Showing 204001 words to 207000 words out of 216282 words

Chapter 69 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

maka matsala."
"Rabon samun abinda yake cikin ki shine silar faruwar duka wannan k'addarar. Tun farkon had'uwa ta dake abinda ya faru wanda Mama tayi miki ko ni nayi miki dan Allah ki yafe mana dukkan mu."

Kai take girgizawa tace, "Ka daina rok'ona Sultan ni ya kamata na ro?e ka afuwa nayi maka abubuwa da yawa, na kira ka da kalma mara dad'i na jefa ka da munanan kalamai sabida rufewar idanuna, na d'aga hannu na mare ka matsayin ka na shugaba ban duba wannan ba, kayi hak'uri ka yafe min Sultan bazan sake aikata makanancin haka ba in sha Allah."

Janta yayi zuwa jikin sa ya rungume ta sosai a jikin sa ta sake fashewa sosai da kuka yana shafa fatar bayan ta yace, "Ya isa ki bar kuka, amma ki yafe min ki yafewa Mamana, ki yafewa Aliyu ma Muwaddaty dan Allah."

"Ni na yafewa kowa ma har Hydar na yafe masa, kaima ka yafe min." Jin ta ambaci Hydar sai ya matse ta a jikin sa yace, "Ina son Hydar Muwaddaty, ina Qaunar Hydar, ban saba da kowa ba sai Hydar, bani da aboki sai Hydar, bani da d'an uwa sama Hydar. Shine abokin shawarata shine abokin kukana, amma Hydar......!" Sai ya kasa maganar ya kulle idanun sa yana furzar da iska sannan yace, "Har yanzu ina son shi."

Tausayi ya bata sosai ta d'ago daga jikin sa tana kallon sa ganin gabad'aya ya canja tace, "kayi ha?uri duk tsanani yana tare da sauk'i, ka yiwa Hydar addu'ar shiriya da fatan samun nutsuwa da sassaucin abinda yake zuciyar sa. Nasan zaka ji ciwo sabida nima da Hydar na sanka amma kayi ha?uri, haka rayuwa take koda hakan bta faru ba wata rana zaka mutu ko shi ya mutu dole wani ya tafi ya bar wani a cikin ku. Ka kwantar da hankalin ka kaga jinin ka ya hau saka damuwa ba naka bane ba. Na tabbatar shima yana sonka wani abun ne kawai ya rufe masa ido amma in kana mas addu'a sai kaga ya dawo Hydar d'in da ka sani a baya."

Numfashi ya sauke yaji dad'in kalaman ta sosai a ransa ya matse ta sosai ya kulle ido yace, "Ina sonki Muwaddaty, ki daina nisa dani in ba haka ba zan iya rasa raina abubuwa sunyi min yawa kece maganin damuwana. Dan Allah ki zauna tare dani."

"Ina sonka Sultan, ina sonka sosai bzan sake yin nesa da kai ba in sha Allah, kullum ina tare dakai daga ban har aljanna." Yayi murmushi ya sassauta rik'on da yayi mata yana kallon ta ya share mata hawayen fuskar ta da hannu yayi mata alamun da tayi murmushi tayi shima yayi murmushin kafin tace, "Yunwa nake ji, kaina na ciwo." Mik'ewa tsaye yayi sa kuma yayi saurin dafe kansa tare da dafa bango tayi hanzarin Mik'ewa itama tace, "Ka zauna Sultan baka da lafiya."

Kai ya girgiza ya kalli agogo yaga k'arfe d'aya na dare harda wani abun ya k'arasa inda kayan sa suke ya buWe kaya ne a ciki kamar a gidan yake rayuwa ya d'auko doguwar rigar sa ya k'araso ya saka mata towel d'in ya fad'i ya d'auke ya saka mata hular ta da tazo da ita ya rik'e hannun ta yace, "muje na miki girki."

