Showing 60001 words to 63000 words out of 216282 words

Chapter 21 - KWANTAN BAUNA BOOK 2 COMPLETE BY Nanah Haleemah.doc

iko da Asad a koda yaushe amma dan Allah ta barni na gujewa abinda Allah baya so kar na aikata shi duk da kasancewar halak." Mama ta girgiza kai tace, "Da alama mallakar da aka yi maka har yanzu tana jikin ka kenan ko? To tunda nazo ko wanne irin asiri tayi maka wallahi sai na b'alla shi wallahi. Na riga na rantse ka sake ta Asad!" Ta k'arasa fad'a da k'arfi tana kallon sa.

Zubewa Rauda tayi a wajan tana kuka sosai hankalin Asad ya kuma tashi zuciyar sa na bugawa a guje kamar zata fito daga k'irjin sa ya kasa furta komai ji yake kamar shima ya zubar da hawaye sabida rad'ad'in da yake ji a zuciyar sa. "Kana yi min biyayya a ko wanne lokaci meyasa kake son b'ata min rai akan wannan mujiyar? Ka fifita ta a kaina kenan?." Da sauri ya girgiza kai yayi alamun a'a tace, "to sake ta."

Suhaima da take gefe tausayin d'anuwan ta ya kamata tace, "Mama dan Allah....." saurin dakatar da ita tayi tace, "ban saka ki a maganata ba." Ba shiri Suhaima tayi shiru Mama ta kalli Asad tace, "Zaka sake ta ko a'a?." Numfashi ya fesar ya had'd'iye yawu mai d'aci ya kalli Rauda da take zube tana kuka kanta na cikin cinyoyin ta ya sake sauke numfashi cikin tashin hankali da bugun zuciya.

? ? ? "Baza kayi ba kenan ko? To ka sani matuk'ar baka sake ta a yanzu ba bazan yafe maka ba Asad sannan kuma wallahi sai nayi maganin ta da ita da dangin ta gabad'aya." Da sauri ya kalli mahaifiyar tasa ta d'aga masa kai tace, "eh kaji ai me nace, in baka sake ta ba bazan yafe maka ba Asad." Lumshe ido yayi cikin zafin da yake ji jiki sa har idanun sa yana ji kamar ya zubar da hawaye amma babu dama.

Kai ya sunkuyar ya juya ya kalli Rauda da har lokacin kuka take ya sake kallon Mama da ta kafa masa ido ya cize bakin sa ya sake had'd'iye yawu bakin sa na rawa amma ya kasa furta ko wacce kalma. Dak'yar ya zame k'asa ya durk'usa yace, "Ni shugaba ne, Abba ya sanar dani komai Mama sakin aure hani ya kamata nayi dashi bana aikata shi ba. Dan girman Allah ina rok'on mahaifiyata da ta janye kalaman ta." Ganin yana b'ata mata lokaci ya saka taja tsaki tace, "Asad in bakayi abinda nace ba zaka had'u da b'acin raina wanda baka tab'a had'uwa dashi ba har abada. Ka sake ta ko na sallama mata kai har abada" ta fad'a a fusace domin ranta a b'ace a yake ganin yadda yake mata gaddama a gaban wata banza bare talaka yar talakawa.

Rauda ya kalla bashi da zab'i sai bin abinda mahaifiyar sa take so yace, "I'm sorry.....!" Mama ta fusata kamar zata dake shi tace, "au sai ka bata hak'uri? Kenan itace wacce ka fifita sama dani Asad? Ashe zaka iya nuna kafi son wata a kaina Asad?." Ya kalli Maman cikin girmamawa yace, "Ban kai wannan matsayin ba Mama, Allah ya wuci zuciyar ki zanyi abinda kike so" ya fad'a jiri yana d'aukar sa.
"To sake ta."

Ya kalli Rauda ya tuna ko cikakken mintina asihrin baiyi da d'aukar mata alqawari ba gashi tun ba'a Je ko ina ba ya karya bai cika mata shi ba daman yasan abinda take tsoro itama kenan gashi kuma ya faru, zai zama makaryaci a idanun ta maci amana mara cika al?awari yace, "Na sake ki saki d'aya!."

