Showing 159001 words to 162000 words out of 216282 words

Chapter 54 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

ki tana cikin rud'ani na sani amma haka Allah yaso jarabawa ce Allah ya baki ikon cinyewa Rauda." Kuka take a cinyar Umma sosai sai da tayi mai isar ta sannan ta tashi Umma ta lalaba ta ta kwanta a akan gadon badan tana jin bacci ba.

*&&&*

"Mum me za'a yi da akace ana kiran meeting? Nidai gaskiya bazan je ba sai daku kuje keda daddy" Jidda ta fad'a a rud'e tana kallon Mum. Mum tace, "Dole kuwa kije domin akan ki maganar take ba'a kaina ba, mahaifin ki baya nan dole nida ke d'in zamu je."

Jidda ta girgiza kai tace, "Nidai bazan je ba Mum, bazan iya zuwa ba tsoro nake ji kar muje an gano komai."
"Nima kaina tsoron nake ji Jidda amma ya zama dole muje in bamu je ba shima wata matsalar ce, zuciyata bugawa take yi sosai ban san me zan tarar a goben ba."

Jidda ta fashe da kuka tace, "Nidai Mum bazan je ba zan iya mutuwa in akace sai naje, bazani ba." Mum binta take da kallo ganin yadda ta tsorata sosai kamar ita tayi wani babban laifin tace, "Jidda ni ya kamata naji tsoro bake ba, amma sai naga kin fini ma jin tsoron. Wannan yanayin naki yana sakawa na sake jin tsoro domin ban san me kika aikata ba."

Jidda kawai ta tashi ta fita dan babu wanda zai saka ta tafiya gobe bazata je asirin ta ya tonu ta shiga uku ba gwara koma meye zai faru ya faru a bayan idanun ta ba a gaban idanun ta.

*&&*

? ? ? ? "Dole a san abinda za'ayi bana son Abba ya kai gobe da ransa ya zama dole na tabbatar ya koma rashin lafiya ko kuma ya mutu gabad'aya" ya fad'a yana hakki cikin tashin hankalin daya bayyana a tare dashi zuciyar sa har bugawa take yi sabida rud'ani da tashin hankalin zuciyar sa. Kamar an tsikare shi sai ta mik'e ya lek'a taga yaga dare ya fara mutanen gidan suna ta raguwa ya kalli d'akin Hydar ya tabbatar yana ciki ya sauke ajiyar zuciya yana sake girgiza kansa.

Komawa yayi ya zauna yana girgiza k'afa tare da cize baki yana ji kamar ya jawo dare yayi sosai yaje ya aiwatar da abinda yake so ya aiwatar. Yana nan zaune k'arfe d'aya na dare ta buga ya zabura ya mik'e ya fita daga falon kai tsaye b'angaren mai martaba ya nufa ba tsoro a tare dashi balle fargaba.

Masu tsaron k'ofar duk sunyi bacci ya shiga falon ya jishi shiru an kashe komai na falon baka ganni koda hannun ka sabida duhu, da yake ya haddace komai hatta hanyar da take falon ya haddace ta a haka ta k'arasa har k'ofar d'akin mahaifin nasa.

Tunanin bud'e k'ofar yake dan yasan tabbas in ya bud'e zai iya ji gashi shi kuma baya son b'ata lokaci. "Sai me ma dan ya ganni? Mtsww" ya fad'a a bayyane yana jan tsaki ya tura k'ofar d'akin cikin dakewar zuciya da son idda nufin sa akan mahaifin nasa kai tsaye.

Hasken a.c kawai ake gani a d'akin ya nufi kan gadon kai tsaye duk da baya gani sosai amma ya tabbatar da yana kwance a kan gadon a wannan lokacjn. Zagayawa yayi ta gefe ya d'auki pillow da yake gefe a ajjiye ya nufi inda yake hango tudun Abba daidai inda yasa kansa yaje ya danna pillow a kai da niyar toshe masa numfashi da k'arfin gaske.