Jan hannun ta yayi ta turje tace, "Baka da lafiya Sultan, ka dawo ka zauna dan Allah kanka yayi zafi sosai fa." Kai ya girgiza mata ya sake jan hannunta ta sake turjewa ya juyo yana kallon ta ya kama k'ugu zatayi magana ya d'auke ta cak suka fita daga d'akin kai tsaye kitchen d'in gidan suka nufa.
[17/12, 10:45 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*093*

? ? ? ? ?? Tana jin fitar Suhail ta fito ya kalle ta yaga ta b'ata fuska suka had'a ido sai ya d'aga mata gira yaga ta sake d'aure fuska sai yayi dariya kad'an ya tashi ya d'auki abincin da Suhail ya buWe yaga abinci ne har kala uku, kallon abincin yaga tayi alamun sun bata sha'awa ya d'auki wanda yaga tana kallo ya kalle ta taga tana kallon sa sai ya mik'a mata hannu ba musu ta d'ora hannun ta man nasa ya zaunar da ita a cinyar sa.

"Baza kisha tea ba?." Ta kalli abincin tace, "Wannan kawai nake so naci." Baiyi musu ba ya ware spoon din da yake nannad'e a tissue ya fara bata tana ci sai yaga ta tsaya kuma tana kallon sa tana yamutsa fuska, da ido yayi mata alama da ya dai sai ta mik'e daga jikin sa tayi wajan sink a guje ta fara shara amai.

A hankalin sa ya tashi sosai ya k'araso inda take ya rik'e ta har ta gama aman ta d'ago ta dafe kai ya rik'o ta suka dawo ta zauna tace, "Abincin babu dad'i." Asad ya bita da kallon tausayi yace, "Sannu." Ta kwanta a jikin sa tace, "Ina jin yunwa Sultan amma bana son duka wannan abincin."

"Me kike so?."
"Farfesun dankali da hanta." Waya ya d'auka zai kira Suhail ta rik'e wayar tace, "Ni kai nake so ka dafa min." Wara ido yayi yace, "Muwaddaty babu komai na girki a nan taya zan iya miki abinda kika ce?." Kawai sai ta fashe da kuka tana fad'in, "ni shi nake son ci in banci ba zan iya mutuwa" ta fad'a tana dukan k'irjin sa tana kuka.

"Oh my god!" Ya furta a bayyane kafin yace, "Is okay!." Suhail d'in ya kira daga can b'angaren yace, "Allah ya taimake ka."
"Suhail potatoes nake so." Suhail mamaki ya kama shi yace, "Ranka ya dad'e akwai dankali a abincin dana kawowa mai martaba." Asad yaja tsaki ya kashe wayar ya rubuta masa text dan ya fahimci baya ganewa.

Kuka take yi har lokacin yace, "Ya isa mana Muwaddaty yanzu Suhail zai kawo." Tace, "Ni kai nake so ka dafa min." Kai ya d'aga yana jiran kiran wayar Suhail. Tsaki yaja ganin mintina biyar Suhail baizo ba ya tashi ya kwantar da ita yace, "Ina tare da Suhail kar ki fito" yana fad'a yayi gaba da sauri.

A falon suka had'u da Suhail ya shigo yaja tsaki yana kallon Suhail yace, "Tuba nake ranka ya dad'e,? akwai abinda ya bani wahalar nema shiyasa." Kitchen ya wuce dole Suhail yabi bayan sa ya same shi ya hard'e hannu a k'irji Suhail ya ajjiye kayan yana kallon sa amma baiyi magana ba.

"Ranka ya dad'e akwai abinda ake so?." Asad ya kawar da kai ya dawo da kallon sa ga Suhail yace, "Dafa min zakayi." Suhail ya kalli dankalin da yake a leda yace, "An gama. Soyawa za'ayi ko farfesun sa za'ayi?."
"Na k'arshen" ya fad'a yana kallon sa Suhail yace yanzu za'ayi a gama.

Suhail ya d'auko wuk'a yana feraye dankalin Asad yana tsaye yana kallon sa ganin yana yi a hankali, wayar sa da take hannun sa yaji tana k'ara yaga sunan ta ya dafe kai yace, "Oh Muwaddaty! Suhail kayi sauri mana tana jin yunwa babu abinda taci fa" ya fad'a ba tare da ya d'auka ba ya ajjiye wayar ya d'auki wuk'a shima yana yin yadda yaga Suhail d'in yanayi.

