana so kayi wasa da hankalina ne kawai amma ta ya akayi Aliyu yasan da abubuwan da suka faru a Cairo?. Ya akayi yasan ka sake ni har yazo ya sake sakina?, ya akayi yasan saki d'aya kayi min yazk ya k'arashe biyun?. Ya akayi ya samu rubutun ka?, Ya akayi maganar Aliyu ta koma maganar ka sak har yadda kake magana shima yayi?, Ya akayi Aliyu yasan ma akwai iddar ka a kaina har yazo ya sake sakina?. Yace min Muwaddaty ya akayi yasan sunan nan? Baka tab'a fad'a a gaban sa ba balle ace ji yayi ya akayi ya san dashi?. Indai har ba kai bane ya akayi yasan da wad'annan abubuwan?" Ta fad'a tana kallon sa yayi shiru shi kuma baya kallon ta.

Gabad'aya ta daure shi da jijiyoyin jikin sa tabbas duk abinda ta fad'a gaskiya ne shi kansa bashi da amsoshin tambayar tata hakan ya saka shi yayi shiru kawai baice komai ba yana sauraron abinda take cewa har ta kai k'arshe. Tayi murmushi tace, "Baza ka tab'a wasa da hankalina ba, a baya duk da abinda ya faru ina ganin mutuncin ka sosai kasancewar kaine shugaba a garin nan ina girmama hakan amma a yanzu ka zubar da wannan mutuncin in za'a ce min ga wuk'a na kashe wanda bana so tabbas kai zan fara kashewa. Ka daina k'ok'arin yawo da hankalina ko kace zakayi min wayo in iyayena sun amince dakai kai kasan ni bazan tab'a amincewa da kai ba, iya zaman da mukayi na fahimce ka daidai iyawata."

Kallon ta yayi akayi sa'a tana kallon sa murya a raunane yace, "Bana k'arya Rauda a kanki bazan fara ba, bazan miki k'arya dan cikar burina ba bayan nasan haramcin da yake cikin abinda nake son aikatawa..." yayi shiru na wani lokacin kafin ya kuma cewa, "A kan gaskiyar ki kike banga laifin ki ba nima a kan tawa nake Muwadda, amma ina so ki sani bazan ce akwai aurena a kanki sabida wata manufa tawa; in kin fahimta dakyau cikin halin Asad babu son kai babu kuma k'arya...." ya sake yin shiru ya dafe kansa kana ya kuma cewa, "A matsayin da nake dashi bazan ce bazan yi k'arya ba amma tunda har na rantse yana dakyau ki amince. Tun bayan rabuwar mu ban sake ganin kia zahiri ba sai da rabon abinda yake cikin ki yazo bance lallai sai kin amince ba ki zauna akan ra'ayin ki shima daidai ne."

Ya mik'e tsaye yana kallon wani wajan daban kana yace, "Amma ki sani bazan amince da sauraren wani namiji daban ba, bazan amince da maganar auren ki da wani ba, in kuma hakan ta cigaba da faruwa bake zan yiwa hukunci ba shi zan yiwa sai ya gwammace bai sanki ba.Maganar abortion da kike yi kiyi duk abinda zuciyar ki ta baki umarni daidai ne."

Mik'ewa tayi zata gifta shi ta wuce ya jawota jikin sa sosai yana kallon fuskar ta itama haka,babu wanda yayi magana a cikin su kallon ta yake tana kallon sa har minti d'aya suna a haka kafin ya motsa bakin sa zaiyi magana ta riga shi tace, "Ya akayi Aliyu yasan da irin wannan rik'on da kai kad'ai kake min irin sa? Ko camera ya saka can Cairo d'in yadda zai dinga ganin duk abinda yake faruwa?. Ina jin dai camera ya saka shiyasa yasan da kayi min alqawarin baza ka rabu dani ba."

Runtse ido yayi tashin hankalin sa ya ninka na baya ya matse ta sosai har sai dai kashin k'ugun ta ya amsa sabida matsar da yayi mata bata wsa bace har lokacin kuma bai bud'e ido ba fuskar sa a yamutse tana tattaro ja tana had'ewa waje d'aya.

Rauda zafin rok'on take ji sosai ta kulle idon ta ta buWe suka had'a ido yace, "Aliyu har rik'e ki yayi? Meyasa kika amimce hakan ta kasance? Ina hankalin da na sanki dashi ina yaje har kika bari hakan ta faru?, Aliyu fa ya rik'e ki like yadda muke yanzu....Hasbunallahu wani'imal wakil!" ya furta yana sakin ta sai ya koma da baya ya zauna a kan kujera ya dafe kansa da duka hannayen sa yana jin d'aci na mamaye masa kan harshen sa sabida tsananin kishi.

? ? ? ? Wani irin abu taji a jikin ta ganin yadda ya koma lokaci d'aya ta bishi da kallo yana zaune a inda ya zauna har lokacin hannun sa yana dafe da kansa sai taji zuciyar ta na bugawa da sauri-sauri ba tare da tasan dalilin hakan ba.

D'ago kai yayi yana kallon ta suka had'a ido sai ya cize bakin sa ya had'd'iye abu mai d'aci ya sake kulle ido ya bud'e cikin rauniyace, "Za'a kai ki gida, kije" yana fad'a ya tashi ya ya shiga ciki ta bishi da kallo har ya b'ace bai sake kallon inda take ba. Duk sai taji jikin ta kuma yayi sanyi sosai ta fita itama bata kuma kallon sa ba tana fitowa taga an bud'e mata mota ta shiga driver yaja basu tsaya a ko ina ba sai a k'ofar gidan su.

Lokacin da ta shiga bata tarar da kowa a falo ba ta shiga falon Umma nan ta ga Umman a zaune ita da Khairi ta k'araso da sallama tana kallon Umma, a hankali ta taka inda Umma take kafin ta k'arasa ta fara kuka ga kanta da yake ciwo sosai, tsugunawa gaban Umma take niyar yi Umma tace, "Ummulkhairi rik'e ta ku shiga ciki kar ta fad'i." Ba musu ta tashi ta rik'e ta suka shiga ciki ta zaunar da ita a kan gado ganin yadda take rik'e kanta sosai sai Khairi ta d'auko mata maganin ta da ruwa tace, "Kisha Anty ko zai daina miki ciwo."

Kai kawai ta d'aga mata Khairi ta fita Rauda ta ture maganin ta kwanta tana sauke numfashi koya ta kulle ido shi take ganowa da kalaman sa da suke mata yawo a cikin kanta har lokacin ta kasa mantawa. Umma ce ta shigo d'akin ta kalle ta bata ce komai ba ta fita jim kad'an sai gata ta dawo da ruwan tea mai kauri ta dawo kuaa da ita tace, "Tashi kisha shayi."

Jin maganar Umma a tausashe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login