Ba zato babu tsammani yaga haske ya gauraye d'akin ya firgita matuk'a ya d'ago kai a firgice yana kallon inda switch d'in fitilun yake don ganin wanda ya shigo a lokacin da bai shiryawa hakan ba.
[17/12, 10:42 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*077*

? ? ? ? ?? A tsaye yaga mai martaba hannun sa hard'e a k'irji yana kallon sa fuskar sa da murmushi da alama baiyi mamaki ko al'ajabi da ganin abinda yake shirin faruwa ba yasan daman hakan zata kasance, bai san pillow hannun sa ya sub'uce ba yayi baya kamar zai fad'i idanun sa kyam akan na mahaifin sa tashin hankalin da ya bayyana a tare dashi ba d'an kad'an bane ba.

Murmushi mai martaba yayi ganin yadda ya firgice sai ya tako a hankali yazo inda yake yace, "Gani gaka zaka iya kashe ni in kana so." Baya yayi ya nisanta kansa daga kusa dashi jikin sa yayi bala'in yin sanyi duk ya dabarbace alamun rashin gaskiya amma babu alamun nadama ko kunya a tare dashi.
Murmushi yayi ya sake cewa, "Kana tunanin ban san waye kai ba? Ko ina tunanin duk abinda yake faruwa a gidan nan ban sani bane ba?. In hakan kake tunani ka d'auka kayi babban kuskure duk abinda kuke aikatawa a tafin hannuna yake kuma k'arshen ku yazo ka tabbatar da komai ya kusa zuwar muku k'arshe."

Zuciya ce take d'aukar sa akan kawai ya shak'e mai martaba ya huta in ba haka ba gobe zata zamar masa barazana ga rayuwar sa gabad'aya in ba kashe shi yayi ba hankalin sa bazai tab'a kwanciya ba, hannu biyu ya d'ago da niyar kaisu wuyan mai martaba sai kuma suka had'a ido ya fasa mai martaba ya sake yin murmushi yace, "Kashe ni mana ya zaka fasa?."

"Ba kai kad'ai kake son kashe ni ba a yau kuna da yawa wanda basa so gobe tayi, baku san me zan tattauna a? goben ba amma dukkan ku hankalin ku ya tashi kun manta da karin maganar da bahaushe yake cewa rana dubu ta b'arawo rana d'aya tak ta mai kaya. Dubun ku ta cika gobe lokacin girbar abinda aka shuka ne."

Kamar wanda aka yiwa allura ya zabura ya kama wuyan mai martaba da k'arfin gaske ya matse yana fad'in, "Bazan iya bari ka kai gobe ba koda nima bazan kai ba, gwara na kashe ka in yaso nima a kashe ni" ya fad'a yana sake matse masa wuya da k'arfi.

Shigowa d'akin akayi aka kwace mai martaba daga hannun sa Uncle ya tsinka masa mari ya sake marin sa ya bishi da kallon b'acin rai yana fad'in, "Ban tab'a d'auka rashin hankalin naka har ya kai haka ba sai yanzu, duk abinda ka aikata baya bai ishe ka ba sai ka had'a da kashe mahaifin ka."

Mai martaba ya zauna gefen gado yana tari kad'an yace, "Mubarak kaje dashi a killace shi a wani wajan bana so ya gudu daga gidan nan, kuje a tabbatar an saka masa matakan tsoro yadda ya kamata." Da k'arfi Uncle ya jashi yak'i tafiya ganin hakan Galadima shima jashi suka fita dashi dak'yar.

Mai martaba ya bisu da kallo bayan sun fita ya shafa wuyan sa hankalin sa ya tashi sosai zuciyar sa tayi rauni dan bai d'auka duk zafin kansa zai iya k'okarin kashe shi ba idon sa yana cikin nasa ba, ya d'auka zai tsaya yi a bayan idanun sa amma bai d'auka yana kallon sa shima yana kallon sa zai iya kashe shi ba. Ya sauke numfashi a bayyane yace, "Me ake da irin wannan haihuwar?."