Suhail dariya yake b'oyewa? ya yanka dankalin ya d'auko kayan miya daman a markad'en su suke ya d'auki tukunya ya d'ora akan gas ya kunna nan da nan ya fara had'a mata abinda take so. Asad yana tsaye yana kallon sa ya k'agu a gama ya kai mata ya kalli Suhail yace, "I'm coming" ya fad'a yana ficewa Suhail ya kyalkyale fa dariya harda rik'e ciki.

Ya jima yana dariya sosai domin yadda Asad din ya rud'e shine abinda ya bashi dariya yagirgiza kai yace, "Lallai a gaida mace, yanzu badan ni ba ko taya zai iya girki oho, nidai nasan babu abinda ya iya sai had'a coffee shima bai jima da iyawa ba da muna makaranta sai dai a dafa a bashi." Motsin sa yaji a bayan sa hakan ya saka shi yin shiru Asad ya k'araso yana kallon tukunyar Suhail yana juyawa.

D'an tsaki Asad yayi yana kallon sa yace, "in banda dole ina ita ina cin abincin wannan." Suhail ya sake fashewa da dariya kafin yace, "Afuwan ranka ya dad'e an kusa gamawa."

Yana nan tsaye Suhail ya gama ya d'auko bowl ya zuba a ciki ya saka spoon yace, "An gama ranka ya dad'e." Asad ya karb'a yace, "Allah yasa da dad'i, jira ni" ya fad'a yana sake fita Suhail yayi murmushi yana cin wanda ya rage dan sosai girkin nasa yayi masa dad'i.

Tana kwance ya kai mata ta tashi zaune ta karb'a tana murmushi tace, "Na gode Sultan" ta fad'a tana fara ci. D'an yamutsa fuska tayi tace, "Yayi yaji, amma babu laifi ya d'an yi dad'i" ta fad'a tana ci. Yana zaune yana kallon ta har ta cinye tass ya sauke ajiyar zuciya ya tashi ya koma wajan Suhail ya ganshi a falon a zaune.

"Ka cika yaji" ya fad'a yana kallon sa Suhail da ya mik'e tsaye yayi murmushi ya sosa kai yace, "Afuwa ranka ya dad'e, a haka na siyo kayan miyan wata?ila suna cika yaji." Asad yayi murmushi yace, "Na gode Suhail, banda kai ba ban san ya zanyi da ita ba."? Suhail yayi murmushi yace, "Haba ranka ya dad'e meye abin godiya?." Asad yayi murmushi ya dafa kafaWarsa sai kuma yanayin sa ya canja alamun ya tuna ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????Hydar.

Suhail ya sassauta murya yace, "Sai ha?uri ranka ya dad'e, dukkan matakin nasara a rayuwa akwai qalubale, qalubalen kuma shine sirrin nasarar a rayuwa gabad'aya." Asad ya d'aga kai kafin ya juya ya koma shi kuma ya fita.

Lemo ya same ta tana sha ya zauna kusa da ita ya nuna mata leda ta buWe taga undies ne sama da goma a ciki harda doguwar riga ta kalle shi tace, "A ina aka samo?." Tab'e baki yayi ya wara hannun sa alamun bai sani ba tace, "Har kwana nawa zanyi a nan ne na gansu da yawa?." Nan ma baiyi magana ba ta kalle shi sai ta d'auki ledar tace, "Bara naje na saka baa......." da baya ya dawo da ita ta fad'a jikin sa gabad'aya ya girgiza mata kai alamun A'a.

"Allah Sultan bana jin daWin zama haka" ta fad'a yana kallon sa shima kallon ta yayi ya rad'a mata abu a kunne tayi dariya ta kifa kanta a k'irjin sa tana b'oye fuskar ta.
"Ina kika samo Sultan?" Taji ya tambaya a sama ta kalle shi tace, "Sultan shugaba kai shugaba ne a ko ina, nima shugabana ne kai."

Tab'e baki taga yayi sai ta kalle shi tace, "Ko baiyi maka ba?." Ya juya idanun sa yace, "It's not a romantic name."
"Wanne kake so nace?." Ya cizi bakin ta yayi murmushi ganin sai ta sake kwanciya a jikin sa shima ya rik'e ta.