A tare zuciyar su ta buga Rauda taja numfashi ta d'ago fuskar ta tana murmushin k'arfin hali hawaye yan zuba amma bata iya cewa komai ba. Mama ta sauke numfashi tayi ajiyar zuciya mai tsaho har tana dafe tace, "Finally mun rabu da k'aya, sai ki fita ki koma gidan ku kije can ku cigaba da zama cikin talaucin da kuka saba zama. Ina miki warning akan y'ay'ana bama Asad kawai ba, kar na sake ganin ki a kusa da k'ofar gidan su ma balle na ki shigo gidan, in kuma ba haka ba zan d'auki mummunan mataki a kanki dake da dangin ki. In kunne yaji jiki ya tsira kin taimaki kanki da iyayen ki, in kuma kink'i ji kin cigaba da yi masa asiri wallahi!, wallahi!!, wallahi!!! Sai naga bayan ki keda iyalan gidan ku gabad'aya."

Rauda tana ji bata ce komai ba Mama ta kalle shi tace, "had'a kayan ka mu bar hotel din nan yanzu." Sai kuma ta kalli Rauda tace, "maza-maza tashi ki fita kije can ki karata ko yau a d'aura miki aure da wani dan nasan baki isa kiyi iddar d'ana ba." Rauda ta mik'e jiki a sanyaye dan hawayen ya tsaya cak Mama ta kalle shi tace, "Ina passport d'inta? Maza bata ta b'ace min da gani bana son ganin ta ko kad'an." Hankalin Asad yayi mugun tashi ya kalli Maman tasa yace, "bata san kowa a nan ba, bata an ko ina ba, ina zata je?."

"Ta tafi ko ina ma bai dame ni ba." Rauda jikin ta ya gama yin sanyi ta fara takawa k'afar ta ko takalmi babu zata gifta su Asad yayi sauri ya zube guiwar sa a k'asa yana kallon Mama ya rik'e hannunta kamar zaiyi kuka yace, "Dan Allah Mama ki barta ta zauna a nan nayi abinda kika ce na kuma barta tunda shine farin cikin ki na cika miki burin ki na rabu da ita, kiyi min wannan alfarmar yadda Allah ya taimake ki ki taimaki d'anki mai rauni ki amince ki barta ta zauna a nan in ta bar nan ina zata je?, babu wanda ta sani babu inda ta gani a k'asar nan. Ki barni na mayar da ita gida kamar yadda na d'auko ta cikin aminci dan Allah."

Mama kallon sa take da mamakin yadda yake magana kamar bashi ba kenan daman rashin maganar tasa iskanci ne yana sane tunda gashi indai akan lamarin tane yana magana yadda ya kamata hakan ya kuma fusata Mama tace, "Wallahi sai ta fita!." A daidai wannan lokacin Rauda ta fita daga falon ya saukar da kai kansa na mugun sarawa kamar zai fashe ya runtse idanun sa, zuciyar sa nayi masa ciwo tare da rad'ad'in da bai tab'a jin irin sa ba a rayuwar sa, ya d'ago kai yabi hanyar da ta fita da kallo ya sauke numfashi mai nauyin gaske..........


*Mama tayi mana yankan k'auna*=?"?
[17/12, 10:40 pm] Nafisat Alwasa: Arewabooks@nanahaleema11
*044.*

? ? ? ?? A fusace ta juya ta kalle shi ta kama hannun sa ya mik'e tsaye tana binsa da kallo tace, "ban tab'a ganin raunin ka akan komai ba sai akan wannan kucakar yarinyar a lokacin raunin ka ya fara fitowa kan fuskar ka, ban tab'a ganin gazawa k'arara a fuskar ka ba sai da yarinyar nan da ta asirce ka. Duk wani ko wata da zai kawo min tangard'a a cikin cikar burina bazan barshi, ba'a san shugaba da rauni ba dan haka ka k'arfafa zuciyar ka ka manta da ita ka d'auka baka tab'a sanin ta bama a duniya domin ka barta kenan har abada."

