Showing 114001 words to 117000 words out of 216282 words

Chapter 39 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

da neman alfarma wajan talakawa...? Mtswww basu kai matsayin na nemi alfarma a wajan su ba. Ku bani waje" ta fad'a tana yi musu alamun su tashi da hannun ta suka fita jiki na rawa ita kuma ta shiga kiran number Asad.

Bata samun sa haka ta hak'ura ta ajjiye wayar a gefen ta lumshe idanu abubuwa sun taru sun cushe mata kanta da zuciyar ta. Bayan sallar i'sha suna zaune ita da Hydar da Suhaima babu mai magana cikin su sai Hydar da yake dafe kansa sabida ciwon da yake masa yana zaune amma jiri yake ji sosai kamar ma zai kifa. Mama ce ta kalle shi tace, "Hydar ya dai?." Ido ya bud'e ya kalle ta sai kuma ya kulle ya furta, "Washhhhh" sai ya kifa kansa a kan kujera yana juya kansa.

Mama tace, "Subahanallah, Hydar lafiya?." Ta fad'a tana tasowa tazo inda yake ta rik'e shi taji kansa yayi mugun zafi tana jijjiga shi amma sai taga yayi luf alamun ya suma.

Suhaima hankalin ta ya tashi tana kusa da Mama ta jijjiga shi Mama ma haka, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Hydar! Ka tashi dan Allah kar ciwon ka ya tashi a wannan yanayin da nake ciki. Hydar! Hydar!!" Ta fad'a tana sake girgiza shi amma babu alamun motsi a tare dashi alamun ya tafi doguwar suman da ya saba tafiya lokaci zuwa lokaci.

Hawaye take yi hakan ya saka Suhaima kuka itama ta tashi ta kira number Dr Yasir ta sanar dashi halin da ake ciki ya tabbatar mata da zuwan sa, ba jimawa ya bayyana a aka kwantar da Hydar kamar ko wanne lokaci aka Jona masa abubuwan da suke taimaka masa ko yaushe nan da nan zafin kan yake raguwa.

Dr Yasir ya kalli Mama da take zaune duk ta fita daga hayyacin ta yace, "Ayi hak'uri ranki ya dad'e, wannan bai kai na baya ta'azzara ba zaiyi saurin dawowa hankalin sa in sha Allah. Kuma dan Allah Mama ta daina saka damuwa a ranta sabida itama bata da lafiya." Ganin babu wanda ya iya bashi amsa cikin su sai ya tafi ya kyale su.

Suna nan zaune babu mai magana Mama tunanin ta ya tafi wani wajan daban ta rasa me zatayi komai ya tsaya mata duka y'ay'an nata babu wanda yake da amfani a wannan lokacin.

Kafin wani lokaci labarin rashin lafiyar Hydar ta bazu a gidan haka aka kwana Mama bacci sai b'arawo tunda ta farka da asuba bata kuma komawa ba ta shiga wajan Hydar ta ganshi bata fito ba sai da gari ya waye rana ta bayyana sosai.

? ? ? Tana fitowa jakadiyar ta ta shigo ta zube tana fad'in, "Barka da safiya ranki ya dad'e, Allah ya k'ara lafiya ya bawa Yarima lafiya ya tashi k'afadun sa." A labb'an ta ta amsa da amin kafin Jakadiya tace, "Fulani Hajiya da fulani Ammi suna neman Izinin shigowa." Mamaki ya kama zuciyar Mama amma sai ta danne tace, "suzo."
"An gama ranki ya dad'e" ta fad'a tana mik'ewa ta fita.

Da sallama suka shigo tana zaune akan kujera ta amsa a dak'ile suka k'araso suka zauna suna binta da kallo, mamakin ramar da tayi sukeyi suka kalli juna suna girgiza kai kafin Fulani Hajiya tace, "Sai muka ji labarin rashin lafiyar Hydar, Allah ya bada lafiya."
"Amin" ta amsa a tak'aice tana shan khamshi. K'aramin tsaki Ammi tayi tace, "akwai gaisuwar da za'a je Bauchi mun shirya zuwa in zaki."

