Showing 33001 words to 36000 words out of 216282 words

Chapter 12 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

mataki." Mama taja tsaki ta furzar da iska ta tab'a wuyan ta tace, "Zazzab'i ne a jikina Sadiya." Mum tace, "dole kiyi Zazzab'i fulani, bara na kira Suhaima ta kawo miki magani" ta fad'a tana tashi ta shiga ciki wajan Suhaima Mama ta sauke ajiyar zuciya tana jin zuciyar ta nayi mata zafi da rad'ad'i.

*&&&*

"Ki taka slowly" ya furta mata daidai kunnen ta yana rik'e da ita hannun sa na zagaye akan shafaffen cikin ta domin ya karb'i sandar yace ta taka a haka. Gabad'aya ta kasa sakewa sabida hannun sa da yake zagaye da ita ga khamshin turaren sa da yake sanya mata kasala kanta na daf da kafad'ar sa hannun sa d'aya yana rik'e da hannun ta guda d'aya suna takawa a cikin asibitin a hankalin.

Babu ruwan wani dasu tafiya suke tana takawa a hankali yana zamar mata garkuwa zuciyar sa na harbawa da sauri haka tata zuciyar ma. Dr muhibba suka gani a gaban su tana kallon su har suka zo daf da ita tace, "Sannu Sister ya k'afar?." Haushin ta Rauda take ji haka kawai hakan ya saka tace, "Da sauk'i" ta amsa a tak'aice tana kallon wani wajan daban. Gaban Asad ta tsaya tana kallon sa tace, "Handsome baka ce min komai ba, wallahi da gaske nake ina sonka. Sister baki fad'a masa sak'ona bane ba?."

Gaban Rauda ya fad'i matuk'a bata san ta matsa hannun sa da k'arfi ba ta dai ga ya kalle ta amma bata san me ta aikata ba idanun ta a runtse suke sai ya d'an saki fuska kad'an baiyi magana ba ya taka da niyar barin wajan. "Handsome pls" ta sake tsawaya a gaban sa tana kallon sa kamar zatayi masa kuka.
Kallon ta yayi na sacan d'aya, biyu, uku, kafin ya d'auke idon sa ya rab'a ta gefen ta ya wuce ta sake bin shi da kallo tana shak'ar khamshin turaren jikin sa.

Rauda tayi kicin-kicin da fuska bata san taqamemen abinda yake damun ta ba har suka gama zagayen suka koma d'aki ta zauna a akan kujera tana kallon wani wajan daban ba tare da ta kalle shi ba. Shima bai damu ba dan bai d'auka zata ji haushi ba ya zauna na wani lokaci kafin ya tashi ya fita tabi bayan sa da kallo tana jin wani iri a ranta.

Bayan kwana biyu.

K'afar Rauda tayi kyau sosai har tana takawa babu sanda ba kuma tare da an taimaka mata ba tana tafiya sai ka lura zaka ga tana d'ingishi. Tayi kyau tayi haske fatar ta ta murje tayi kib"a amma ba sosai ba kana dai ganin ta kasan ta samu canji rayuwa sosai musamman a fatar ta da take kyalli tamkar chocolate.

An basu sallama da magani a ranar sai zuwa da zata dinga yi ana duba k'afar sun fito da daddare zasu shiga mota zuwa hotel d'in da suka sauka babu mai magana a cikin su kamar koda yaushe shi yayi shiru itama haka. Yana bud'e motar tana tsaye tana kallon wani wajan daban Muhibba ta k'araso da sauri inda suke tsaye ta kalli Rauda tace, "Sis zaki tafi shine ba sallama?." Rauda ta kalle ta tace, "Ban ganki bane." Muhibba tace, "Saka min number ki ta Nigeria mu dinga gaisa." Rauda tayi jim tana kallon ta domin bata san sabuwar number da ya sake mata ba ita dai kawai tana kiran y'an gidan su amma bata tab'a dubawa ba.