Wayar ta taji tana k'ara ta d'ago ta mik'a hannu ta d'auka ta kalli wayar ta kalle shi tace, "Kaga number outside country ce." Ya kalla yaga number Saudia ce yace, "pick it." Ta wara ido tace, "Na sani ko scammers ne? Wa nake dashi a k'asar waje?." Da kai yayi mata alama da ta d'auka tana kallon sa ta d'aga wayar ta saka a speaker.

"Rauda Umman kice!." Jin muryar Umma a cikin wayar sai ta zabura ta mik'e daga jikin sa ta zauna tana rik'e da kafad'arsa sa tace, "Ummana?." Umma tace, "Na'am Rauda, kinga number Saudia ko? Ai jiya muka tafiya gabad'ayan mu yanzu haka muna Madina."

Rauda ta kalle shi sai taga ba ita yake kallo ba tace, "Umma Saudia kuma? Wai da gaske Ummana kece nifa gani nake kamar bake bace ba." Muryar Yaya Ummi taji tana cewa, "Sai nayicmagana zaki tabbatar itace?."
"Lahh Yaya Ummi? Harda ke? Nifa kun kulle min kai dan Allah kuna ina?."
"Ke Rauda wallahi da gaske muna Madina gabad'aya y'an gidan mu keda Rahma ne kawai babu."

Rauda tace, "Amma shine zaku tafi ko a sanar dani ai da nazo munyi sallama ko?. To wai waye ya biya muku dukkan ku kuka tafi ban sani ba?." Yaya Ummi tace, "Mijin ki mana, akwai wanda zai biya mana ne in bashi ba Rauda?." Gaban Rauda ya fad'i ta kalle shi sai ya d'aga mata kai tace, "Amma Yaya Ummi ban sani ba."

"Mijin kine yace kar mu sanar dake shiyasa mukayi shiru, yanzu kin ganmu har mun fito daga Rauda munyi gaisuwa a kabarin annabi mun koma masaukin mu." Rauda ta lumshe ido hawaye suna sakko muryar ta na rawa tace, "Har su Yayar mu?." Yaya Ummi tace, "Na fad'a miki gabad'ayan mu ne, kin gan mu zaune ma gama cin abincin mu kenan." Rauda ta fashe da kukan farin ciki Yayar mu da take jin komai tace, Kaji min Rauda da shashanci, to meye na kukan keda zakiyi farin ciki ki taya mu godiya sai ki fara kuka kuma?."

Datse kiran Rauda tayi ta kwanta a k'irjin sa tana kuka sosai, shiru yayi yana sauraron ta dan yasan babu lallai ta daina in yace ta daina tana jikin sa baice mata komai ba. Sai da tayi mai isar ta sannan ta d'ago ta kalle shi tace, "Shine ko ka fad'a min." Yayi murmushi yaja kumatun ta amma baice komai ba.

Bud'e baki tayi zatayi masa godiya ya d'ora hannun sa bakin ta ya girgiza kansa yace, "Bana son jin komai." Rauda tace, "Addu'a zanyi maka."
"Kiyi a zuciyar ki. Tashi muyi sallar la'asar" ya fad'a yana sauke ta daga jikin sa ya rik'e hannun ta suka shiga d'aki.

Alwala sukayi sukayi sallah ita dai har suka idar ji take wani iri wai iyayen ta da y'an uwan tane duka a Saudia ta dalilin ta, me ya kai wannan dad'i da farin ciki a duniya? Ace ta dalilin ka iyayen ka sunje Saudia ai abin murma ne. Yana lura da ita ganin zata sake yi masa kuka ya saka yace, "Bana son kuka Muwadda kin sani." Tace, "Farin ciki ne yayi min yawa Sultan, na rasa inda zan saka raina sabida farin ciki ji nake kamar bani bace. Ta dalilina iyayena suna Saudia sai naji kamar ana wanke min zuciyata sabida farin ciki Sultan shine yake sani kuka."

Idanun take gogewa ta matsa kusa dashi ta kwanta akan cinyar sa bai hanata ba ya fara karatun alkur'ani a bayyane ba tare da alkur'anin ba. Nan da nan ta d'auka itama suna yi tare a hankali duk da kira'ar ba iri d'aya sukeyi ba amma yana k'ok'arin yin irin tata suna tafiya a hankali. Sunyi sama da izu biyu a haka sai da yaji muryar ta tana rawa zatayi masa kuka ya saka shi ya dakata yace, "Haddar ki ta zauna sosai, kina ganin zaki iya national world Quran competition?."