Mama ta kalle su tace, "Waye ya bada izinin zuwan?." Hajiya ta kalle ta tace, "Sai an bamu izinin zuwa?." Mama tace, "nice nake da ikon bada umarnin aje ko kar aje."

Hajiya tace, "A matsayin ki nawa?" Ta fad'a tana yi mata wani irin kallo na rainin hankali. Mama tace, "A matsayina na wacce take jagorancin gidan nan in shugaban gidan baya nan, a sama nake da kowa ni nake da bada ikon bada umarnin ayi ko kar ayi." Fulani Hajiya ta kyalkyale da dariya ta tafa hannu tace, "Allah shugaba?, kin manta ya kike a gidan nan ne? Kin manta matar Asad itace take mulki a gidan bake ba?."

Mama zatayi magana Hajiya tace, "Kinga dakata malama, meye bamu sani ba ko dan kinga munyi miki shiru hakan sai yake nufin har yanzu kina da wani matsayi a wajan sa..?. Kamar ba shine ya koro ki daga b'angaren saba lokacin da kika je, kamar ba shi bane ya kalli idanun ki yace bazai rabu da matar sa ba, kamar ba shi bane ya tafi England bai sanar dake ba?. A haka kike da ikon? Yana ina to nuna mana mu gani." Mama ranta ya b'aci matuk'a tana wuci tace, "amma duk da haka d'ana ne nice na haife shi!."

"To yana ina yanzu? Duka Y'ay'a ukun da kike tak'ama dasu kina d'ga kai y'ay'an ki sune manya kina da guda uku nuna mana amfanin su a halin yanzu mu gani. D'aya yana can neman matan sa wata k'asar, d'ayan da kika fi ji dashi kuma ya zab'i matar sa akan ki, d'aya kuma gashi a kwance dashi da gawa basu da maraba nuna mana amfanin su mu gani in akwai Rabi. Ko yanzu in ina buk'atar wani abun ina da wanda zan kira ya kawo min duk da kank'antar shekarun sa ke ina nakin suke...? Kinga kenan namu da ake rainawa k'anana sune suke da amfani ba naki ba. Nasha fad'a miki lokaci kad'an ne kawai naki in ya juye sai kinyi kuka gashi kuma kina gani, kina kallo wad'annan ukun sunfi k'arfin ki wallahi duk wata tak'ama da kike yi a banza da wofi kike yinta domin a tafin hannun mu kike" ta mik'e tsaye ta gyara zaman alkyabbar ta tace,

"Zamu tafi gaisuwa ko kin bada umarni ko baki bayar ba sai munje duk da daman baki isa ki hana mu ba, nasan ke baza kije ba sabida abubuwan kanki ma sunyi yawa naji labari ance harda hawan jini. In baki kwantar da hankalin ki ba nan gaba har ciwon zuciya zai saka miki domin kuwa yanzu kika fara ganin abubuwan da kika aikata suna dawowa kanki. Rukayya muje" ta fad'a tana fita Ammi tabi bayan ta ba tare da ta tofa ko wacce kalma ba amma a zuciyar ta taji dad'in wanke ta da Hajiya tayi tasss.

Mama kamar an dasa ta a wajan haka ta koma idanun ta suka ciko da ruwa tayi saurin mayar dasu zuciyar ta na bugawa a guje kalaman Hajiya na dawo mata cikin zuciyar ta. Tabbas gaskiya duka su ukun basu da amfani a wajanta a yanzu dasu da babu duka d'aya tunda gashi tana buk'atar su babu kowa a kusa da ita. kai ta dafe da hannayen ta duka biyun tana jin zuciyar ta fashe jikinta na rawa tace, "Ladidi!" Ta fad'a da k'arfin gaske a guje Jakadiya ta shigo ta zube a a gabanta tace, "Gani ranki ya dad'e."

"Muje gidan dana aike ku jiya" ta fad'a tana mik'ewa ta shiga d'aki jim kad'an ta fito ita da Suhaima suka fita tare jikin Ladidi sai rawa yake haka aka shiga mota suka d'auki hanyar gidan su Rauda...