Kansa na k'asa bai ce komai ba harta gama bai ce komai ba sabida yadda yake jin zuciyar sa na tafasa bazai iya furta ko wacce kalma jikin sa kamar anyi masa allurai na sagar da gangar jiki bashi da kuzari ko kad'an kana kallon sa kasan yana cikin damuwa mara misaltuwa yana k'ok'arin kawarwa ne amma hakan yaci tura. Mama ta bar kusa dashi ta k'arasa d'akin farko ta tura k'ofar ganin nasa d'akin ne ta dawo da baya ta kalli Suhaima tace, "Zo ki tattara min kayan sa mu bar nan." Jikinta a sanyaye ta taka ta shiga d'akin sun d'an jima a ciki kafin su fito da jaka a hannun su hannu Mama da passport guda biyu ta kalle shi tace, "Wuce muje."

A hankali ta tako yazo kusa da ita ya kalli Suhaima suka had'a ido cikin tausayin Yayan nata ta kalli Mama tace, "Mama akwai wasu kayan sa drawer da ban d'auko ba naga kuma kamar documents ne masu mahimmaci." Mama tace, "jeki ki d'auko" ta fad'a tana bud'e k'ofar ta fita ya biyo bayan ta.

Da Suhaima ta fad'a d'akin da take tunanin na Rauda d'in ne ta had'a kayan da ta da ta gansu a wajan wanda zasu shiga wanda baza su shiga jakar ba ta barsu a wajan taga wayar ta a kan gado ta d'auko ta cusa magani a aljihun jakar ta jawo da sauri tana addu'ar Allah yasa Mama sun bar wajan. Tana fitowa babu Mama da Asad a wajan ta sauke numfashi ta hango Rauda a zaune a gefen wani d'aki ta had'a kai da guiwa sai passport d'in ta a kusa da ita ta k'arasa inda take tace, "Ga wayar ki ga kayan ki na bar wasu a ciki baza su shiga ba. Kiyi ha?uri da abinda Mama tayi miki na tabbata Yaya Asad yana sonki zai kuma dawo gare ki" abinda tace kenan ta ajjiye mata tabi bayan su da sauri ta shiga elevator ta sauka.

Da kallo ta bi bayan ta ta kuma fashewa da kuka mai tsuma zuciya ta kwanta a wajan ba tare da tasan abinda zatayi ba. K'arar bud'e elevator taji bata d'ago ba taji anzo kanta an tsaya idanun ta sunyi nauyi bazata iya kallon ko waye ba hakan ya saka bata motsa ba sai ajiyar zuciya da take yi.

Cikin harshen turanci taji ance, "Hotel d'in mu baya buk'atar zaman ki ki tashi ki fita ko mu kira miki y'an sanda su kama ki." Gabanta ya fad'i ta daure ta d'ago ta kalli wanda yake magana taga security ne ta tashi zaune ta dafe kanta da hannayen ta duka biyun zatayi magana akazo wajan bata iya kallon wanda yazo wajan ba taji ance, "A'a chocolatly lafiya kike a nan?" Dr Khalifa ya fad'a yana k'arasowa inda take kwance.

Kallon security d'in yayi cikin harshen larabci yake tambayar sa lafiya, security d'in yace, "an sanar damu babbar mai aikata laifi ce daga Nigeria,.ta fita daga hotel din nan ko mu kaita wajan y'an sanda bama som zaman ta a nan." Da mamaki Dr Khalifa ya kalle shi ya kalle ta yace, "Chocolaty me yake faruwa haka? Ina prince yake?." Ta kasa magana sai rawar jiki da jikin ta yake yi hakan ya saka shi tab'a wuyan ta yaji zafi rau yace, "Subahanallah" ya kalli security d'in yace, "waye ya baku wannan masaniyar? Ina wanda suke tare da ita yake?."

Security d'in yace, "bai dame mu ta tashi ko mu fitar da ita ta k'arfi." Dr Khalifa yace, "basai anje nan ba" ya kalli Rauda yace, "tashi mu tafi kafin su saka a kama ki kin san nan ba Nigeria bace tunda aka fad'a musu baza su amince dake ba." K'okarin tashi take yaga ta kasa ya kama hannun ta duka biyun ta tashi tayi baya zata fad'i tana dafe kanta yayi saurin rik'e ta yana fad'in, "Sannu." Jakarta yake jaya d'auki wayar ta da passport d'in ta suka shiga elevator suka sauka.