? ? ? Ba jimawa Uncle ya dawo ya k'araso wajan Mai martaba yana fad'in, "Ranka ya dad'e babu abinda ya faru dai ko?." Mai martaba yace, "Babu abinda ya faru, ina kuka ajjiye shi?."
"Yana d'akin cikin b'angaren nan yanzu haka Galadima yana wajan sa an masa d'auri mai kyau. Mai martaba zufa yake a kunna a.c" ya fad'a yana d'aukar remote zai danna yayi saurin dakatar dashi ta hanyar fad'in,

"Kar ka kunna, yanzun nan na kashe ta akwai wanda suka zuba guba a cikin ta da zarar na shak'a zan mutu kamar yadda akayi a wancan lokacin." Uncle yace, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, mutane me suke nema a duniya suka mayar da kashe musulmi ba komai ba?. Jinin ka shine yake son ganin bayan ka a koda yaushe meyasa duniya ta koma mai amana kad'an ne?." Mai martaba yace, "Dukkan su basa so na kai gobe dalilin da ya saka hakan kenan, suna nan da yawa domin ba mutum d'aya bane dukka kuma na san su d'aya bayan d'aya."

Kai ya girgiza yace, "Ai gwara Allah ya tona asirin su kodan suji kunyar duniya su kuma jira jin ta lahira." Mai martaba yace, "Kaje ka huta Allah ya kaimu goben."
"Bazan iya tafiya na bar mai martaba a a wannan yanayin ba."
"Kar ka damu jeka" ba musu Uncle ya fita ya kulle masa k'ofa zuciyar sa babu dad'i.

Washe gari.

? ? ? ? ? "Rauda wai meye haka ne? Amma kin san dai na fad'a miki mai martaba shine yace yana neman mu ko?" Umma ta fad'a tana kallon Rauda da take a zaune a gefe. Rauda ta kalli Umma da jajayen idanun ta kamar ko yaushe tace, "To Umma me zanje nayi a can?."

"Tunda ya neme ki me zai hana baza muje ba kika san abinda ya faru?." Rauda tayi shiru tace, "Umma gabad'ayan iyalan gidan su bana son ganin su duka, sun yi min mugun tabo a rayuwata bana son sake had'a ido da ko wanne su."

Umma ta kalle ta tace, "Na sani Rauda duk abinda ya faru ai babu wanda ban sani ba, tun shigowar iyalan gidan su rayuwar ki komai yake lalacewa amma Allah ne ya rubuta hakan kuma shine zai gyara komai ai." Sunkuyawa tayi tana kuka Umma taga shatin dukan da tasha a hannu Baba a kwance a bayan ta sai jikinta yayi sanyi ta sauke numfashi tana kallon ta.

Sai kuma ta d'ago daga kukan ta kalli Umma tace, "Umma Rahma ta takura min akan naje gidan ta har yanzu Allah bai bani iko ba, bana son zuwa sai naga kamar zuwana gidan ta bazai zama alkhairi ba" ta fad'a muryar ta na rawa sosai. Umma ta zauna a gefen ta ta dafa ta tace, "Me zai hana shi zama Alkhairi Rauda? Daman fa ba kece matar Anas ba duk wannan fad'i tashin da yayi a kanki Rahma ce matar sa bake ba, Allah bai bayyana mana hakan bane sai yanzu da lokacin bayyanar tayi. Ki duba k'addarar farko da ta raba ku sannan ki duba wannan wacce ta sake raba ku in kikayi tunanin nutsuwa zaki tabbatar da daman ba shine mijin ki ba kuma kin sa baka tab'a auren mijin da ba naka ba kamar yadda baza ki shiga kabarin da ba naki ba, shiyasa hausawa suke cewa matar mutum kabarin sa."

Kai ta d'aga ta goge siraran hawayen ta tace, "Haka ne Umma. Amma ina jin kunyar had'a ido dashi ita kuma kar taga kamar da biyu nak'i zuwa gidan." Umma tace, "babu komai ki bari ki samu lafiya sosai sai kije."? Rauda tayi shiru kanta a sunkuye Umma tace, "Me kike so kici yanzu? Tun safe baki ci komai ba."

? ?? Rauda bakin ta ya fara rawa tana so tayi magana kuma kuka ya hanata fad'a. Umma tace, "Wai sau nawa zaki kuka ne a rana Rauda? Bakya gudun idanun ki su samu matsala sabida zubar da hawaye?. Haba dan Allah ki d'auki k'addara mana kamar yadda muma muka d'auka, mun san kin fimu jin ciwo amma ya za'ayi fad'an da yafi k'arfin ka sai ka mayar dashi wasa, waye ya isa yaja da jarabawar ubangiji a cikin mu?."