*Fan's ga Mama zata je neman alfarma a gidan su Rauda.....* @&?>?#?
[17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*061.*

? ? ? ? Mama dafe take da kanta har akaje k'ofar gidan su Rauda bata sani ba tiririn da take ji a zuciyar ta har cikin idanun ta hakan ya haifar musu da canja launi zuwa ja suka tara ruwa kamar wacce take shirin fashewa da kuka. "Allah yaja zamanin ki mun iso" Jakadiya ta fad'a tana nunawa Mama gidan. Ta jima bata d'ago ba sai daga baya ta kalli gidan ta kalle ta kamar zatayi magana sai ta fasa ta bud'e motar ta fita dole suka biyo bayan ta kai tsaye ta nufi cikin gidan.

A guje Jakadiya ta rufa mata baya ta wuce ta ta bud'e mata k'ofar gidan ta shiga ta tsaya tana k'arewa gidan kallo, d'an k'aramin tsaki taja Jakadiya tace, "Ga hanyar nan ranki ya dad'e." Gaba tayi tana binta a baya har cikin falon gidan wanda suke a zaune Rauda da Umma da Anty Ummi suna hira da dariya da alama suna cikin nishad'i.

Sallamar jakadiya ya saka su suka amsa tare da kallon bakin k'ofar wacce suka gani a tsaye a wajan ya saka Rauda mik'ewa tsaye tana kallon ta itama ita take da kallo da alama ta gane ta. Ran Mama ya b'aci matuk'a ganin wacce take a gabanta zuciyar ta na zugata ta juya ta koma amma wata zuciyar na hanata aikata hakan.

Shiru babu wanda yayi magana a cikin su ita bata ce ba suma basu ce Rauda ta koma ta zauna nan taji muryar Jakadiya tace, "Sannun ku mutanen gidan nan, Fulani Rabi'atu matar sarkin katagum mai murabus, mahaifiya ga sarki mai mulki na yanzu Sarki Aliyu Asad."

Yaya ummi tace, "Sannun ta da zuwa, bismillah ku zauna." Jakadiya ta kalle ta tace, "Allah yaja da ranki bismillah." Har lokacin idanun Mama yana kan Rauda wacce itama a kai a kai ita take kallo ba dan wani abun ba sai kamar Asad da take gani akan fuskar ta. Ta kasa motsawa kallon su take rashin kunyar da Rauda tayi mata yana sake dawo mata cikin kanta kamar a lokacin abin yake faruwa, ji take kamar ta jawo ta ta bawa dogarai su ta jibgar ta har sai ta daina numfashi.

"Baiwar Allah ki zauna mana" Umma ta fad'a tana kallon ta itama ta kalle ta kamar zatayi magana sai ta daure ta fasa ta zauna d'in jakadiya ta zauna kusa da ita a k'asa Mama ta kalle ta alamun tayi musu jawabi. Zata fara magana Suhaima ta shigo da sallama suka amsa tace, "Sannun ku." Suka amsa da yawa ta tsaya a gefe tana kallon Rauda itama ta kalle ta amma sai ta d'auke kai.

Suhaima mamaki take yi sosai har ta kasa b'oyewa tace, "Nasan fuskar ki." Kallon da Mama tayi mata ya saka ta yin shiru bata cigaba da maganar ba Jakadiya tace, "Kamar yadda muka shaida muku a daren jiya shugabar mu ta aiko mu wajan ku akan ganin Baba Malam gata da kanta tazo kamar yadda kuka ce." Umma tace, "to me take so ayi mata?."

Jakadiya tace, "Tana buk'atar ganin Baba malam ne bata da hanyar ganin sa cikin sauk'i amma nasan in kika shiga maganar kamar anyi an gama ne." Rauda tayi murmushi cikin rainin hankali tace, "Kenan alfarma tazo nema?." A fusace Mama ta kalle ta tace, "Baku isa na nemi alfarma a wajan ku ba, su waye ku? Me kuke dashi?." Rauda ta d'an bud'e idanun ta kana tace, "To zaku iya komawa inda kuka fito" ta fad'a tana nuna musu hanya alamun su tafi.