Muhibba ta saci kallon Asad da yake zaune a mota tace, "ki saka min ta yayan ki ma." Rauda ta kalle ta tace, "Wayata ta fad'i ban san inda na ajjiye ta ba." Muhibba tace, "Kuma baki haddace ba?." Rauda ta d'aga kai alamun eh Muhibba ta kalli Asad ta matso kusa da inda yake zaune tace, "Handsome zaka tafi ko goodbye baka ce min ba." Rauda ta zaga ta shiga gaban motar suna har loakcin bataji ya kula Muhibba ba, Rauda na rufe k'ofar motar shima yaja tasa zai kulle Muhibba ta rik'e tace, "Ka bani koda number kane please."

Asad ya d'aga kai ya kalle ta yaja siririn tsaki yaja murfin motar ta saki ya kulle ta kalle shi tana murmushi har suka ja motar bata daina kallon su ba. Suna barin wajan Rauda tayi tsaki tace, "Bata da hankali gabad'aya yarinyar nan ta cika nacin tsiya, haushin ta nake ji" zancen zuci ya fito fili ba tare da ta san hakan ba.

Kallon ta yayi kafin ya d'auke kansa ya cigaba da tafiya. Hotel d'in da suke dai nan suka koma d'akin yana nan tas dashi an gyara tana takawa a hankali ta shiga wanda ta sauka a ciki tana kallon sa tsaf dashi sai khamshi yake yi. Bata jima da zama ba ya shigo da ledar maganin nata ya ajjiye a gefen ta kanzil baice mata ba ya fita ta bishi da kallo kafin tace, "Ina ganin mulkin mallaka ni Rauda, magana ma ta dinga gagarar mutum kuma a haka ace wai yana tare da wacce yake so ne?, mtswwww" ta fad'a tana jin haushin hakan a ranta dan ita sam bata ga wata soyayya a tare dashi ba.

Tana nan zaune ya dawo ya canja kaya zuwa jallabiya blue ya saka hular sanyi blue itama har kunnen sa ya rufe yayi kyau sosai khamshi na tashi a jikin sa ya kalle ta itama shi take kallo yace, "Zaki iya fita?." Kamar tace a'a amma sai ta amsa masa da eh baice komai ba ya juya ya fita. Zaman ta tayi domin baice mata ta taso ba bata d'auka shirun yana nufin ta tawo ba kusan mintina goma tana zaune tana jiran yace ta tawo su tafi.

Gajiya tayi da jira ta fito falon bata ganshi ba kamar b'arauniya take takawa zuwa d'akin da ya sauka ta tura k'ofar ta shiga tana k'arewa d'akin kallo, kamar nata tsaf shima haka yake sai littafai da suke a kan gado na addini dana zamani. Burge ta d'akin yayi sosai ta taka tana k'are masa kallo a hankali domin ya had'u ga girma ga tagar d'akin nasa har tafi wanda take ciki kyau motoci kawai ake gani suna wucewa ta glass d'in.

Har zata juya ta fita kan mudubin ta hango wani katin magani kamar nata da ya b'ata ta dawo da baya ta k'arasa inda yake ta d'auka ta bud'e shi taga katin tane wanda ta yar ranar da suka fara had'uwa dashi ta dawo da wajan mai magani, juya katin take yi kafin tace, "Me ya kawo shi hannun sa har ya tawo dashi k'asar nan?" Ta tambayi kanta ba tare da tasan amsar ba tana sake kallon katin ga sunan tana nan rad'au a jiki.

"Maganin da aka zage ni aka wulak'anta ni a kansa, aka zage ni aka zagi iyayena dan kawai muna karb'ar bashi a kansa. Nifa kome ya faru dani a rayuwa silar gidan su ce" ta fad'a tana ajiiye katin maganin abinda ya faru yana dawo mata. 'Amma kuma ai an siya miki maganin har kika tawo baki daina shan sa ba, kinga kenan an wanke miki ciwon zagin da akayi miki' zuciyar ta ta bata amsa da sauri ta wara idanun ta a bayyane tace, "Kenan hakan yana nufin shine ya siyi maganin...? Anas yace bashi bane daman kuma shi muka d'auka ya siya yace bai siya ba kenan shine....?."