Rauda ta goge idon ta tace, "Umma ciki ne fa dani." Umma tayi murmushi tace, "Cikin halak ne ai wanda aka same shi da aure da meyasa kike damuwa aka sa?."
"Bani da tabbacin cikin Asad ne Umma, zuciyata tana fad'a min cikin Aliyu ne bana Asad ba."
"Ni jikina yana bani cikin Asad ne, zuciyata ta gamsu da Asad mijin kine cikin sane a jikin ki bana dan uwan sa ba."
"Ni kuma in na tuna ance bashi da lafiya sai naji jikina yayi sanyi na sake tabbatar da cikin na Aliyu ne Umma, in hakan ta kasance na shiga uku na lalace."

"Kar na sake ji kince kin shiga uku na fad'a miki komai ya faru da bawa daga rabbil alamina ne kema tak'i jarabawar shine ya jarrabo miki in kina furta irin wad'annan kalaman sai kizo ki fad'i, fad'uwar jarabawar ubangiji ba fad'uwar jarabawar duniya bace ba da zaka jure kace ka sake rubutawa, fad'uwa ce ta har abada domin kuwa imanin kine yayi rauni shiyasa kika fad'in."

Rauda tayi shiru ta lumshe idanunta ta buWe tana kallon bangon d'akin Umma tace, "Me kike so kici?." Rauda ta kalli Umma ta sunkuyar da kanta k'asa tace, "Shinkafa da miyar manja mai kifi." Umma ta mik'e tace, "Yanzu za'a kawo miki" ta fad'a tana fita zuciyar ta cike da tausayin Rauda d'in.

Babu b'ata lokaci Umma ta had'a mata shinkafa da miyar manja kamar yadda tace ai kuwa taci sosai dan ta jima bata ci abinci mai yawan wanda taci ba dan taji dad'in ta musmaman da Umma ce tayi mata da kanta sai take jin wani abun na zuciyar ta na raguwa.

Bayan sallar azahar aka aiko da mota daga gidan sarauta gidan su Rauda dan d'aukar su aje inda mai martaba yake neman su gabad'aya, Umma dak'yar ta lallab'a Rauda Baba ya dawo suka tafi a motar baza ma ka d'auka su bane da glass d'in ta bak'i ne sosai baka ganin na ciki sai dai shi ya ganka.

Can wajen gari suka nufa dan a can ne za'a taru ba cikin gidan sarauta ba sabida abinda za'a tattauna baza'a yishi kowa yaji ba, babban gida ne ginin sarauta mai kyau da tsari tamkar masarauta haka yake sabida kyau da kuma zanen jikin sa. tunda suka doshe shi gaban Rauda yake fad'uwa haka kawai bata san dalilin hakan ba jikinta ya sake jin sanyi fargabar da take ciki ta saka take jin marar ta na ciwo kad'an-kad'an.

A harabar gidan suka ga tarin motoci da alama mutanen da suka danganci taron duk sun hallara aka faka tasu motar drivern ya kalle su yace, "Ranku ya dad'e ciki zaku shiga." Da to suka amsa suka fito Umma ta rik'e hannun Rauda suka nufi inda ya nuna musu dukkan su zuciyar su rawa take.

Duk takun da zasuyi da bugun zuciyar Rauda ake yin sa har suka bud'e wata k'ofar glass suka shiga sai ga mutane a zaune a falon dukkan su a k'asa, kan Rauda yana k'asa tana ji suna gaisawa dasu Baba ita kam bata iya kallon kowa ba kirjin ta bugawa kawai yake yi tashin hankali yayi mata yawa. D'ago ido tayi a hankali idon ta ya fad'a na Jidda da take binta da kallo ta d'auke kai ta kalli gefen ta taga Asad a zaune ya dafe kansa kana kallon sa kaga mara lafiya dan ya rame sosai.