? ? ? Jakadiya tace, "Hattara y'an mata, macece a gaban ki macen ma kuma shugabar ki. Ki iya bakin ki har ya kai ki ya baro." Rauda ta tab'e baki tace, "Shugabar ki dai, ni ga tawa shugabar nan" ta fad'a tana nuna mata Umma da take zaune. Umma tace, "Rauda meye haka ne? Kiyi shiru bana son sake jin maganar ki."

Umma ta kalli Mama tace, "Baiwar Allah ki fad'i abinda kike so in da dama zamu iya taimaka miki in babu dama sai mu baki hak'uri." _inda dama zamu iya taimaka miki._ abinda ya dawowa Mama kanta kenan cikin kalaman Umma wato ita zasu taimakawa ma dan wani dalili ya kawota wajan su suke k'okarin fad'a mata maganar banza.

"Nafi k'arfin taimakon ku daku da dangin ku baki daya, abinda nake so Ladidi ta fad'a muku baku ji me tace bane?." Yaya Ummi tace, "To tunda kinfi k'arfin taimakon mu dana dangin mu kiji wajan wanda basu fi k'arfi ba mana kin sa sai su taimaka miki, kinga da baki sha wahalar zuwa nan ba. Kije ki nemi wanda baki fi k'arfi ba sai mu gani."

Mama tayi shiru ta rasa me ya kamata tayi dan tasan ita ta kawo kanta, a ka'ida rashin mutunci ya kamata tayi musu ta bar gidan amma kuma tana buk'atar ganin Baba malam kodan bakin da yayi yawa a kansa hakan ya tilasta mata yin shiru badan taso ba zuciyar ta nayi mata mugun suya sabida b'acin rai.

? Suhaima da take gefe a tusashe tace, "Mamana tana so zata ga Baba Malam ne tana so ayi mata hanyar ganin sa dan Allah." Umma tace, "Abinda za'a ce kenan fa tun d'azu ake jan maganar. Rauda shiga ciki ki kira shi a waya ki sanar dashi abinda yace sai kizo ki fad'a mana." Rauda kallon Umma take alamun mamaki kafin tace, "Wai Umma me kike cewa ne? Kina nufin alfarmar zaki yi musu?." Umma ta zare mata ido tace, "baki ji me nace bane kike kallona?."

Tashi tayi ta shiga d'akin falon ya zauna shiru babu motsin kowa duk sunyi shiru Jim kad'an Rauda ta fito ta kalle Umma tace, "Yanzu bashi da lokaci yace amma zuwa dare bayan sallar i'sha zai jira ta. Bayan sallar i'sha ki dawo sai a had'a ki da wanda zai raka ki in hakan ta samu, in bata samu ba kuma abi wani sarkin" ta fad'a tana kallon Mama da kanta yake a sama amma tana jin me take cewa.

Mama ta juyo ta kalli Rauda suka had'a ido ta jijjiga kai ta had'd'iye yawu mai d'acin gaske kalaman Rauda na sukar ta a zuciyar ta amma duk da hakan babu abinda zata iya sabida halin da take ciki taimakon take so dole.

Umma tace, "Anjima in Allah ya kaimu zaku iya dawowa kamar yadda yace sai Rauda ta raka ku." Jakadiya tace, "Mun gode Allah ya bar zumunci." Umma tayi murmushi tace, "kar ki damu, ai mu zuciyar mu a wanke take tas da ruwan zamzam muna rama alkhairi ga sharri komai munin sa. Haka zalika muna rama alkhairi ga cuta komai yawan ta, haka zalika muna rama alkhairi ga cin zarafi komai d'acin sa. Mutane ne mu mun kuma san me muke yi muna taimakon kowa musamnan ma wanda ya kawo kansa" ta fad'a tana wani murmushi wanda kana kallon sa kasan akwai manufa a cikin sa.

Mama ta kalle ta har lokacin da murmushin akan fuskar ta sai ta sauke k'aramin numfashi ta tashi ta fita jakadiya ta rufa mata baya Suhaima ta matso cikin falon tace, "Mun gode sosai Mama, Allah ya saka da alkhairi. Amma kamar na sanki" ta fad'a tana juya kallon ta ga Rauda da take tsaye.