Sai kuma tayi shiru tace, "ta ya zai siya kin magani daga ganina a hanya?."
'Kin manta abinda Khalil ya fad'a a lokacin? Hakan zai iya sakawa ya siya miki magani tunda daman yasan k'anin sane ya buge ki' zuciyar ta ta kuma bata amsa. Rauda ta fito daga d'akin har lokacin tunani take ta zauna a falo tace, "Kenan shine ya siya min magani, shine ya bawa Baba na keke napep, shine ya kawo mana kayan abinci kud'i kuma Anas ne ya aiko dasu. Amma meyasa d'an aike d'aya ne duka ya kawo? Ya akayi yasan kuma Baba na son napep tunda da Anas sukayi magana?" Ta fad'a cikin d'aure kai tana so ta gano bakin zaren.

Bud'e k'ofar akayi aka shigo ta ganshi ya shigo da ledoji k'anana da alama har yaje ma inda yace zata je d'in ya dawo ta bishi da kallo har ya ajjiye ya zauna tace, "shine kaje ka dawo bayan nace zanje." Kallon ta yayi jin tama raina masa hankali wato zaman jiran ta zaiyi har sai sanda ta fito sannan zai tafi.

"Baki son zuwa" ya bata amsa a tak'aice yana bud'e leda guda d'aya ya fito da ice cream a roba sai gumi yake sabida sanyi ya bud'e ya fara sha kafin ya tura mata d'aya ledar gaban ta sai tace, "Ina so naje mana na fito ban ganka ba kuma baka ce min nazo muje ba."
"Oh sai nace kizo?" Ya sake fad'a ba tare da ya kalle ta ba tace, "Eh mana, ai da sai kace min tawo mu tafi sai kawai kayi tafiyar ka bayan nace zanje."

Kai ya girgiza kawai baice komai ba ta bud'e ice cream d'in ta fara sha kamar yadda taga yana sha itama tayi shiru kamar yadda yayi shiru. Knocking d'in k'ofar akayi kafin ya tashi karanbanin Rauda ta riga shi mik'ewa dan tana so ta buWe k'ofar yadda take bada sauti in an bud'e yana burge ta sosai tana bud'ewa suka had'a ido da Dr Khalifa.

"Lallai patient k'afa yayi kyau" ya fad'a yana shigo yana kallon ta. Murmushi tayi domin sun saba dashi sosai tace, "Alhamdulillah."
"Haka ake so ai" ya fad'a yana kawo hannu yaja kumatun ta yana murmushi itama haka. D'ago idon da zatayi suka had'a ido da Asad ya tsaya cak da shan ice cream d'in yana kallon su kafin ya d'auke kansa ya mayar kan TV.

K'arasawa Khalifa yayi ya zauna kusa dashi yana kallon sa yace, "Prince ga ragowar maganin nata da ba'a karb'a ba d'azu, Sister zo na nuna miki duration d'in kar kiyi mistake." Ba musu Rauda tazo ta zauna ya nuna mata yadda zata sha da yadda zata shafa da ya gama ya bata duka tace, "na gode." Murmushi yayi yace, "haba chocolate colour you deserve anythings from me."

Murmushi tayi bata ce komai ba Asad dai bai tanka musu ba Khalifa ya mik'e yace, "bye deaf dan nasan ba kula ni zakayi ba. Sister Allah ya k'ara lafiya" ya fad'a yana fita ta amsa da amin yaja k'ofar ta zauna ta cigaba da shan ice cream d'inta.