Suna barin wajan Asad ya dawo yaga bata wajan ya bud'e d'akin duk yasan bazai ganta ba ya duba ya sake kullewa yana kallon wajan yana tunanin ina taje zuciyar sa na bugawa sosai fiye da d'azu. Komawa k'asa yayi ya koma reception wajan ma'aikatan wajan da harshen larabci yace, "Ina son ganin camera na wajan k'ofar d'akin 012 special room." Dannawa wanda yayiwa maganar yayi nan take akazo inda security suka je kanta da inda Dr Khalifa yaje kusa da ita har yadda ya rik'e ta suka tashi suka shiga elevator.

Mummunan sarawa kansa yayi ganin yadda Khalifa ya rik'e k'ugun ta ga hannun sa a cikin nasa ya dafe zuciyar sa yana jan numfashi dak'yar yayi baya zai fad'i sukayi saurin tare shi ta baya suna jera masa sannu, zaunar dashi sukayi aka kawo mai ruwa mai sanyi amma bai iya sha ba abinda yake gani kawai a idanun sa shine yake sake tayar masa da hankali sai numfashi yake ja dak'yar kamar wanda zai bar jikin sa.

"Asad!." Mama ta fad'a daga bayan sa ganin an zagaye shi ta k'araso wajan tana kallon ma'aikatan wajan tace, "me kake jira ne basu key d'in kenan?." Kai ya dafe ya zaro key d'in motar hotel d'in da yake amfani da ita ya basu ya tashi tsaye dak'yar yana jin jiri na d'aukar sa ma'aikacin da yake kula da computer yace, "akwai ragowar kud'i da bai k'are ba na d'aki da kuma na motar." Da hannu Asad yayi musu alama ya wuce Mama tabi bayan sa zuciyar ta a cushe tunanin ta kawai kenan baiyi niyar dawowa ba yana nan yana kashewa y'ar talakawa kud'i.

? ? ?? Taxi suka shiga Asad tunda suka shiga motar baice komai ba titi yake kallo yana jan numfashi dak'yar amma kuma a idanun sa Khalifa yake gani rik'e da k'ugun Rauda sai yaji kamar an soka masa mashi a zuciyar sa, _ina zai kaita? A ina zai ajjiye ta? Me zai mata da ya suka bar hotel d'in tare? Meyasa ya rik'e ta?._ Babu wanda zai bashi amsa ya sake kallon titi zuciyar sa ta kuma cewa, _meyasa ta bari ya rik'e ta? Meyasa ta bishi bayan tasan bazai iya tafiya bai nema mana mafita ba?, yanzu ina zasu je? Gidan sa zai kaita?, to su zauna ita dashi kenan?._

Tunanin hakan ya saka shi dafe kai tare da furta, "Hasbunallah!." Mama ta kalle shi batayi magana ba suka tsaya a hotel d'in da sukayi booking suka fita bashi da zab'in da ya wuce ya fita shimq duk da jirin da yake ji suka shiga ciki. Upstairs hotel ne dole suka shiga elevator zuwa d'akin da suka kama suka shiga ciki.

Babban falo ne k'ofa biyu a cikin sa da alama shima dak'una biyu ne Mama ta bud'e d'aki na farko tace, "Shiga kayi sallah." Bai musa ba ya shiga ta kulle k'ofar ta kalli Suhaima da take kallon ta tace, "meye kike bina da kallo?."
Ta langwabar da kai tace, "Mama bashi da lafiya fa kamata yayi mu wuce asibiti ba nan ba, jiri yake yi fa kamar zai fad'i." Ta tab'e baki tace, "Asirin ne yake sakin sa sai a hankali."

D'aya d'akin Mama ta shiga zuciyar ta fesss tayi wanka ta da alwala ta canja kaya tayi sallah ta d'auki wayar ta tana neman number Mum amma bata same ta ba. Suhaima ma a d'akin ta shirya tayi sallah ta fita zuwa restaurant d'in hotel d'in ta debo musu abinci ta dawo d'akin ta kawowa Mama ta kalli abincin tace, "bara na duba sji" ta fad'a tana tashi ta nufi d'akin da Asad yake.