Rauda tayi murmushi tace, "Wata?ila mai kama dani kika sani bamu tab'a had'uwa ba." Suhaima ta tab'e baki ta d'aga kafad'a tace, "Maybe, sai anjima" tana fad'a ta juya ta fita.

? ?? Rauda kamar tayi kuka ta kallo Umma tace, "Yanzu Umma wannan matar kika yiwa alfarmar ganin Baba malam? Kin manta abubuwan da suka faru ne a baya? Kin manta zagi da cin fuskar da tazo gidan nan tayi mana?, har sakawa tayi a kashe ni har cikin gidan nan amma shine zata zo da guntuwar izzar ta wai da niyar neman taimako kuma ayi mata?. Kina gani fa ko neman alfarmar ta kasa sabida a ganin ta fad'uwa ne kuma mu kamar masu jin tsoron ta sai mu taimaka mata?."

Umma ta kalli Rauda zatayi Magana Yaya Ummi tace, "Nima wallahi banji dad'in hakan ba, naso koda zamu taimake ta sai ta sauke izzar da take ji da ita ta rok'i alfarma da bakin ta in mun ga dama sai mu taimake ta. Kamar masu ji tsoron ta bata fad'i abu ba sai muyi mata." Umma ta kalle su tace, "to ku dake ni akwai ku wuce haushin ku." Jin hakan sai Rauda ta zauna tace, "ba batun duka Umma kawai dai bamu ji dad'i bane ba wallahi."

Umma tace, "meye danrangamin ki da ita Rauda? Ni in nice ke wallahi bazan nuna na santa bama balle na d'aga ido na kalle ta, in ma na nuna mata b'acin raina kenan na damu da d'anta ma. Ina izzar take? Ina mulkin yake? Ina sarautar take? Ina k'asaitar take? Ina ji da kan yake?. Har cikin falon nan tazo fa neman alfarma koda batayi magana ba ai munyi nasara a kanta tunda yadda muka ce sai ta tako tazo sai da tazo d'in rashin maganar ta ba wani abun bane ba. Kuma dan ka rama alkhairi ga sharri ai babban aiki kayi ko yanzu tasan muna da amfani gashi tazo neman alfarmar da ta rasa wanda zaiyi mata sai mu d'in dai da take ganin mu k'ask'antattu."

Rauda ta runtse idanun ta kafin tace, "Bata da kirki matar nan Umma. Ni ba ina magana akan saki ko wani abun ba; ki duba yadda tazo ta zauna kamar falon gidan su tana wani shan khamshi ita a lallai ga gimbiya maganar ma sai dai ayi mata."

Umma tayi murmushi tace, "Mun sani amma babu abinda zamu cewa d'anta, ya zama silar abubuwa da yawa cikin rayuwar mu baki d'aya, badan shi ba da yanzu muna neman gidan zama lokacin da aka zo rushe mana wannan gidan kodan shi mayi mata dan mu ba butulu bane ba."
Yaya Ummi tace, "Uhummm!." Alamun maganar bata wani ratsa taba kawai babu abinda suka isa su iya ne.

Umma tace, "An koya mana rama alkhairi ga wanda ya nufe ka da sharri tun a gidan mu, in badan haka ba shi kansa Baba malam din bazai saurare ta ba dan ke y'ar sace duk wanda ya tozarta ki shi ya tozarta. Ki shirya anjima suzo ki raka su." Rauda tayi wani irin juyi tace, "Umma wai da gaske ni zan rakata?" Ta fad'a tana zaro idanu waje. Umma tace, "Ke zaki rakata Rauda" ta fad'a tana shiga d'aki.
Rauda ma d'akin ta wuce tana ji a ranta ko za'a yi tashin hankali bazata raka Mama wajan Baba Malam ba sai dai duk abinda zai faru ya faru kawai.


? ? ? ? Yadda Rauda take jin zafi a ranta haka Mama ma a haka suka koma gida ji take inama tana da bindiga ta harbe kanta kawai ta huta da wula?ancin da ta jawowa kanta, tunda suka koma take a zaune fad'i take, "Sadiya kin cuce ni, kin cuce ni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login