Kallon da taga yanayi mata ne ya saka ta kasa sakewa da ta d'ago sai taga sun had'a ido in ta sauke idon ta ta sake d'agowa sai taga dai kallon ta yake sai ta rud'e ta fara juya cokalin ice cream d'in a cikin robar ba tare da tana sha ba ji take kamar ta tashi ta zura a guje sabida yadda take jin idanun sa a jikin ta.
"Raudaaaa!" Ya kira sunan ta can k'asan makogwaron sa har lokacin idanun sa yana kanta.

D'ago ido tayi ta kalle shi kana tace, "Na'am." Ya bud'e baki zaiyi mata magana sai kuma yayi shiru taga ya runtse idanun sa yana cize baki ya fara nuna ta da yatsa yana karkad'
a shi kamar mai magana amma kuma ba magana yake mata ba. Duk sai taji tsoro ya mamaye mata zuciya ganin yanayin sa gabad'aya ya canja lokaci guda fuskar sa ta kuma d'aurewa fiye da d'azu.

Fusata taga yayi yayi cilli da robar ice cream d'in ta daki bango ta b'ata wajan gabad'aya ta firgita ta kama jikin ta tana kallon sa sai taga yana had'd'iye saliva dak'yar har lokacin cizon bakin sa yake yi yana kuma kallon ta alamun magana yake so yayi baya son yi d'in ne kawai.

Dak'yar ya fizgo maganar daga bakin sa yace, "He touched you a gaban idanuna...." Sai kuma yaja numfashi mai tsaho yace, "why.....!." Jin abinda yace sai ta gano inda maganar ta nufa kenan kishi yake dan Khalifa yaja mata kumatu wanda itama bata san hakan zai faru ba da zata dakatar da faruwar sa, zatayi magana ya d'aga mata hannu yana murza yatsun hannun sa amma bai ce komai ba ya mik'e ya shiga d'aki.

Rauda sai ta kasa nutsuwa hankalin ta taji ya tashi ganin yadda yake nuna ta da yatsa fuskar sa duk ta canja hakan ya tabbatar mata da ba k'aramin abu yaji a ransa ba tunda gashi ya bayyana har ya kasa b'oyewa kuma laifin tane. Rauda tace, "to yanzu ya zanyi? Ni ban san hakan zata faru ba da ban bud'e k'ofar ba, sannan ban san zaiji haushi haka ba."

'Kije ki bashi hak'uri tunda ke kika yi masa laifi kuma matar sace ke, zunubi kika aikata babba barin wani namijin da ba maharramin ki ba ya tab'a ki kuma a gaban mijin ki. Kije ki nema ya yafe miki fushin sa gare ki ma illa ne' abinda zuciyarta ta fad'a mata kenan ta kuma gamsu da hakan ta mik'e da niyar zuwa sai kuma tace, "to naje nace masa me?" Dafe kai tayi cikin rashin sanin mafita. Nufar d'akin tayi bayan ta samo dabarar da zatayi amfani da ita zuciyar ta na bugawa kamar zata fito daga k'irjin ta.
[17/12, 10:39 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*037.*

? ? ? ? A hankali take tafiya har taje k'ofar d'akin tana tunanin ta yadda zata shiga in ma ta shiga tace masa me..?. A haka tayi bismillah ta tura k'ofar d'akin da sallama a bakin ta ta hango shi a tsaye a jikin taga yana kallon motocin da suke wucewa yana sauke ajiyar zuciya da alama har lokacin bai wuce ba.

Takowa take a nutse har tazo kusa dashi ta kalle shi shi kuma ba ita yake kallo ba tagar yake kalla tace, "Kayi hak'uri bazan sake ba, ban san zai tab'a ni ba da bazan bud'e k'ofar bama." Kamar jira yake tayi maganar ya sake fusata cikin maganar sa da bata fita sosai yace, "Ohh bud'e k'ofar da kikayi u think kinyi daidai?. I think tun a hospital nace miki bana son wannan shirmen da kuke yi dashi ko?." Taji tsoro sosai ranar farko da taji doguwar magana a bakin sa har haka kuma tana fita da k'arfi ba kamar yadda ya saba magana ba.