Nan take gabanta ya sake fad'uwa ta mayar da kanta k'asa zuciyar ta na tafiya a guje kamar zata fito sabida tashin hankali. Sallama sukaji dukkan su suka mik'e tsaye ganin hakan Rauda ma ta tashi mai martaba ya shigo yana kallon kowa da murmushi a fuskar sa ya zauna a akan kujera yana bin su dukka da idanun sa kafin ya girgiza kai yace, "muna fatan mun same ku lafiya dukkan ku."

A tare aka had'a baki aka amsa yayi shiru kafin ya kalli Uncle yace, "a bud'e mana taro da addu'a." Uncle kalle su yace, "Salati ga annabi." Aka amsa gabad'aya kowa yayi shiru ana salati kafin Uncle ya kuma cewa, "A karanta suratul iklas k'afa uku da niyar saukar alkur'ani duk abinda muka saka gaba a taron nan Allah ya tabbatar mana dashi, duk sharrin da yake ciki Allah ya watsar dashi a wannan lokacin." Aka amsa nan ma akayi ya kalli mai martaba alamun an kammala.

Mai martaba yace, "Alhamdulillah. Ina godiya ga Allah da ya bani ikon ganin wannan rana mai cike da rud'ani da farin ciki da tashin hankali da bayyanar wasu abubuwa a cikin ta, nasan akwai wanda basu so ganinta ba amma da yake Allah ya k'addara zuwan ta babu abinda mutum ya isa yayi a akan hakan."

"Da yawanku baku san Malam Adam da kuma iyalan sa ba wasun ku suna ta mamakin me ya kawo su taron cikin gida to suma y'an gida ne domin y'ar sa itace tsohuwar matar Asad duk wani abu da za'a tattauna ya shafe ta domin kuwa tana cikin rud'ani itama tana so a warware mata duk abinda yake wakana a cikin tata rayuwar.

Kowa ya d'ago yana kallon su ita dai Rauda bata kalli kowa ba mai martaba ya sake cewa, "Ina so dukkan ku ku kalli Asad da Aliyu ku nuna min waye Sarkin Katagum a cikin su." Mamaki fal zuciyar dukkan su kowa ya kalle su cikin mamakin tambayar mai martaba aka nuna Asad da yake zaune cikin manyan kaya har lokacin hannun sa na dafe da kansa.

Mai martaba ya girgiza kai gani wanda suka nuna yace, "Rauda!." Gabanta ya fad'i ta d'ago kafin tayi magana yace, "Nuna min mijin ki a cikin su." Ta kalle su dukkan su duka babu wanda yake kallon ta a cikin su ta nuna Asad da yake zaune kamar yadda aka nuna shi d'azu.

Mai martaba yayi murmushi ya kalli Mama da take a firgice matuk'a yace, "Rabi'a nuna min d'anki Asad kuma sarkin ku a cikin su." Mama ta firgita dan bata hankalin ta ta fara zare idanu cikin tashin hankali, "baki ji abinda nace ba?" Ya sake maimaitawa sai lokacin ta dawo nutsuwar ta ta nuna Asad da yake zaune kamar yadda kowa ya nuna.

Mai martaba yayi murmushi yana kallon su shima kafin yace, "Duk wanda kuka nuna kunyi daidai shine Asad kamar yadda kuka sani amma fa kamar yadda ake nuna muku." Kowa ya kalli mai martaba alamun karin bayani dan basu fahimci kalmar sa ta k'arshe ba. Ganin hakan ya saka shi ya girgiza kai yace, "Wanda kuka nuna ba shine Asad ba, wanda yake zaune a gefen sa shine Asad duk wanna kuke nunawa yanzu Aliyu ne ba Asad ba!."
[17/12, 10:42 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*078.*

? ? ? ?? A tare dukkan su k'irjin su ya buga nan take kowa ya d'ago kai yana kallon mai martaba ana kuma kallon Asad da Aliyu da suke zaune kowa d'auke da zallar mamaki da tsoro a tare dashi. Rauda firgitar da tayi sai da ta bayyana a gangar jikinta tayi baya kamar zata fad'i tayi saurin dafa carpet ta kai kallon ta ga wanda akace shine Asad idon ta ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login