? ?? A zaune ta same shi da alama ko alwalar ma baiyi ba hannun sa a kansa yayi shiru ko motsin kirki bayayi, k'arasowa tayi kusa dashi zuciyarta na sake jin haushin Rauda da tsanar ta tace, "Taya bazan tsani yarinyar nan ba tayi maka abinda ko sallah ka kasa tashi kayi bayan ba haka kake ba?" ta fad'a tana isowa inda yake ya kalle ta da jajayen idanun sa kafin ya saukar da idanun sa k'asa.

"Daurewa zakayi ka tashi kayi wanka then kayi sallah sai kasha magani ko muje asibiti." Baya son mata musu ko kad'an hakan ya saka shi ya tashi ta rik'e shi tace, "Sannu Zaki, sai a hankali asirin zai bar jikin ka."

_Asiri_ ya maimaita a zuciyar sa cikin wani irin yanayi na tunani da mamakin kalmar ya shiga band'aki, fita tayi ta barshi. Lokacin da ya fito yaga jakar sa ta kaya ya ya bud'e ya saka doguwar riga kamar kullum ya tayar da sallah bayan ya idar ya zauna yayi shiru yana jin kewa a zuciyar sa kamar marayan da ya rasa iyayen sa a lokaci d'aya. Hawaye yaji suna taruwa a idanun sa zuciyar sa na bugawa sosai amma yak'i barin kukan ya sakko.

Kamar ya tuna wani abu sai ya d'auki waya da sauri da niyar kiran ta yaji Mama tace, "In ka sake ka neme inda take zaka had'u da fushina Asad, bana so ka sake waiwayar ta daga nan har a tashi duniya indai na kasance uwa a gare ka." Ajjiye wayar yayi a gefen jikin sa a sanyaye ba tare da yayi kiran ba ya daure zuciyar sa da ta karaya yana ji idanun sa na kawo ruwa kamar zaiyi hawaye amma ya mayar dasu ya hana faruwar hakan dan farin cikin Maman sa.

Abinci ta ajjiye tace, "d'auki kaci." Kai ya girgiza alamun bazai iya ba yana runtse idanun sa, waya ta d'auka yana dannawa kafin ta saka a kunne tace, "Suhaima kawo masa tea." Ba jimawa ta shigo dashi a kofi ta Mama ta karb'a ta bashi ya karb'a yasha kad'an ya ajjiye kofin Mama ta bashi maganin hannun ta tace, "sha zaka ji dad'in jikin ka." Ya karb'a yasha ta sake fita jim kad'an ta dawo ta bashi wani a kofi tace, "karb'i wannan ma."

Shima baice komai ba ya karb'a yasha ta kuma kallon sa tace, "ka kwanta ka huta yanzu anjima in ka tashi zaka ji dad'in jikin ka." Kai ya d'aga ya tashi tsaye kamar yadda tace ya zauna a gefen gadon tayi murmushi kana tace, "Allah yayi maka albarka Asad, Yadda kake son abinda nake so Allah ya baka abinda kake so kaima." Sai ya kalle ta sai kuma ya sunkuyar da kansa a zuciyar sa yace, _Abinda nake so kin raba ni dashi Mama._

"Suhaima kin kira Hydar d'in ya jikin mahaifin naku?" Ta fad'a tana niyar fita sai kuma ta dawo tace, "Nasan baka san bashi da lafiya ba ko?, suna Germany da Hydar jikin sa ya rikice lokaci d'aya." Idanu ya lumshe sai yanzu ya fahimci yadda akayi Mama ta sub'uto ta tawo Cairo ashe mahaifin nasa bashi da lafiya.

Bayan sun fita yaso ya kira Hydar amma bazai iya ba haka ya kwanta lamo yana jinyar zuciyar sa ya lumshe ido abubuwa da dama suna yi masa ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?yawo a ido ya bud'e yana jin sautin muryar ta a lokacin da take cewa yayi mata alqawari. Wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login