? ? ?? "I'm sorry" ta furta kamar zatayi kuka tana kallon sa ya d'auke ido daga kanta yana kallon tagar iska na kad'a shi yana ji kamar ya dira mota ta buge shi kowa ma ya huta. Baya son yaga wani ya rab'i abinda yake so ko kad'an balle ace ma mace macen ma matar sa har wani banza zai rik'e mata kumatu a gaban sa kuma matar bata hana faruwar hakan ba balle ta d'auki mataki. Ganin yayi shiru amma da alama bai wuce ba Rauda tace, "bai san ina da aure ba beside bai san ni matar ka bace, d'auka yake ni Sister d'in kace shiyasa."

"Ke kuma u can't tell him, just because u feel ashamed to tell him that I'm your husband right?" ya fad'a ba tare da ya kalle ta ba har lokacin kallon tagar yake yi. Rauda tace, "kaine baka bada damar hakan ba sabida baka nuna musu ni matar ka bace kace ni Sister kace, waccan likitan ma a gaban ka take cemin sistern kan but baka tab'a ce mata I'm your wife ba, why ni zan fad'a musu?. In na fad'a karyata ni ma zasuyi but ban dace da zama hakan ba shiyasa kaima baka nuna musu ni ba sabida kar kaji kunya."

? ? Banza yayi mata bai ko kalle ta ba balle ya amsa tagar sa yake kallo kawai ganin hakan ya saka tace, "I'm stand here to tell u akwai mission da ya saka ka aure ni amma badan kana sona ba kamar yadda kace, ni nasan akwai abinda kake nufi dani amma bawai kana sona bane. Banga wani sigh da zai tabbatar min da kana sona ba, kayi amfani da power da kake dashi ka d'auko ni daga gidan mu ka ajjiye ni a nan kana k'inyi min magana. For how kake tunanin zan d'auka kana kishin wani dan ya tab'a ni for god sake?" ta fad'a with full confidence babu tsoro a tare da ita duk da gaban ta yana fad'uwa.

Kallon ta yayi ya cize bakin sa ya girgiza kai kafin ya nuna msta k'ofa yace, "Out!." Murmushi Rauda tayi tace, "Zan fita, but stop pretending like u feel jealousy about me, I know your target ka kawo ni ne kawai dan kayi humiliating d'ina not love" tana fad'a ta fita ta k'yale shi kamar baiji me tace ba sai bayan yaji ta kulle k'ofa zuciyar take angiza shi akan ya fad'a k'asa kawai mota ta take shi ya mutu tunda har zata iya tsayawa a gaban sa ta fad'a masa haka duk da tarin son da yake mata.

Zantuttukan ta ne suke tayi masa amsa kuwa a kunnen sa ya toshe kunnen sa ya bar jikin windown ya dawo ya zauna a gefen gado idanun sa a kulle. Shi kansa yana jin haushin rashin maganar da bayayi mta amma ya zaiyi halittar sace a haka baya iya magana kamar yadda mutane sukeyi. Yana sonta ya sani yana kuma son kasancewa da ita a ko yaushe amma baya iya furta mata hakan ko yaushe bakin sa nauyi yake yi ga kuma jinin sarauta da yake yawo a jikin sa abun sai ya zama biyu ga halitta ga kuma gadon sarauta komai sai ya k'ara tunzura.

'Ba mayafi taje ta bud'ewa wani k'ofa, tayi masa dariya har yana rik'e kumatun ta maimakon ta baka hak'uri da kalamai masu dad'i matsayin ta na matar ka sai taso yi maka rashin kunya? Tama raina maka hankali dan kawai taga kana sonta ne shiyasa ta furta abinda ta fad'a amma badan so ba da ita in akace tayi baza ta iya ba" zuciyar sa ta fad'a masa ya koma da baya ya kwanta yana sauke numfashi haushin ta dana Khalifa yana sake ninkuwa a zuciyar sa musamman ma ita.

? ? ?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login