Da sauri ta tashi daga kan cinyaar sa tana kallon sa tace, "Zan iya Sultan, shine burina ina so nayi koda bazan ci ba ace na shiga shima nasara ne." Ya girgiza kai alamun gamsuwa ya dawo da ita jikin sa ta jingina da kafad'ar sa yace, "Zakiyi."

"Thanks you Sultan. Allah ya kare min kai a duk inda kake, ya yaye maka dukkan damuwar da take zuciyar ka, ya saka maka da gidan aljanna yasa mu rayu tare nida kai a can. Ina sonka Sultan" ta fad'a tana jikin sa baice komai ba sai sake rik'e ta da yayi.

Itama shiru tayi bata ce komai ba sun d'auki lokaci a haka akwai hango en gidan su a Saudia take yi taji yace, "Naso na had'a dake ku tafi gabad'aya sai na fasa" ya kalle ta yace, "Maje tare dake ko?." Ta girgiza kai tana murmushi shima murmushin yayi domin farin ciki ne kwance a kan fuskar ta daka gani zaka gane basai ka fad'a ba.

Shiru tayi tana murmushi ita kad'ai ganin ta a farin ciki saka shi farin ciki yake sai yaji dukkan damuwar sa tana yayewa kamar bashi ne wanda yake da damuwa a kwanakin baya ba.? Sun jima suna a haka babu mai magana a cikin su ko wayar sa baya d'auka in an kira sunyi shiru basa magana.

Cikin ta taji yana shafawa ya kalle ta sai ta mik'e ta jawo abincin tace, "Tunda kaci dan kad'an banga ka kuma ci ba" ta fad'a tana buWewa takai bakin sa tace, "Kaci abinci." Bai mata musu ba yaci tana yi tana d'auke kanta daga kan abincin dan bata son khamshin hakan ya saka ta tashi ta d'auki ledar kayan ta shiga d'aki.

Bayan sallar i'sha tayi wanka ta saka riga da wando na bacci wanda ya siyo mata a cikin kayan ta saka hula sunyi mata kyau shima ya saka nasa riga da wandon suka fito suna zaga cikin gidan hannun sa na sark'e da juna. Kallon gidan take tana girgiza kai tace, "Sultan!."
"Sultana" ya bata amsa ba tare da ya kalle ta ba tace, "Ban tab'a ganin gida irin wannan ba tunda nake."

Yayi murmushi suka tafiya yace, "Badan Abba ya d'ora min nauyi ba da a nan gidan zamu zauna."
"Tsarin ginin gidan larabawa akayi gabad'aya." Baice komai ba suna cigaba da tafiya tace, "Wai kuna waya da Dr Khalifa kuwa?."

Cak taga ya tsaya ta kalle shi sai taga ya canja gabad'aya kamar ba shine yake murmushi ba sai jikin ta yayi sanyi tace, "I'm sorry." Tafiya suka cigaba da yi bata ce komai ba shima baice ba. Kallon sa tayi taga har lokacin fuskar a d'aure take sai tace, "Sultan yaushe zan fara makaranta? Ina son zama y'ar jarida."

Banza yayi mata kamar baiji ba suna tafiya har ta fitar da rai zai amsa sama da mintina goma kafin taji yace, "Ki ha?ura." Ta kalle shi jin abinda yace sai ta sauke kai k'asa bata sake cewa komai ba. Gama zagayen sukayi suka zo zasu koma ta tsaya yana kifta masa ido ya kalle ta tace, "Na gaji, ka goya ni."

Cikin ta ya kalla itama sai ta kalla sai tace, "Bafa abinda cikina zaiyi." Yak'i magana ta fara bubbga k'afa tana cewa, "Nidai na gaji ka d'auke ni bazan iya tafiya ba." Hard'e hannu yayi a k'irji yana kallon ta kamar bazai saurare ta ba sai kuma ya sunkuya ya d'auke ta suka cigaba ciki.

Har cikin d'akin ya ajjiye ta baiyi magana bai kuma yi murmushi ba ya juya ya fita, biyo bayan shi yayi ta same shi a zaune yana danna waya da alama aiki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login